Breaking News

Munayamaleek 14


 MunayaMaleek

 

https://whatsapp.com/channel/0029Va5o0Gc4o7qU8MCJuN32

 

https://www.facebook.com/groups/1346404966270527/?ref=share_group_link

 

Xiv…..
(14)

 

Jingine take jikin bango, yayin da idanun ta ke kallon sama, tsayuwar Mota taji a kofar gida, da ba dan doctor Abbas bai jima da tafiya ba, da ta ce shine ya zo, waka ta ji yana tashi sosai, wanda take kyautata zaton Wanda ke motar ne ya sanya, Wani Irin emptiness da kewa ke kara shigar ta sakamakon wakar dake fita slowly, tausayin kanta ya ƙara kamata, a hankali bakin ta ya fara motsawa cikin bin wakar, hawaye na sintiri a fuskar ta, kwarai wakar ya ƙara fama mata ciwon da bata san Ranar warkewar sa ba.

_im so lonely broken an angel_梁

_im so lonely listening to my heart_❤️

_One and only broken an Angel_

_Come and save me before i fall apart_ 凉

_im so lonely broken an angel, I’m so lonely listening to my heart_紐‍♀️

Haka ta cigaba ta rera wakar, daga baya karfin sauti na wakar na ƙara raguwa har ta daina ji da alama mai motar ya tafi ne, hawayen bai bar zuba ba, Kyakkyawar fuskar ta ya kara ramewa sakamakon damuwar da take ciki, duk wanda ya ganta cikin wanna halin dole ya tausaya Mata domin maraicin ta ya fito muraran a tare da ita, haka zalika rayuwa ita kadai a cikin gidan ke kara sanya mata damuwa, domin in dai ba doctor Abbas bane yazo, takanyi kwanaki ba tare da ta furta ko da “a” ba, a yau ta tashi da matukar kewar Amnah da Umma, bayan sallar asuba tayi kuka mai tarin yawa kana ta roki Allah ya yafe mata zunubin da ta aikata, tun asuba har kowa yanzu bata dawo daidai ba, Dama rabon ta da walwala tun ranar data rasa abubuwa biyu masu matukar muhimmanci a tare da ita, dan zabura tayi a lokacin data ji tamkar abu ya karci fatar marar ta daga ta ciki, ta mike tana kallon cikin ta a tsorace, domin tunda ta san ta samu ciki bai taba motsi ba sai yau dinan, can taji motsin ya karu tamkar kifi na wasa cikin ruwa ko tace kadangare, tsoron ta ya karu, har tasa hannu ta daki gefen cikin, abin mamaki kuma sai ya daina motsin, hannun ta dafe da cikin still taji inda ta dafe din yayi tauri, taji cikin na bada wani irin abu tamkar ana kyankyasan abu, ta kuma ji kamar ana hurawa, ta rasa yanda zata fasalta wanna abin da take ji, rikicewar data yi ba a maganar sa, ta sulale kasa cikin rashin sanin abin yi.

***

*Doctor Abbas*

Tsaye yake a bedroom din dakin sa, yana gyara kwalar long sleeve shirt din daya sanya, bayan ya gyara ya taje sumar sa da bai fiye yawa ba, ya kai hannu ya dauki turaren sa, har zai fesa wata murya daga can kasan zuciyar yace “Munaya bata so, remember?” and he dropped the perfume, ya saki wani irin murmushi da shi kadai ya san ma’anar sa, yana tuna yanda munaya ke kwarara amai a ranar nan, and that hurt’s him so much ganin karamar yarinya na shan wuyar rayuwa haka, sai daya tabbatar baya kamshin komai, domin a matsayin sa na likita ya san ba kowace Mace mai ciki ke kaunar jin kamshin turare ba, and Munaya is one of them, car key ya dauka kana ya bar gidan.

