Breaking News

Munayamaleek 5


MunayaMaleek 

 

_by NoorEemaan_✍️

https://www.facebook.com/groups/1346404966270527/?ref=share_group_link

 

V…
(5)

 

Cikin sauri doctor’n ya bi bayan ta, domin Ya lura tayi matukar fita a hayyacin ta.
*Munaya*
Cikin wani irin zafin nama da bata san tana da shi ba ta bude dakin da aka kwantar da Amnah, sai dai abinda tayi tozali da shi yayi sanadiyyar daskewar ta a bakin kofar, idanunta kuri kan Amnah dake kwance flat rufe da farin yadi irin na asibiti, ji take tamkar bata duniyar, komai ya tsaya mata cak, a hankali ta sulale kasa, hawaye na cigaba da fita a idanun ta, kallon gawar kanwar ta dake lullube a farin zani take, ta rasa wani kalar tunani ya kamata tayi, ji take tamkar ƙwaƙwalwar ta ya daina aiki…

Tana a wanna halin likita ya bude Kofar shi ma ya shigo, damuwa kwance ƙarara a fuskar sa, bai taba damuwa da ko wani mutum daya zo asibitin nan kamar yadda ya damu da su Munaya ba, tayi matukar bashi tausayi sosai, yar yarinya da ita amma tana shan gwagwarmayar rayuwa.

“Munaya!” Ya kira sunan ta cikin Muryar tausayi.

Sunanta da doctor ya kira ya ɗan taimaka wurin dawo da tunanin ta data fara rasawa, ta dago jajayen idanunta ta watsa masa su, tamkar mara hankali haka ta zuba masa manyan idanun ta tsawon mintuna uku, ya kara kiran sunan ta, ta dauke kanta daga kallon sa, ta rarrafa zuwa gadon da Amnah ke kwance, hannun ta na rawa ta shiga yaye farin zanin da aka rufawa Amnah, Kyakkyawar fuskar kanwar ta daya kara matukar haske ta kurawa ido, tana kara ƙaryata managar doctor, tana dan bubbuga fuskar Amnah cikin raunin murya tace “Amnah, bacci kike har yanzu? maza tashi ayi Miki aikin nan ki warke gashin ki ya fito, kin tuna nace zan Miki kitso?” Ta faɗa cikin kuka mai haɗe da Murmushi, ta kara kallon doctor tace “likita ka gani, nace maka bata mutu ba, kalli kalli kaga murmushi fa take min, kuma ka san me, Amnah bata taɓa kyau irin na yau ba, tana raye ku mata aikin nan dan Allah ta huta da ciwon nan” ta karasa maganar da kuka, so take ta bawa kanta hope na cewa Amnah tana raye, duk da ta san bata ko motsi, she’s lifeless, babu rai a tare da ita, amma bata son ƙwaƙwalwar ta ya dauka balle har ta yarda da hakan a ranta.

Likita da jikinsa ya gama sanyi ya tako a nutse zuwa gaban gadon, ya ɗan rage tsayin sa yace “Munaya! Kiyi hakuri, Amnah ta rasu, babu abinda take bukata yanzu fiye da a sadata da mahallin cin ta, wanda ya fi son ta fiye da mu, ki sani ko wani rai sai ya dandani zafin mutuwa, and who life is given to, death is a promise, Dan Allah ki dauki hakuri da dangana, i know you are too small to bear this, but you can do it, cos you re very strong, more than you can imagine…”
Ihun da Munaya tayi wanda ya karade har wajen dakin da kuma shirun daya biyo baya shi ya kara dagawa doctor hankali, ya kara matsawa kusa da Munaya, a daidai lokacin nurse ta shigo, ya dago kan Munaya data kife kan gawar Amnah ya ga ta suma, ajiyar zuciya yayi, yayin da lugudan bugun da kirjin sa ke yi ya ragu, ya mayar da rufin Amnah wanda Munaya ta yaye, sannan ya dauki Munaya zuwa wani dakin domin bata taimakon gaggawa, bayan ya fada wa nurse din da a shirya gawar Amnah shi zai yi settling sauran bill’s dinsu.

