Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 55


[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: Majeederh na Æ™oÆ™arin ambatar sunan “Mr No name” Da Uncle Isma’il ya furta ta ji ya ce “Yana Æ™ofa ai, izini yake nema a cewar shi ni É—an gida ne dole zan iya shigowa duk da cewa shima zuwan nasa akwai babban dalili” Ta kasa magana ganin Khalil ya miÆ™e yana nufar Æ™ofa tasan halinsa daman kuma yau mulki yake ji da shi tunda ya zauna ko cikakken tari baiyi ba, balle magana, ba zaka ce yana wajen bama, hango shi yayi a tsaye sai dai ya juya masa baya, hannu ya dunÆ™ule da nufin kaiwa Æ™eyarsa naushi yaga ya juyo Khalil ya ware fitinannun idanunsa yana kallon Akeeth laÉ“É“ansa na rawa wajen furta “Uncle Akeeth? You? Mr no name” Akeeth ya yi murmushi ya ce “Yes, ni ne ranar wanka ba a É“oye cibi Dr Ibrahimul-khalil, ka ce idan ni É—an halak ne na biyoka so I’m here don na tabbatar da cewa É—an halak É—in ne…,”
“Kana son rabani da matata why?” Khalil idanunsa rufe yake maganar yana dunÆ™ule hannunsa saboda ba zai iya dukan Akeeth ba, ya masa halarci a rayuwa Akeeth ya ce “Muje ciki, ba zuwa kuma na yi domin na rabaku ba, i am here to ask of your forgiveness friend” wata É“oyayyiyar ajiyar zuciya khalil ya sauke ba tare da ya yi magana ba suka shiga ciki, Mai martaba Ajlaal Sultaan ya miÆ™e ya rungume Akeeth ya ce “Marhaban bika ya Ahki” Ajlaal da Akeeth abokai ne sosai,suka zauna, mamaki ya hana Majeederh motsi, kenan Akeeth shike bibiyarta da sunan Mr no name? Yake son lalata mata rayuwa haka kurum? Da farin cikin aurenta? Me ta yi masa idan ta fahimta dalilin daya kawo shi gidan t.v Arewa24 kenan? (Wonders shall never end). Abin mamaki baya Æ™are wa.

“Dr Khalil, Malama Majeederh na san na É“ata muku amma ni kai na ban jima da fahimtar kuskurena ba sai kwanan nan, Allah ya gani ina son Majeederh so bana wasa ba, tun kina kawo Khalil wajena gidan marayun nan Matsayin Little É—inki, ban san menene ya hanani tun kararki ba, a ranar da jarrabawa ta sameki kika haihu a sannan na faÉ—i a sume na yi jinya kafin na dawo daidai na samu labarin aurenki da Tsohon Gwamna Abuturab, bayan nan kuma na samu labarin kin auri Khalil, na kasa jurewa wannan Æ™addarar hakan yasa na dinga bibiyarki da sunan Mr no name, burina wai ko hakan zai sanya Khalil sakinki na aura, amma kamar Æ™ara muku fahimtar juna ake, duk da cewa ko tsakanin harshe da haÆ™ori ana saÉ“awa, yanzu na fahimci ban kyauta ba, idan zan kashe aure to zan iya kashe mutum kuma na raunata zuciyarku ne, al’amarin shafin soyayyarku ko Romie da Juliet zasu shafa muku lafiya, bambancinku da Layler da Majnoon kaÉ—an ne, shi ne Khalil bai haukace ba saÉ“anin Æ™ais, Majeederh na raye bata mutu ba saÉ“anin Layler, mai zai sanya na raba wannan zuciyoyin? Lallai Ubangiji ba zai barni ba dole zunubaina su zama jarrabawa a gareni, na yarda ita É—in ba rabona ba ce, she’ll just be my first love and my destiny” Ya yi shiru sai kuma ya kalle su da kyau
“I am sorry, i knew I made a mistake nayi shirme na cika mai son zuciya, kuma faÉ—in Allah da Manzonsa ne; ka so wa É—an uwanka abinda ka so wa kanka, Dr Khalil ka yi haÆ™uri ka yafe mini don Allah, and you too Malama Majeederh” Majeederh ta kalli Miskilin mijin nata kamar yadda tayi zato waya yake dannawa abinsa, tana so tayi magana bata son damuwar shi
