Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 47


“Ina son shi tun ban san yana duniya ne ko ya mutu ba? Ina son shi tun baya cikin rigar musulunci, ina son shi tun kafin na san cewa jininmu É—aya, ina son shi…” Ta kasa Æ™arasawa saboda wani irin abu daya caki zuciyarta, can Æ™asan zuciyar tana jin kamar bata kyauta mata yadda ta buÉ—e sirrin da babu wanda ya san da shi ba, daga ita sai zuciyarta wacce kuma ita ce ma’adanar ajiye wani ingantaccen sirrin hijabin rayuwarta bakiÉ—aya.
Wata kunya ta ji ta lulluÉ“e ta, tare dayi mata hijabi wa gangar jikinta, tana jin inama wajen da take zaune ya tsage ta shige ciki? Amma ina! Duk yadda ta kai da yiwa bakinta linzami a yanzu bata da Æ™arfin qiwar ci-gaba da riÆ™e hakan, raunatacciyar zuciyarta ta kasa riÆ™e kanta da cigaba da iya ajiye sirrin da yafi Æ™arfin ta, an jima ana ruwa Æ™asa na shanyewa, kamar yadda ta jima tana ajiye surruka da yawa, amma duk yadda takai da riÆ™e zurfin cikinta a yanzu bata da kuzari balle ta hub’É“asa riÆ™e hakan.
“I love my husband Khalil! Irin son da ba zan iya furtawa ko gamsar da wanda yake tsagina, ji, ko saurarena ba, zuciyar dake son shi da gaskiya ita kaÉ—ai tasan how much i love him” Ta goge idanunta tana riÆ™e yanayin da take ji da dukkan kuzarinta da ajin da take da shi, cikin nuna jarumta ta ce “Ina raye, ina numfashi kamar kowa, ina gani,ina ji, amma gani nake tamkar matacciyya ce ni a rami, haske nake ciki amma duhun zuciyata nuna mini yake kamar dare biyu ake!. Ban san cewa akwai wani abu da ake halitta a jikin rayayye ba, sai da na fahimci bayanni akwai halitta a jikina ZUCIYA, Na rasa sukuni na rasa meke mini daÉ—i a duniyata, zurfin cikin da nake da shi ya sanya ba kowa ya fahimta ba, gabaÉ—aya zaton jama’a JINKIRIN AUREN dana samu shi ne raunin dake raunata jaririyar zuciyata; zato ne kawai kuma mara inganci, tsammanin so da Æ™aunar Abraham ita ke damuna, na ji kunya i have been ashamed, idan na tuna É—an dana raina shi zuciyata ke so! So É—in ma na aure” Ta kasa Æ™arasa maganar saboda nauyin da kalaman sukaiwa halattaccen harshenta sai ta yi shiru kawai tana rufe ido.
“ÆŠan uwana General Alpha Bello khan! Shi ne mutum na farko daya fara so na a duniya, ni kuma Dr Ibrahimul-khalil Abraham shi ne first love É—ina daga nan duniya har lahira, an ce so makaho ne (Love is blind) amma bana gani saboda a kullum da Idanun zuciyata nake son shi, yaushe na fara jin haka mene dalilin har yanzu bani da cikakkiyar amsa ni da kai na, tunani fal ya yiwa Æ™waÆ™walwata murfi, tun a baya na furta Æ™addarori ne suke zagaye dani, É“oyayyun mane mana da rashin sanin wanda zai zama mijin malama ya sanya na rasa madafa, sai dai komai na da farko yana da Æ™arshe, kamar yadda tayi silar rusa farin cikina haka tayi silar haÉ—ani da abokin rayuwa,iya hakan kaÉ—ai zai iya sawa na yafe mata zunubanta idan ina da tabbacin tuban da zata yi” Khalil na tsaye kamar an dasa shi, kalaman Majeederh sun É—aure masa jijiyoyin jikinsa, suna neman kassara masa zuciya, ya rasa kuma a wanne bigire ko tubalin zai ajiye wannan zancen nata mai shirin tarwatsa masa zuciya? A hankali ya sake duban lokacin yaga yaci ace suna airport yanzu gashi already John ya shige da su Alhassan, jin Æ™afafuwansa na neman kasa É—aukan gangar jikinsa ya sanya ya jingina da bangon wajen yana mai zuba mata narkakkun idanunsa masu cike da wasu kalar zantuka wanda baki ba zai iya furtawa ba, sai dai gangar jiki tayi aikinta wajen nuna zahirin abinda zuciya ke ciki.