Zaune su mummy suke a Wasu alfarman kujeru dake dakin, sam mutum bazai taba zaton dakin mushiriki bane, yafi kama da normal falo irin na masu rufin asiri, bambancin dai shi wanna dakin akwai abubuwan duba a ciki da sauran kayan aiki da mushrikai kan yi amfani da su.
Cikin karan sauti, takalmin mutumin ke tunkora inda suke zaune kana ya bayyana a falon cikin shigar alfarmar tamkar malami har da dan carbin sa, a zahiri idan mutum ya ganshi zai yi tunanin mutumin kirki ne, sai dai a badini sam ba haka yake ba, son zuciya da son duniya ne fal cikin sa, fuskar sa babu yabo babu fallasa ya zauna a kujerar dake kallon su mummy, mummy cikin rawar jiki da baki tace “Barka da fitowa malam” har da dan rissinawar ta…

“Yawwa sannu ku” ya amsa .

Hajiya maimoon ta zunguri mummy alamun tayi magana, mummy ta sake gyara zaman ta tace “Malam na aiwatar da komai yanda ka umarce ni, sai dai har muka taho nan bai zo gareni ba kamar yadda ka fada….”

“Sa’adah kin yi kuskure!” Ya katse ta cikin Muryar sa mai kaushi.

“Kus…..kuskure kuma malam?” Mummy ta fada cikin damuwa daya bayyana a fuskar ta.

“Eh kwarai kin yi kuskuren barin sa fita, kinyi kuskuren barin wani ya ganki”

“Innalillahi wa Inna ilahi raju’un! Ban bari kowa ya ganni ba wallahi, ban san waya ganni ba, ni daka ce za a dinga k’awata masa sura ta na zata ko a ina ne yake zai dawo gareni malam, shiyasa na bari ya tafi, da yake kaninsa na nan da safe na rasa yanda zan yi kin hana sa fita gudun kada ya zargi wani abun” Mummy ta fada hankali a tashe har hawaye ya cika idanunta.

Mutumin ya sake gyara zaman babbar rigar sa yace “kuma mafi girman kuskuren da sakacin ki ya janyo shine Maleek ya sadu da wata mace, macen ma karamar yarinyar….”

“Na shiga uku” mummy ta katse mutumin hadi da mikewa tsaye ta fashewa da kuka, tamkar zararriya ta tayo kan Mutumin, sai kuma ta durkusa a gaban sa tace “dan Allah dan Annabi malam ka taimaka min, wallahi zuciya ta zata fashe, ina matukar kishin sa” ta karasa cikin dacin murya alamun abinda take faɗa daga can kasan zuciyar ta yake fitowa”

Hajiya maimoon ta mike zuwa inda mummy ke durkushe ta kamo ta cikin rarrashi take fadin “haba Sa’adah ki nutsu mana a samu mafita, ni wanna yaron ko shine autan maza sai haka, gaba-daya kin damu kanki domin shi, bayan akwai maza zarata cikakku bila adadin a duniya”

Mummy kam bata ma jin abinda kawarta ke cewa, sai rusar kuka take tamkar yar yarinya.

Cikin shakiyanci mutumin daya Kira kan sa malam yace “gwara kina faɗa mata gaskiya, ko ni nan zan jiyar da ita fiye da daɗin da take kwadayin samu daga wanna yaron, amma ba lallai, sai ta amince”

Hajiya maimoon ta masa wani kallo hadi da jefa masa hararan wasa wanda hakan ke nuni da cewa ba sanin yau suka yi wa juna.

Mutumin ya saki dariya, kana ya tsuke fuska tamkar ba shi ya gama magana ba.

