Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 52


Aisha Baby Novel: *Ku shiga wannan link É—in domin cin gasar Arewabooks a facebook*
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid0FmezASrxXqPu36esVQepCtpQo8kQa3YDTRg86S35nuLfyEH4MQkuRExrgvZxsaxal&id=100067047050886&mibextid=Nif5oz

Ta zare Idanu tana riÆ™e numfashinta saboda gabaÉ—aya nauyinsa ya sakar mata,ta rufe bakinta da hannu yadda yake kallon idanunta zuwa bakinta tasan tana buÉ—e baki da niyyar magana akwai abinda zai biyo baya, Khalil yaÆ™i tashi sai bin fuskarta zuwa dogun wuyanta da kallo yake a hankali yana sake sauke mata nauyin nasa ya É—ora fuskarsa akan tata ya sauke numfashi da wani Æ™aramin voice ya ce “Kin zalunce ni…” Tayi saurin zare ido ya manna mata kiss a Idanun ya ce “Ina nufin zuciyata” Majeederh dai bakinta a rufe ya saka hannunsa da Æ™arfi ya fisge hannayenta yana É—aga su sama kamar mai shirin caje ta ya kalli yadda ko’ina na jikinta ke shinning ga wani Æ™amshin kwalacca mai kwantar da hankali da sanya nutsuwa, hannunsa É—aya riÆ™e da hannun É—ayan kuma yana murza cibiyarta ya ce “Lallai yarinya, Ibrahim zaki ma wayo?” Ta haÉ—e fuska ta ce “To tunda yarinya ce sake ni” Ya yi wani kalar murmushi yana kashe mata ido É—aya da É—aga mata gira ya ce “Na isa, tunda har kin lalata ni lokaci guda kika haifi twins” Ya ci-gaba da murza abinda yake ya ce “Lalata Ibrahim abu ne mai wahala but it’s very easy to my wife, sexy Mama” Majeederh ta haÉ—e fuska tana tura bakinta a hankali muryarta can Æ™asan maÆ™oshi ta ce “Bad boy” Yana cire ribbon É—in kanta ya ce “Yhhhh, but untill on bed” Ya tura yatsun hannunsa cikin sumar kanta, gabaÉ—aya ya manta azumi ya kai ya gama kunce masa lissafin kansa, gently Jee ta zura hannayenta a Æ™asan hannayensa ta rungumesa sosai Æ™irjinsu manne a hankali ta ce “Man” Bai ce komai ba, sai dabara da ya yi mata yana É—agota a hankali ya fara unhooking bra É—in tayi saurin riÆ™e shi tace “Not now” A hankali ya ce “Saboda ke kika biya sadaki?” Da sauri ta ce “Sadakin da ba a bani ba?” Ya yi saurin sakinta tare da ja baya ya yi zuru domin da gaske shi bai bada sadaki ba ya yi kalar tausayi ya ce “Don Allah?” Ta hararesa tana miÆ™ewa tare da É—aukan abayarta sai a lokacin ya fahimci dabara take masa ya miÆ™e yana shafa kansa kamar zai nufi upstairs sai ya sunkuya gabaÉ—aya ya yi sama da ita ya ce “Yaushe ki kai wayon yiwa Ibrahim dabara? Ke kina jin idan nayi niyyar abu zaki hana? Shuka sai da ban ruwa” Ta yi murmushi kawai ya ce “I love you, and I’ll always love you Jee” Ta mintsine shi ta ce “No is the man without a woman” Ya girgiza kai kawai can ya ce “Muje mu gaisa da wannan mala malan naki, naga how big they are yanzu?” Jee mamakin rashin kunyar Khalil take gabaÉ—aya baya jin nauyin sakin magana. Suna shiga bedroom É—insa ya saketa ta zauna saman kujera ya nemi waje a gabanta ya durÆ™usa hannunsa akan cinyarta yanayinsa ya sauya a hankali ya hargitsa sumarsa ya É—ago kai ya kalleta itama shi take kallo ya ce “You didn’t tell me Hawwa’u?”

