Mijin Malama Book 2 Page 5
Ko waye zai zama MIJIN MALAMA?
Idan na so mugunta da kuma jan labarin…. Sai kawai na É—akkowa Akeeth na bashi auren Malama Majeederh ai shima namiji ne? Idan kuma nagarta nake so sai kawai bawa Sheykh Ajlaal Sultaan? Idan kuma dangantaka nake so sai kawai Alpha ya dawo ranar auren a bashi ita? Idan kuma ramuwar gayya nake so sai Majeederh ta auri Aliyu…. Idan soyayyar gaskiya nake so da kulawa, da kuma dole ki so ni ko zaki mutu love by forch madly love sai kawai na bawa Ibrahimul-khalil, Abraham bad boy auren Majeederh…. Na tsaya da typing tunani kawai nake樂樂樂to ita matsalar ma Abraham yaro ne wai ya yi Æ™arami bai isa aure ba…. Congratulations TEAM MAI MARTABA AJLAAL SULTAAN殺
[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: Dad ya miÆ™e tsaye looking at his son reaction ciki nuna isa irin ta mahaifi ya ce “Abraham Denial David” Abraham na huci ya matsa dab da mahaifin nasa kamar zasu haÉ—e ya ce “It’s my name, kuma zan sauya soon” Dad na murmushin takaici ganin yadda É—an cikinsa ke musayar yawu da shi ya ce “Baka isa ba, ka yi kaÉ—an auren wannan babbar macen ba da kai ba, hakan ba zai faru ba, she’s older than you, tama fika wayo ko anyi auren wayo za tana maka” Mutumin dake zaune tun É—azo watching all of them ya kasa riÆ™e dryrsa ya yi Æ™asa da kansa kawai yana mmkin girman Abraham kuma deep down na zuciyarsa. Abraham ya girgiza kai ya ce “Zan nuna maka zuciya, na ci taurin kai da jijji da kai a wajanka na gada, É—an na gada ya fi É—an na koya” “Jesus” Dad ya faÉ—a ganin Abraham É—in na neman juyawa ya yi saurin riÆ™e hannunsa, da wani expression yake kallon mahaifinsa yana haÉ—e fuska tamau ya ce “let go of me, ba tafiya zan ba balle kasa a Æ™ara mayar dani mahaukaci” Ganin kallon da Dad É—in ke masa yasa ya É—auke yana huci sai kawai ya ji ya jawo shi jikinsa tare da rungumesa sosai a very tight hug, Abraham ya yi shiru tare da sauke kansa a shoulder É—in Dad yana lumshe idanunsa, sosai Dad É—in ya yi mamakin yadda zuciyar É—an nasa ke bugawa da Æ™arfi, sai abin ya bashi tsoro bai dai nuna masa ba, cikin sauri Abraham ya zame jikinsa sbd wani irin Æ™aunar Dad É—in nasa daya tasu masa. Upstairs ya haura yana hargitsa kansa kamar mahaukaci. Dad ya bisa da kallo sai ya yi murmushi domin a tsaye Abraham tsayayyen namiji ne har yafi Dad buÉ—ewar jiki gashi black skin É—insa wani Æ™ara kyau take da É—aukan Idanu wai a hakan ma hankalinsa ba a kwance yake ba. Ya nemi waje ya zauna yana É—aukan ruwa tare da sha. “Amma daka barshi ya yi auren, yana da ilimi, da tunaninsa idan kuÉ—i ne bashi da shi ai kai kana da shi” President Denial ya yi murmushi ya ce “Money? Shi É—in, idan bai fini kuÉ—i ba to zamu iya yin daidai for sure” Chancellor É—in ya buÉ—e ido ya ce “Wow! When last Debaka meet him at Naija? Ina tunanin this is the right time da zamu haÉ—a su aure immediately daman kullum sai ta mini complain akan baya kulata he just ignored her always, Debaka ta gama karatun ta aiki zata fara na dakatar da ita sbd rawan kanta” Dad dai jin Chancellor É—in yake yana tunanin taya zai fara masa explanation ba Æ´arsa Debaka Abraham yake son aure ba? “President kayi shiru? Did i say something bad” Dad ya juya kaÉ—an ya ce “Zan ji daÉ—in hakan, bana son Debaka ta auri wanda