Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 46


Ta bisa da Idanu kamar yadda yake kallonta gudun kada ya zaro mata wani zancan ta yi shiru, Khalil bai fasa kallon duk inda idanunsa yake son gane masa ba clamly yana Æ™asa da murya ya ce “Yanzu Æ´an uku zaki haifa ko?” Ta kalle shi ya É—aga mata gira ta ce “Kawo kunnenka na faÉ—a maka” Ya matsa yana riÆ™ota dragging her more closer to himself ya É—ora kunnensa a bakinta ta É—an yi baya tare da saka hannu ta murÉ—e kunnen ya ce “Auchhhii” ya É—an yi wani erotic and emotional sounds yana rufe ido a hankali ya ce “FaÉ—a mini” Ta ce “Eh, da Bad boy, Abraham, the one whose Love always tortures my heart..” Wanda kullum soyayyarsa ke azabtar da zuciyata. Idanunsa lumshe ya ce “Who? Waye?” Ta saka hannu ta shafa fuskarsa tana jan gemunsa muryarta na fita a hankali ta ce “My love, Ibrahimul-khalil” Ya buÉ—e ido ya kalleta sai bai ce komai, ba wanda ya Æ™ara magana har suka isa gidansu na lafiya Round wanda tuni Khalil ya bada umarnin a gyara, driver ya yi parking a parking lot na harabar ajjiye motoci na gidan, Khalil ya wani soja ya buÉ—ewa Æ™ofa, ya fito a hankali É—aya vangaren ya nufa bayan ya tabbatar Majeederh ta gama gyara liÆ™ab É—inta ya buÉ—e mata Æ™ofa ta fito a nutse, ta É—an tsaya tana kallonsa ya ware mata manyan idanunsa alamar ya akai? Sai kuma ta É—auke kai ta nufi entrance na gidan ya bi bayanta, tana isa cikin main parlour ta cire liÆ™ab É—in da duguwar rigar daga ita sai Æ™ananun kaya ta ce “Man me za a dafa maka?” Bai kalleta ba, domin yasan abinda kallon zai haifar yana haurawa upstairs da sauri da sauri ya ce “No, thank you” Ta bisa da ido sai ta maida kanta wajan fridge tana tunanin ko akwai drinks a ciki, miÆ™ewa tayi saman kujerar ta kwanta tana jin wani irin nutsuwa na saukar mata gata ta dawo gidan mijinta hakan na nufin babu wata damuwa data rage mata, harta fara bacci ta ji Æ™arar shigowar saÆ™o ta É—auki wayar saÆ™on ta gani daga kalli magana ce bata huce biyu zuwa uku ba, kamar haka;
“Wifey i want to see u in a special and sexy dress” Majeederh ta saki wani lallausan murmushi tana jin a ranta yau akwai rigima kenan ta dinga karanta text É—in nasa sai kuma ta ajjiye wayar tana tunani me yake shiryawa? Ta miÆ™e cike da nutsuwa ta nufi part É—inta, komai yana nan killace ita dai bata san wanda ke gyarawa ba, amma ta tabbatar ba haka aka bar gidan ba, wanka tayi da ruwan zafi ta Æ™asa jikinta sosai, kafin ta shafa lotion ta fara É—aukan turaren sandal ta kunna ta É—ora kayanta akai yaÆ™in ya fara ratsasu, ta É—auki sauran turaren na icce ta turara jikinta sosai, ganin location zai É“ata mata lokaci ta É—akko haÉ—aÉ—É—iyar kwalacca É—inta mai azabar Æ™amshi wacce ta gigita bedroom É—in lokaci É—aya, fara ce tas kwalacca É—in kana shafawa fatar wajan na glowing tana sheÆ™i ta mulke ko’ina na jikinta duk wani sashi na musamman sai data goga a wajan, fatarta tayi shinning luwai-luwai so masha Allah.
