Breaking News

Rainon Soja 5

 *🕊️RAINON SOJA🕊️*


*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story .

              Free page 5




________________________

        MAMAN TEDDY

           Marubuciyar

           My Lady boss

           Walijaam

           Siyasata

           Yar maula 

           Kwaryar sama

           The virgin maid

           Gidan Ƙwarata

           The Sexy Boss

                Yar aiki 

          Bafullatanan Ruga

          X world duniyar shahara

           Mr romantic

           Dijama 

           Kwarton manya

           Yar tsakar gida

           Zuma da maɗaci

           Sadaka yalla

           Yar waye

           Gidan zaurawa

           Taɓarah

________________________

"Da sauran su💃🏻 a yanzu kuma gata ɗauke muku da sabo mai ɗauke da sabon Salo na musamman wato Rainon soja , niko da kaina nace za'a sha duka😹soja da raino ai abun ba'a magana 🤣labarin sai wanda y karanta shi kar ki bari ayi babu ke Hajjaju...labari ne mai tafe da rikirkirteccen Al'amura wanda da fari sai kunce ya abun yake , Gaban yafi farkon🕊️dadi tun a yanzu ina sauraren comments din ku da masu fatan alheri na gode sosai . Sannan masu buƙatar daga farko don Allah kuna rinƙa tambaya ne a wasu groups da kuke ciki , idan kuka biyo Ni ayyukan da hidimomin nawa suna da yawa , bana samun damar turawa ta private 🙏🏻.  Gare ku masu buƙatar fara payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake ; Regular group ₦500 

Vip group ₦1000

SPC payment ₦1500

Via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 Vtu transfer number 09061466409 Yan Niger zaku turo da katin Airtel 500f free page ya fara nisa a page 10 Free zai ƙare maza ku hanzarta wurin biyan naki ana ta payment💃🏻Ni kuma ina ta adding😹🤗 to kar a barki a baya, ko kiyi tunanin samun na bulus mutane na yan amana ne..........!



                     •••••


Ganin haka yasa Ali sakin Murmushi yana saurin ƙarikowa inda Suke.  Da hannun sa ɗaya ya ɗagota yana Girgiza ta tare da yin wani tambul yana juyata sama zuwa ƙasa kan ta na kallon ƙasa yana dariya tare da cewa “ Kema Bara kiyi naki morning exercise ɗin ”. Innalillahi...Aliyu Meye haka? Bafa ƙashi a jikin ta”. Muryar Su Ibrahim ya katse shi a tare . Kallon su yayi yana kallon Ma'eesha dake ɓaɓɓaka dariyar ta babu alamun Taji tsoro . A'a dole itama zata rinƙa yin morning exercise sannan sai nayi mata wanka na bata break ɗin ta kamin mu wuce class . 


Humm to yanzu a ina ne zamu bar Ma'eesha kasan ba zai yiwu mu bar ta anan ita kaɗai ba , sannan kuma ba zai yiwu mu tafi da ita class ba. Areef ya katse Aliyu Haidar da a wannan lokacin yana cigaba da tambula Ma'eesha yanda yake mata kaman ɗan namiji....Itako gani take wasa yake mata dariyar ta take yi abun ta . Ƙwantar da ita yayi bisa gadon nasa yana kama hannayen ta biyu tare da ɗagota sama yana maida ta kusan mintuna biyar yana mata wannan salon motsa jinin nasa , yayin da bai Bama Areef amsar tambayar sa ba.  Jin shirun nasa na wasu mintoci babu amsa yasa Areef juyawa yana nufar Toilet shima don ya fito ya kimtsa sannan sai su cigaba da maganan. 


A haka nan dukan su suka shirya cikin shigar su ta uniform ɗin sojoji duka layi ɗaya suke wato Sojojin Airforce ne. Wannan yasa komai nasu tare suke yi . 


Miƙewa Aliyu yayi yana sauke Gwauron numfashi kana ya kalli Ma'eesha da take bin sa da kallo War War War ta yara . Ina zuwa ma'eesha. Ya furta yana nufar inda yake jin maganan masu kawo masu breakfast.


“uhm common baby ”. Ya furta a lokacin da yake dawowa hannun sa ɗauke da basket dake shake da kayan karin kumallon su . Maganan yayi yana sakin mawa ma'eesha murmushi wanda nan take naga yarinyar ta juya da sauri tana miƙewa tare da rarrafowa zuwa inda yake.  Tea ya fara haɗa mata tasha sosai, kana ya fara kokarin bata shinkafan da mai ne ta ture kan ta don bata buƙata . Murmushi yayi yana cewa “ Ok bari Nima nayi break fast sai mu wuce aji tare 😱” . Humm da rabon yau ma ya ƙara amsar wani horon 🥴 Allah dai ya kiyaye Ali” . 


