Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 50


Aisha Baby Novel: Khalil ya sake rungume Gimbiya yana jin kamar ya shige cikinta ya huta wani irin kewarta ta saukar masa tare da mamaye jikinsa, ƙofofin zuciyarsa suka bubbuɗe da soyayyar Ummien nasa, idanunsa sun yi jajur saboda yadda a karo na farko tun bayan sanin wace mahaifiyarsa ya ji tana kuka, a hankali hawayenta masu zafi suke sauka a bayansa wajen wuyansa, ta ƙanƙame shi da kyau kamar zata sake yin cikinsa ta haife shi, a hankali a kuma nutse tana babbuga bayansa tana shafawa saboda jin yadda yake sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri, wata na korar wata.
“Ummieeeyyy” Iya abinda bakinsa ya furta kenan, saboda bashi da Æ™arfin zuciyar da zai faÉ—i abinda yake saman harshensa a yanzu, ya sake rungumeta, wata gamsasshiyyar nutsuwa na sauka a jikinsa, sai yanzu ya Æ™ara tabbatar uwa, mahaifiya rahama ce, dole wanda ya rasa tashi ya zubar da hawaye.
“Ibrahim? Khalil yarona”
Gimbiya ta furta a kamalance tana jin dukkan wata damuwar zuciyarta na shekara wajen uku ta yaye nan take, zuciyar ta wanke tare da yin fari daga duhun damuwar da Mr President ya sanyata “Kana raye? Zan sake ganinka?” Yadda take maganar da Æ™yar zaka san cewa ba Æ™aramin Æ™arfin hali tayi ba wajen furta kalaman, Khalil ya É—ago a hankali ya zubawa mahaifiyar tasa ido, shi mamaki yake wai ita ta haife shi? Ya É—an yi Miskilin murmushi kafin ya ce “Allah bai É—auki raina ba, ina tare dake, zan ji daÉ—in uwa Ummie” Sharr! Wasu hawayen suka sake sakko mata a hankali tayi murmushi mai laushi ta ce “Ya Allah!” Ta kama hannunsa tana tattaÉ“a shi ya riÆ™e hannunta ya ce “The real Ibrahimul-khalil is back, your son É—anki ya dawo” Da sauri ta sake jawo shi ta rungume a wannan sa’ilin kasa riÆ™e kukan ta yi, ta sake shi bisa umarnin zuciya. Majeederh dake tsaye ta yi Æ™asa da idanunta hawaye na zuba a cikin idanunta, lallai uwa! Daban take a cikin rayuwar yaranta, yadda Khalil ya narke jikin Ummie kaÉ—ai ya isa ya fahimtar da ita yadda ya yi kewar mahaifiyarsa, ta rufe ido tana jin soyayyar mahaifiyarta fulani na Æ™ara sauka a zuciyarta ko wanne motsi tayi sai ta tuna da ita, bata san soyayyar uwa ba, babu rabon kuma zata samu É—in Ubangiji ya fita sonta tunda ya É—auke ranta ya barsu. Jin an kira sunanta a taushashe ya sanya ta É—aga kanta Gimbiya ta gani riÆ™e da hannun Khalil tana kallonta alamar ita ke kiran nata, ta nufeta jiki a sanyaye da sauri twins da Yaa K suka mara mata baya, tana zuwa Gimbiya ta ce “ke fa ba Daughter-in-law ba ce, you’re my daughter ko baki auri Khalil ba” Kunya ta kama Majeederhn ta sunkuyar da kanta Khalil ya É—an shafa kansa speaking calmly a taushashe ya ce “Ummie ki rungumeta itama” Gimbiya ta kalli Khalil sai kuma ta É—auke ido ta ce “Come closer dear” Ta haÉ—a su ta rungume a jikinta tana rufe ido a ranta ta ce “Alhamdulillah!”

