Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 44


Da sauri cikin wata kakkausar murya General Alpha ya ce “Ƙarya kake! Cikina ne a jikin Hawwa’u ba naka ba, Liar, maÆ™aryaci” Lokaci guda suka kalli direction d’in sashin da General É—in ke tsaye, domin babu wanda ya hankalta da zuwan nashi cikin parlourn. Ba wanda ya furta ko alifun balle ya ja doguwar maganar da zata É—auki hankalin jama’a, ko wanne a parlon wani razanannen tashin hankali ne ya mamaye masa zuciya, rashin madafa da sanin abin yi, akan aure biyun dake bisa mace É—aya! Mene GASKIYAR LAMARI? Wake da haÆ™ik’anin samuwar cikin na Majeederh? Wani abu ne mai kama da kunya a sa’ilin da akai yunÆ™urin binkan asalin uban, ALLAH YANA GANI, shi zai basu haske wajan fahimtar abinda ke cikin duhu.
“Ni ne wanda yake da nasaba da cikin Hawwa’u, saboda ita É—in mallakina ce She’s my wife, kenan babu doubting a É“ullowar ciki a jikinta? Tunda tana iya yiwuwa na kaÉ—aita da matata” Babu shakka,ko tsoro a fuskar General! Yanayin fuskar shi na tabbatar da asalin abinda ya bijiro daga Æ™asan zuciyar tasa ne, bisa rikiÉ—ewar Æ™aryar daya shirya zuwa sahihiyar gaskiya wacce ya yi mata rajista da kansa. Uncle Isma’il ya juya ya kalli Dr Khalil wanda yake danna wayarsa haÉ—aÉ—É—iyar iphone 15 promax wacce aka launcher ta, not too long ago. Idan kaga yadda Khalil ke acting da basarwa ba zaka ce shi ake Æ™aryatawa ba, ta hanya É—aya zaka san kalaman sun ratsa zuciyarsa yadda gargasar hannunsa ke mimmiÆ™e ita kaÉ—ai tana zubewa, Abbu bashi da hurumin magana domin batu ne akan Æ´arsa daya shafi É—an, É—an uwansa, ita kuma Majeederh ya shafi mijinta da kuma jininta, dole ya zuba Idanu yaga yadda al’amarin zai wakana, baya da magana tun fil azal dama.
“General zauna, maganarka ta sanya firgici ina son kar mu shiga hak’Æ™in Ubangiji, duk da cewa bamu da masaniyar Ibrahim yana raye, ALLAH YANA GANI”
General ya zauna yana jin wani ƙarfin quiwa da ganin alamun nasara, wacce da ita zaiyi amfani wajen kassara zuciyar ta uban girman kan nan da tsaurin idanu.
“Ya akai cikin ya zama naka? Shin bayan aurenku yaushe ka samu nutsuwar keÉ“ewa da Majeederh? Tunda kasan mun san cewa taÆ™i yarda tayi accepting naka matsayin mijinta ko? Ya akai hakan ta faru?” General ya yi shiru can zuciyarsa yana tunanin “What should I do?” Majeederh kuma mamaki da tu’ajjubin lafiyayyiyar Æ™aryar da General ya shimfiÉ—a take, wanda ya hanata magana sai kallon shi da take.
