Breaking News

Munayamaleek 48


XLIII…
<48>

*MunayaMaleek is five hundred naira, pay to 3200689860 Haruna Rukayya first bank, then send evidence of payment to 07082281566*
_Thanks for your patronage_

Little ta yi fuskar kuka, yayinda take kallon Munaya bata kuma fasa tunkarar Maleek da warmer din ba, Wani irin É“acin rai da Munaya bata san daga ina ba yazo mata, ta mike ta isa wajen little, ta daga hannu zata kai mata duka, karaf taji lallausan hannun sa mai sanyi ya riko hannun ta, ta kalle shi da sauri yayinda É“acin ranta ke karuwa tana kokarin fisge hannun ta, shi din ma sosai ya zuba mata rikatattun idanun sa da suka dan rine kadan, ya bari ta gama fadan kwatar hannun ta ta kasa, a karan kan sa ya saki hannun na ta a hankali, looking straight into her eyes yace ” ki dake ni, ba ita ba, na san kina jin tsana da haushi na, kada ki sauke abinda kike ji a ranki game da ni kan angel” ya fada yana sakin hannun na ta.

Sannan ya yi Æ™asa da Muryar sa Yace “bana son muna yin haka a gaban angel, bana son yarinyar ta ta kasance cikin damuwa, domin ita din duniya ta ce, ki kiyaye Please” yace yana karban warmer din daga hannun little ya ajiye kan table din munaya sannan ya rage tsawon sa yace “angel Daddy have to go now, but I will see you tomorrow okay?”

“Okay Daddy bye bye” little tace tana daga masa hannu.

Yayi mata murmushi kana
Ya juya ya fice daga office É—in Cikin wani irin taku mai burgewa.

Munaya yaji hawaye ya cika idanun ta, dan me zai dinga mata kutse cikin rayuwar ta, idan tayi magana yace saboda yarsa yake yi, she’s till hurt da abinda ya mata, yin shirun ta ba ya nufin ta manta abinda ya faru a shekarun baya bane, ta koma kan kujerar ta ta zauna, taji dumin jikin sa daidai inda ya zauna ya ratsa cikin jikin ta, ta rufe idanun ta zuciyar ta a jagule, ita ma angel bata yi gingin zuwa kusa da Munaya ba, ta shiga wasa da teddy É—in ta, domin tana matukar tsoron Duka, idan aka tambaye ta wa tafi tsoro tsakanin mummy da Daddyn ta, mummyn ta zata ce domin Daddyn ta bai taba dukan ta ba.

Bayan Maleek ya kamalla dukkanin abubuwan daya kamata a office É—in sa ya fiddo wayar sa, ya kira Munaya sai dai har ta katse bata yi picking ba, bai yi fushi ba, duk da ya ji ba dadi, sai ya turo mata massage kamar haka

_hey! Bayan rowar abinci har da rashin kula da patient, baki bani magani da zai busar da ciwon nan ba, ko so kike bakina ya rube na rasa na sumbatar ki?_

A lokaci da Munaya ta karanta sakon sai da gaban ta ya bada dam! Wai me ke damun Maleek ne, me yake nufi da ita duk ya bi ya takura mata.

_ka rabu dani, ka fita hanya ta_

ta ce masa, salon rubutun kadai ya saka shi fahimtar lallai da fushi ta rubuta masa.
Yace

_i can’t, bazan iya rabuwa dake ba_

Munaya ta rasa abinda zata ce masa kuma, kawai sai ta kashe wayar ta.

Munaya kuwa daga wanna lokacin ta sake kauracewa haduwa da shi, sai dai bata ci nasara ba domin kwatsam ta sake ganin sa a office É—in ta kan sa tsaye, ta bishi da kallo cikin mamakin hali irin na sa, ya kan yi duk wani abu da zai saka ta kula shi amma a banza wai an tsikari kakkausa, domin bata ko kula shi bare wata maganar arziki ta shiga tsakanin su.

Wata rana Alhaji Dawood ya kira Maleek dakin sa domin so yake ya masa maganar daya tsaya masa a rai tun ranar da ya je ganin little Amnah.

“Nace matar nan da ta zo gidan can da muka je ka san ta ne?”

Maleek ya girgiza kansa hadi da furta a’a, domin sai a ranar ma ya fara ganin ta.

“Lafiya Dad?”

“Lafiya Lou” Alhaji Dawood ya fada kawai, Maleek har ya kusan ficewa daga dakin, Alhaji Dawood yace “Maleek!”

“Maleek ya juyo, Alhaji Dawood yace masa “zan maka tambayar nan a karo na biyu kuma na karshe, kana son yarinyar nan Munaya?”