“Me?” Ya kwaÉ“e fuska yana Æ™ara haÉ—e hannayensu waje guda ya ce “Kina so na, tun sanda bana ji” Tayi dariya mai kyau ta ce “Oh, yanzu ji kake?” Ya É—an yatsuna fuska ya ce “Be serious Maa” Ta zame hannunta ta É—ora a kansa a hankali ta shiga tura hannunta cikin tulin sumarsa cikin murya mai laushi sosai ta ce “Me ya sa zan faÉ—a? Bayan lokacin ko auren baka san ma’anar shi ba? Kana ji da rigima, dukan jama’a haura katangar Abbu?” Ya yi shiru kamar mai nazari while he keeps his eyes on her, tasan kuma dole ya karanto gaskiya a hankali ya yi dariya sosai yana girgiza kai ya ce “Kawai kina tunanin ban isa gona ruwa da Æ´a Æ´a shuka ba, kina tunanin kayan aikin noman sun yi kaÉ—an ko?” Ta zare ido sosai ta kasa cewa komai ya zauna sosai saman carpet yana lumshe idanunsa jin tana yamutsa gashinsa kamar babu laka a jiki ya ce “Da gaske kin zalunce ni, kuma ki gaggauta neman yafiya” Ta ranÆ™washe shi a ka ya É—aga mata gira ya ce “Ni nasan ko niyyar gado ne ni, ko motsi lafiyayye ne wlh, kuma da kin faÉ—a mini komai I’ll fight don na aureki, I’ll fight for my love, zan iya sadaukarwar da komai just to be with you Sexy mama, ni nasan ban cancanta da ke ba, bani da qualities na mazan da suke so…,”
“Stop, bana so” Ta furta muryarta na rawa sosai ta kalle shi ta ce “Me ake buÆ™ata a zaman auren Man? So da Æ™aunar juna, yarda da amincewa, riÆ™e gaskiya da amana, kishin juna, kulawa, kyautatawa, i love you, and you love me too, ci, sha, sutura, magani duka kana bamu ka faÉ—a mini Qualities É—in da suka fi wannan?” Kallonta kawai yake without blinking,yana jin kansa wani daban Majeederh ta shafi fuskarsa zuwa gemunsa ta ce “The most important thing in your character is your honesty” Shi a ransa yake jin bai yarda ba kawai taimaka masa tayi da kuma Æ™arfa Æ™afan da ya yiwa rayuwarta “Are you sure?” “Yes, of course Aby-Alhassan” Ya kwaÉ“e fuska ya ce
“Ni ban so” Ta ce “Sai me?” Calmly yana saka idanunsa cikin nata ya ce “Say my name, ina son ji” Ta É—auke ido tana miÆ™ewa tsaye sai kuma ta juya sosai ta ce “I can’t” Ya miÆ™e tsaye shima yana riÆ™e Æ™ugu kamar yadda tayi yadda yake sakin jiki da iyalinsa ba zaka taÉ“a yarda yana da azababben miskilanci ba ya ce “Kina son É—aukawa kan ki zunubi, yanzu dai ki zaÉ“a” Ta juya Idanu alamar tana ji ya ce “Ko kice Ibrahim, ko yau a casar bugun dawar da zamuyi Kiyi riding nawa” Ta zare ido sai kuma ta yi saurin É—auke kanta ya juya ya kalleta sai kuma ya nufi waje ya ce “Zoki ban abinci”
Washegari da safe Khalil ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda gezner dark blue É—inkin jamper da babbar riga, bai saka hula ba sai sumar kansa daya É—aure zuwa Æ™asan wuya, bai saka babbar rigar ba ya bar iya half da wando hannunsa É—aya zube cikin Aljihu É—ayan kuma yana danna wayarsa da É—an sauri yake sakkowa daga kan steps É—in benen sumar kansa na tashi sbd iskar dake kaÉ—awa ta Main parlour, yana sakkowa Alhassan ya miÆ™e da sauri ya ce “Aby” Al’hussain ma ya miÆ™e baby khalil na tsaye gabaÉ—aya shaddar jikinsu iri É—aya ce, Baby Khalil ya fara miÆ™awa Abyn nasu hannu yana durÆ™usawa ya ce “Assalamu alaika Aby” Khalil