“Ina magana? Bamu da cikakken lokaci” General ya ce “Uncle binciken sirrin ma’aurata haramun ne fah, faÉ—in yadda akai daidai yake da furta kalaman batsa a gabanku” Uncle Isma’il ya rasa bakin magana, General ya girgiza kai cike da tausayawa ya ce “Ita ta sani, tasan ni ne uban” Sai a lokacin Khalil ya ce “Ƴar Shaye-shaye ce ita, irinka da zata sani?” Khalil ya ajiye waya ya Kalli General sosai da kyau ya ce “Yadda Ubangiji ya tsarkake ni daga shiga gonar matar wani, haka ya tsarkake matata wani ya shiga gonata” Khalil ya saka hannu ya hargitsa kansa, a hankali ya miÆ™e hannunsa a bayansa like yadda Mai martaba Ajlaal yakeyi, tafiya yake sai kuma ya juyo ya kalli General ya ce “Kasan ko gaskiya za ta yi ajalina sai na faÉ—a, ban taÉ“a furta Æ™arya ba da wasa ko akasin haka” Ya juya ya kalli Innati da Yaya Bilkisu ya ce “Ko sanda kuka É—auka ni fatalwa ne, tarayya na gama yi da matata ita kanta zatonta mafarki take but it was reality” Kunya ta kama Majeederh tana jin kamar ta nutse, ya akai Khalil har ya yi mata wayo haka? Ta kasa kallon kowa, a hankali Abbu ya miÆ™e tare da ficewa,Yaya Bilkisu tayi tsuru da Idanu Innati ta hangame baki tana jin zunzurutun rashin kunya irin ta surukinsu Dr Ibrahimul-khalil Abraham. Uncle Isma’il girgiza kai kawai yake yana jin da ana mutuwar gaske a dawo Khalil ba zai taÉ“a sauyawa ba, hali zanen dutse, cikar mutum suffar shi, gaskiyar ka nagartarka.

“MaÆ™aryaci, ka shirya zancenka ne, amma ciki nawa ne” Khalil daya fara birkicewa yana É—an nufo General shi kuma yana yin baya tare da riÆ™e kansa, ya ce “Haba? Ashe kai ne ka farke É—inkin haihuwar da akai mata?” General ya ce “Ohho dai ai ni ba É—an iska bane da zan dinga rashin kunya a gaban mutane, Majeederh is my wife dole mu kasance tare” Khalil ya fara tattare hannun riga idanunsa jajur ya ce “Ni Ibrahimul-khalil cikakken É—an iska ne akan matata, tunda gashi daga dawowata na bata wani cikin, ka tabbatar ni da kai akwai bambanci nayi abinda ka kasa a shekara biyu, Loser!” Kunya ta kama kowa na wajan, Innati ta share zufa ta ce “Balkisa É—akko mini ruwa mai É—an iskan sanyi suma nake ji”
“Innati lafiyarki lau ba wata suma, sha ruwa ki nutsu” Ta fashe da kuka ta ce “To tsakani da Allah a nemo abu a toshe min kunnuwana” Khalil ya fara hauka jikinsa yana jijjiga, Yaya Bilkisu ta miÆ™e ta nufi wajen Khalil tana zuwa ya saka hannu ya É—auketa cak! Ya nufi wani bedroom da ita ya kulle, ya dawo Gadan-gadan kan Alpha da sauri Majeederh ta shiga tsakiya yaÆ™i kallonta, domin Æ™wayar Idanunta sune weakness dinsa masu raunata masa zuciya, ta saka hannu a hankali ta juyo da fuskarta tare da sanya idanunta cikin nasa, ya É—an kwaÉ“e mata fuska ya kasa cewa komai,ta kama hannunsa ta É—ora a cikinta a hankali daidai shi ta ce “We’re one single family, no one can separate us ok? Ni da kai jini É—aya ne, ma’aurata ne, kai Mijin Malama ne, ni kuma Mrs Ibrahimul-khalil Ranka ya daÉ—e,mu É—in masoya ne KHALJEED” Wata É“oyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke yana damÆ™e hannunta cikin nasa, ya dinga kallonta shi kansa baya da zarafin faÉ—a mata yadda yake jinta a zuciyarsa.