baya sonta, ban son ta wahala” Chancellor ya ce “But you promised me that, ina da tabbacin Abraham yana son Debaka kai kke bamu information na komai har zuwanta Naija a gidansa ta sauka” A taÆ™aice Dad ya ce “I’ll talk to him, ayi a hankali ka dai ga irin halinsa he’s stubborn boy” Chancellor ya miÆ™e tsaye ya ce “Ok i think i am leaving now, we will talk later” Ya jinjina kai tare da yin baya yana lumshe idanunsa. Har dare bai Æ™ara saka Abraham a idanunsa ba a haka har gari ya waye. A hankali yake taka steps É—in benen wanda zai kai shi part É—in shi ya jima tsaye kafin ya danna password na Æ™ofar ya buÉ—e, ya shiga sanyin a.c ya ratsa shi sosai komai na cikin first parlour É—in shi white colour ne, duk wani abu na jin daÉ—in rayuwa akwai shi yadda part É—in Abraham yake zube da narkakkiyar dukiya ba zaka taÉ“a cewa shi yake wannan rayuwar da Gang team a Naija ba, da yadda ya jure wulaÆ™ancin Abbu yana ce masa É“arawo mara gata sbd kawai yana ganinsa a gantale ya maida Æ™ofar ya rufe without making any sounds, gently ya Æ™ara buÉ—e wani Æ™ofar zuwa other parlour shi kuma komai na ciki peach ne har ya fi na farko haÉ—uwa baka jin Æ™arar komai sai na a.c da wasu Birds da suke gefe. Daga nan ya buÉ—e wata Æ™ofa tare da yin corridor ya sake danna password Æ™ofar bedroom É—in ta buÉ—e, Dad ya hango Abraham a tsakiyar bed ya Æ™udundu ne waje guda ya Æ™arasa tare da zama a gefen shi idanunsa akan fuskarsa ko da yake baccin fuskar nan a haÉ—e take sbd tsabar zafin zuciya. Ya yi ta Kallonsa tare da juyawa ya kalli carbon paper É—in dage gefe da pen a sama da wasu different colors ya É—auka ya shiga kallon zanen, ya jima yana kallon matar dake jikin paper É—in budurwa ma zai ce bama mata ba domin jikinta ba wani shekarunta daya nuna, ya jima yana kallon zanen kai tsaye kuma ya fahimci ita ce Majeederh. Ya ajjiye inda yake tare da mai da idanunsa akan fuskar Abraham dake baccin wahala wayarsa riÆ™e gam ya zare wayar still nan ma photonta ya gani a screen É—in, she’s more beautiful than he expects, wani jikin arziÆ™i gareta ba sai mahaukacin kyau nan ma ya jima yana kallon photon. Tunda yake a rayuwa bai taÉ“a farantawa Abraham ba, shi É—ansa kuma namiji ya musgunawa rayuwarsa, bai taÉ“a jan shi a jiki ba ya azabtar dashi azaba mai yawa yawanci kuma akan Majeederh ne da tafiya Naija, amma ko sau É—aya Abraham bai taÉ“a jin ladama ya ji azabar da ake masa ta ishe shi ya haÆ™ura da batun ta, yana zane ya sanya aka dinga masa allura wacce ta kusa zautar da tunaninsa, ya fahimci soyayyar da yake mata kamar da Æ™ais ce Majnoon na labarin Layerh da Majnoon amma ko su ai basu mallaki junan su ba, ita ta mutu shi kuma kamar ya haukace. Dad ya ji duk duniya ba abinda yake so kamar É—an shi Abraham da farin cikinsa amma musuluntar Abraham da auren Musulma da zai yi daidai yake da sauka daga kan muÆ™amin shi na President, jamaa za su yi masa tawaye koma ayi juyin mulki.
“What should I do!?” Ya tambayi kansa ga al’Æ™awarin da ya yi wa Debeka na auren su da Abraham, shi tsoran zafin zuciyar Abraham yake, kuma san akwai lack of parents careless daya taka rawa a rayuwar shi, yana da kuÉ—i da komai me zai yi da mulkin ma? Dole ya yi sacrifice mulkinsa wajan samawa Abraham farin ciki, shafa kansa ya yi tare da ficewa.