Yana tsaka da fara break fast din ne dukan su sauran abokanan nasa suka iso don sun kammala shirin su suma , zama suka yi suna fara nasu , wanda kamin su gama ne suka ga Aliyu ya miƙe yana kai hannun sa zuwa inda Ma'eesha take , ɗaukar ta yayi yana nufar Toilet da ita .  Da ido Areef ya bishi , yayin da Ibrahim yace “ Aliyu fa ba zai iya yi mata wanka ba , Mene ya iya , nifa mamaki ma nake yi yanda yarinyar har take dariya da nuna so idan ta gannshi , bai iya komai ba Wallahi , Don Allah ku dakatar dashi Bara na kira Joy tayi mata Wankan just give me 1 minute I'll be back ”. Yana Ida maganan yana miƙewa cikin sauri tare da nufar ɗakin da su joy suke.  Suma tare suke duka a wannan shekarar suka fara karatun duka . 


Miƙewa Areef yayi yana biyo bayan Aliyu tare da shiga Toilet ɗin , kallon kallo suke yi don zaune ya tadda Aliyu ya tasa Ma'eesha yana kallo ya rasa ta ina zai fara wanke ta . Wani dariya ne ya taho ma Areef amma sanin halin Fushin Ali da jarabar sa yasa shi danne ta don dole . Aboki ka dakata yanzu joy zata taho sai tayi mata wankan . Areef ya furta yana ƙariƙawa zuwa ga Aliyu. Kallon sa Aliyu yayi kana juya yana kallon Ma'eesha, ba tare da ya kalli Areef ba idanun sa na kan ma'eesha yace “ Ai matsalar baka gani ba , bafa baf ɗin wanka duba ka ga , to a ƙasa ne za'a yi mata wankan? . 


Eh mana yo shi yasa Nace ka kawota mu kai ma mummyna nasan zata kula da ita sosai.


Please stop saying that..”! Ni zan iya kulawa da Ma'eesha tun da mami ta wulaƙantani akan ta , dole da kaina zan raine ta kuma zata girma cikin kulawa ba zata mutu ba . Cikin sauri Areeef ya ware idanun sa a zuciyar sa yana cewa “ Ai ko indai kai ne zaka raini ma'eesha har girma to ko bata mutu ba ,zata ɗanɗana azaba . Ni kaina azabtar dani kake yi bare kuma ita dakake iƙirarin zaka raine ta ka bata tarbiyya . Sorry for you ma'eesha ”. Yana tsaka da wannan tunanin ne Ibrahim da joy suka shigo Toilet ɗin . Wata irin gabjejiya ce a tsaye take kaman namiji, Ya ne mutumin ? How are you?. Tayi maganan tana kai hannun ta tare da kama hannun Aliyu wanda yayi kinini da rai . Ali ya kake ?”. Ta kuma tambayar sa a karo na biyu wanda a daƙile yace “ Lafiya” . Wannan ce yarinyar ? Wow cutie😻  . Kyaƙyƙyawa ta furta tana kai hannun ta tare da amsan ma'eesha.  Wasa ta fara yi mata tana cire yagalgwalin rigar jikin ta irin ƴan gobe sunan nan , da gani kasan yarinyar ta taso ne in a poor condition sai dai duk da haka kyawunta bai ɓoyu ba don tun a yanzu kyaunta mai fuzgar hankali ne ƙwarai . Sauke ta tayi ƙasa tana fara takawa da ƙafafun ta kana Joy ta sauke heater tana sirka ruwan. Skirt ɗin jikin Ma'eesha ta sauke , yayin da su Aliyu suka ja daga baya suna jiran ta kammala ko nace yana jiran ta kammala ya saɓa kayan sa . 


Muryar Joy yaji tana dariya tare da cewa “ Oh my God, this girl she's beautiful...Areef kaga yarinya tun tana ƙara da shape da hips ? Jikin ta luwai........Keeeeee.....!!! “muryar Aliyu ya katse ta cikin doka mata Wani irin tsawa mai kama da saukar Aradu sai da joy ta firgita , ba ita kaɗai ba ma Har ta ma'eesha kuka ta saka cike da tsoro tana ƙanƙane hannun joy. 