ya amsa yana bashi side hug twins ma suka miÆ™a masa hannu har sun saba da gaisuwar musabaha, yana tsaye da yaran yana jin abubuwan da kowa ke cewa bugun zuciyarsa da ya ji ya sauya yana tafiya da sauri yasan she’s here, tana tsaye kuma shi take kallo ya É—ago kansa suka haÉ—a ido, farar lafaya ce a jikinta mai bala’in tsada ta kwanta jikinta sosai, ta É—aura wani siririn liÆ™ab hatta flat shoe É—in Æ™afarta fari ne, har wayar hannunta wacce Khalil ya sauya mata fari, gabaÉ—aya tayi shigar da Khalil ke so yana Æ™aunar farin abu, a fili ya furta “Allhamdulillah!” Ya yi saurin É—auke tunanin da yake sanda ya tuna azumi suke, ya sunkuya ya É—auki Al’hussain, Alhassan ya fara kuka ya ce duk kukansa ba zai É—auke shi ba wlh, yau mai halin matarsa zai É—auka Majeederh ta yi murmushi ta É—auki Alhassan tana rungume shi, a tare ita da Khalil suka kama hannun Baby Khalil, Alhassan ya ce “Baby” Khalil ya buÉ—e ido ya ce “What? Baby?” Ya juya ya kalli Majeederh ya ce “Mimi É—anki ake cewa Baby fa?” Ta ce “Haka suke faÉ—a, amma zasu koma faÉ—in Yaya K” Ya jinjina kai suna fita driver ya buÉ—e musu jibgegiyar mota yaran a tsakiya, Kspider da Jee suna baya, suna É—aukan hanya yaga tana buÉ—e Azkar a hankali ya ce “Ki faÉ—a a fili, I’ll repeat after u” Haka akai har suka nufi gidan Abbu, suna zuwa suka samu Aaliyyah da cikinta ya fara girma sosai suka gaisa da Mami Abbu kuma baya nan, kasancewar jirgi baya jira suka tafi gidan Uncle Bello tunda Uncle Isma’il ba kowa a gidan, Jawaad ya dawo gidan Uncle B da zama, Sona kuma tana gidan Abbu. Tun a Æ™ofa suka fara jiyo maganar Innati

“Ku kawo ruwa mai É—an iskan sanyi, ina Æ™ara Saa guda macewa zan yi, wannan azumin Allah ka yafe Ubangiji ka cika kabarina da gwala-gwalan lada Allah ka yafe mini zunnubaina, a bani ruwa ana taÉ“a cikina lotsewa zai Æ™waranÆ™wasa” “Karya azumi kuma?” A hargitse Innati ta ce “Waye wannan kamar ana tashin hankali zai shigo kai tsaye ba sallama?” Majeederh ta Æ™arasa shigowa ta zauna tana cewa “Ina yini Innati?” Innati tayi banza ta sake cewa “Ina yini?” Tana Æ™anÆ™ance Idanu ta ce “Ibro ka rabani da munafukar matarka, bani ba ita ni ta munafurta” Khalil dai na tsaye idanunsa zube akan majeederh shi har yanzu ya kasa fahimtar wanne kalar so yake mata? Innati ta miÆ™e tare da É—aukan kwano ta kwaÉ—awa Majeederh aka ta ce “Algunguma, irin wannan ranar nake jira gashi tazo, babu tashin hankalin da bamu gani ba akan bakya so da Æ™aunar Ibro” Majeederh ta runtse Idanunta cike da baÆ™in cikin kalamanta a baya kuma tayi nadama yanzu duk wanda ya furta haka ma haushinsa zata ji wallahi Innati ta ce “Ba dole ki runtse ido ba? Wannan azababbiyar Æ™aryar ta bugawa a jaridu a haÉ—a? Ina har Aljanu ki kayi wai Allah ya kashe Ibro ki huta, kika dinga suma kin tsane shi baki son shi? Yanzu ubanwa kika bajewa tika tiki ya Æ™unsa miki ciki? ÆŠan gwaninin yaron ko? Shi ne ya buga miki iska?” Majeederh ta rasa me zata ce sai kawai ta fashe da kukan takaicin Innati, Khalil ya dinga riÆ™e murmushin shi ya Æ™arasa kusa da matarsa yana bata side hug ya ce “To ke ina ruwanki ne? Idan ta tsane ni ina son ta ai?”