Mutumin É—azu ya sake kallon Majeederh cikin yanayi na damuwa a hankali ya ce “Na yi sake, É—an zaki ya girma why? Me ya sa kayi mini shigar sauri haka Khalil? Kasan yadda nake son matarka kuwa? Me ya sa tawa Æ™addarar da zuciyar ta rasa wacce zata so ko Æ™auna sai MATAR AURE? Matar Auren ma da nasan Khalil ba zai taÉ“a sacrifice a kanta ba?” Ya riÆ™e kansa da hannu bibbiyu saboda juya masa da yakeyi a zaune yake ji yake kamar zai kifa saboda masifaffan tashin hankalin da yake ciki, zufa ta shiga yanko masa a fili ya sake furta “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Ubangiji idan Majeederh alheri ce ka gaggauta kashe aurenta da mijinta na aureta, i don’t care da shekarunta, Ya Allah; soyayya da matar aure? Matar Dr Ibrahimul-khalil Abraham? Anya alÆ™iyamarsa bata kusa tsayawa ba?” Duk ya firgice ya fita hayyacinsa he looks so old amma ba mai lura da hakan saboda wani irin arziÆ™i da kwarjini, ya zaro hanky ya dinga share zufar dake tsastsafowa daga goshinsa tana sauka a fuskar shi. Jajere ta kalli Majeederh ta ce
“Mun sha ganin mutane ko nace mata da dama, wanda suke ganin kuskure ne ko rashin dacewar ko zubar da aji ne ka auri wanda ka girma, musamman irin tazarar girman naku ke da Dr Ibrahimul-khalil Abraham, ke ya kika ji kuma ya kika É—auki abun? Ya surutun jama’a ya yi tasiri a zuciyarki?” Majeederh ta yi murmushi cikin tattausan harshe da kalami mai daÉ—i ta ce “Tunani akan cewa zaka burge mutane, wannan abu ne da ba zai taÉ“a yiyuwa ba, ko da ace rayuwarka zaka bada a kan su; ko da ace gaskiyarka zata fasa Æ™irjinka ta fito,sam sam ba zasu yabeka ba, yafi maka ka saurari zuciyarka a kullum, mutanen da suke kewaye da kai sune suke sare maka quiwa a yayin da kaso aikata wani abu,sai kayi nasara a rayuwa sannan kowa ke son Æ™ulla alaÆ™a da kai, babu haramci akan auren wanda ka girma idan zai girmama ra’ayinka, ku girmama na juna, yana da wadata, da zuciyar nema, yana da kyakkyawar mu’amala abinda ake buÆ™ata kawai nagarta da cancanta, idan gaskiya zaka faÉ—a, duk gaskiyarka ba zaka kai Sayyiduna Abubakar ba, duk Æ™aryarka ba zaka kai Musailabatul kazzabu ba, munafurci sai Abdullahi É—an Ubayyu É—an salo, Æ™arfi sai adawa girman jiki sai samudawa, muni sai Julaibibi, matar da akafi so a duniya ba kamar Nana A’isha matar Annabi Muhammad S.A.W, Æ´ar da akafi so a duniya babu kamar Nana FaÉ—imatu, Mulki sai Annabi Sulaimanu, kuÉ—i sai Æ™aruna, talauci sai Mus’ab ibn Umairu shi ne wanda ya mutu likkafani bai ishe shi ba, idan taurin kai mutum yake ji da shi akwai su Ƙuddaru, duk iskancin da mutum zaiyi a duniya ba zai kai Hamana ba, a fito na fito da Allah sai shaiÉ—an, shi daman ba mutumci ne da shi ba, ya ce tunda aka fifita shi akan É—an adam tabbas sai ya halakar da rabin