Yana fita Abraham ya buÉ—e ido,daman ba wani bacci yake ba, a hankali ya mirgina gefe yana ware narkakkun idanunsa zuciyarsa na harbawa da Æ™arfi, ko wacce dakiÆ™a da zata shige akwai abubuwan da zata tafi dasu a zuciyarsa,babbar damuwarsa a yanzu Envelope! Where’s Taj?.
Majeederh na zaune saman ladduma hannunta riÆ™e da carbi tunda akai kiran assalatu tayi raka’atul fjr take zaune har aka data subhi bayan ta yi ta zauna zaman azkar, har lokacin kuma bata runtsa ba tsayin 40days bata bacci damuwa ta mata yawa ta rame sai idanunta daya Æ™ara manya. A hankali ta ji an turo Æ™ofar tare da shigowa, bata kalle shi ba deep down na zuciyarta tana mamakin abin da ya kawo shi domin tun ranar data zo gidan bai taÉ“a shiga bedroom É—inta ba. “Mrng” Ta faÉ—a a sanyaye ya daÉ—e kafin ta ji ya ce “Yaushe ki ka samu tsarki?” Kanta a Æ™asa ta ce “Jiya” His Excellency ya ce “Kuma sbd kin isa baki faÉ—a mini ba?” Bata san lokacin data É—ago ta kalle shi ba ta ce “Ina nake ganinka? Ko wayata ka amshe fa” Abuturab ya jingina da jikin Æ™ofa ya ce “Oh” Ta runtse Idanunta sosai ita bata ma fahimtar me yake cewa “Are you okay?” Ta buÉ—e Idanunta wanda sukai wani iri sbd bacci silently ta ce “Headache” Ya ce “Ba kya bacci shi ya sa, ina zuwa” Not too long ya dawo riÆ™e da kwalba ya bata ya ce “Drink” ta É—an kalle shi ta ce “Maganin mene?” Ya haÉ—e fuska ya ce “Zan cuceki ne? Kalli Æ™addarar data faÉ—a miki na aure ki sbd ina son ki, Drink” Duk wani tashin hankali bata son shi sai ta amsa ya ce “Drink all” Ta jinjina masa kai ta É—aga kwalbar ta shanye ya ce “Good Wifey, zuwa minutes zaki bacci kina farkawa zuciyarki za ta yi wasai babu wata damuwa” Ya faÉ—a yana zama gefen gadon ta, domin ya jima da lura depression ne ya yi mata mugun kamo. Tunda Majeederh ta shanye maganin kanta yake a gefe bata motsa ba, zufa ke yanko mata all over herself can ta miÆ™e tana dafe kai jiri na É—aukanta ganin haka yasa His Excellency damÆ™ar hannunta ya jawota ta faÉ—a saman jikinsa, ya rufe Idanunta tana jin duniyar ta rabe mata gida biyu tana jinta kamar a saman gajimare “Jiddo, Wifey?” Ya É—an girgiza ta, ta buÉ—e Idanunta da sukai jajur cikin wata kalar murya ta ce “Abbu… My father hate me, ya tsane ni, ya tsine mini” kallonta kawai Abuturab yake yana riÆ™e da ita a cinyarsa a hankali ta ce “Bana jin daÉ—in duniya, wanda na yarda da shi ya ci amanata, ban san me ya sa abubuwa suke faruwa dani ba, É—an uwana ya gudu ranar aurenmu, Little…..” Ta yi shiru Abuturab ya ce “Uhm, go on wifey say it faÉ—i duk abin da yake ranki” Ta Æ™ara ja baya kamar zata faÉ—i ya riÆ™eta da kyau bakinta na rawa lip’s É—inta na kakkarwa ta ce “I love him, na raine shi with all my heart and soul, ya ci amanata pls ka yarda dani Excellency ban san komai ba, kada ka juya mini baya sbd wannan Æ™addarar, kada ko gorantawa É—a na idan ya girma ko yaran da zamu haifa” surutai take masa wanda kuma da dukkan zuciyarta take yin su ita kanta kuma bata san lokacin da suke sakin kan su ba, kallonta shi dai kawai yake a hankali ya ji numfashinta na sauka a Æ™irjinsa jikinta ya sake, daga nan kuma al’amarin ya sauya mmki ya kama his Excellency Abuturab AlÆ™asim ya san lafiya