“Brother” Clara kuma Fatymerh ta kira Khalil tana murmushinta irin na Ummie, Khalil ya kalleta sosai suke kama da ita bambancin kawai ita fara ce komai nasu iri É—aya ne, nata zubin halittar na mace ne, shi kuma nasa namiji. Ta sake murmushi ta ce “Ko na ce Biyunina” Ya É—aga mata gira da dukan kafaÉ—arta sai kuma yi yi mata rungumar gefe (Side hug) Kamar an masa dole ya ce “Sweetheart” Fatymerh ta yi murmushi ta ce “You’re welcome Kspider” Ya lumshe idanu ya buÉ—e, ya kalli Zizi da Badi da suke ta kallonsa jikinsu duka a sanyaye sai ya miÆ™a musu hannu da gudu suka rungume shi suna cewa “We miss you alot Kspider, Welcome back to the kingdom, among your relatives and parents” Khalil ya yi guntun murmushi iya laÉ“É“ansa kafin ya juya ya kalli Majeederh yaga harta shige motar da Ummie take, ya tsaya cak da mamaki domin basu saba haka ba Ummie ta kalle shi sai kuma ta ce “Me?” Ya É—an yatsuna fuska ya juya zuwa motar da Fatymerh Clara ke ciki, ya tarar su Al’hussain na ciki ya kwanta a bayan motar yana lumshe idanunsa zuciyarsa na bubbuÉ—ewa na fargabar abinda ya aikatawa Jee har ta raba mota da shi, har suka isa cikin Palace idanunsa rufe ko tari bai yi ba, yana jin wata sarewar Algaita na tashi mai sanyi da daÉ—in saurara sounds É—in na musamman kamar yadda ko wacce masarauta kalar Algaita É—inta daban yake, wanda Sarkin Busa ke yi ya gada kuma wajen iyaye da kakanni, Khalil ya tsani duka irin wannan shi kaÉ—ai sai siririn tsaki yake jaa. Majeederh na fitowa daga motar ta bi masarautar da kallo wata kamala, nutsu izza da isa irin ta masu jinin sarauta na game jinin jikinta, a ranta tana yiwa Ubangiji kirari rashin sani ya fi dare duhu sau biyu tana zuwa cikin Palace É—in nan ba tare da sanin cewa gidan grandparents É—inta bane, ashe duk wata soyayya da Ƙhulud Arzaan ke nuna mata jininsu É—aya,ita É—in Æ´ar uwarta ce, Lillahi wahidur Qahhar, buwayi gagara misali banda Al’hakkamu waye zai yi wannan? Ta goge hawayen dake bin idanunta, yadda take tunani haka Khalil ke yin nasa shi da keÉ“antacciyar zuciyarsa, ya karÉ“i Musulunci wajen Uncle É—insa, ya kalli Mahaifiyarsa ba tare da sanin matsayinta a wajensa ba, ya zauna cikin danginsa ba tare da saninsu da nasa ba, komai yana zuwa bisa tsarin Ubangiji da kuma yadda yaso. Ya lula duniyar tunani ya ji an rungume shi ta gaba data baya ya buÉ—e idanu, Mai martaba Ajlaal Sultaan ya gani tsaye a gabansa ya rungume shi idanunsa na rinewa, Rohaan ya sake rungumesa ta baya, Zaytoon kasa magana tayi sai kuka data fashe da shi, Majeederh da Ƙhulud Arzaan suka rungume juna, farin cikin ganin Khalil da Ahalinsa ya wanke zuÆ™atan Granny da sauran, nan da nan aka fara shirya kayan buÉ—e baki na musamman ga baki na musamman wanda ba’a zaci zuwan nasu ba, musamman Dr Ibrahimul-khalil.
