Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Munayamaleek 21


XXI
<21>
Tun lokacin da Shakur ya fara masa magana gashin jikin sa suka mimmike, maganganun na shiga ko wani huda na gashin jikin sa, yanayin is indescribable, a hankali ya sauke kansa kasa zuwa ga tsadaddiyar wayar Shakur din dake kan cinyar sa, the first thing he saw shine tululen cikin ta da jinin sa ke kwance a ciki, bai iya karya ba, ko min girman laifi baya taba Æ™aryatawa saboda tsoron hukunci, domin idan yayi karya wa Mutanen duniya, zai iya boye wa Allah ne matsanin ganin abinda ke boye da bayyane? Bai da sani kan addini but ya yasan lying is a sin, he knows cewa cikin jikin ta na sa ne, duk da yana cikin fitar hayyaci a lokacin amma ya san cewa he’s the first person that disflowered Munaya, she ya fara sanin ta, amma abinda ke damun sa har yau shine meyasa ya haÉ—a jiki da ita, saboda bata da sura ko wani abun da zai ja hankalin sa gareta, infact yar karamar kwailar yake ganin ta.
Kara mai da idanun sa kan hoton yayi baya ko kiftawa, yanda komai ya faru a office din sa na dawo masa, a takaice bai dauke idanun sa daga kan hoton ba, musamman kan cikin har sai da hasken wayar ta dauke da kanta, a wanna daren bai iya bacci ba, juyi kawai yake.
Da misalin karfe ukun dare ya mike tsaye, a nutse yake zagaye dakin, hannun sa daya riÆ™e da da kugun sa, yayin da yake murza goshin sa da dayan hannun, fuskar sa a matukar hargitse take unlike gangar jikin sa, tun lokacin da Shakur ta nuna masa hoton Munaya dake dauke da gudan jinin sa komai ya tsaya masa cak, he has not been his self just that tsananin jarumtar sa tasa kai tsaye mutum bazai gane halin da yake ciki ba, amma har ran shi, ya raina komai na Munaya, everything about her, and gashi zata zama uwar babyn shi, “gosh! What an insult?” Ya fada cikin dacin murya yana furzar da iskar bakin sa, har yanzu ya kasa gane meyasa ya haike wa kazamar yarinyar nan da ko kallon kirki bai taÉ“a mata ba, meya bashi sha’awa bayan ita din yar karamar kwailar ce, gashin kansa ya hargitse yana jin bacin ransa na ninkuwa, shi har laifin Munayan yake gani, me ma ya kawo ta office din sa a lokacin da yake cikin gushewar hankali har ya farmata, he just wish da ma hannun agogo ya koma baya ya sanja komai, hatta zuwan Munaya zai cire, ta yanda bazata shigo rayuwar sa ba.Da gaske kenan gudan jinin sa ta jikin Munaya zai tsaga Ya fito? He can’t believe it.

Sosai yake sharara gudu a mota, Shakur na gefen sa, AA DAWOOD MOTORS suka nufa kamar yadda suka saba zuwa matukar Shakur din bai da lecture da zai koyar, shiru motar ta dauka,, can ya rage gudun kana yace “zan baka kudi kayi Mata duk abinda take bukata” ya faÉ—a saboda a tunanin sa hakan zai saka Shakur farinciiki, domin gaba-daya ya daina ganin dariyar kanin sa, suna komai tare yanda suka saba amma babu sakin fuska a tare da Shakur.
Kamar Shakur bai fahimci abinda yake nufi ba yace “wa fa?”
Maleek ya cije labban sa, yaki jinin a raina masa hankali, an fahimci abu mutum yayi kamar bai gane ba, ya danna É“acin ransa yace “that girl”V
“Which girl are you talking about please, bata da suna ne?”Da gaske Shakur yake son fusata shi.
“Shakur Please i know ka fahimce ni, menene amfanin abinda kake yi”
“Ohhh really, kana tunanin kudi sune komai, a kodayaushe abu na farko da kake kawowa a ranka sune kudi, You think kudi zai goge tabon dake zuciyar ta? Abu É—aya nake so da kai shine ka bata kulawa, begged her, ka nemi ta yafe maka, ba wai maganar kuÉ—i ba, nasan kana da kudi sosai ai”
Ran Maleek ya bace a take, dama da biyu Shakur ya fada domin ya san Maleek ya ki jinin a fada masa haka.