lou yake gama shaida nan Æ´ar shi Jidda amma yanzu ya ji ya kasa aikata komai. Ya mirgina gefe zuciyarsa zuciyarsa a cunkushe baya son ya ji haushin Majeederh at all amma tunda ya ji ya kasa samunta ya ji kamar ta fice masa a rai. Ya miÆ™e tare da ficewa daga É—akin… Majeederh na zaune a parlour ita da Latifa da Aaliyyah, Latifa Omar tana sakin murmushi ta ce “Daman na ce ba zan zo ba sai kin muri amarci gashi kam yanzu sai da ki kai wata biyu” Murmushi kawai Majeederh ta yi hannunta riÆ™e da Baby Khalil da ya yi wani irin kyau da Æ™iba sai harba Æ™afa yake abinsa. “Aaliyyah je ki duba lunch” Aaliyah ta miÆ™e tsaye tare da nufar É“angaren kitchen. Latifa Omar ta ce “Majeederh shawara nake nema, ina cikin damuwa tun abinda ya faru na kasa shawo kan Aliyu” Majeederh ta kalli Latifa Omar ta ce “Ki yi haÆ™uri” Latifa ta ce “Haba besty ni da mijina bani da kwanciyar hankali, ko yana son ki ai yana da kyau yanzu ya haÆ™ura tunda kin yi aure, shi yasa fa na kasa faÉ—a masa kin yi aure tunda ba cikakkiyar lafiya gare shi ba” Majeederh ta ce “Da kin faÉ—a” Idanunta ya ciko da hawaye sai kawai ta saki kuka ta ce “Bestie ki taimaka mini ki taimaki aure na, ki faÉ—awa Barrister da bakin batun auren ki please bani da sama dake shi ya sa nazo ki bani shawara” Murmushi kawai Majeederh tayi ta ce “Latifa ko wacce mace a gidan mijinta haÆ™uri take, kowa yana da damuwa fa?” Da sauri Latifa ta ce “Baki da wata damuwa ke, gashi nan hankalin ki kwance ni kuma soyayyarki ta hana mijina sakat” Majeederh ta lumshe idanunta “Latifa tunda na yi aure wata biyu babu abin da ya shiga tsakani na da Abuturab, ya kwance wayata sai na yi sati ban sa shi a idanuna ba” É“oyayyiyar ajjiyar zuciya Latifa ta sauke a ranta tana cewa “Well-done Turzum” A fili kuma ta zare idanu ta ce “Kuma ke baki nema ba? Kamar wacce bata da lafiya?” Majeederh ta yi shiru “Tab ki ce ke masifar feelings ne ke cinki aure wata huÉ—u miji bai raÉ“i inda kike ba ko tunaninsa sadaÆ™a aka bashi shi ya sa ya samu lasisin wulaÆ™anta ki?” Majeederh ta rungume É—anta da ya yi bacci ta ce “To me zan?” Latifa ta gyara zama ta ce “Idan kin yarda dani zan baki shawara, ki shirya yau ki je har part É—insa ki ce anan zaki kwana hakÆ™in ki kikeso, tunda dai ke ba dutse bane shi ma his Excellency yana abu kamar ba Mijin Malama shi da zai zage ku kwashi soyayya” Majeederh ta girgiza kai ta ce “Ina mace na bisa har part É—insa? Ai ko abinda nake ji zai kashe ni bana jin zan haka” Latifa Omar ta girgiza kai ta ce “to mene a ciki kuma? Ni fa barrister yadda kika san É—an taure haka yake, baya gajiya mijina ya iya soyayya shi na musamman ne bana jin a yanzu zan iya bari ko wacce mace ta raÉ“u inda yake, yanzu ki ce ke kina zaune kamar fankon ashana sunan kin yi aure amma babu abinda kika sani na rayuwar aure duk daÉ—i da zumar dake cikinsa baki sani ba? Ko soyayya bai fara nuna miki ba, to wlh tallahi kada ki yarda ki je yau duk abinda zai faru ya faru kawai” Kafin Majeederh ta yi magana suka ji an shigo Latifa ta kalli Hassenatou wacce ta shigo tana taunar cimgam da wata budurwar yarinya Æ´ar firit da ita, suka nema waje suka zauna Latifa ta ce “Sannunku” Hassenatou ta ce “Sannu da shan a.c da cin arziÆ™i” Latifa ta ce “Ikon Allah! abin nema ya samu, matar É—an doka ta haifi É“arawo” Intisar ta ce “Wannan ne shegen É—an kenan? To wajan zama ne da shi a gidan?” Hassenatou ta ce “Waya sani ne, bana son dai a dinga cin amanar His Excellency kin san zina masifa ce idan ka fara baka iya dainawa” Latifa ta ce “Ashe kun san da haka kuke É“ata bakin ku? Nan fa gidan mijinta ne ta fiku iko da gidan” Intisar ta ce “Hold on my dear, bana son Shisshigi waya kasa dake balle ki É—auka?” Majeederh ta miÆ™e tsaye riÆ™e da Baby Khalil ta nufi bedroom suka kwashe da dariya, sai kuma suka miÆ™e tare da ficewa daga parlourn da sauri Latifa ta bi bayansu. “hi” suka tsaya duk ta Æ™arasa tana miÆ™a musu hannu ta ce “Friends?” Sukai mata banza ta ce “Nazo na tayaku yaÆ™i ganin É—an uwanku ya rabu da mugun iri, bai dace ya zama mijin malama ni da kuke ganina best friend É—in Majeederh ce amma babu wacce na tsana sama ita” Sai kuma fashe da kuka sosai ta ce “Za ku yi mamaki idan na ce malama Majeederh har mijina take nema, shi ya sa kullum bata da wajan zuwa sama da gidana lokacin dana sameta ita da mijina turmi da taÉ“arya a ranar ban iya bacci ba, na ji kamar na kashe kaina na huta wallahi, har yanzu zuciyata zafi take ta hana ni kwanciyar hankali a gidan mijina yanzu kuma tayi aure hankalinta kwance, mijina ya daina kulani sbd ita baya kwana a gidan kullum cikin maganarta nake, ki duba duk yadda na yarda da ita duk wata matsalata na kawo mata amma a haka taci amanata ta zame mini muguwar Æ™awa” Ta Æ™ara rushewa da kuka sosai Hassenatou ta ce “Kan uban nan kuma kike zaune?” Ta ce “To ya zan?” Haseena ta ce “Na miki al’Æ™awarin cikin satin nan sai auren nan ya mutu wama ya sani ko tana da hiv?” Da sauri Latifa ta ce “Ba mamaki tunda har hotels na sha rakata, kuma can baya ta taÉ“a É“ata muka nemata muka rasa har tsayin sati guda , ni wallahi kamar na ce Barrister ya sake ni” Intisar kishi ya cika zuciyarta tana addu’ar Allah ya sa Majeederh bata da ciki balle ta shafa musu mugun taÉ“o “Akan me zaki rabu da mijinki? Ai wallahi bata isa ba sai dai ke ki hanata jin daÉ—in rayuwa, i have an idea” Duk suka kalli Haseena ta ce “Kin tabbatar turmi da taÉ“arya kika samu Majeederh da mijin naki? Kin san sharrin zina dai” Latifa ta ce “Wallahi Allah da gaske nake” Haseena ta ce “Good, yanzu ki bani numberki sannan ki turo mini photon mijinki da yake ba riga yana kwance akan gado, ni ma zan É—auki Majeederh cikin dare sai ayi editing photon a nuna suna manne da juna, kamar miji da mata ana gama edited zan tura miki ta I.g ko WhatsApp ki san duk yadda ki kai kika É—auki wayar Barrister Aliyu ki shiga WhatsApp É—insa ki turo pictures É—in ta prvt number É—in His Excellency wacce yake WhatsApp da ita kina turawa zai gani ai government house free Wi-Fi ne, bayan ya gani ni kuma zan ce ya É—an ara mini wayarsa zan kira Meema daga nan zan shiga WhatsApp É—in na nunawa Mama mahaifiyar His Excellency”
Muje dai zuwa.
MIJIN MALAMA na kuÉ—i ne pay before you read….. 08119237616
Nimcyluv sarauta
[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *#The Stubborn*
Post a Comment for "Mijin Malama Book 2 Page 5"