Har dare lokacin kiran Magriba a Æ™asar Saudiyya Khalil bai sanya matarsa a idanunsa ba, sai yaran kawai yake gani hakan ya dame shi yana son ya ji wanne hali take ciki, gefe guda kuma ganin Ummie a parlour ya hana shi tambayar Majeederh, haka kurum Ubangiji ya sanya masa jin nauyi da shakkar Ummie É—in hadda kunyarta. A hankali ta ajiye azkar É—in hannunta ta kalle shi yana zaune saman dadduma ya É—an kishingiÉ—e idanunsa rufe hannunsa É—aya akan haÉ—aÉ—É—an kushin a lokacin sai ta gan shi bashi da maraba da Ajlal ta jima tana kallonsa kafin ta É—an yi gyaran murya, Khalil ya buÉ—e gajiyayyun idanunsa tare da kallon Ummie a taÆ™aice ta ce “Idan kayi buÉ—e baki, sai ka zauna zaman jin mulki”

Ya zare idanu sosai ya ce “Mulki?” Ta haÉ—e rai ta ce “Eh, naga sarautar kake ji da ita yau” Ya É—an kwaÉ“e mata fuska domin shi baya son wata sarauta bashi da wani zaÉ“i wanda ya shige hutawa, tunda ba gun aiki za shi ba, kuma ba zai iya zaman surutu da kowa ba da Jee na nan shi ne za su yi hira mai daÉ—i irin ta mata da miji. Ta kalle shi da kyau ta ce “Ibrahim” Ya kasa amsawa idanunsa dai na zube a kanta ta ce “Bakai kake da ikon zaÉ“ar sarauta ba, sarauta ke zaÉ“ar mutum kuma ta riga data shiga jikinka ta zame maka jinin jiki, either you like it or not, kai É—in jinin sarauta ne kuma kana son ta” Ya girgiza kai kawai yana miÆ™ewa tsaye tare da dawowa kusa da Ummie tareda juyawa gabaÉ—aya a taushashe kamar zai mata raÉ—a ya ce “Goodness, takura ce” bata ce masa komai ba,ya miÆ™e zuwa sashin da aka basu har ya shige ya dawo yana shafa kai, Ummie ta miÆ™e tana gyara zaman lafayar jikinta ta dube shi a tsanake ta ce “Lafiya?” Ya ce “Ummie irin takalmin Uncle Ajlaal” Ta ce “Ya yi me?” Ya kasa cewa komai ta ce “Kai kuma da baka son sarauta mene haÉ—inka da takalmin sarauta?” Ya juya da sauri yabar wajen, a tare Mai martaba Ajlaal Sultaan shi da Prince Rohaan suka fito suna tsaye hannunsu riÆ™e da Dabinon ajwa Khalil ya fito cikin wata kyakkyawar jallabiya mai zare shuÉ—i irin zanen jikin sarauta ne da ita, yadda yake a tsaye saman Æ™afafuwansa zaka kula da yadda ya kerewa Mai martaba Ajlaal Sultaan a tsayi girma da faÉ—in jiki, Rohaan ya ce “Mijin Malama an fito?” Khalil bai ce komai ba, addu’ar daya koya wajen Majeederh yake nanatawa a Æ™asan zuciyarsa a haka yana tsaye Alhassan da Al’hussain suka fito da Yaa K gabaÉ—aya jallabiya ce a jikinsu irin ta mahaifin su Khalil, Ajlaal da kansa ya É—auki Alhassan Rohaan ya É—auki Al’hussain Khalil ya kama hannun Babban É—ansa kuma takwaransa Ibrahim Khalil.