Cikin fushi yace “ina yawan gaya maka ka daina fada min cewa ina da kudi, kamar kai baka da iko da shi, kana gyara kalaman ka muna da kudi domin dukkanin abinda na mallaka naka ne”
Shiru Shakur yayi bai kula shi ba, yasan dama zai ji haushi, da a cikin walwala yake zai yi dariya saboda yanda Maleek din ya dauki abin too personal.
Daidai sanda ya yi parking a haraban na companyn sa ya kalli Shakur yace “kuma ka sani cewa hakurin da kace na bata shi zai zama abu na karshe da zan yi” ya fice daga motar yana bugo murfin da karfi.
Da kallo Shakur ya bishi, yama rasa yanda zai bullo wa Maleek, he’s too stubborn, amma ba zai tsare ba, zai cigaba da bashi shawara hadi da cusa masa maganar Munaya a kodayaushe, har ranshi yake da wata kyakkyawar manufa akan MunayaMaleek, numfashi ya sauke,kana ya bude motar ya fito hadi da kulle ta ya nufi cikin building din.
Mummy ce zaune a daya daga cikin hadaddun kujerun falon, Centre table ke gabanta mai dauke da kwalbar wine na tattaciyar inibi, lokaci lokaci take sipping wine din, yayinda tayi nisa a tunani, tunanin yanda zata cimma ma burin ta, tunanin data dauki tsawon shekaru bai barta ba, ba kuma ta jin zai barta har sai ta samu abinda take so, numfashi mai zafi ta sauke, kana a bayyane yanda ita kadai zata iya ji tace “lokaci yayi daxan yi amfani da kirssa wajen samun ka Maleek, na yi rantsuwa bazan kara barnatar da kudina kan malam tsubbu da bokaye ba…” Ta karasa tana dora kafa daya kan daya, she looks damn serious alamun wanna karon a mugun shirye take, domin the moment data lissafa kuÉ—aÉ—en da bokaye suka ci Mata shock ya kamata, a hakan ba duka ba, iya na baya bayan data tuna kenan.

*1:03am*
Cikin sauri ta mike zaune, dama ba bacci take ba, jira take sha biyu yayi ta fara aiwatar da plan din ta kamar yanda ta tsara, domin ta san Shakur yayi nisa a bacci yanzu, kara gyara zaman shedaniyar nighty dake jikin ta tayi ta kara fesa turare mai jan hankali, ta buÉ—e Kofar dakin ta ta fito, she makes sure Bata yi wani motsi mai Æ™arfi da zai ja hankalin kowa ba, sadaf sadaf ta isa bakin kofar maleek ta buÉ—e ta shiga kana ta saki numfashi tana dafe da kirjin ta, ta kai jarababbun idanun ta kan maleek dake kwance rigingine yayi matashi da hannun sa, yana sanye da jersey armless da gajeren wandon sa farrare, he looks so handsome tamkar wanda yayi wani shiga na musamman, yayinda Sa’adah ta shiga wani yanayi mai wuyar fassaruwa, just looking at his Giant sexy body ta ji hakan a jikin ta? Wani yanayi zata ji idan ta taji ta a jikin sa, “wayyo Allah na” ta fadi tana buÉ—e hannuwan ta irin na shaukin nan, Sai dai tuno abinda ya kawo ta dakin yasa ta saki wani kuka cikin tashin hankali, ta nufi gadon, maleek da bai da nauyin bacci ya bude idanunsa cikin sauri jin sautin kukan mummyn sa, kafin yayi yunkurin tashi zaune ya ji ta akan gadon sa, tamkar da kiftawar ido ya ganta kwance a jikin sa, cikin kirsa ta kankame shi tana fashewa da kuka tace “Allah na gode maka, my boy is fine, babu abinda ya same ka ko? I had a bad dream akan ka”