Mintuna ashirin kacal ya kawo shi kofar gidan su Munaya, ya yi tsayen mintuna biyar kana wani yaro yazo gifta shi, cikin sauri yace “Ammmm abokina ji mana” Yaron ya dawo da baya yana kallon shi
“Dan Allah shiga gidan nan kace Munaya tazo”

“Toh” yaron yace ya nufi cikin gidan da gudu, sai dai a soro ya tsaya sakamakon duhun daya gani, ya daga murya sosai yace “an ce Munaya tazo inji wani mai mota a waje” daga haka yaron ya fito not minding an ji ko ba a ji ba, shi kam bazai iya shiga cikin duhun da ko tafin hannun sa baya iya gani ba.
Doctor Abbas ya zaro dubu ɗaya sabo fil daga aljihun sa ya bawa yaron bayan ya fito.

Munaya dake zaune a tsakar gida cikin duhu ta ji saukar Muryar yaron, ta san ba Kowa bane fa ce doctor, duk uban sauron dake cizon ta ba ta ji saboda nisan data yi cikin tunani, domin yawan motsin da take ji a cikin daga shekaranjiya ya kara daga hankalin ta, a hankali ta mike da hijab din dake jikin ta ta fita, as usually yana tsaye jikin motar sa idanun sa kafe kan bakin kofar gidan.

Tun kafin ta karaso inda yake yake kallon yadda ta ƙara zabgewa, hakan kuma yasa zuciyar sa sosuwa, ya sauke numfashi yana sakar mata murmushi a lokacin data karaso inda yake, sannan yaji sallamar ta cikin dashashiyar Murya wanda da bai saka kunne ba, bai zama Lallai ya ji ta ba, cikin sakin murya ya amsa mata, kana ya shiga tambayar ta ya take, ya kuma jikin ta?

Shar shar hawaye suka dinga rige-rigen sauka a idanun ta, a dame ya kara kusa da ita yana fadin “ya Salam! Munaya meya faru?”

Cikin sanyi murya mai cak’ude da tarin damuwa tace “Ni wani abu ne yake yawa a cikina tun jiya, ni kamar numfashi yake fitar wa, sai kartata yake a ciki, anya ba kadangare bane ya shiga cikina doctor?” Ta faɗa zuciyar ta daya, domin bata san mai juna biyu na jin wandannan alamomin ba.

Da a ce cikin nan na halak ne, daɗin dadawa ace na sa ne, da sai yayi dariya saboda maganar Munaya, amma ya ji dadi at Long last dai ta buɗe baki yau ta masa magana mai tsayi, dama zai dinga samun hakan daga gareta a duk lokacin ɗaya zo da yayi farin ciki, domin hakan ma zai taimaka wurin rage mata damuwa idan tana fito da wasu abubuwan daga zuciyar ta. “Munaya” ya kira sunan ta.

Ta kalle shi ba tare da ta amsa ba.

Ya sake gyara tsayuwar sa, yace “Munaya ba wani abu bane, wanna abin da kike ji sign ne na cewar abinda ke cikin ki yana cikin koshin lafiya, kin fahimta, the baby is so healthy, saboda haka kar ki wani damu ”

Munaya taji wani tukikin bakinciki ya tsaya mata a rai, musamman kalmar baby daya ambata, sosai taji ta kara tsanar cikin jikin ta, kamar yadda ta tsani uban, ta saka hannu ta goge hawayen ta, still ya cigaba da zubowa, doctor dake kallon ta yace “Munaya har yanzu kin ki daina saka kanki a damuwa, ki sani cewa if you focus on the hurt, you will continue to suffer. But if you lesson, you will continue to grow, that’s life, babu abinda zai Sanja, abinda ya faru ya riga ya faru bazaki iya gogewa ba, so the best thing to do is ki yawaita istigifari, da rokon Allah yafiya kin ji ko?, Sannan ki kwantar da hankalin ki, kina bukatar hakan sosai a wanna matakin”

Ta budi baki sau uku ta ƙasa magana saboda kuka, sai a karon na hudu tace “doc… doctor ban so wanna cikin ba, ban so wata alaƙa musamman irin wanna ya ƙara hada Ni da Maleek, ban so kara hada komai da shi ba, kamar yadda ya tarwatsa rayuwata na so bacewa a tasa rayuwar, doctor Maleek is a monster bashi da Imani bare tausa…”ta kasa karasa maganar saboda kukan daya ci karfin ta, ta saka bayan hannun ta tana goge hawayen.