“Hawwa’u!” General ya kira sunanta da Æ™arfi ya ce “Cin amana? Akan shi zaki mallaka masa jinina?” Khalil ya sake damÆ™e hannun Majeederh kamar zai raba gida biyu naman jikinsa duka rawa yake. Maman Alpha kasancewarta barrister ta gama fahimtar komai ta ce “Ok a zubar da cikin kawai” Ta faÉ—a tana kallon kowa tana son ganin reactions É—in su, a gigice Khalil ya kalleta idanunsa na shigewa ciki da Æ™arfi ya ce “Maaa, cikin nawa za a zubar? Kamar cikin shege?” A fili kuma General ya sauke numfashi ya ce “Better! A zubar kawai kowa ya huta zanfi jin daÉ—in hakan” Maman Alpha ta girgiza kai ta ce “You are ashamed, You are a liar” Uncle Bello ya ce “Ka bani kunya, ka bani mamaki, daman tabarmar kunya da hauka ake naÉ—eta, kaga duk duniya ba abinda zaka sake faÉ—a mini na yarda, Firstly ka ce Majeederh na sonka har muka É—aura aure, ashe Æ™arya ne, secondly ka ce Zuleehart ba matarka bace nan ma Æ™arya kake, thirdly, ka ce cikinka ne shi ma Æ™arya ne, When will you stop lying? when will you be an honest person? you are nothing but a liar”
Innati ta saki baki sosai sai kuma ta ce “Tirr! Amma ka ji jiki sosai soja Æ™arya zagin Allah ka bani kunya, ya akai kamar wannan yaron mijin Malama da yake tun farko Ahlul kitabb ya fika iya faÉ—in gaskiya?” Ta girgiza kai ta ce “ALLAH ya isa a gaskiya zaman jiran jin matsiyaciyar Æ™aryar da kake zabgawa, yanzu da za’a zungura tsinke a kunnena wuta za a tsokalo” Uncle Isma’il ya kalli Khalil da General a hankali ya ce “Ku zauna” Khalil ya nemi waje ya zauna, Jee ta miÆ™e ta bar wajan, Uncle Isma’il ya fara ta kan Khalil ya furta.
“Da yawan lokaci dole ne ka koyi tanÆ™wara zuciyarka Ibrahim, ba komai ne zaka ce zaka fara duka ko faÉ—a ba” Khalil bai kalli Uncle ba, yana tunani to shi me ya yi? Bayan bai damu da hayaniya ba yaushe ma yake duka? Uncle ya sassauta muryar shi ya ce “Lokacin da ba ku da ikon sarrafa tunaninku, tunaninku da motsin zuciyarku na iya yin ta’adi. Kuna iya samun kanku kuna yawan jita-jita akan abubuwa da yawa, kuna shakkar kanku akai-akai, ko kuma kuna fuskantar matsala game da motsin zuciyarku. Bai kamata ya kasance haka ba! Kuna iya sarrafa tunaninku kuma ku maye gurbin tunani mara kyau na rashin kulawa tare da tabbatacce, daidaitattu. Bayan lokaci, za ku fara jin daÉ—in farin ciki, Æ™arin daidaitawa, da kuma kula da yadda kuke ji da tunaninku, Khalil na san a haka Ubangiji ya halicceka sauya mutum É—abi’a ko wani hali nasa wanda ya ginu a kai abu ne mai matuÆ™ar wahala, amma ka dinga haÆ™uri Plx!” A hankali ya kwantar da murya kamar ba zai ce komai ba tsayin seconds kafin ya ce “Thank you!” Uncle Isma’il ya ce “Allah ya yi maka albarka” Ya É—an yi jim sai kuma ya ce “Zamu tafi Palace” Uncle Bello ya ce “Yaushe?” Khalil ya É—an shafa kansa domin sam ya gaji da magana wallahi “Gobe” Suka ce “Da wuri haka?Ina a nan za ku yi Ramadan gabaÉ—aya bai fi saura kwana uku ba a fara” Khalil bai ce komai ba, ya miÆ™e tsaye tare da ficewa daga parlourn.