Majeederh na zaune a saman dining bayan ta gama zubawa kowa abinci dake daman ita tayi, Rohaan ya kalli plate É—in Khalil lafiyayyen Æ™osai ne wanda ya ji Æ™wai da kayan Æ™amshi, sai kuma kunun gyaÉ—a wanda ya ji madara sai nau’in kayan itatuwa ya ce “Ya mu duk kika zuba mana abinci shi kuma sai kayan ruwa?” A tare Ummie da Majeederh suka ce “Dare ne ai, sun masa nauyi” Roohan ya ce “Ya Allah ka aurar dani ka kawo wacce zata ce tana so na” A tare Zizi da Badi sukai dariya gabaÉ—aya sun yi zuru-zuru saboda basu taÉ“a zama da yunwa sai wannan shekarar ba. Ƙhulud na kallon yadda Khalil ke bin Majeederh da kallo yama kasa cin abincin ita kuma taÆ™i yarda ya sanya idanunsa a nata, Ƙhulud Arzaan ta É—aga murya da Æ™arfi ta ce

“Na’am, Majeederh kike kira Granny?” Jee ta É—ago kanta ta kalli Ƙhulud Arzaan ta ce “Malama Majeederh Granny na kiranki fa, tun É—azu maybe ba kiji bane” Majeederh ta miÆ™e daman ta gama abinda take Ƙhulud ta kalli Khalil tare da kashe masa ido É—aya, ya shafa kai yana É—aukan ragowar kunun gyaÉ—ar da yake a cup ya miÆ™e tsaye hannunsa É—aya zube cikin Aljihu Zizi ta ce “Baka gama cin abincin ba Kspider” Bai juya ba balle ya bata amsa, Ummie bata ce komai ba domin tasan me zai aikata,ta kalli Zoya da Zohal da twins ta ce “Kuzo muje, zaku harami?” Suka É—aga mata kai da sauri ta kwashi yaran zuwa sashinta.
A hankali Majeederh ta shiga bedroom É—in Zaytoon idanunta ya sauka akan Granny wacce take kwance saman bed É—inta tana bacci dalilin maganin data sha, gyara mata kwanciya tayi tare da juyawa ta nufi waje a daidai wani corridor wanda aka kashe hasken wajen ta tsaya tana lalubar hanya, tana Æ™oÆ™arin tafiya ta ji an rungumeta ta baya, ta sauke ajiyar zuciya gabanta na faÉ—uwa sosai Æ™amshin turaren shi ya jima da bayyana mata waye, sun jima haka kafin ya juyo da ita gabansa bakinta na rawa ta ce “Ka sake ni?” Ya yi mata shiru sai sake matseta ya yi a Æ™irjinsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali, ta fara kokawar kwacewa ya san kuma hakan na nufin ta yi fushi ne, ya É—an kurÉ“i kunun hannunsa tare da ajiye cup É—in saman window ya damÆ™o kanta yana haÉ—e fuskokinsu waje guda laÉ“É“ansa a saman nata, Majeederh ta buÉ—e baki da niyyar yin magana ya yi saurin juye mata kunun bakinsa hakan ya haddasa mata yin shiru bisa dole ba dan tayi niyya É—in ba, ya sunkuya tare da É—aukanta ya bi ta can Æ™ofar baya ya nufi sashinsu da ita, idanunta rufe tana sake kwantar da kanta a lafiyayyen Æ™irjinsa tare da shaÆ™ar Æ™amshin turaren shi na Boadicea The Victorious mai kwantar mata da zuciya,a nutse a hankali kuma ta buÉ—e maÆ™oshinta tare da shanye kunun É—aya juyewa mata, har daÉ—i da garÉ—in gyaÉ—ar suka mamaye bakinta.
Khalil na zuwa ya kwantar da ita saman gado ganin tana Æ™oÆ™arin tashi ya bi bayanta ya danneta da Æ™irjinsa tayi saurin rufe Idanu tana damÆ™e damtsen hannunsa muryarta na rawa saboda hancinsa da yake goga mata a dugan wuyanta ta ce “Ma…man cikina, our baby” Ya sassauta nauyinsa yana zame abayar jikinta hannunsa É—aya ya sauka a kan mararta data fara girma sosai daga nan kuma ya fara shafa dugwayen Æ™afafuwanta idanunta rufe jikinta ya fara É—aukan rawa ta ce “Let go of me?”