“Don Allah Khalil, ba zan samu nutsuwa a zuciyata ba idan baka yafe mini ba, ni da kaina, nasan na yi kuskure” A taÆ™aice Khalil ya ce “It’s okay” Akeeth ya gane ya yafe kawai faÉ—a ne ba zaiyi ba, ya ce “Saura ke Malama” Khalil ya miÆ™e tsaye yana kame fuska ba walwala ya ce “Yafiyarta kake so ko muryarta kake son ji?” Idanunsa zube akan Akeeth ba shakka a jikinsa ya yi maganar can ya É—an buÉ—e kafaÉ—a ya ce “Idan yafiya ne an yafe” Yana faÉ—in hakan ya yi gaba tare da cewa “Madam kawo mini Mac book” Ta miÆ™e tabi bayansa Uncle Isma’il ya bisu da kallo cike da burgewa ganin yadda Khalil ke nuna son matarsa da kishinta a gaban kowa. Gaisawa suka shiga yi Ummie ko inda Uncle Isma’il yake bata kalla ba, shi kuma kamar maye sai binta yake da kallo zuciyarsa a bubbuÉ—e da sabon yanayi. Bayan ansha ruwa Fatymerh ta kaiwa Akeeth kayan buÉ—e baki tana Æ™oÆ™arin tafiya ya ce “Zahraah” Ta yi cak sunan ya soki zuciyarta tunda daman an mata bayani akan sunan FaÉ—imatu ta juya ta kalle shi, a hankali ta ce “Kana son wani abu ne?” Akeeth ya É—an langwaÉ“ar da kansa ya ce
“Are you going to leave me?” Ta kasa cewa komai ya É—an sauke murya ya ce “Zauna, let’s eat together, ki fanshi Nene” Ta kasa yi masa musu saboda Æ™wayar idanun Akeeth akwai wasu abubuwa na ban mamaki. Maimakon ya É—auki spoon sai taga ya wanke hannu a bowl tare da saka yatsu ya fara cin abincin yana kai na biyu ya ce “Identify yourself” Tayi shiru shi kuma ya ce “Ni ga sunana kin gani, ina tare da Nene (My mother), bana da wa ko Æ™ani, i lost my Papa when i was little, so Nene ta fanshe shi na yi karatu sosai, Nene cikakkiyar Hausa ce babana kuma Yoruba ne, so na kan É—an juye Yarabawa some times, Business man ne kamfanin takalmi bag shoes kai many things, bana É—aukan raini but i am friendly to everyone, i am simple like 1,2,3… kuma difficult to understand, I love sakwara da miyan egusi ina son nama sosai”

“Ohho, that’s nice”
Fatymerh ta ce tana lumshe sexy eyes É—inta, hakan ya Æ™ara jirkita zuciyar Akeeth Yoruba demon ya motsa daman su basu da kunya akan Soyayya ya kasa cin abincin ya ce “Yanzu kuma ina son kiyi replacing Nene, kin ji Fatymerh Zarahh?” A hankali ta ce “Ina Saudiyya kana Naija? Taya zanyi replacing?” Calmly ya ce “By marring me” Ta waro idanunta sosai akansa sai kuma ta É—auke kai, ya ce “Don Allah don Annabi karki ce a’a, say Yes Dear karki raunata zuciyar marayan Allah” Ta haÉ—e fuska ta ce “Yanzu ka ce wata ce Destiny naka? Kuma first love” Akeeth ya ce “Na tuba, na bi Allah da Manzonsa da Nene na biki” Ta miÆ™e zata fice ya yi saurin kamota yana dawo da ita jikinsa duk a rikice yake da sauri kuma ya saketa yana cewa “Aahh.. Asstagafirullah i am sorry” Bata amsa ba ya ce “Jeki, kina cigaba da zama a nan da matsala we’ll talk on phone” Ita mamaki ma yake bata wallahi ta juya tare da barin parlourn.
Ummie na Æ™oÆ™arin fitowa daga Æ™ofa zuwa waje domin fita Masallaci suka ci karo da Uncle Isma’il ya yi saurin ja baya, yana cewa “Afuwan, ban kula ba” Idanu kawai ta É—an zuba masa kafin ta É—auke ido ba tare data tanka ba ta nemi shigewa ya yi saurin cewa “Ina son magana dake ki bani dama” Ta sake kallonsa fuska a haÉ—e domin taga take taken shi, kamar za ta yi magana sai kuma ta shige, tun daga ranar kullum Uncle Isma’il sai ya takura Ummie, dake daman oumara yazo sai ya fara zaman palace gabaÉ—aya ba wanda bai fahimci Uncle Isma’il ba, Gimbiya ta tattara shi ta watsar a gefe.