Malam ya jefa carbin sa kan tiles din dakin, sai bin carbin yake da kallon tamkar mai neman wani abu a jiki, bayan wasu seconds ya dago hadi dacewa “bana iya ganin fuskar yarinyar har yanzu, haske Mai tsanani ya rufe fuskar ta, sai dai karamar yarinya ce sosai, haka zalika zanen ƙaddara su a haɗe take”

Mummy da tun fara maganar Malam tayi dif da kukan, sai dai tashin hankalin ta ya karu, cikin dacin murya tace “malam ina mafita? Maimoon kin yi shiru, ki ce wani abu”

A dame itama Hajiya maimoon tace “malam ko da wata mafita ne da za a taimaka mana da shi, kawata na cikin damuwa”

” Hajiya Maimoona kin fi kowa sanin ka’idar aikina, bana aiki wa mutum sau biyu, sau daya tak nake aiki akan abu daya, sai dai idan tana da wata damuwar zan yaye mata shi, amma kan yaron nan Maleek babu abinda zan iya yi akai kuma, ta riga tayi kuskure a farko”

Ran mummy a jagule ta mike fuuu ta bar dakin zuwa waje, ita gani take kamar malam baya son mata aikin ne, amma yanda maimoon ke bata labarin sa zai iya cika mata burin ta yasa ta amince masa, mota ta bude ta shiga, tana jiran fitowar Hajiyar maimoona su tafi, ta rufe idanun ta, tana watsafa yanda al’amarin ya kasance tsakanin Maleek da kuma yarinyar da malam yace ya kusanta, tsana mai yawa ta ɗora a kan Munaya duk da bata santa ba, ta bude idanun ta da suka yi matukar kadawa saboda kukan data sha tace “babu macen da zan sake kuskuren ta rabe ka, kai nawa ne ni daya, wallahi zan iya komai domin cikar burina a kan ka Maleek, idan nace komai, ina nufin komai”
*MALEEK!*
A hankali ya fara bude idanun sa da suka bata awani uku a rufe dalilin bacci mai nauyin daya dauke shi, tarr ya sauke idanun sa kan had’add’en pop’n saman dakin, ya yunkura zai mike ya kasa sakamakon nauyi da kansa yayi, har Wani ciwo yake ji, ya lumshe idanunsa hadi da komawa ya kwanta yana cije labb’ansa da suka kara yin ja, tsawon mintuna biyar ya ɗan ji dama-dama ya sake bude idanun sa, wannan karon kan farin sofan da yake kwance ya sauke ta, zaro idanun sa waje yayi sakamakon ganin jinin da ya ɗan bata sofan, sai kuma ya ga wani tsohon jan ribbon na gashi a can bakin sofan, ya runtse idanun sa yana kokarin haɗe tunanin sa waje daya, a hankali komai ya shiga dawo masa daki-daki tun shigowar Munaya office din sa da komai ɗaya faru, cikin sauri ya mike ya naushi bango hadi da dafe kansa, ya dawo bakin sofan ya zauna hannun sa dafe da kansa, “damn it!” Ya faɗa can kasan makoshi yana fatan abubuwan da suka faru su zama mafarki, sai kuma ya mike cikin sauri zuwa gaban cctv Cameran dake dakin yana karfafa wa zuciyar sa cewa mafarki ne, domin babu ta yanda idanun sa biyu zai taba kusantar kazamar yarinyar nan, forwarding zuwa baya yayi, ya ga lokacin daya shigo da Munaya rungume a kirjin sa, sannan yaga ya kwanta ya danne ta, saurin kashe cctv Cameran yayi, lallai baya bukatar ƙarin bayani, a gaske abin nan ya faru, gumi ya ji ya wanke masa fuska, ya dawo da baya ya zauna dabas kan sofa’n daidai lokacin da Shakur ya turo kofa ya shigo, sallamar Shakur ya katse a lokacin da idanun sa ya sauka kan jinin dake sofa, cikin tashin hankali ya yo kan Maleek daya ga ya dafe kansa.

Maleek! Are you okay, Jinin meye wanna?” Shakur daya Dafa shi ya tambaya cikin tashin hankali hadi da duba jikin sa domin ya zata ko wani abu ne ya same shi.