Ya runtse idanun sa, tausayin ta daya mamaye zuciyar sa ya sa kasa magana, tsawon dakika goma kana yace “Munaya! Ni kai na banaso ko kallo ta kara hadaki da Maleek balle magana ta fatar baki, bai cancanci haka ba, Kula da cikin nan da kuma haifo shi duniya hawai yana nufin saboda Maleek zaki yi ba, domin Allah da kuma shi bawan Allah dake cikin ki da bai da laifin komai, amma kike son hukunta shi da abinda uban sa yayi? Ki saka a ranki cewa kin fi karfin Maleek, ki saka a ranki cewa abinda ya faru ƙaddara ne wanda shi ya haɗa ku, abu na karshe da zan fada miki shine ki rike Allah a ko wani hali shi zai miki maganin komai ba dai mutum, matukar kika rike hakan zaki ga haske da tarin sauyi a rayuwar ki”
jinjina kai Munaya ta shiga yi, tana dan ji nutsuwa na saukar mata, musamman kalaman da doctor yayi amfani da su ya taka muhimmiyar rawa wajen samun saukin nauyin da zuciyar ta ke mata.

Haka doctor Abbas ya cigaba da kwantar mata da hankali hadi da bata shawarwari masu amfani a matsayin sa na wanda ya girme mata ya Kuma fi ta hangen nesa, ya sauke numfashi da ya lura ta ɗan saki jikinta, yana son yi mata maganar Maleek kan ya kamata ya san da cikin amma yana tsoron kada hankalin ta ya tashi, domin ya fahimci bata kaunar ko jin sunan sa, bazai yi gaggawa ba, zai bari zuwa wani lokaci ya kara mata magana, she kansa bazai so Munaya ta kara ganin shi ba kamar yadda ya faɗa, he really mean it, amma zai yi hakan ne saboda darajar jaririn innocent soul din da bai san komai ba, bai kamata yaron ya tashi da maraici ba, bayan yana da uba, da haka yayi mata sallama, ya kuma bata ledar da yayi mata siyayyar kayan kwalama, domin ya san ba a rasa mai ciki da cima irin wanna, karon farko da Munaya ta masa godiya.
“Thank you, Ubangiji Allah ya saka maka da gidan aljanna, You re truly a kind man” ta karasa hawaye da suka zame mata aboki ya gangaro mata…

Ya saki murmushin jin dadi, ya kuma ji dadin improvement daya gani yau tare da Munaya, ko ba bakomai ta danyi magana yau, ya san har da kewa rashin mutum ke kara wa Munaya damuwa, da da yanda zai yi da ya dinga kasancewa da ita daga safe har dare, da sauran murmushin da bai gushe daga fuskar sa ba yace “Ameen Ameen, wa’iyyakum”
Munaya bata ƙara cewa komai ba ta juya zuwa cikin gidan.

Washegari da safe Munaya taji cikin ta ya Murda, kana ya bada sautin mai ƙara alamun yunwa, ba shiri ta janyo ledar da doctor Abbas ya kawo mata jiya, jikin ta da hannun ta na rawa ta bude ledar ta ga snacks ne da yoghurts a ciki, sai dai yoghurt ɗin yayi tsami ya dauko hanyar lalacewa saboda zafi, hannu ta saka ta dauki meat pie daya ji filling din naman Sa, amma shi bai lalace ba, hannu baka hannu kwarya ta shiga ci sosai, tun da take bata jin yunwa irin na yau ba, gaba-daya ta kasa controlling yunwar, sai da ta ci meatpie din guda uku gasu manya kana ta ji daidai, ta sha yoghurt din duk da ba dad’i a baki, ta shiga sauke ajiyar zuciya, domin dazu ji tayi kamar zata mutu….