Ana washegarin sallah Majeederh ta sha Æ™unshi bini bini Khalil sai ya kama hannunta ya tsura masa ido da sun haÉ—a ido sai ya marairaice ya ce “Da gayya ki kayi” ta ce “Kamarya?” A hankali ya sake damÆ™e hannun kamar yana so ya zura yatsun a bakisa ya ce “Ina so, nawa ne farashin?” Ta kwanta saman cinyarsa tana wasa ya Æ™irjinsa ta ce “Bazaka iya biya ba” Ya buÉ—e gajiyayyun idanunsa sosai ya ce “FaÉ—i kawai”
“Ka rayu dani, har zuwa numfashin Æ™arshe bana son kishiya ba zan iya jure ganinka da wata mace ba a duniya Man” Ya yi zuru yana kallonta sai kawai ta fashe da kuka ta ce “Farashin ya yi girma ko?” Ya jinjina kai ya ce “Gaskiya, sauya wani dai” Ta ce “Oh aure zaka Æ™ara?” Ya girgiza kai ya ce “Bana ce ba”

“Ba zaka sake aure ba?”
Still ya sake girgiza mata kai ya ce “Bana ce ba” Ta kai Æ™arshe wasu hawayen na bin Æ™uncinta ta ce “What do you mean by that?” Ya kashe ido ya ce “My jealous cat, bani da tabbaci ne zan Æ™ara ko a’a” Majeederh ta sake fashewa da kuka tana shagwaÉ“e fuska ya yi saurin rungumeta ya ce “Mijin mace É—aya kike so na zama? Ko mijin ta ce, ko kafin ta ce?” Ta yi shiru bata kula shi ba, ya sake matseta a Æ™irjinsa ya ce “Kin Isheni daga nan duniya har jannatul fir’daus, you’re my one and only wife” Ta Æ™anÆ™ame shi tana sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce “Wallahi Khalil mutuwa zan yi idan na ganka da wata na tabbata” Ya yi mata dariya ce “Ni mutuwa na yi da ake ta tururuwa a kan ki? Jee” Ta kwantar da kanta a Æ™irjinsa bugun zuciyarta na Æ™aruwa daidai kunnenta ya ce “You are a gift from God, kin wadata ni da komai musamman a…..,” Ya raÉ—a mata a kunne tayi saurin rufe ido tana cewa “Uhm uhm ni dai!” A hankali ya furta “Hawwa’u” Ta É—ago kai da sauri ta kalle shi cike da tsoron jin sunanta ya ce “I love you, i so much love you Sexy mama” A tare suka rungume juna cike da soyayya.
Uncle Isma’il na zaune idanunsa akan Ummie dake duba Alkyabbar da aka kawo mata ya juya ya kalli Majeederh ya ce “Hawwa’u na je Gombe, Hajiya Luba ta faÉ—a mini dukkan abinda tayi muku ke da mahaifinki, abinda ya shige ya shige ba sai na faÉ—a miki ba domin hakan zai iya Æ™ara rusa farin cikin da kike ciki, halin data tsinci kanta kaÉ—ai abin tausayi ne, ta gane yawon gidan boka bashi da wani amfani ko rana, ita data dogara da shi gata nan cikin wuta, domin babban tashin hankali ne ace mutum ya rasa Æ™afa ga tsutsotsin da suke bi mata al’aura, zuwa gidan boka sallar kwana 40 bata karÉ“uwa balle ka yarda da abinda ya ce? Ke da kika dogara da Allah ki kai imani da shi ba gashi kina cikin kwanciyar hankali ba? Idan ba labari aka bayar ba waye zai ce wata Æ™addara ta faÉ—a miki? Shi yasa ake cewa watarana sai labari, don Allah don Annabi taci albarkacin Sona da Jawaad ki yafe mata please” Majeederh ta girgiza kai ta ce “Na yafe mata, wallahi na jima da yafe mata duniya da lahira” Uncle Isma’il ya yi murmushi ya ce “Alhamdulillah, Ubangiji ya albarkaci aurenki da zuciyarki ya ci-gaba da baku kwanciyar hankali na har abada” Ta yi shiru Ƙhulud ta ce “Amin” Ummie dai ko tari ba ta yi, sabgar gabanta kawai takeyi hankali kwance.