Tsawon mintuna uku kana Maleek ya dago jajaye idanun sa da suka yi matukar kadawa ya zuba su cikin na Shakur, kirjin sa har wani harbawa take, bawai na tsoro ba, illa na tsananin tashin hankali, bai iya karya ba, ba kuma zai fara yau saboda Munaya ba, besides Shakur is his only brother da yake shi a duniya, his other half, bai taba boye masa komai ba, cikin murya mai sanyi kamar ba tashi ba yace “i slept with her bro!”

Wani dum Shakur yaji a kunnen sa kana yace “What! Ban gane ba, wacece ka kwanta da ita?” ya karasa fada cikin tashin hankali mara mistaltuwa ya kuma shiga jero addu’o’i a ransa yana fatan ya kasance mafarki dan’uwan na sa yayi.

Shiru Maleek yayi na wasu sakwanin kana yace “yarinyar daka bawa aiki…”

Shakur’s heart skip a bit, cikin wani irin zafin nama ya cakumi Maleek yace “kana cikin hankali ka kuwa? Don’t tell me Munaya kake nufi? innalillahi wa Inna ilahirin raju’un!”

“Bana cikin hankalina Shakur, i wasn’t my self, Ina cikin maye ne, ina cikin hankalina ka san Bazan aikata hakan ba, kai ma ya kamata ka san da hankalina bazan kusanci kazama kuma karamar yarinyar nan ba”

Shakur da tunda Maleek ya fara magana ya zuba masa ido, yana ganin kamar a Sanja masa dan’uwan sa ne yau, Wato duk da abinda ya aikata yana da kwarin guiwar kiran ta kazama, ya hadiyi yawun daya taru a bakin sa, kana cikin raunananiyar murya yace “daman kana shan giya Maleek?” Ya fada yana jijjiga shi sosai, ga bacin rai ƙarara a fuskar sa, domin da ba dan yana controlling kansa ba, zai iya rufe Maleek da duka saboda yanda ransa ya kai kololuwa a ɓaci.

Maleek sai yanzu ya gane subutar da yayi, amma bashi da zabin da ya wuce fadin gaskiya a yau, “Ina sha Shakur, ina sha tun muna kanana, basan ta yaya ba, na dai tsinci kaina cikin shan Kayan maye ne”

Jikin Shakur ne ya mutu Saboda tsabar shock, ya samu ya koma da baya ya jingina da bango idanunsa kan fuskar Maleek, da wani ne ya fada masa wadandanan maganganun da sai inda karfin sa ya kare, amma abin takaicin dan’uwan sa mafi soyuwa a ransa ne ke faɗa masa ya aikata zunubi mafi girma cikin manyan Manyan zunubai, Maleek ya mike ya isa ga Shakur, a ƙoƙarin sa na son yi wa shakur din bayani, domin sam baya son dan’uwan na sa ya ga laifin sa, ko fara maganar Shakur bai Bari ya yi ba ya daga masa hannu cikin tsananin fushi, kana a fusace ya bar dakin…
Maleek ya naushi bango cikin bacin rai hadi da hargitsa sumar kanshi, ya dawo bakin sofan ya zauna hannun sa rufe kan fuskar sa, jikin sa har wani rawa-rawa yake.

★★★
*Munaya*
A hankali ta fara bude idanun ta, ta sauke su kan farin celling dake saman dakin, tunanin ta ya tsaya cak yayin da ƙwaƙwalwar ta ya daina aiki, Tamkar statue haka ta dawo, tsawon mintuna biyar tana a haka sai ga likita ya shiga, ganin idanun ta a bude yasa ya karaso cikin sauri hadi da mata sannu, ta bishi da kallo, tana ƙoƙarin tuna abubuwan da suka faru amma brain dinta yaki bata hadin kai, bayan wasu mintuna komai ya shiga dawo mata daki-daki har izuwa sanda tayi tozali da gawar Amnah, ta rufe idanun ta yayinda wasu zafaffan hawaye suka zubo mata, ta dafe kanta dake matukar sara mata, sannan ta mike, ta kalli doctor da jajayen idanunta, cikin raunananiyar muryar ta tace “ina Amnah doctor?”