Mintuna uku da gama cin meatpie din nan amai ya taho mata, kafin tayi yunkurin mikewa amai ya zubo, ta shiga kwararawa a nan dakin, cikin seconds kalilan ta jigata sosai, da kyar ta iya jan kafa ta dauki summa ta goge aman kana ta wanke bakin ta, ta dawo dakin ta kwanta tana jan numfashi tamkar wacce zata mutu, ramar data yi ya kara fitowa ƙarara, idanun ta ya shige can cikin loko, gwanin tausayi, ta na a cikin wanna yanayin har bacci mara dadi ya dauke ta.

*Mummy *
*(Sa’adah)*

Zaune take a dakin ta, tsadaddiyar wayar ta a kunnen ta tana waya da Hajiya maimoona, cikin damuwa tace “maimoon bazaki gane ba, wallahi na gaji fa, mutumin nan yaki komawa inda ya fito bare na samu in aiwatar da abin da yake raina, bai taba zuwa ya jima irin haka ba, ko jikin shi ne yake bashi I’m after something? domin kin san jiya a lokacin da muke tarayya da shi, saboda yanda na kai kololuwa a bukatar dan sa, bashi ba, sunan sa na dinga kira, gaba-daya ban sani ba, ke na so tona asirin kaina, da asuba yake tambaya ta wai ya ina kiran sunan Maleek, wani Maleek din? Na ji tashin hankali amma na maze nace Ni Alhajina, a’a Ni ban kira sunan kowa ba, sai dai idan kunne ka ne bai juyo maka ba daidai ba, ai Ni jiya kaso zautar dani Alhajina, ina gaya miki da haka na samu ya bar maganar”…

Daga can bangaren Hajiya maimoon tayi dariya sosai tace “wato Sa’adah kin cika shu’uma, Wato dai kin nace sai kin dandani yaron nan, anya Sa’adah baki hada dangi da Mayu ba wanna naci yayi yawa, bayan akwai yara irin sa da suka fishi komai”…..

Cikin sauri mummy ta katse ta da cewa” bazaki gane ba maimoon, kin san Ni na raini yaron nan, na san mena gani, ke da ba dan ina kishin sa ba da wallahi bayan na cika burina a kan shi zan baki aron sa ki dandana ko sau daya ne, amma ina bazan yi ba, yanzu ma dana yi maganar baki ji ba zuciya ta suya take, ke ina kishin yaron nan sosai fiye da tsamanin ki, Kin san Allah wanna yarinyar daya tare da ita da zan ganta kuma na san inda zan same ta babu abinda zai hanani yi mata ko me yazo raina, kai! I can kill person because of that boy ooo” ta karasa maganar cikin yanayin su na kangararrun mata da suka manta cewa jindadin duniya ƙadan ne.

Daga can bangaren Hajiya maimoon ta tabe baki tace “a’a rike Kayan ki Sa’adah bana so, ina da masu gamsar dani yanda nake so, kice zaki iya wanna wahala amma banda ni wallahi, yanzu dai ki samu ki lallaba Alhajin naki ki ji yaushe zai tafi”

Da haka da suka yi sallama da Hajiya Maimoona ta ajiye wayar, kana ta mike domin zuwa wajen Alhaji Dawood, ta tarar da shi a general falo yana karanta jaridar Daily trust mummy ta zauna a hannun kujerar da yake zaune tace “Barka da hutawa Alhajina”

