Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 53


Khalil na tsaye bakin Æ™ofa ya kasa É—aga kai ya kalli Ummie dake cewa “Me kayi mata?” Ya É—an marairaice ya ce “Ummie ba zan cutar da ita ba, matata ce..,” Tayi saurin É—aga masa hannu fuska a haÉ—e ta ce “Na san matarka ce, me ka yi mata? Jinin nan na jikinka na mene?” Kansa a Æ™asa ya ce “She is bleeding” A gaggauce Ummie ta nanata maganan a fili ta ce “Bleeding?” Kamar zaiyi kuka ya ce “Please ki fara dubata, kafin komai” Ta girgiza kai tare da murÉ—a handle É—in Ƙofar bedroom É—in ta shiga, idanunta ya sauk’a akan Majeederh dake durÆ™ushe fuskarta ta jiÆ™e da hawayen azaba, sai girgiza kai da yarfe hannu take, wani irin masifaffen ciwo ne yake karta mata a mararta zuwa cikinta, bayanta ya riÆ™e kamar mai naÆ™uda, zufa ta jiÆ™ata sosai tamkar wacce ta fito daga wanka. Ummie ta Æ™arasa tana kallonta ta ce “Daughter meke miki ciwo?” Majeederh ta kasa magana sai girgiza kai take tana cije baki, a hankali kuma cike da dauriyar data aro ta yaÉ“awa kanta cikin jarumta a fusge ta ce “Marata Ummie, cikina, bayana Innalillahi, i don’t want to lose my baby”
Ummie ta miÆ™e tana danna wayarta ta ce “Babu abinda zai faru, sannu kin ji?” Kai kawai ta samu zarafin É—agawa, Ummie ta kara wayar a kunnenta magana kaÉ—an tayi kana ta kashe, tana zaune kusa da Majeederh tana mata sannu wayarta tayi Æ™ara ta kalli Majeederh ta ce “The doctor is here” Sai kuma ta miÆ™e ta fita, not too long ta dawo tare da wata farar likita kasancewar babbar likita ce kuma Ummie ta faÉ—a mata condition É—in da Majeederh ke ciki ta taho da komai na buÆ™ata, injection ta fara yi mata na tsayawar jinin, kana ta mata gwaje-gwaje cikin ikon Allah zafin ya fara sauka jinin ya tsaya jikinta ya saki, Dr ta ce
“Ranki ya daÉ—e ta fara gyara jikinta zan sanya mata drip jikinta ba Æ™wari” Da taimakon Ummie Jee ta wanke jikinta ta sauya kaya, Ummie ta kama hannunta zuwa sashinta ta ce “Dr follow me” Drip aka sakawa majeederh da wata injection É—in (Allura) mai sauk’e zafin ciwo da sanya bacci (Pain reliever).