Body spray ta É—auka tabi dukkan gabÉ“anta da shi zuwa bayan kunnenta da wuyanta, wajan wardrobe ta nufa kamar zata É—auki inner wears ta saka sai kuma ta mayar ta rufe white É—in duguwar rigar cotton ce mai wuyan net ta saka da Æ™aramin hannu, rigar tabi jikinta ta kwanta shap É—inta na asali ya bayyana, ta kama sumar kanta ta tufke da ribbon jelar ta dawo da ita gefen wuyanta na dama, wata siririyar necklace ta saka sai É—an kunne ta É—auki flat shoe ta saka da sarÆ™ar Æ™afa, kana ta fesa MONIQUE Midnight ta zauna gefen gado hannunta riÆ™e da waya a karo na farko bisa dalilin nutsuwar zuciya data samu ta kunna network ta shiga facebook domin tafi duba muhimman abubuwa a can É—in, kai tsaye offline É—inta ta shiga ta duba a nan take ganin yadda followers É—inta suka Æ™aro da yadda aka dinga tagged da mentioned, shiga tayi wajan “What is on your mind?” tayi posting na magana guda uku mai muhimmanci ta ce
“Halitta mara adalci wa gangar jiki, tsarkakkiyar ga mai Æ™yakÆ™yawan nufi,ka wanke mana tamu ta tsarkakken nufinmu” tana yin posting kiran Khalil na shigowa tana ganin kiran taÆ™i É—auka a kira na biyu ta É—auka bayan ta gama saita muryarta cikin yauÆ™i ta ce “Naga…,”
Ya katse ta a taÆ™aice wajan furta “Ki zaman yanzu” Ta ce “A ina?” Bai bata amsa ba ta kashe kiran yana tura mata direction na inda yake a gidan, ta miÆ™e tana tafiya harta shige garden daga can ta hango wani part shi ba hall ba shi ba club ba, kamar special waje ne a gidan na Dr Ibrahimul-khalil, ta nufi shiga wani irin sanyi ne ya ratsa saman fatarta zuwa ilahirin gangar jikinta, yana mamaye dukkan wani tsatso na naman zuciyarta ta tsaya cak tana bin haÉ—aÉ—É—an wajan da kallo dake bata hasken blue da green da red, ta É—aga idanunta zuwa sama inda aka rubuta “Happy Anniversary Mr and Mr Dr Ibrahimul-khalil” ta furta a fili a hankali taji an tsaya a bayanta kafin ta juya taga waye zuciyarta ta sanar mata da cewa gwarzon mijinta ne Khalil ya saka hannu zuwa Æ™ugunta ya saÆ™o tare da mannewa da nashi ta baya ya fita tsayi tuni ya zartata, ya rungumeta tsam yana É—ora kansa a kafaÉ—arta ya kalli inda take kallo É—in, kafin a hankali ya ce “Amincin Allah ya tabbata ga ruhin Dr Ibrahimul-khalil”.
Majeederh ta kasa cewa komai lokacin da idanunta ya sauka akan makeken photonsu, ita, Khalil, twins da Baby Khalil a rubuta One single family sai wani kuma ita dana Khalil, sai nata da tayi masifar kyau an rubuta.

“I don’t know what I have done to deserve such an amazing wife like you, but I do know that I love you more than anything. I appreciate everything that you do for our family, honey, I love you wife i love you i love you” Ta juya da sauri ta kalle shi ya É—aga mata gira yana kashe mata Idanu É—aya, a hankali in a romantic style ya sake manne mararsu waje guda hannayensa zube a faffaÉ—an Æ™ugunta, Majeederh ta kasa furta komai sbd bakinta ya yi kaÉ—an wajan furta abinda zuciyarta ke ji game da mijin nata Khalil, wani irin rauni, rauni na mace zuwa ga mijinta ya mamaye zuciyarta ya yiwa gangar jikinta inuwa, yana fuskarta murfi, a hankali ta sake juyawa ta kalli haÉ—aÉ—É—an cake É—in dake ajjiye saman wani farin Glass an wadata shi da kayan kyalkyalin, pictures É—insu ne manne a jiki. A sanyaye ta saka hannunta ta zare hannunsa daga jikinta ta taka a hankali zuwa anniversary Inbox gift É—in take tana zuwa tsakiyar wajan ta ji an saki red É—in flowers ta tsaya idanunta rufe tana shaÆ™ar Æ™amshin furanni, cikin yanayi na É—aukan hankalin mutum ta shiga sauya taku tama mance Little ne a gabanta, Little É—in da aka ce ba za a taÉ“a so ba, balle mafarkin aura, É—an yaron nan, wannan gwaninin. Abubuwan data gani suka girmi zaton da zuciyarta take ta juya da sauri ta kalli Khalil yana tsaye harÉ—e da hannayensa, sai a lokacin ta kalli shigar jikinsa wata farar Floral jacquard one button suit ce a jikinsa white colour, kansa ya sha saloon an tufke shi a tsakiya shanyayyun idanunsa sun yi wani haske tas sai laÉ“É“ansa da suke jajur, Æ™afarsa cikin Leather shoe black colour, hannunsa maÆ™ale da Rolex mai kyau da tsada sai Æ™amshin perfume É—in Boadicea The Victorious daya hargitsa wajan, kyan kayan ya fallasa tsadar su a fili.