Ya dago kansa daga jaridar yace “Yawwa Sa’adah kin fito?”……

“Eh” ta amsa tana sakin murmushin da bai kai zuci ba

Shiru ya ɗan ratsa na wasu mintuna kana mummy tace “Ni kam Alhaji wanna karon ka dade sosai, hakan bazai shafi kasuwanci ka ba tunda baka nan? Kasan mutanen yanzu babu tsoron Allah, mutum yana nan ma ya aka kare bare an ga babu idanun sa”

Alh.Dawood ya saki murmushin jin dadi na samun mace mai damuwa da duk wani abu ɗaya shafe shi, ya kalle ta yace “wato Sa’adah tunda na dawo wanna karon sai na ji ban son komawa can, baki ga yaya Laraba data zo rannan har da kukan ta ba kan kar na koma, Ni ma kuma na yi kewar kasa ta sosai”

Dum dum!! Kirjin Sa’adah ya shiga bugawa, hankalin ta ya kai kololuwa a ɓaci, saboda Alhajin ta yana son jiga mata aiki.
Alhaji Dawood ya ɗora da cewa “amma in sha Allah na kusan dawowa gaba-daya, tunda Allah ya bani zaratan samari har biyu zasu na zuwar min lokaci zuwa lokaci Domin kula da harkokina na can, kin ga nima na huta ko?”

Sa’adah ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, ta sa a ranta cewa kafin ma ya dawo ta gama cika Burinta a kan Maleek, a lokacin ta riga ta lalata shi da soyayyar ta da bazai iya guje mata ba, wanda ko da Alhajin ya dawo Maleek zai dinga nema musu hanyar gamsar da junansu, tunda ya shigo hannu, da wanna tunanin ta samu ta kwantar da hankalin ta…

 

***

Kamar kullum idan Shakur bai da lectures da zai koyar yana tare da Maleek, cikin kaunar juna suke hira, a cikin hirar ne Shakur yace “Maleek da bana nan Munaya bata zo ba har yanzu? wallahi kullum ina tunanin yarinyar nan, jikina na bani like she’s not okay”

Maleek ya hade fuska yana girgiza kansa alamun bata zo ba, ya Shakur zai tambaye shi yarinyar nan, yana kokarin cire maganar ta a ransa shine Shakur zai tambaye shi, Shakur bai lura da canjin yanayin da dan’uwan na sa ke ciki ba ya riko hannun sa yace “Maleek ka tuna alkawarina? Ka tuna nace idan Munaya ta bayyana a garemu, zan fada maka wata magana, za kuma ka cika min Ita”

“Yeah I remember, Amma ka fadamin me kake so na maka Shakur, dole sai ta dawo, What if ba’a sake ganin ta” a ransa yana fatan kar a ganta har abada, domin a kullum yana ganin shigowar ta Cikin rayuwar sa ba alkhairi bane, abinda ya fi kona masa rai shine ta saka ya aikata abinda bai taba aikatawa ba koda a Spain ne da yayi karatu, shi da yake ganin mata kusan rabin su tsirara, amma abin takaici a jikin kwaila Munaya ya fara sanin ya Mace, ya hadiyi wani yawu mai daci a bakin sa.

“In Sha Allah zamu ganta” Shakur ya katse masa tunani Cikin tabbaci, Maleek ya sauke numfashi a boye, ya zare hannun sa daga na Shakur ya cigaba da aikin da yake a system, so yake ya dawo daidai, domin yana kokarin rasa nutsuwar sa, duk sanda aka yi maganar ta sai yaji kirjin sa ya Sanja bugu, ya rasa meke masa dadi, he hate Munaya with passion, ya tsane ta, daga lokacin data shigo rayuwar sa komai ya dagule masa, ya saki siririn tsaki mara sauti yana rufe system din Domin ko aikin baya ganewa….

****

Tsaye yake a kofar gidan su Munaya kamar yadda ya saba, yana jiran ta fito, bayan shudewar mintuna biyar ta fito, amma maimakon ta fito inda yake, Sai ta sulale a soron gidan ta zauna, tana jin bazata iya fito ba, domin sam bata jin ƙarfi a jikin ta, cikin sauri ya shigo soron bakin sa dauke da sallama, ya durkusa gaban ta yana kiran ta “Munaya, Munaya Are You ok?”