Bayan kammala komai Dr ta ce “Ina mijin nata? Ina buÆ™atar ganinsa urgently” Number shi Ummie ta kira yana É—agawa ta ce “Zo part É—ina” Suna zaune ya buÉ—e Æ™ofa ya shigo basu da tabbacin ya yi sallama ko akasin hakan ya É—an zauna saman kujera idanunsa akan Majeederh dake bacci tayi fayau, tayi wani irin kyau dan fuskarta har ta faÉ—a. Dr ta ce “Sir i need your attention” Khalil dai bai kalleta ba, Ummie tayi kamar bata san me ake cewa ba idanunta akan wayarta tana dannawa. Dr ta sake kallon Khalil ta ce “Ni zaka kalla ba matarka ba, ba ta dalilinka ta samu wannan ciwon ba? Ko a matsayinka na likita baka sani ba?, wai ma menene amfanin kasancewarka likitan? Tunda baka san matsayin matarka ba idan tana da ciki, ko kuma kaga wani sauyi a jikinta ka tsaya ka duba duk mene….,” A gigice Khalil ya ce “Stop, enough pls” Ummie waya take dannawa, amma kamar ta yi wa Khalil dariya ko bata kalle shi ba, tasan tambayoyin na Dr sun masa yawa surutun kuma hawar masa kai yake, a hankali ta kalle shi taga duk jijiyoyin kansa sun fito sun yi É—oÉ—ar a saman goshinsa idanunsa jajur.
“Ki faÉ—a mini me Zaki faÉ—a, kina juya mini kai!” Dr ta yi ta kallon shi kafin ta miÆ™a masa paper É—in hannunta ta ce “A binciken da mukayi cikin jikinta bai fi wata biyu ba, yana cikin gaÉ“a ta haÉ—ari kuma akwai rauni a bakin mahaifarta, yanzu Alhamdulillah mun samu nasarar tsayar da jinin dama cikin bakiÉ—aya” Khalil ya sauk’e É“oyayyiyar ajiyar zuciya jin unborn É—insa yana lafiya, ya lumshe idanunsa yana hamdala ga Ubangiji Dr ta ce “Ya kamata ka É—auk’e mata Æ™afa, ka bata hutu akan gado domin tsananin takurarka ya jawo haka” Dr Khalil ya kalli likitan ya mayar da kansa kan fuskar Majeederh calmly ya ce “Yadda Daddy bai zama silar zubar cikina ba, nima ba zan zama silar zubar cikin Matana ba” Ummie ta tsaya da abinda take jin Khalil yau ya ambaci mahaifinsa kenan all this years tunanin mahaifinsa na ransa ko me? Son baban nasa yake?
“Khalil!” Ummie ta kira shi bai kalleta ba ya sauke kai Æ™asa ranta ya É“aci sosai sai bata nuna masa ba, Dr tayi murmushi tana jinjina Æ™arfin hali da zuciyar Khalil É—in a hankali ta ce
“Bana nufin haka, abubuwa da yawa suna causing miscarriage kamar su; Matsalar sinadarin halittar jariri wannan matsala ce wacce ake samu tun kafin halittar ÆŠan Adam ana kiran sa (fatal genetic problems). Infection sanyin mata wanda yake sa Æ™aiÆ™ayin gaba, zuban farin abu, ciwon mara da ciwon baya. Sai kuma
Yin aikin ƙarfi: Yin aikin ƙarfi wanda ya wuce misali na daga cikin abubuwan da yake kawo zubewar cikin. Da kuma
Rashin lafiya: Dukkan rashin lafiya mai zuwa da matsanancin zazzaÉ“i ya kan iya haifar da yin É“ari”

Dr ta É—an yi shiru tana kallon yanayin Khalil bata da tabbacin yana jinta ma, domin hankalinsa gabaÉ—aya yana kan Majeederh da yaga tana É—an É“ata fuska a cikin É“acin nata, sosai ya ji sanda take cewa “Cikina marata” Sai ya yi tunanin gajiya tayi zata gudu, gefe guda na zuciyarsa kuma yana jin tunda suke bata taÉ“a nuna masa gazawa ko ragwanta ta wannan bangaren ba, tana Æ™oÆ™ari da duk irin yanayinsa wanda hakan ke Æ™ara sawa ya sota fiye da ko wanne lokaci Likitan ta ce “Shan magunguna:Shaye-shaye magunguna ba bisa Æ™a’ida ba, inma na Hausa ko na bature yana kawo zubewar ciki. Sai kuma
Nakasar maniyyi: samun nakasar maniyyin miji ko ƙwan mace ya kan iya haifar da zubewar ciki.
Matsalar bakin mahaifa: Idan mace tana da matsalar bakin mahaifa shima cikin ba zai zauna ba” Khalil ya dakatar da ita da cewa “Oh kina nufin cikin Matana ba zai zauna ba?” Dr ta ce “A’a, ban ce haka ba ina lissafa maka abubuwan da suke haifar da irin halinda matarka ta tsinci kanta ne” Ya girgiza kai kawai yana rufe Idanu, Ummie ta lura Khalil ya raina Dr É—in gabaÉ—aya Already ya san abubuwan da take zayyana masa É—in “Matsalar thyroids ciwon sugar hawan jini rashin ishasshen abinci rashin jini, shan sigari, suma duka suna haifar da zubewar ciki, idan mace nada ciki ga abubuwan daya dace ta rage yi, Jima’i, aikin Æ™arfi, kada tasha ko wanne magani, ta dinga ziyarar asibiti akai akai domin tabbatar da lafiyarta dana babyn” Ta kalle shi ta ce “Matarka akwai abinda ya É“ata mata rai wanda ya haifar da tashin hawan jininta, tayi tafiya mai É—an tsayi kamar ta mota ko jirgi,bayan nan ta jijjiga jikinta for sure, sannan kazo ka É—ora mata da wannan fitinar naka, na rubutu mata some drugs bayan nan kana dubata ka bata tazarar a Æ™alla wata huÉ—u cif kafin ka sake kusantar ta”
Khalil ya miÆ™e tare da ficewa yana jan tsaki a fili wai wata huÉ—u kamar wani nakashasshe? Shi burinsa ma ya É—auke matarsa ya lallasheta ya kuma dubata da kansa, amma bashi da zarafin hakan saboda kaifin Idanun Ummie. Tun ranar Ummie ta raba musu kwana tsakaninsa da Majeederh wajen suhur ne kawai ko buÉ—e baki, babu abinda ke damun Khalil tun yana Æ™arami amma yanzu dalilin Majeederh rauninsa ya fito Æ™arara a fuska sai ya daina ma yin suhur É—in buÉ—e bakin ma ya daina, daga Æ™arshe bashi da wajen zuwa sai masallacin Æ™a’aba ya yi ta addu’a da neman yafiyar Ubangiji akan abubuwan da ya yi na baya, hakan nan ya samu kansa da yiwa Daddy addu’a duk da cewa shi É—in ba musulmi bane da kuma Fulani wacce itama ta kasance uwa a gare shi. Ya hau yin fushin gaske da Majeederh ko waya ta kira shi baya É—auka, ta rasa ya zata yi a haka har azumi ya shiga ashirin.