Maleek yayi shiru for some seconds kana yace “Yes Dad” I hankali, sai kuma ya shafa kansa ya fice daga dakin da sauri, how can he deny it? tabbas soyyayyar Munaya is all over his body and soul, duk da cewa Munaya bata bashi dama ko kankani amma bazai hakura ba, duk wani abu da zata ce ko yi masa yana mata uzuri mai tarin yawa, lallai ya cutar da ita, ya cutar da ita a lokacin da take da Æ™ananan shekaru sosai, wanda zai yi wuya ta manta, duk da shekarun da dan dama yana iya tuno zafi da rarradin daya bayyana a tare da ita lokacin data watsa masa kudi a fuska, da sauran abubuwan da suka biyo baya.

Bayan Sati biyu da Alhaji Dawood ya yi wa Maleek tambayar nan ya shiga ya fita har ya samu ganin Ammi, kasancewar tana zaune da yayar ta ne, domin mahaifin barrister Abrar ya rasu tun tana da karama sosai, abin ka da babban mutum bai bata lokaci ba wurin sanar mata abinda ke ransa, yayinda Ammi ta ki, sai dai yayar ta taki yarda da ra’ayin Ammin ita ma, domin ta jima tana son Ammin ta kara yin wani auren amma taki, tun bayan data rasa mijin ta na biyu, sosai yayar ta ta yi mata fada, har kanwar sajeed zulaihat (sajeed shine mahaifin barrister Abrar) da suke mutunci sosai ta kira ta daga Nijer ta bata shawara, ta kuma roki Ammi kan ta amince, domin ta gama nuna duk wata soyyayya ga yayan na ta, a karshe dai suka yi nasarar convincing din ta har zuciyar ta amince da Alhaji Dawood É—in, rigiman da tayi tunanin zasu yi da barrister Abrar kan yin aure kamar yadda suka yi a lokacin auren ta da maragayi Alhaji shettima bata yi ba, domin tun a kananan shekaru barrister ta kasance mai kishin mahaifin ta ba kuma ta so ta ga Ammi ta amince da ko wani namiji, amma ga mamakin ta sai barrister’n bata fushi ba, tayi murmushi domin ta kara tabbatar da cewa lallai yarta ta girma.

 

Maleek kuwa bai san duk abinda ke faruwa ba, sai ana yi gobe daurin aure, ya sha mamaki sosai, hankalin sa ya koma kan tambayar da Alhaji Dawood ya masa a rannan, ina ma zai samu amincewar Munaya haka? Domin ya rasa abinda ke masa dadi a zuciya, tsananin jarumta ce ta saka ba’a saurin fahimtar yana da damuwa, abinda kuma ke dan kara kwantar masa da hankali shine daina ganin doctor Abbas a gidan, bai san abinda ya faru ba amma ya ji matukar farin ciki daina ganin sa close to Munaya, tabbas idan mutun zai yi kiyayya yayi ta tsetsa-tsetsai, domin kiyayyar da yake mata ya juye zuwa wata mahaukaciyar soyyayya Mai zafi.

Daurin aure kadai aka yi Ammi ta tare gidan Alhaji Dawood, a wanna ranar Hajiya Sa’adah ta Æ™asa bacci, duk da cewa ba’a sanar mata aure yayi ba amma ta fahimta daga sauye-sauyen da gidan ya samu, tayi nadama mara iyaka yayinda take jin cigaba da zaman ta a gidan bai da amfani, Duk da bata san yadda za’a karbi maganar mutuwar auren na ta ba, amma gwara ta fuskanci wancan tashin hankalin da cigaba da zama a gidan nan.

Bayan kwana uku da auren Alhaji Dawood Sa’adah ta fito daga dakin ta, daidai lokacin da Ammi itama take kokarin kwankwasa kofar dakin, sai ta É—an ja baya ta sakarwa Hajiya Sa’adah murmushi, tace “Barka da fitowa, ni wallahi ban san kina nan ba, sai da yan aiki ke hirar basu ganki ba na sani, ki zo muyi breakfast”

Hajiya Sa’adah ta ji wani nauyi a kirjin ta, ta kalli Ammi da kyau, ta ko ina Ammin ta fita kyau, duk da itama ba fara bace amma fatar ta ta goge sosai, domin Sam ba za’a ce mata baka ba, daga kuma yanda take mata magana lallai bata san matsayin ta a gidan ba.

Ta kirkiri murmushi mai ciwo ta daura a fuskar ta tace ” toh nagode” ta dai amsa ne amma bata jin zata iya kara zama a dinning da sunan cin abinci, ta riga ta rasa wanna damar.

“Alhaji yana dinning ne?ina son magana da shi”

“A’a yana dakin sa,ki shiga mana” Ammin tace mata.

Hajiya Sa’adah zata yi magana kenan sai ta hango tahowar Alhajin, a kallo dayan data masa ta fahimci Lallai hankalin sa a kwance yake, tsufan da take ganin ya mata a da, babu shi yanzu a zuciyar ta.