su, Ubangiji kasa mu dace muyi kyakkyawar Æ™arshe” GabaÉ—aya suka amsa da amin. Kowa jikinsa ya yi sanyi Khalil dai wani irin nutsuwa yake ji idan ya kalli Majeederh kuma ya tuna matarsa ce sai yaga bashi da wani sauran buri a duniya. Ta gyara zama a hankali ta ce “To kuma duka wannan sai mutum ya tsaya girman kai don wanda zaka aura ko yake sonka yana Æ™asa da shekarunka? Idan zanen Æ™addararku iri É—aya ne fa? Idan iya rubutu ne ba kamar Annabi Isa, abi Annabi sau da Æ™afa sai su Sayyiduna Abubakar SaddiÆ™u, a bada rayuwa saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama sai Umar Farouk, a yin kyauta sai Sayyiduna Usman Zannur, ayin aike a isarwa da Annabi saÆ™on shi sai Gadanga Æ™usar yaÆ™i Sayyiduna Aliyu, to da yawan mutane suna take abinda yake farilla suna mai da shi sunna, sunnar ma wasu take ta suke, ban wani ji abu mai kama da damuwa ba saboda babu wani challenges dana samu game da hakan” GabaÉ—aya suka jinjina kai cike da gamsuwa.

“Before you pray, believe, before you speak, listen, before you spend, Earn, before you write think, before you Quite try, and before you die live, Assalamu alaikum” Daga nan program ya Æ™are sukai sallama Majeederh ta miÆ™e tana sauke niÆ™ab É—in fuskarta hankalinta yana kan Khalil, sam bata lura da wanda yake zaune ya zuba mata idanu kamar ya cinyeta ba, tana zuwa ta kama hannun Khalil ta ce “Afuwan Ranka ya daÉ—e tuba nake” Ya kasa ce mata komai sai hannunta daya kama suka nufi waje, mota ya buÉ—e mata ta shiga shi dai kallonta yake ita kuma ta kasa haÉ—a Idanu da shi saboda kunya ya nufi wajen driver ya shiga ya jima zaune ya sake juyawa tayi saurin É—auke kai sai kawai ya girgiza nasa kan murmushi yayi a taushashe ya nufi Lafiya Round a hanya ya kira John ya ce ya kawo masa su Alhassan sun riga da sun yi missing flight É—in sai gobe. Majeederh ta riga sauka tana shiga Main parlour taci karo da Alhassan ya yi mata kaca kaca da milk cake a saman carpet cikin faÉ—a ta ce “Alhassan” A gigice ta miÆ™e tsaye jikinsa na rawa kansa a Æ™asa ta nufe shi kafin ta Æ™arasa tuni ya kwasa da gudu tana cewa “Stop, stop dear” Ina ya kama makaken windown ya dire zuwa bayan garden ta dafe kai a ranta tana jin yaya za ta yi da Alhassan yanzu? GabaÉ—aya halin babansa ya É—auka ya kwashe shi tas ta juya tun kafin su haÉ—a ido Khalil ya yi saurin haurawa upstairs yana shafa kai, shi da kansa ya san idan halinsa Alhassan ya É—auka to wallahi za a sha fama, ta girgiza kai ta nufi part É—inta wanka tayi tare da sallah ta nufi kitchen domin fara tunanin abinda zata haÉ—a na buÉ—e baki. Khalil na zaune a parlourn shi wajen dab da magariba sau uku yana zuwa bedroom É—in Majeederh sai ta gudu shi sam ya rasa dalilin hakan sai kawai ya barta, a hankali ya jinjina kansa