“I won’t” Ya furta a taÆ™aice kafin ya mirgina gefe yana jawota ya É—orata saman Æ™irjinsa, hannayensa rungume da Æ™ugunta ta baya wanne ya haÉ—a da nasa ya manne waje guda, bakinsa a kunnenta yana fesa mata numfashi mai zafi Æ™amshin kunun na fitowa saboda ko brush bai yi ba, bayanta yake shafawa a hankali har ya samu nasarar É“alle rigar jikinta ta rage sai Inner wears, jikin Majeederh ya saki domin Khalil ya san duk abinda tafi Æ™auna a nutse a taushashe kamar mai raÉ—a yana Æ™asa da muryarsa ya ce “I’m sorry” Ta yi masa shiru ya sake cewa “please” Ta buÉ—e ido tana kallonsa kafin ta ce “Sorry for?”
“My mistake” Ya mirgina kai yana tallafo fuskarta ya ce “Na miki ihu gaban mutane, babban damuwata gaban yaranmu” Ta É—an yi murmushi ta ce “It’s ok” Ya shagwaÉ“e mata fuska yana kwaikwayon muryarta ya ce “Kiyi haÆ™uri i won’t do it again, ina tsananin son ki kuma shi ne sanadi ALLAH YANA GANI, and ba laifi na bane”

“Laifi na ne kenan?”
Ta tambaye shi tana tsare shi da sexy eyes É—inta wanda nan take suka sake sauyawa Khalil lissafi ya kasa furta komai sai lip’s É—inta daya fara zagayewa da hannunsa ta ce “You don’t trust me, kana tunanin zan iya cin amanarka ne? Idan zan ci me ya sa lokacin da ake zaton ka mutum banci ba? Sai yanzu, da nake ganin ba zan iya rayuwa babu kai ba? Da nake ganin ka riga ka cike dukkan gurbin zuciyata da soyayyarka, da nake ganin ka zama silar yaye damuwata, sai yanzu da hankalinmu ya kwanta, babba abu kuma ina sonka amma shi ne zaka mini ihu a gaban mutane harda ma John?” Sai kawai ta fashe da kukan shagwaÉ“a tana buga Æ™afa da yarfe hannu tare da girgiza jikinta, hakan yasa gabaÉ—aya na jikin nata motsawa Khalil ya Æ™arasa susucewa ya rarumota ya rungumeta sosai yana sauke wani irin numfashi a kiÉ—ime ya fara sauke mata wasu Single Lip Kiss, breathing É—insa na sauka a zafafe, so yake ya rarrasheta amma sam bai san ya zai yi ba, ita kanta Majeederh sai data tsorata, tun tana dauriya ta fara ture shi zufa ta wanke mata jiki a gigice a kuma wahale ta ce “Cikina, marata” Maimakon ya saketa tunda ya samu abinda yake so amma kamar ta Æ™ara masa Æ™arfi ne ya sake mata Leave a Mark Kiss, yana ficewa daga hayyacinsa jikin Jee ya fara saki ta raina kanta yau asalin Dr Ibrahimul-khalil take gani, wasu irin hawayen so da Æ™aunar mijinta suka dinga fita daga cikin idanunta, tasan baya hayyacinsa da tuni ya fahimci halin da take ciki kuma daman tarata ya yi ta wannan hanyar yake son rarrashinta can Æ™asa ta ce “Ya Allah kada kasa Khalil ya yi sanadin fitar cikin nan” idanunta na rufe hannunta ya saki, gudun ruwan da Khalil ya ji a cinyoyinsa wanda suke fita da zafi ya dawo dashi cikin hayyacinsa, ya zame daga jikinta da Æ™yar wani buÉ—e Idanu ya yi lokacin da idanunsa ya sauka akan bedsheet É—in da cinyoyinta jini yake fita daga jikinta harda guda-guda a gigice cike da tsoro ya tallafota yana “I am sorry Sexy mama, na rasa tunanina” Da Æ™yar ta ce “Ka kira Ummie karmu rasa babynmu khalil….,” Wani gudan jini ne ya sake fitowa wanda ya sanya Majeederh Æ™anÆ™ame Khalil jikinta na rawa.

No comments