Uncle Isma’il ya juya kan Alpha da yake durÆ™ushe zuciyarsa kamar zata fito haka yake ji, shi kaÉ—ai yasan wanne so ya kewa Majeederh ba kowa zai fahimci ko gane hakan ba, kalaman Zuleehart ne suka shiga yi masa amsa kuuwwa! A cikin kunnensa. Uncle ya ce “General kai da kanka baka ji nauyin Ibrahim ba? Ka dinga shirga Æ™arya bisa son ranka? Saboda cikar burinka, duk lalacewar mutum idan ya riÆ™e gaskiya da amana wallahi yafi haiba da kamala cikin mutane nagarta ta ban mamaki mene ribarka akan yin Æ™arya? Kasan hukuncin masu Æ™arya bisa son rai ba don kare kai ba? Ka ji tsoron Allah tun kafin lokacin ya Æ™ure maka kaje ka nemi matarka” General ya ce
“I am sorry Uncle, zan gyara yanzu a bani matata” A hargitse Uncle B ya ce “Kasan Allah idan baka daina kiran Majeederh matsayin matarka ba, hukuncin da zan É—auka akan ka mai tsauri ne” Yaya Bilkisu data fito ta ce “A’a yana da ikon faÉ—ar haka saboda an É—aura musu aure, bayani za ku yi masa yadda ya kamata” Ta zauna ta ce “General kasan ba a aure akan aure ko? An É—aura maka aure akan rashin sanin mijinta na raye, kuma Allah ne ya Æ™addara babu rabon wahala da samun zunubi shiyasa bai Æ™addara ka É—ora mata idda ba har kawo yanzu, kuma idan an samu matsalar aure a irin wannan maslahar ba wani babbar maudu’i za a ja ba, idan mace tana son mijinta na farko shikenan sai na biyun ya saketa ta komawa mijinta, ko ma bai saketa ba ya zama dole ta koma, idan tana son ko wanne sai a bata zaÉ“i na zama da wanda take so” Yaya Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya cike da tausayin General ta ce

“Kalaman Majeederh a kullum sun isa su sanya ka fahimci irin son da takewa mijinta, a tarihi na soyayya ban taÉ“a ganin kalan tasu ba, shi yasa nake musu uzuri da rashin kunyar su a wani sa’ilin, ka yi haÆ™uri ka amshi hakan matsayin Æ™addara, kana son Majeederh wannan ra’ayinka ne, Majeederh bata son ka Khalil take so wannan Æ™addarar ka ce, our destiny depends upon whether we live in harmony with God, following His moral teachings, baka da ikon sauya Æ™addararka, rashin samuwar Majeederh hakan na nufin Zuleehart ita tafi dacewa da rayuwarka ita ce alheri ga duniyarka”

Murya can Æ™asa yana kallon Yaya Bilkisu ya ce “How do i know my destiny?” Yaya Bilkisu ta taÉ“a kafaÉ—arsa cike da Æ™warewa irin tata ta tsohuwar Æ´ar boko ta ce “Destiny can never be figured out it can only be revealed by trusting and following what feels right, a Karan kanka za ka ji wannan abun kana son shi ne har zuciya, to wannan abun shi ne Æ™addararka, da yawanci abinda mukewa mugun so ko tsana shine yake kasancewa Æ™addararmu” Ta kama hannunsa domin haÆ™iÆ™a son wanda baya sonka jarabta ce, ko da iya haka nan Ubangiji na iya yi maka azaba da laifukan ka. Ta ce “Your destiny is determined by your decisions, abu ne mai sauÆ™i cire Majeederh daga ranka idan ka nutsu ka fahimci dalilin daya sanya kake jinta a ranka, wanda kake so shi ne wanda kake jin motsin shi a zuciyarka a kullum, wanda kake so shi ne wanda ko sunan shi aka kira sai zuciyarka ta girgiza, wanda kake so a kullum shi ne zaka ji ko yana nesa dakai kake jin shi kusa da zuciyarka, wanda kake so da gaskiya shi ne wanda zaka sadaukar da komai saboda da shi, yana da kyau ka sadaukar da soyayyarka ka Khaljeed sau É—aya kawai su samu nutsuwa da farin ciki”
Hawaye na zuba a idanunsa yana kallon Yaya Bilkisu muryarsa na rawa ya san ba zasu gane su fahimta ba a hankali ya ce “Can i change my destiny? Ta dafa shoulder É—insa ta ce ”
“Why not? Wata Æ™addarar daman mu ke É—orawa kanmu, wata kuma jarabawa ce daga Ubangiji,In simple terms, your destiny is decided by your karma. Every human has the power to change his destiny by changing his karma, karma means “Action” Ya yi shiru a hankali kuma ya tashi yabar parlon yana zuwa daidai Æ™ofa ya yanke jiki ya faÉ—i a sume. A gigice sukayi kansa ganin jini na fita ta hancinsa da baki, haÆ™uri da juriyar da Maman Alpha keyi ta Æ™are ta fashe da wani irin kuka na tausayin É—an nata, tasan Soyayya jarabta ce kuma addu’ar Zuleehart dole ta bisa saboda ya cutar da ita bisa yardar da tayi masa, a mota aka saka shi zuwa hospital.