Cikin Muryar bacci ya kara jefa Hajiya sa’adah a wani yanayi yace “I’m fine mum, it’s just a dream” ya karasa yana kokarin tashi da ita zaune, ta kamkameshi tamkar yar yarinya, duk da ya zaunar da ita a gefen sa amma taki barin jikin sa, ita kaÉ—ai ta san abinda taji da jikin su ya haÉ—u, ta rasa wane irin yaro ne wanna a yanda ta kwanta a jikin sa ya kamata ya fita a hayyacin sa ya neme ta da kansa, a yanda ta san wasu yaran zamanin nan da jaraba, toh ko dai bai da lafiya ne?, tayi saurin kawar da wanna tunanin a ranta, domin ita shedace a irin halittar maleek tun yana Karami balle yanzu, kanta ta kwantar a kirjin sa tamkar yar yarinya dake tsoron a kamata, maleek ta É—ora hannun sa a kafadar ta yayi patting “mummy I’m fine, please go back to sleep”
Wani kalan kankame shi ta kara yi cikin dabara take shafa shi tana cewa ” i can’t sleep anymore, kasan irin mafarkin dana yi a kan ka kuwa? Ni zan zauna da kai a nan, domin ko da na koma dakina tsoro bazai barni na yi bacci ba, ya Allah ka tsare mini yarona, i don’t want to lose him”
Shiru maleek yayi, yana tunanin wani irin mafarki ne ya tsorata mummyn sa haka, cikin son kwantar mata da hankali ya kamo hannun ta ya sumbata yace “trust me mum, babu abinda zai faru by God’s willing”
Sa’adah ta ji haushi, a lips ya kamata ya mata wanna kiss din ba a hannu ba, ita fa ba mother’s love take so Daga gareshi ba, soyayya irin ta masoya take so ya nuna mata, amma yaron nan yaki gane wa.
Tana cikin tunanin nan ta ji ya mikar da ita, sai a lokacin ta ga maleek a tsaye which bata san sanda ya mike ba, ganin ya nufi kofa da ita yasa ta rungume shi da sauri a jikin ta tana cewa “Are you sure you will be fine my boy Ko na kwana a nan?” Ta tambaya cikin marairaita, wallahi idan tana tare da Maleek jin ta take yar yarinya.
Murmushi ya saki yace “worry not Mum, I’m fine” ya fadi haka kana ya raba jikin su again wanda bata so hakan ba, ya riko hannun ta suka fice daga dakin, sam bai kawo komai a ransa ba, ya danganta hakan da tsoratan data yi ne.
sai daya tabbatar she’s ok domin har ruwa mai sanyi ya siyaya ya bata a kofi ta sha kana ya bar dakin zuwa na shi.
Yana fita Hajiya Sa’adah dake matse kafafun ta, ta daki gefen gadon ta dan takaici, tamkar tayi ihu saboda abinda take ji, wato maleek na daban ne, kwarjinin sa na daban ne, duk yanda ta so fito masa da abinda ke zuciyar ta game dashi kasawa tayi, wani abu mai kama da tsoro ke hana ta, amma kuma ba laifi ta É—an dana yau compared to lokutan baya da bata iya komai ba, amma a yau shame shame ta kwanta a jikin sa, hakan ma ta dauko hanyar Nasara, kamar yanda kawarta Hajiya maimoon ta fada “don’t rush Sa’adah!” bazata yi gaggawa ba, sannu a hankali komai zai mata yanda take so, yanzu ta soma, babu gudu ba ja da baya, ta kara wa kanta karfin gwiwa kana ta mike, toilet ta shige domin ta yi wanka hakan kadai zai rage Mata abinda take ji.
Da asuba kamar yadda Shakur ya saba ya tada shi sallar asuba, bayan yayi alwala suka nufi masallaci, ana sallame sallah ya fice abinsa, Shakur ya bishi da kallo, dama duk Wanda yasan su tare yasan cewa maleek is not a religious person, Shakur ya fi shi ilimin addini da kuma aiki da shi nesa ba kusa ba. dakin mummy ya nufa domin duba ta, ya tarar tana Bacci, ganin she’s fine yasa ya fice daga dakin zuwa gym room dinsa Wanda yake next to dakin sa.