“Dama ku Arna babu wanda ya kai ku Iskanci, to amma ke naki iskancin yafi na kowa , yar iskar banza ...wasu irin ashar yake Aunata mata tamkar wanda yayi zaman tasha, yanayin sa kaman wanda zai buge ta , don jikin sa har tsuma yake yi . Shi kan shi bai san mene ya hasala shi bisa kalaman nata ba . Fice mun daga nan kar ki sake dawowa. 


Kuma malamai duka ku fita Nine zan rinƙa mata wankan ta da koman ta bana buƙatar taimakon kowa , tun da abun ya koma harijanci🙊😹 . Gimtse Dariya su Ibrahim suka yi don yanda joy take kyarma daga taimako sai ta baka dariya . Da sauri ta fice bata ce dashi komai ba . Haka suma suka fita ,suna barin sa daga shi sai Ma'eesha.


Hannun sa yakai yana ɗago Ma'eesha tare da fara cire ƙaramin Pant ɗin jikin ta. A kan ƙafafun sa ya zaunar da ita yana fara Wanke mata jikin ta don yanda ake ma yara wanka bai fa sani ba . Sai da aka gama wanke jikin ne ya fara zuba mata ruwan ɗumin yana mata Wasa da ruwan tana dariya, a haka ruwan da ya ƙarar mata a jiki yafi ƙarfin bokiti babba uku , yanda take dariyar shi yake sanyaya zuciyar sa . 


Kallon Areef Ibrahim yayi kana yace " saura mintuna biyar fa mu makara ”. Shiru Areef yayi kana Adam yace “ Leka kace masa yayi sauri ”. A'a kai dai kaje . Hahahahaha....suka fashe ma Areef da dariya . Ibrahim ne yace “ Wai tsoron Ali kake yi ne ?”. A'a bana ce ba ,amma kai zaka iya zuwa ”. Ok ya furta yana kama hanya tare da kutsa kan sa cikin Toilet ɗin . Wasa yaga yana yi mata da ruwan suna dariya , Dariyar da bai taɓa ganin Aliyu yana yin irin shi ba . Shi da ko murmushi ne sai yaso yake yi. Amma yau dariya har da kyakyatawa da ƙaramar yarinya . Aliyu saura mintuna biyar mu makara ”....Wani ɗauke wutaaa Aliyu yayi cikin fushi da ɗan ɗaga murya ya furta “ Dole sai dani zaku tafi , zaku iya tafiyar ku abin ku ”. Jin haka yasa Ibrahim juyawa har yakai ƙofa Yaji Muryar Ali ya katse shi da cewa “ Daga yau kar wanda ya sake shigo mun Toilet indai ina tare da Ma'eesha 🤗 . Saurin kallon sa Ibrahim yayi kamin yayi magana Nan Take Haidar yace “ Yessss haka nace kar wanda ya sake shigowa ko baku ga mace Bace ita , Idan ina mata Wanka kar wanda ya ƙara shigomun ka faɗa masu ”. Sakin baki Ibrahim yayi yana ficewa daga Toilet ɗin tare da isa inda Su Areef suke yana mai labarta masu yanda suka yi da Ali yanzu a Toilet . 



Wani irin dariya Areef keyi har da buga ƙafa kana Adam yace “ Ok to shi ba namiji bane kenan, me zamu kalla a wannan jaririyar yarinyar? Kai nifa Ban gane ba ne ma🥴 . Ya furta yana kama ƙwiɓin sa . Fashewa da Dariya Ibrahim yayi kana yace “ Kasan halin Aliyu fitina ce kawai irin nashi yake neman kan wa zai sauke ,kaga kuwa ba Dani ba , Ni nayi na class kuma zaku tsaya ne ko na tafi Ni kaɗai . 


A'a mu jira shi ya fito sai mu tafi duka. 


Adam ne ya kalli Areef kana yace “ Ok tom mu jira shi kaga ikon Allah yana fitowa zaice mu fita daga waje ya shirya Ma'eesha 🤣 kar a ga mata jiki . Yarinya kaman kazar turawa wata can ƙasa da ita gata fa gijib. Dariya suka saka baki ɗaya cikin sauri suna ficewa tare da nufar inda ajijiwan karatun su yake.


Shi kuwa Aliyu koda ya fito yaga babu su bai damu ba ,don dama ya kuɗurta a ransa indai ya fito ya gansu sai yasa sun fita sannan zai shirya ma'eesha su tafi aji tare ....jama'a kuji mun Bala'i, ta ina zai yi karatu da yarinya abun da ba'a taɓa yi ba kenan. 