Ammi tace “yawwa gashi ma ya fito, bari na karasa dinning din sai kun taho”

Hajiya Sa’adah tayi kasa da kanta, bayan Ammin ta tafi tace “dama Alhaji, ina… Ina son zan koma gida” tace da Muryar tausayi.

Ko ya kuke da mutum, duk tsabanin daya shiga tsakanin ku idan irin wanna rabuwar ta zo sai mutum ya ji ba dadi tabbas, musamman da aka dibi shekaru masu yawa ana tare, kamar Alhaji Dawood sai da zuciyar sa ta motsa, amma sai yace “TOH babu damuwa”

Hajiya Sa’adah tace “dan Allah Alhaji a yayyafe, a rokon mun yafiya wurin Maleek domin ko saur ara ta baya yi” ta fada hawaye sharr kan kamatun ta.

Alhaji Dawood yayi wani murmushi mai ciwo, ba tare da ya iya furta komai ba ya bar wajen, Hajiya Sa’adah na shiga dakin ta ta fara hada abubuwan da zata iya tafiya da su.

Ammin bata san Hajiya Sa’adah bata gidan ba sai Bayan kwana biyu kasancewar a ranar data hada kayan ta, bata tafi a lokacin ba sai da ta daidai ci an shiga sallar magrib sannan ta fice daga gidan.

Tayi wa Alhaji Dawood maganar, ya gaya mata gaskiyar babu aure a tsakanin su, Ammi bata ji dadin hakan ba, amma bata ce komai ba tunda ita din bata jima da shiga cikin su ba, bai kamata tana yin magana ko yin kutse kan abinda bai shafe ta ba.

Alhaji Dawood ya katse Mata tunanin ta da cewa “kin samu kun yi magana da ita Abrar É—in?”

“Eh mun yi magana, kuma tace zata tutunbi munayan”

“Dan Allah a kara tuna mata, domin ina son shima Maleek yayi settle down yanxu domin ya samu nutsuwa” hakan ne ma ya saka yayi wa Ammi magana domin ta shige masa gaba Wurin gabatar da maganar Maleek din ga munaya.

“Munaya!” Barrister ta kira ta.

“Na’am Mami” Munaya tace tana wasa da yatsun ta.

“Did you love Maleek?” A firgice Munaya ta dago kanta, domin tambayar ta zo Mata a bazata.

“Ki amsa min Munaya, kina son maleek zaki iya auren sa?”

Wannan karon hawaye ne ya zuba a fuskar ta, Meyasa kowa ya kasa fahimtar ta, yanxu duk sun manta abinda Maleek yayi mata a shekarun baya, dama ance wanna yayi kashi yana mantawa, Amma wanda ya kwashe kashin bazai taba mantawa ba, shine kawai abinda ta fahimta.

“Munaya magana nake so muyi ta fahimta, kada kiyi kuka kinji? Kina da dama da yancin zabar dukkanin Abinda zuciyar ki ta kwanta da shi, babu wanda zai miki dole”

“Yanzu Mami kin manta abubuwan da ya faru? Zaki goyi baya na kasance da shi, Maleek fa Mami?”ta yi maganar tana rushewa da kuka.

Barrister ta dafa kafadar ta tace “my dear Munaya, duk na fahimci yanda kike ji, amma Maleek is a change person, ya sauya matukar sauyawa, yana kuma kaunar ki, why not ki bashi dama, tuna Baya babu abinda zai kara miki sai kunci a zuciyar ki, a da bana son wata alaka ta shiga tsakanin ku, amma a yanzu ina mai baki shawara ki bashi dama munaya, musamman da mahaifiyar Abbas taki amincewa da auren ku, haka zalika idan wani ya zo shima ba Lallai ya yarda da auren ki ba idan ya san kin taba haihuwa, idan kuma ya yarda ba zai yi accepting yar ki ba, idan kuma ya amince da yar ki zai iya goranta miki, idan bai goranta Miki ba, dangin sa zasu iya, amma Maleek fa, bai isa ba, domin shine silar faruwar komai, therefore bai da bakin magana, Munaya forgetting our past makes us to appreciate nature, love, care, and make unity among us, souls were bound for Allah to be pleased with, bazan tilas ta ki ba, illa na baki shawara, please think, ki tunani sosai kan magana ta, ki kuma yi addu’a domin neman zabin Allah”.

A sanyaye Munaya ta mike ta fice daga dakin barrister, ta sauka zuwa na ta dakin, zuciyar ta a cunkushe take, yayinda take ji wani irin daci ya mamaye harshen ta, ta rufe idanun ta hawaye suka zubo mata, ta saka bayan hannun ta ta share .

#munayamaleek2023
#fathers love
#hatred
#sorrow
#heartouching
# destined for each other
#love
#selfishness

No comments