Sai da misalin karfe tara Hajiya Sa’adah ta farka, yamutsa fuska tayi saboda kanta data ji ya buga Mata saboda tsabar jaraba da kulafucin data daura wa kanta, mikewa tayi ta shiga toilet, tayi wanka hadi da alwala ta fito, ta gabatar da sallar asuba a matukar makare, sai dai ko kadan hakan bai dame ta ba, sai ma tunanin boy dinta data shiga yi, wayar ta ta janyo ta yi dialing number’n Hajiya maimoona aminiyar ta, bugu uku kacal Hajiya maimoona ta dauka, cikin Muryar bacci tace “hello Sa’adah ya ne, an kashe boss ne, wanna kira haka?” Hajiya maimoon ta fadi Cikin shekiyanci tana sakin dariyar mugun ta.
“Hmmm!” HAJIYA SA’ADAH ta fadi, ina ma an kashe boss din, data zama da luckiest woman on earth, har party zasu shirya da maimoona saboda farin ciki.
“Menene hmmm ko akwai matsala ne?”
A takaice mummy ta bawa Hajiya maimoon labarin yanda komai ya faru a daren na jiya.
“Mtswwwee, kin ji matsalar ki, jiyan nan shine perfect time daya kamata kiyi yanda kike so da shi, sai kace ba mace ba? wai taya zata dinga jin tsoron yaron da kika raina da hannun ki, karki manta rainon ki ne, kawai dan tunatarwa zaki aikawa kwakwalwar sa ya dawo miki asalin little boy dinki that he was lokacin yana yaro” cewar Hajiya maimoona cikin jin haushin kawar ta ta.
“Bazaki gane ba maimoona, yaron nan ba dai shegen kwarjini ba, da zarar na shirya yin yanda na tsara wallahi ganin sa sai ya sanyaya min guiwa, maimoona You know Maleek nau, ko wasu maza na shakkar sa, amma at least jiya is better, domin na samu kwanciya a jikin sa, and I’m not giving up, kwana nan zaki ji Good news Hajiya ta”
“Abinda nake so kenan, just act smart, and ga Wata shawara” Hajiya maimoona ta mike zaune daga can É“angaren domin jin daÉ—in yin magana, bata jira amsawar mummy ba tace “matuÆ™ar kin sake gwada kissa bai bada kai bori ya hau ba, just go to pharmacy ki siyi desire tablet ki saka masa ko a drink ko smoothie, sai ki je gareshi, kuma ki tabbatar da cewa kin yi video na komai daya faru tsakanin ku, amfanin videon shine just in case ya dawo hayyacin sa ya bijire Miki, sai ki masa barazanar cewa zaki nuna wa Shakur da mahaifin sa da ma duniya baÆ™i daya, tuni zaki ga ya amince kun É—ora daga inda kuka tsaya, tunda yaki ta dadin rai ba, wanna hanyar ce kadai mafita, zaki ga yanda zai dawo tafin hannun ki ku dinke abin ku”
“ALLAH k’awata?” Mummy dake ta sakin murmushi tun dazu ta fadi, domin tunda Hajiya maimoona ta dauko bayanin ta tiryan-tiryan take ganin kamar hanyar zai bille da ita zuciyar ta ya cika da farinciki.
“Allah nake faÉ—a Miki, ke kina tunanin zai so irin wanna mummunan abun ya bayyana duniya ta gane? He will do anything domin ya kare martabar sa a idanun mutane duniya, musamman a idon Shakur da shi mai gidan naki”
“Kai kawata kin ji dadin da nake ji kuwa, meyasa ban yi tunanin hakan ba tuntuni? I most confess this is the best advise ever da kika taÉ“a bani, daga yau kin zama special adviser dina” Hajiya Sa’adah ta fada, sai suka kyakyale da dariya a tare.

*MunayaMaleek is 500 via 3200689860 First bank Haruna Rukayya*.
*Evidence of payment to 07082281566*.
*Dan girman Allah idan ba ki shirya siya ba don’t chat me*.

Post a Comment for "Munayamaleek 21"