Likita ya sauke ajiyar zuciya, domin ya dauka zaka birkice masa idan ta farka, amma to his greatest surprise ta nutsu, duk da kallo daya mutum zai mata tayi matukar bashi tausayi, ya yi kasa da murya yace “tana gidan ku, na duba address din ne ta file din ta dake asibitin nan, an Mata wanka an suturtata, har za’a sallace ta nace musu kina asibiti, Bara naje na dauko ki domin ki mata sallamar ƙarshe magriba na gabatowa, ko zaki iya tashi muje?”
“Sallamar ƙarshe” Munaya ta maimaita abinda doctor yace, kalaman biyun nan sun narke zuciyar ta, kamar yadda suka mata nauyi a kunnuwan ta, da gaske kenan zata rabu da Amnah a yau? Rabuwa ta har abada! Ta share hawayen daya zubo mata kana ta mike cikin dauriya tayi gaba likitan ya bi ta a baya, yana ƙara mamakin danganan da Allah ya sa mata, domin bai yi expecting nutsuwa da hakurin nan daga gare ta bayan ta farka ba.

Mutanen unguwar su ta gani makil a dan kofar gidan na su, hannun ta dake matukar rawa ta sa ta bude murfin motar, kana ta fito kanta a kasa, nan mutanan unguwar su har waɗanda basu taba mata Magana ba suka shiga yi mata gaisuwa hakan ya balai’n ƙarya raunananiyar zuciyar ta mai cike da damuwowi.

Tsakar gidan su ma ta ga tarin jama’a, domin Amnah yarinya ce mai farin jinin jama’a sosai, kowa nata ne, ta sa kafar ta cikin dakin, nan ta ga Amnah kwance cikin farin kal din likkafani, ta zube gaban gawar hadi da rungume ta ta saki wani marayan kuka, tana jin muryoyin jama’a na bata baki hadi da fada mata cewa ta daina ba a son ana yi wa mamaci kuka, sai da tayi mai isar ta sannan ta bude fuskar Amnah data ga ta kara haske fin yanda tayi dazu a asibiti, hannun ta kan fuskar Amnah da idanunta ke rufe tamkar mai bacci tace “Amnah rabin raina….” Ta kasa karasa maganar saboda wani mugun kuka daya taho mata, tayi kokarin hadiye kukan tace “Amnah Ummu ta tafi, ke ma tafiya Zaki yi ki bar ni? Kece komai nawa, ya kike tunanin zan jure rashin ki? Zan yi kewar ki sosai, ki yafe min, ina ji a jikina Kamar na gaza, kamar ban yi kokari wurin ganin kin samu lafiya ba, ina ji a jikina cewa ban cika wa Umman mu alkawarin dana Dauka na kulawa dake ba, but i tried all i could Amnah, Allah ya jikan ki da Rahama, Allahu Ya sadaki da annabin rahama, Allah yasa ki kasance cikin makarantar Annabi Ibrahim, ki yafe min Amnah, ina kaunar ki sosai, har abada zaki kasance a zuciya ta, Allah ya haɗa fuskokin mu a aljannatul firdausi, till we meet again my blood” ta karasa hadi da dora fuskar ta saman ta Amnah tana cigaba da rera kuka, kusan kowa a wajen sai daya zubar da hawayen tausayin Munaya, har masu shesheka da sautin ya bayyana, a daidai nan mazan suka shigo zasu tafi da gawar domin yi mata sallar, nan Munaya taki sakin gawar ta fara kuka mai sauti sosai, da kyar aka raba su aka fita da gawar, anyi sallar jana’izar ciki har da doctor, sannan aka tafi domin kai ta gidan ta na gaskiya. Hakika Amnah tayi jama’a sosai har wasu mutane na mamakin yawan jama’ar ta.