Tana zaune Ƙhulud Arzaan na kusa da ita ta ce “Wai kam lafiya kwana biyu Khalil baya zama?” Majeederh ta É—an yi murmushi sau ta ce “Lokacin ibada, waye zai yi sake da wannan lokacin? Musamman da zamu shiga ranaku mafi girma?” Ƙhulud ta ce “Haka ne, Ubangiji ya amshi ibadunmu ya sanya ba mu yi k’ishirwar banza ba” A hankali ta ce “Amin” Fatymerh Clara dake jinsu ta ce “Ni kam Kspider yana dariya don Allah?” Majeederh ta watsa mata harara ta ce “Me kike nufi?”
“Ina nufin kamar kema baya miki dry, za kiga ko hira ake ya yi ta yin tsaki kenan, fuska a haÉ—e kullum ga É—an banzan isa da gadara miskilancin jaraba, sai zuciya kamar kuturu”
Majeederh ta riÆ™e haÉ“a ta ce “Au haba? Yayan naki kike faÉ—awa haka?” Da sauri Clara ta ce “Waye yayan? Ai ki tambayi Ummie ni ta fara haifa kafin shi ya biyo bayana”
Daga bakin Æ™ofa aka ce “Ita Ummie ta ce haka?” Suka juya gabaÉ—aya banda Majeederh yana tsaye gabjeje da shi a bakin Æ™ofa jallabiya ce a jikinsa sai hiramin daya É—aura a saman kyakkyawar sumar shi, fuska a kame ba walwala ya kafe Clara da kallo
“Ni bance Ummie ta ce haka ba, amma ko Daddy za’a tambaya ya san ni ce babba” A hankali yana shigowa daidai nan Ummie da Mai martaba Ajlaal Sultaan suka fito Khalil ya ce “Opps je ki lahira ki tambayo ok” Jikin Clara ya yi sanyi hawaye ya cika idanunta, tasan Daddy ya É“ata mata rayuwa amma ya sota fiye da komai ya bata kulawa da jin daÉ—i tattali da soyayya. Shi kansa Idanunsa sun yi jajur ya dubi Ummie ya ce “I got a message on my email from Latifa” Ya faÉ—a mata haÉ—uwar Latifa da Mr President da kuma musuluntar shi sai neman yafiyar da yake wajen su da ita kanta Ummie, ya shaida mata su Latifa sun kuÉ“uta ne a wani daji da jami’an tsaro suka kama motar daga nan ko wacce ta tafi garin su, yanzu haka tana gidan mijinta Aliyu zaman ba yabo ba fallasa. Ummie bata ce komai ba ta juya tare da barin wajen, Khalil ya shige part É—insu ko Majeederh bai kalla ba duk da tsananin kewarta da yakeyi yana jin kamar ya jawota ya rungume ya fahimci da sauranta. MiÆ™ewa ta yi tare da kiran number shi sai da ta yi kira huÉ—u kafin ya É—auka, ya yi shiru a hankali kamar zata yi kuka ta ce “Man” Ya ce “Kirani da Ibrahim ko Khalil Hawwa’u, tunda baki san darajata ba” Idanunta ya yi rau rau “Ni kuma?”
“A’a ni, faÉ—a mini dalilin kiran zan kwanta ne” hawayen da take riÆ™ewa ya Æ™wace ta ce “You ignored me, bana jin daÉ—i” Ya yi mata shiru kawai sai ta fashe da kuka, ya yi saurin runtse idanunsa zuciyarsa na bugawa da Æ™arfi wato tasan menene rauninsa? His weakness! Ta jima tana rera masa kukan kafin ya ce “Kiyima kanki Æ™iyamullaili, ko wacce mace tana neman lada a wajen mijinta da azumin nan amma ke ana hanaki? Kin dage kina É—aukar zunubi aljannarki na Æ™afata fa?” Tana shassheÆ™ar kuka ta ce “Ummie ce, i am sorry” Kamar zai mata ihu sai kuma ya yi Æ™asa da muryarsa ya ce