Jee ta durƙoshe a wajan sbd nauyin da zuciyarta ke mata, tayi expecting gani wani abu daban, tasha gani,ta kuma san yadda mijinta Khalil ke sonta, sai dai, bata taɓa sanin girman son da yake mata mizaninsa ya kai har haka ba, bata ɗauka ta shiga jerin irin matan nan masu sa a, a rayuwa har haka ba. Ashe haka zuciyar Khalil take? Ashe zai iya komai sbd ita ɗin kamar yadda idanunsa suka sha faɗa mata? Jikinta na wani irin rawa ta ƙarasa kaiwa ƙarshen saman qiwwoyinta, tana jin wani abu mai kama da zazzaɓi na kamata, zazzaɓin daba na komai bane sai na soyayyar mijinta Khalil. Kunya na hanata yiwa Khalil abubuwa da yawa, amma a yanzu ta fahimta ta kuma gane babu wata kunya tsakani zaman auratayya na tubalin kasancewarku miji da mata. Idan ta ce kuka za ta yi; wanne kala zatai?
Khalil dake tsaye yana kallonta, cike da nutsuwar dake alamtawa cewa jinin ke gudana a jikin nasa, duba da wanzuwar kamala da tarin haibar fuskarsa wacce ke sauka zuwa jikinta tana zame masa wani abu mai kama da (A man’s personality, his appearance).
Zubin halittar Khalil da kamalar shi ba zaka É—auka na Æ´an 22yrs bane, yana zuwa ya saka hannu ya miÆ™ar da ita tsaye yana zuba Æ™wayar idanunsa cikin maiÆ™atattun idanunta ya buÉ—e nasa rikitattun idanun a fili cike da kasala ya ce “Wonder Woman” Ta yi Æ™asa da kanta sbd kunyarsa daya mamaye mata zuciya ya daki kafaÉ—arta ya ce “C’mn ke Matana ce, abokiyana, my supporter and adviser” Ta kalle shi zuciyarta na kasa riÆ™e dauriyar rungumarsa da take azalzalar ta da tayi, a hankali ta shige jikinsa tana É—ora kanta a Æ™irjinta wani irin kuka ya Æ™wace mata, kuka na zallar farin ciki da samun abinda zuciyarta ke so da muradi na har abada.

Khalil ya matseta a Æ™irjinta gudun zuciyarsa na Æ™ara yawa da Æ™arfi yana Æ™oÆ™arin kasa riÆ™e kansa, shi kansa da zai iya kukan zai, sai dai jarumtar shi da Æ™arfin zuciyarsa bana kuka bane a gaban matarsa, kukansa zai iya kassara gabÉ“anta, ya raunata zuciyarta, ya makarantar da ita bayan kasancewarta mai Idanu, ya doÉ—e jinta, ya zautar da Æ™waÆ™walwarta, a hankali yake É—an bubbuga bayanta can Æ™asa yek furta “shiiiyy, shiiiittt” ita kanta ba ji take ba, ya tallafo fuskarta da hannayensa yana kifa tasa fuskar saman tata ya murza hancinsa akan nata a hankali ya fara sauke numfashi yana Æ™arewa lip’s É—inta kallo wanda suka jiÆ™e ga lamp lipstick a bakinta, jikin kukan yaÆ™i tsayawa gashi bashi da wani option na rarrashi wanda ya a shige “Kiss” a nutse yana sake rungumeta numfashinsu na sauka zuciyarsu na bugawa a daÆ™iÆ™a guda ya shiga sauke mata wasu special kisses asalin sumbata kukan ya tsaya ta kalle shi kamar yadda shima ke kallonta a hankali ta rufe Idanunta zuciyarta na buÉ—ewa, gangar jikinta na janta akan linzamin zuciyarta da wani irin firgitaccen sihirtaccen yanayi suka shiga kissing juna da sukkan su da Æ™auna mara algus irin son da akewa laÆ™abi da (eternal true love, pure purity built for God).