Innati ta sake kallon Yaya Bilkisu ta ce “Balkisa sake miÆ™o mini ruwa don Allah don Annabi, wanda yafi na É—azu É—an iskan san yi” Har dare suna hospital Majeederh na son cewa Khalil zataje amma tana tsoro tana lura da yanayinsa a sama yake, kuma yanzu jinin sarautar ke aiki a jikinsa, yana zaune hakimce a tsakiyar gadonta daga shi sai red É—in gajeren wando, cinyoyinsa masu É—auke da kyawawan gargasa a bayyane a tanÆ™washe su jikinsa babu riga gefen cinyarsa Alhassan ne ke kwance yana bacci bayan ya gama fashe mata plate da sauyawa É—aki kama, Khalil na kallon faÉ—an da takewa Alhassan hadda tsawa shi dai bai kulata ba, saboda bai san yadda ta kula dasu ba tsayin shekaru biyu, ga kuma ciki daya Æ™ara mata masifa. Hannunta riÆ™e da Æ™aramin cup mai É—auke da black tea da Honey ta zauna gefen gadon tana ajiye cup É—in akan table ta kalle shi taga hankalinsa yana kan system sai ba tayi magana ba, ganin kallon ya yi yawa ba tare daya kalleta ba ya ce “Uhm” Can ya kalleta suka haÉ—a ido sai kuma ya kalli system clamly ta ji ya ce “Meye MATA A YAU?” Jee ta juya idanunta ta ce “A ina kuma?” Ya juya mata system É—in yana matsawa kusa da ita ya É—ora kansa a cinyarta kamar mai jin bacci Alhassan ya dawo dashi Æ™irjinsa Jee ta ce “Oh wani program ne a Arewa24, naga sunyi inviting nawa tun last week” Ya yi shiru Ta shafa kansa a nutse ta ce “Ban zuwa ai” idanunsa rufe ya ce “Uhm, kuma na yi Accepting request gobe” Tai jim domin bata É—auka zai amince ba, ta ci gaba da juya yatsun hannunta a cikin sumar kansa ya yi saurin riÆ™e hannunta ya ce “Kina son taÉ“a ni? Zaki jama kanki? Mun samu yaro mai wayo fa” Jee tayi dariya cike da kwanciyar hankali ta ce “Photocopy É—inka ne, harsu haura katanga da fashe cups da yake da su plate da É—an banzan ci” Ya mirgina gabaÉ—aya ya kalleta yana kwaÉ“e mata fuska kamar zaiyi kuka ya ce “Kuma ni ne É—an banza? Ba na daina ci ba?” Ta shafa fuskarsa zuwa kwantaccen sumar Æ™irjinsa ta ce “Hucewa salamun Ranka ya daÉ—e” Ta faÉ—i hakan tana kifa fuskarta a tashi tana Æ™oÆ™arin kissing É—insa suka ji an banko Æ™ofa a gigice an shigo Maman Alpha na kuka sosai wanda ya sanya Majeederh miÆ™ewa shi kansa Khalil zuciyarsa ta girgiza ta zube a gabansu da Æ™arfi ta ce “Alpha is dead”

Allah ya a nuna mana Monday Lafiya, labari yana ta jana bana son skipping shi ya sa yanzu nake tunanin sai shekara zuwa shekara zanna new book, gashi dai a 2023 shi ne kawai Novel É—in da nayi, kuma an hanani na Æ™ara samun costumers sai fitar mini da littafi ake kamar bani da gatabana son fiye surutu wlh tallahi Æ™imata ta zube amma dai ba komai….. 08119237616

No comments