“Ummie! Ita Ummie aure ne da ita yanzu kin san me take na samun lada a waje? Kin faÉ—a mata wajen mijinki zaki?” Majeederh ta marairaice fuska ta ce “Taya zan faÉ—a mata haka Man?” Siririn tsaki ya ja sanda zai kashe wayar yana ji ta sake fashewa da kuka, a daren bacci baiga idanun Majeederh ba, ta sake kiran number Khalil a kashe. Ita kaÉ—ai ce a bedroom É—in bata san ina Ummie ta yi ba, ta rufe Idanunta a haka bacci ya fara fisgarta, can cikin baccin ta ji an rungumeta da kyau tana kwance male male a Æ™irjin mutum yana shafa sumar kanta a nutse, a hankali ta buÉ—e Idanunta tare da yin motsi, ya sake shigar da ita jikinsa da kyau muryarta na rawa alamar taci kuka ta ce “I am sorry..,”
“Its my fault, sorry wifey”
Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya a hankali tare da sake shigewa jikinsa, daidai kunnenta yana sauke numfashi ya ce “Kina da laifi ina da shi, nawa babba ne forgive me, forgive your husband Khalil” Ta yi murmushi tana shafa Æ™irjinsa ta ce “Bakai mini laifi ba, kuma ba zaka yi mini ba Love” Ya matseta tsam! Tsigar jikinsa na tashi Æ™ofofin gashinsa na buÉ—ewa abubuwan da yawa suna masa yawa, komai na jikinsa ya bubbuÉ—e “I miss you!”.
Clamly ya ce “I see” LaÉ“É“anta yake ta kallo sai kuma ya É—auke idanunsa gently ta kamo fuskarsa ya yi saurin matsawa ya ce “No please ba wannan ya kawo ni ba” Ta hararesa yana Æ™oÆ™arin magana ta haÉ—e bakinsu waje guda, daga ita harshi sukai loosing control sama sama suka ji ana “Aby.. Aby.. Mimi Mimi nina” Da sauri Khalil ya zame jikinsa daga na Majeederh yana gyara zaman rigar ya juya Allah yasa hasken a kashe yake idanunsa ya sauka akan Alhassan dake zaune saman window ya hauro yana Æ™oÆ™arin dirgowa cikin bedroom É—in, Khalil ya yi sak wato sanda yake haurowa bedroom É—in Ummie Alhassan ya ganshi? Ya nufi wajan Alhassan yana zuwa wajensa ya kawo kai wai suyi gware Khalil ya riÆ™e Æ™ugu, Alhassan ya yi murmushi yana lumshe idanunsa wannan shi ake kira da abin cikin Æ™wan ya fi Æ™wan, gado mai wahala hali zanen dutse shi da kansa ya san cewa Alhassan suffar shi ne, ya saka ya É—auki yaron yana saÉ“a shi a kafaÉ—a ta gefen ido Majeederh ta dinga dariya Æ™asa Æ™asa. Azumi na ashirin da biyar suna zaune a parlour bakiÉ—aya ana tattaunawa akan yadda za a yi sallah da hawa Khalil baya cewa komai idanunsa rufe duk a takure yake bai saba zama waje guda ba,sallama aka yi gabaÉ—aya suka kalli mutumin kafin kuma Majeederh ta miÆ™e ta ce “Uncle?” Uncle Ismail ya yi mata tattausan murmushi kana ya ce “Bani É—aya bane” Ta ce “Da waye? Uncle B? Abbu?” Ya girgiza kai ya ce “Mr no name…
[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *NIMCYLUV*

*_MIJIN MALAMA_*
Book 2 page 107
Final Episode

ArewaBooks: Nimcyluv
Okadabooks: Nimcyluv
Wattpad: Nimcyluv
Facebook: Na’ima Sulaiman Sarauta
Both Twitter and Instagram.
08119237616.

No comments