Khalil ya yi mata murmushi still yana riÆ™e da fuskata ya ce “Not every husband is lucky enough to have a wife like you. My whole life I have dreamed of getting a woman like you, The woman who is a perfect homemaker, lovely mother, a successful manager, and the best wife is not a myth; it’s YOU. Thanks for everything, INA SON KI”
Jee ta girgiza kai ta ce “Na fi kowa dace da sa a Khalil, i love you more than anything, Ubangiji ya wadata lemanka ya sanya alheri a ciki, ya rabaka da haramun ya sadaka da halak ya tsarkake zuciyarka a kullum ya baka ikon kula damu, I love you so much &most MAN”
“MAN?” Khalil ya furta yana ware idanu irin sunan bai kwanta masa ba ya jata zuwa wajan cake É—in tana dariya ta ce “Yes, my stubborn husband mai karya jama’a for know reason” Ya ware Idanu ya ce “No reason? A taÉ“a ruhin babban likitan kice no reason” Ya miÆ™a hannu zai damÆ™ota tayi baya ya ce “Funny woman” Ta rungume shi ta baya tana É“alle maÉ“allar rigarsa hannunta a kwance a Æ™irjinsa ya lumshe gajiyayyun idanunsa ya ce “Sexy mama”
A ranar Majeederh taga hauka wajan Khalil hauka na soyayya idan ta ce cikinta zai iya zubewa babu mamaki, domin wani irin ciwo mararta keyi na azaba da sun haÉ—a ido da Khalil yake kashe mata idanu a lokacin ya faÉ—a mata dukkan wasu plans É—insa na cikin watan Ramadan da yadda zai yi handling ayyukan shi ta sake bashi shawara wacce ya ji daÉ—inta sosai ya sake rungumeta yana faÉ—in “Thanks Malumana”
12:00 aka buga bindiga daga gidan sarki wacce ake shaidawa al’ummar musulmi ganin jaririn watan Ramadana, zuÆ™ata su kwanta da niyar É—aukan azumi, tun a lokacin daga Khalil ya yi zukuÉ—i ya zama abin tausayi ta san kuma abinda yake tunani a ransa ta dinga masa dariya bai kulata ba can ya mirgina cinyarta ya ce “Kwana nawa ne ma?” Ta ce “Wata guda ne cif mijin Malama zai azumi” bai kulata ba ta ce “Dame za ka yi shur?” Sbd ya huce haushin da take bashi ya ce “Towon shinkafa miyar kuka a saka man shanu, sai farfesun kai da Æ™afa” Ta shafa kansa ta ce “Done” tasan ba zai taÉ“a cin wannan da daddare ba. Tana fita ya gyara kwanciya bacci ya É—auke shi na gajiya, ya jima bai yi bacci mai daÉ—in wannan ba, yana ji tana tashinsa amma ko Idanunsa ya kasa buÉ—ewa Majeederh ta zuba masa idanu ta jima da sanin nauyin baccinsa a hankali ta saka hannu ta jawo tafin Æ™afarsa jin ana jan shi ya buÉ—e ido ba can ba ya ce “What?” Ta ce “Shur” Ya girgiza kai ta ce “pls dear ka samu ladan shur É—in” Ya miÆ™e gabaÉ—aya ya nufi bathroom ya sakarwa kansa ruwa ya fito da towel ya kalleta can ya ce “To time É—in da a shiga?” Ta girgiza kai sai kawai ya damÆ™ota yana kashe switch É—in bedroom É—in. Washegari miliyoyin musulmai dake duniya banda wasu sassan garuruwa suka tashi da azumin watan Ramadan a bakinsu, gari ya sauya yana yi na ibada ya bayyana, tun safe Khalil ya fita sbd zakkar da za a fitar da maganar kayan sallar Orphans É—insa da abinda za ayi musu ya kashe kuÉ—i miliyoyin da bai san kan su. 11:00 ya dawo ya É—auki Majeederh zuwa Arewa24 akan program É—in Mata a yau da aka gayyaceta.
Kowa na azumi gaban iyayensa, wasu gidan mazajan su ita kuma Æ™addararta azuminta na farko a gidan yari, bayan fitowarsu kowa da uniform na jikinsa an raba musu aiki, wani gandiro ba ne yazo yana tambayar “Latifa Omar?”
A hankali ta ce “gani nan” ya ce “Kina da vistor” tayi shiru sai kuma tabi bayansa, tsaye ta samu Barrister Aliyu Sufyan Alhassan cikin wani tattausan voyel ya Æ™ara yi mata kyau fiye da ko yaushe Gandirobar ya ce “5 minutes sir” Aliyu ya ce “Thank you” magana sukai da Latifa a nan yake shaida mata an É—auke ta daga gidan prison É—in san zuwa Ikot Ekpene Prison dake Akwa ibom, Latifa Omar ta dinga kuka kamar ranta zai fita daga nan kuma mota aka zuba su ita da wasu akai gaba da su. Lokacin da suka isa gidan yarin tana shiga was the first data tara gani shi ne Mr President..
[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *MIJIN MALAMA*
BOOK2

No comments