Innati ta fashe da matsanancin kuka hankali tashe ta ce “Asstagafirullah! Allah na tuba bana iya bacci idan na tuna a gidan nan aka bunka iska ta biyu, a gidan nan aka dinga lalata, bani da nutsuwa ana tsokala tsinke a kunnena wuta za a tsokano saboda tashin hankali” Uncle Bello da yake shigowa ya ce “Ibrahim ku tashi ku tafi kar ku yi missing Flight É—inku” Majeederh dai kuka take, Alhassan ya cika ya yi fam ya kafe Innati da ido, Baby Khalil ya kalli Abynsu ya ce “Aby mene buga iska?” A harzuÆ™e Innati ta ce “Ubanka Ibro shi ya bugawa babarka iska, ya Æ™unsa mata ciki wallahi tallahi” Da wani sauri Majeederh ta miÆ™e tana yin waje domin Uncle Isma’il ya ce har yanzu Alpha na asibiti kuma karta kuskura ta je, ta jima tsaye kafin taga Khalil ya fito shi da Jawaad da yaran tana ganinsa ta buÉ—e Æ™ofa ta shiga saboda wata matsananciyar kunya data lulluÉ“e mata jiki, bata taÉ“a jin kunyar mijin nata Dr Ibrahimul-khalil irin yau ba, bata son ma haÉ—a Idanu da shi, shigowa motar ya yi bayan ya saka yaran tana ganinsa ta rufe ido sarai ya ganta ya share, a haka suka nufi airport, Uncle Isma’il tuni ya sanya ayi masa binciken gidan su Zuleehart a can Ghana accra É—in. Zuwan su airport ba wahala bayan an musu komai passengers sun fara shiga, Khalil na sallama da John yaga wani ya tsaya kusa da Majeederh kallon su yake, a tsorace Majeederh take kallon mutumin fuska rufe ya miÆ™a mata envelope babba fara tas sai wani Æ™aramin rose dake maÆ™ale a jiki ta ce “Waye kai?” Ya ce “Sanin ko waye ni bashi da muhimmanci, domin bani ne wanda yake zuwa gareki ba, ni É—in Manzo ne, bi ma’ana É—an aike, Boss Ubangida shi ne wanda ya aiko ni…..,”
“Ok da kai da ubanka yake ko wa?” Khalil yama kasa Æ™arasa maganar ya nufi kan mutumin “Ni fa É—an aikene, ko a zamanin jahiliyya É—an aike baya laifi kuma..,” Wani mugun naushi da Khalil ya sauke mutumin shi ne ya hana shi Æ™arasa maganar, ya damÆ™i wuyansa tare da yi masa gware nan take jini ya É“alle, Alhassan me zai yi ba ihu ba yana tsalle yaga ubansa na faÉ—a, mutumin ya É—aga hannu ya ce “Ka saurare ni please, zan faÉ—a maka ko waye” Bai bashi damar magana ba ya damÆ™i hannun ya karya Ihun azaba ya saki da wani irin fitsarin wahala, ya ce “Ka tsaya ka ji” Khalil ya sake kaiwa bakinsa naushi haÆ™ori É—aya ya fita ya saka hannu ya zare ribbon É—in kansa a kausash ya ce “Bana buÆ™atar reasons, ka zama shaiÉ—an mai raba aure ko?” Ganin Khalil na Æ™oÆ™arin yin kisa yasa majeederh cewa “Man…,” Wata masifaffiyar tsawa ya daka mata tare dayi mata nuni ta kama yaran su nufi jirgi, polices É—in wajen suka tsaya domin babu wanda bai san waye Khalil ba, ya kalli mutumin ya ce “Kai kayi kaÉ—an wajen siyan soyayyar Matana, Ubangidan naka ya fito muyi gaba da gaba, zan tafi Saudiyya idan É—an halak ne shi cikin uwarsa da ubansa ya biyoni zuwa Palace ga i.d card nan” Yana faÉ—in hakan ya cilla masa I.d card ya nufi cikin jirgin bai yarda ya nufi wajen Jee ba domin sai yanzu yake jin nauyin tsawar da ya yi mata, yana shiga cikin jirgin mutumin ya nufi mota jiki jina jina da jini, yana shiga wanda ke cikin motar ya ajiye azkar É—in hannunsa ya ce “Sorry” Mutumin ya ce “Boss Ubangidana Akeeth ni zan baka haÆ™uri” A hankali Akeeth ya girgiza kai ya ce “Ka yankar mini ticket na zuwa Saudiyya now, I’ll follow him….
[10/12, 2:09 PM]

No comments