Ranar daya kama É—aya ga watan Sha’aban dubban jama’a suka halacci masallacin idi, Dr Khalil ya fita cikin wata fitinanniyyar Alkyabba milk mai yafin golden idan ka ganshi zaka É—auka shi ne sarkin Makka gabaÉ—aya, a hankali yake fitowa idanunsa lumshe bakinsa na motsawa ana zikirin tafiya masallaci, Alhassan da Al’hussain da Yaa K gabaÉ—aya sun saka Alkyabba Ummie ta ce “Mene haka?” Ya buÉ—e ido alamar me? Ta nuna kayan jikinsa ya kwaÉ“e fuska bai ce komai ba a karo na farko tayi dariya mai gamsarwa akan idanun Uncle Isma’il hakan ya Æ™ara gigita shi ta ce “Ibrahim kenan, ai sarauta ke zaÉ“ar mutum ba shi ke zaÉ“ar ta ba” Shi dai ya yi shiru, ya nufi bedroom ya samu Majeederh na tsaye ta saka haÉ—aÉ—É—an farin lace mai manyan zane É—inkin Buba ta kafa É—auri ture kaga tsiya sai baza Ƙamshin da ya yi masifar missing take, jin Æ™amshin perfume É—in Boadicea The Victorious ya tabbatar mata shi ne ta juya suka haÉ—a ido kallonta kawai yake ya kasa magana sai kawai ya juya. Ana idar da sallah Khalil yaga an cika a fada kuma an kira shi wai ashe Mai martaba Ajlaal Sultaan ne ya yi murabus saboda baya da cikakkiyar lafiya, Rohaan baya sha’awar sarauta shi ne ake Æ™oÆ™arin sanya sunan Khalil matsayin wanda zai zama sarkin Makka, ai kuwa ya rufe ido ya ce bai san wannan ba, ya dinga surfa bala’i a ranar har Ummie ido kawai ta saka masa, ya gaji ya yi shiru ba wanda ya kula shi aka sanya ranar naÉ—a shi wanda yake daidai da cikar Edd É—in Majeederh, Mijin Malama ya ce garin ma zai bari ya koma Naija daman duk a wahale yake a nan. Kafin tafiyar Akeeth suka daidaita da Fatymerh soyayya suke sosai ya gabatar da kansa kuma aka bashi Ita, Uncle Isma’il ya nema ma Jawaad auren Zizi shi ma aka bashi.
Khalil na zaune ya rasa inda zai saka kansa don farin ciki, Mami ta ce “Allah ya shirya ka Khalil, kwana shida da haihuwa gobe suna amma kamar yanzu aka haihu? Ko kunyar idanunmu baka ji? To kwashe yaran naka kayi gaba” Khalil ya shafa kansa idanunsa zube akan tagwaye yaran nasa mata, babu inda suka bar matarsa Mimi kuma Malama Majeederh, soyayyar duniya ya É—orata akan yaran da suka kasance mata, Majeederh ita kunya ma yake bata Aaliyyah dake riÆ™e da Baby boy É—inta mai sunan kakansa mahaifin Barrister Aliyu wato Sufyan ta ce “Ni matsalar ma yadda ba kunya yake Æ™anÆ™ame matarsa a idanunmu, kai dai baka data surukai” Khalil ya juya ya kalleta sai ya ce “Bani da ita wallahi, kuma na fi lusarin mijinki, jinin Ibrahimul-khalil daban yake ki duba haihuwata ta farko tagwaye, Alhassan da Al’hussain, yanzu a ta biyu ma tawaye ne Noha da Soha, Ma’ana Gimbiya da Fulani” Aaliyyah ta riÆ™e baki ta ce “Au kai ka haihu ma?” Ya É—age mata gira ya ce “Yes, saboda ni ne mijin Malama, malama kuma tawa ce menene bambancin wanda ya bada ciki da wanda ya haihu?” Da sauri Mami ta É—aga waya tana karawa a kunne cike da kunya ta ce “Hello magana kike ok gani nan..” Majeederh ta yi murmushi kawai domin tasan halin mijinta sak abinda zuciyarsa ta raya masa yake faÉ—a sai dai haÆ™uri, shi yasa kafin ya yi magana zai daÉ—e. Aaliyyah tayi sak ta juya tana kallon Innati dake firfita hankali tashe ta ce “Innati lafiya?” A gigice Innati tana fashewa da kuka ta ce “Gobara ake a kunnena, buÉ—e firiza ki É—akko mini ruwa mai É—an iskan sanyi idan da Æ™anÆ™ara mai kwantar da tashin hankalin ki haÉ—o, batsa Æ™arara” Ta Æ™ara fashewa da kuka tana girgiza ta ce “Wallahi tallahi batsa ce wannan yanzu don Allah meye yin ciki kuma? Kamar wani É—an iska?…..

No comments