“Bana jin ƙarfi a jikina” tace wasu hawaye na zuba a idanun ta, ya dauke kansa gefe, yana jin tausayin ta mai yawa a zuciyar sa, ta kara ramewa da lalacewa, hakan kuma na tabashi sosai idan ya ganta, cikin kulawa yace “Munaya bakya cin abinci, ba ke kadai bace kin tuna? Ko da bazaki ci ba dan kan ki, just be eating for the sake of the innocent baby you re carrying please, Ina jin ba daɗin ganin ki cikin wannan halin”

Ta tsuke fuska har girar ta na tattarewa “dan Allah ka daina min maganar cikin nan wallahi banasooo”

Doctor Abbas ya yi saurin cewa “toh shikenan kiyi hakuri” lallai akwai tarin kuruciya a tare da Munaya, ya kara tabbatar da hakan yau. Cikin lallabawa yace “TOH naji babu ruwan ki da shi amma kina ci dan lafiyar ki kin ji ko, yau ma na kowa Miki kayan dadi, na san zaki so shi”…

Suka yi shiru na wasu dakika, sannan yace “yawwa ina ta son in yi Miki magana, babu yan’uwan ki a nan kusa ki fada min, Ni zan je na musu bayani da kaina, karki ji tsoro, nan gaba bazaki dinga zama ke kadai ba babu idon babba ba, so tell me idan akwai yan uwa ko dangin ku Ni zan je na faɗa musu, kuma za su fahimta in Sha Allah ”

Idanun Munaya suka soma kafewa suka ƙara ciko da kwalla tace “bamu da Kowa a nan kasar, asalin mu yan Chadi ne, daya baya iyayena suka bar Chadi zuwa nan Nigeria, dama can dangin mu dana sani yan sirarru ne, kuma iyayena basu kara zuwa Chadi ba, haka ya saka ban san Kowa na mu ba, a ranar da Umma ta haifi Amnah, Abba mu ya tafi ya bar ta, wai bazai iya cigaba da zama da ita ba saboda tana haifen ya’ya mata, har yau bai dawo ba, ban san Kowa nawa ba wallahi” ta karasa maganar da fashewa da kuka” doctor Abbas yaji ransa ya ɓaci, kana tausayin Munaya mai yawa ya kara cika zuciyar sa, dama akwai maza masu irin wannan jahilcin har yanzu, menene bambancin ya’ya maza da mata? Idan wani abu na daukakar rayuwa ne akwai matan da suka fi maza, ta yaya wasu mazan zasu ce lallai sai namiji suke so, abinda basu isa su siya da kudin su ba Amma suna zaba? kyautar Allah ce, ga wanda yaso yake bawa, Allah da kansa ya karrama ya’ya mata cikin littafin sa mai tsarki, wane mutum, wane dan adam da zai ce bai son ya mace, ya sauke numfashi, ya shiga kwantar wa Munaya da hankali, da alƙawarin zai cigaba da kula da ita da dukkanin iyawar sa, da kyar ya samu tayi shiru, ya koma mota ya dauko kayan daya siya mata ya tilasta mata Lallai sai data ci wani abu a ciki a gabansa, ya ɗan jima yana ɗebe mata kewa kana yayi matsy sallama ya tafi.

 

 

*Na kusan kamalla free pages, a Yau kuma zuwa gobe nayi promo, duk wanda ya biya dari uku zai samu karanta* *MunayaMaleek har karshen sa, amma ranar Litinin ainihin farashin sa na 500 zai cigaba da aiki ngd*.

 

 

MunayaMaleek is not for free, it’s 500 via 3200689860
first bank, shaidar biya ta 07082281566, thank you for your patronage! Allah ya kara muku budi.

No comments