Zuwa bayan isha kowa ya watse a gidan ya rage saura Munaya ita daya, bata taɓa jin ciwon rashin yan’uwa irin yanda taji ba yau, musamman daya rage ita daya yanzu, tsabar kuka kuwa idanunta har yaji suke mata, suka yi luhu-luhu har bata iya bude su da kyau, amma hakan bai sa ta daina kukan ba, domin data tuno abubuwan da suka faru da ita a yau bata iya rike kukan ta, wanna ranar bazai taba goguwa a ran ta ba, haka zalika shine rana mafi muni a rayuwar ta, wanna rana ta zance bakar rana a gareta wanda bazata manta ba.
Tsoron Allah da nadamar abinda ta aikata ya cika zuciyar ta, tayi matukar nadamar zinar ɗata aikata a yau, gashi kwalliya bata biya kudin sabulu ba, domin samun kudin aikin asibitin Amnah daya sa ta aikata zina bai amfana Mata komai ba, gashi ko aikin ba a kai ga mata ba Allah ya dauki abar sa.
Ta shiga buga kanta a bango tana fadin “kaico na, kaicona, ya Allah ka yafe min, Amnah Allah ya jikan ki, wayyo Allah na” haka Munaya ta dinga kuka tana maganganu masu matuƙar ratsa zuciya har maganar ta ya daina fitowa saboda tsabar kuka, sai a yanzu ta tuna cewa bata yi sallar azahar har zuwa isha ba, ta mike a sanyaye, tana jin kasanta na mata radaddi har yanzu domin tsami wajen ya kara yi sakamakon bai samu kulawa ba, ta taka a sannu zuwa tsakar gidan ko damuwa da duhun gidan bata yi ba, domin gwara duhun nan da take gani a idanun ta akan mugun duhun da zuciyar ta yayi, ta dinga ji kamar zata ga Amnah ta biyo ta hadi da kama hannun ta tace “muna zan biki banɗaki” sai dai ta san har abada bazata kara jin Muryar kanwar ta ba, Domin ita mutuwa gaskiya ce, ba kuma a dawowa, ruwan sanyi ta diba ta shiga banɗakin su, duk da sanyin ruwan da kuma sanyin gari bata ji shi ba, haka tayi wankan tsarkin ta fito, ta daura alwala, kana ta shiga daki ta Sanja wasu kayan, ta shiga jero salollin da ake abin ta a zaune saboda ko jimawa bata iyawa a tsaye, bayan ta iddar ta daga hannun ta sama ta shiga jero addu’o’i ga Amnah sannan ta nemi yafiyar Ubangiji kan abubuwan data aikata musamman na yau, tana yi tana kuka, bayan ta gama ta sulale ta kwanta hannun ta dafe da kanta dake mugun ciwo, sosai ta kudundune kanta kamar kayan wanki, kewar Amnah na nurkukusan zuciyar ta, she’s so lonely, basai an fada wa mutum ba, kallo daya mutum zai mata ya fahimci hakan, ta kuma baka tausayi mai yawa.

_Bayan sadakar bakwai_
*4:34pm*

Tana zaune a dan taskar gidan su ta zuba tagumi, ta ƙara ramewa sosai daman ba kiba ce da ita ba, tunda Amnah ta rasu ba ta sa komai a cikin ta ba sai ruwa. Wani almajiri ne yayi sallama cikin gidan, har sau biyu kana Munaya tayi firgigit saboda nisa a tunani ta zubawa yaron ido, yaron yace “wai ana sallama da Munaya a waje”
Her heart skip a little bit, ta shiga tunanin waye ke neman ta, ta jinjina wa yaron kai alamun “toh” dama da hijab a jikin ta tun wanda tayi sallar Asr, ta mike hadi da zura takalmin ta ta nufi waje tana jin bugun zuciyar ta na karuwa.

No comments