yana sauraren John dake cewa “Mun ware adadin mutanen da za a bawa zakkar, mun ware adadin mutanen da za a bawa kayan abincin, bayan marayun da muke da su…,” Kallon da Khalil ya yi wa John ya sanya ya yi shiru a hankali ya ce “how many times zance ba marayu bane?” John ya shafa kansa ya ce “Tuba nake, kai ne uwa kai ne uba” Khalil ya kame fuska John ya É—ora da “Suma an ware musu kayan sallar su, abincin azumi, dana sallah, Gidan Uncle’s É—in Malama da gidan Abbu duka an kai musu kayan azumi” Khalil ya lumshe idanunsa ya buÉ—e calmly ya ce “Batun zakka, babu buÆ™atar Æ™arawa mai Æ™arfi, Æ™arfi ok” John ya ce “In sha Allah, daman wasu masu kuÉ—in ke yin haka, ba za a bawa talaka zakka ba sai mai kuÉ—i” Khalil ya jinjina kai, John ya miÆ™e ya ce “Zan shige, sai goben” A taushashe ya ce “Abinci?” John ya zare Idanu ya ce “Rufa mini asiri da matata, azumin farko naci abincin a wani wajen ba wajenta ba? A’a zan shige yanzu kawai” Yana faÉ—in hakan ya É—auki wayarsa da komai nasa, Khalil ya shafa kai ya miÆ™e gabaÉ—aya bashi da wani Æ™wari a hankali suka sakko downstairs shi da John É—in lokacin Jee ta gama komai tana tsaye gaban plasma tana jona bonner Alhassan yana leÆ™awa yaga me take domin ya haddace, ta yi wanka ta shirya cikin wata abaya lemon green ta mata kyau sosai fuskarta ta É—an faÉ—a, Khalil ya yi kicin kicin da rai saboda kishi musamman da yaga tana murmushi mai taushi, john ya ce “Malama zan wuce sai goben” Majeederhn tayi jim sai kuma ta ce “Ba zaka yi buÉ—e baki ba a nan?” Ya girgiza kai ya ce “Idan kin sallama Dr ya biyoni muyi a wajen FaÉ—imatu?” Majeederh ta zare ido bata ce komai ba, shi kuma ya yi gaba yana É—agawa Alhassan hannu, yana barin wajen Khalil ya nufi inda take kafin ya Æ™arasa tayi saurin shigewa part É—inta daidai nan kuma kiraye kiraye ya fara tashi a masallatai, hankulan jama’a ya koma yadda za a jiÆ™a maÆ™oshi ya juya ya nufi part É—insa, wanka ya yi da alwala ya sanya tattausan voyel É—in jallabiya ya zama irin baÆ™in Balaraben yana sakkowa yaga biyuni da yayansu Baby Khalil gabaÉ—aya cikin jallabiya ya kama hannun Baby Khalil ya É—auki Al’hussain ai kuwa Alhassan ya saka ihu saboda kishi ne dashi bisa dole ya ajiye Al’hussain ya É—auki Alhassan suka nufi masjid, Majeederh sallah ta yi itama ta shirya musu abinci a dining room tana Ajiye mug É—in coffee ta ji an rungumeta ta baya a hankali ya kwantar da kansa a wuyanta, cikin sabon sonta da yake fisgarsa ya matseta a Æ™irjinsa da kyau yana fesa mata iskar bakinsa a kunne a hankali ya ce “Guje gujen na mene?” Ya faÉ—a da Æ™yar yana manna mata laÉ“É“ansa masu sanyi, Jee ta yi shiru tana sauke numfashi ya sake matseta sosai yana jin kamar ya mayar da ita tsaginsa ya ce “Saboda kin tonawa kan ki asiri ke kika fara crushing nawa?” Ta yi saurin rufe ido abinda take ta gujewa kenan, ya yi murmushi yana jan kumatun ta ya ce “Shy Girl” Ya juya tare da nufar saman carpet ya zauna akan dadduma yana tanÆ™washe Æ™afafuwansa Jee ta Æ™arasa inda yake zaune ta durÆ™usa ta ce “Ina yini?” Ya yi mata shiru sarai ya jita ta sake cewa “An sha ruwa lafiya?” Ya juya ya ce “Me?” Ta kasa Kallonsa ya miÆ™a mata hannu tayi sak sai kuma ta É—ora nata a kai sukai musabaha ya ce “Assalamu alaiki Uwar gidan Dr Khalil” Ta É—an yi murmushi ta ce “Fatan kasha ruwa lafiya?” Ya matse hannun sai kuma ya É—auki dabinon ajwa ya saka bakinsa ya sake d’akkowa ya saka mata, kusan a tare suka lumshe idanunsu saboda daÉ—i da garÉ—in haÉ—i zaÆ™in dabinon daya ratsa bakunannsu zuwa jijiyar dake bawa gangar jikin amsa kuuuwa da yanayin da take ciki, ta gyara zamanta Alhassan ya miÆ™awa Khalil hannu ya ce “Aby” Khalil ya hargitsa kai yana kama É—an Æ™aramin hannunsa sukai musabaha ya nuna Jee ya ce “Ka gaisa da matata Mimi” Alhassan ya miÆ™awa Majeederh hannu ya ce “Mimi” Ta kame kunnen shi ta ce “Wato kai dole ka nuna mini jinin Dr Ibrahim ne ko? A gado abinda ka manta ne kawai baka É—auke ba? Allah duk sanda ka sake haura katanga kamar É“arawo jikinka ne zai faÉ—a maka fitinanne kawai” Alhassan kallonta kawai yake, ta juya kan Al’hussain ta ce “Kai kuma sarkin haÆ™uri wannan haÆ™urin zai maka illa watarana” Ta kalli Baby Khalil ta ce “Kai kuma kana babba idan sun yi laifi baka san ka make su ba ko? Maza su rainaka kaga yadda zanyi da kai” Tana faÉ—in hakan tayi shiru ta fara haÉ—a musu tea ta bawa kowa bata sakawa Baby Khalil suger sosai ba, tana bawa Alhassan ya yi cilli da cup É—in ya daki center table, tea É—in ya zube cup É—in ya fashe, Khalil ya yi saurin Æ™asa da kansa domin gani yake kamar vedion Æ™uruciyar shi ake nuna masa, Majeederh ta juya ta kalli mijin nata ya haÉ—e rai sai kawai ta fashe da kuka Khalil ya zare idanu ya kalli Baby Khalil ya ce “Friend kama abokan ka kuje part É—inku now” Ya miÆ™e ya kama hannun Al’hussain, Alhassan yaÆ™i tafiya Khalil ya daka masa wata gigitacciyar tsawa tuni yabi bayansu, suna barin wajen Khalil ya zare jallabiyar jikinsa ya rage daga shi sai trouser faffaÉ—an Æ™irjinsa a buÉ—e, ya zare abayar jikinta ya fizgota yana rungumeta a hankali a kunnenta ya ce “Kin zauna kina yiwa yarana faÉ—a tas, ban ce komai ba shi ne kuma zakiyi kuka?” Ya shiga zagaye lip’s É—inta da yatsar shi tayi saurin cewa “Amma wannan gadon da ya yi na zuciya ba zan iya da shi ba” Ya tari numfashinta da cewa “Ya kike da ubansa?” Ta yi shiru ai kuwa ya bi ya danneta da Æ™irjinsa ya saka hannu tare da É“alle net É—in bra É—inta ya ce “Kukan shagwaÉ“a kike, bari gwarzon mijinki Dr Ibrahim ya saki me dalili….
[

No comments