Kallon ta yayi yana tunanin to wani kaya ma zai sanya mata ? Palmers oil ya shafa mata yana ɗaukar kayan da ya cire mata yana mai da mata . Idan kina buƙatar wani Abu Kice Uncle Zan sha ruwa ? Ko zanci abinci idan fitsari zakiyi sai ki mun magana kinji Ma'eesha? Yayi Maganan yana kallon ta , da itama take bin sa da kallo ganin babu alamun ta gane Hausan nasa ne yasa shi cewa “ Bata ma fahimta ba ,muje ”...ya furta yana kai hannun sa tare da goya ta a bayan sa , hannun sa ɗaya yana ɗaukar jakar bayan sa . 


**

Shigar sa ajin yasa duka kowa kallon sa tare da bin bayan sa da kallo ganin kyaƙyƙyawar yarinya tayi lamo kan ta ko hula babu , gashi a warware yanayin tsayin gashin ta da cikar shi kaman yarinyar larabawa yafi komai tafiyar da hankalin su gare ta. Hango Su Ibrahim yayi da Areef Adam a can sama Captain Isma'il yana basu horo , wani kallo Ali yayi masu yana kauda kan sa a Zuciyar sa yana cewa “ Taɓ ashe duk ma saurin da suke yi sun makara ,aikin banza kenan”. Nufar mazaunin sa yayi yana aje Ma'eesha kana ya dawo gaban inda Captain Isma'il yake yana ƙamewa tare da cewa “Morning sir” .


Ya akayi ka zo a makare? Me yasa baka kai yarinyar section ɗin su ba ? . Captain yayi maganan yana kallon Aliyu don a tunanin sa Ma'eesha makarantar yara na cikin NDA ɗin take yi. Magana ce ta fara tashi ƙasa² . Ai ƙanwar Aliyu ce . Joy ne tace “ Eh nima naga suna kama sosai ”. Ɗauke ta ka kaita idan ka dawo kayi joining ɗin abokan naka . Captain Isma'il yayi Maganan tare da kallon ɓangaren da su Areef suke . 


Ok sir . Aliyu ya furta yana isa inda Ma'eesha take , taho ma'eesha ”. Hannun sa yakai yana ɗaukar ta tare da ficewa da ga class ɗin.  


“Khaleel dake can nesa mamaki yake yi a ina Aliyu ya samu yarinya? Gaba ɗaya kan sa ya kulle , Ya rasa wane zai tambaya ,gashi abokanan sa sai tambayar sa suke yi wai dama bayan Jidderh suna ƙanwa ce? . Shi dai ya kasa basu amsa , zuciyar sa fal tsoro halin Aliyu na damunsa. A jikin sa yake jin da wani Abu dai gami da yarinyar haka kurum Aliyu ba zai goyo yarinya ya taho da ita ba . Shi da ko magana bayayi bare wai ya tsaya bata lokacin sa akan yara . 


Bayan Fitan Aliyu kai tsaye section ɗin yara ya nufa da ma'eesha , ba tare da jin tsoro ko abun da zai kai yakawo ba ya kutsa kan sa zuwa class ɗin Anty docas. New comer . Gyaɗa mata kai yayi yana cewa “ eh a bata abinci da duk abin da zata buƙata ”. Cike da kulawa tasa hannu tana amsan ma'eesha kana tace “ Kai ne ka shirya ta ?”. Eh . Ya furta a takaice. Ok bata wanku ba gaskiya, bari a ƙara mata wanka sai na kimtsa taci abinci . Dama haka tsarin wurin yake , yawanci yaran ma'aikata ne kaman dai irin rainon da Mami tayi masu Aliyu,basu da lokacin yaran su , sai na aiki . Anan ake shirya yara ayi masu wanka hatta kaya da Pampers zaka ga anan ake saka masu . Jin maganan Madam docas yasa Aliyu har yayi gaba ya dawo yana kallon Gaba ɗaya yaran da duka sa'oin Ma'eesha ne maza da mata sun kai 15 . 


Eh to Madam hakan na da kyau, amma idan za'a yi mata wankan a dan shiga da ita daga ciki kar yaran waiiiiii....yanda ya tsaya yana ƙasa ƙare maganan yasa Madam docas sakin Murmushi don ta fahimci inda ya dosa ...Ok ai privacy ake shiga dasu kar ka damu . Tom godiya nake.  Yana furtawa ya juya da sauri tare da komawa can ɓangaren su , tafiya ce na kusan mintuna talatin kana ya kai shi .


**


Kina tsammanin Haidar ya maida yarinyar nan kuwa ? Kin fa san shi da kafiya akan abin da yayi ra'ayi?. 


Kallon General Saleh Yelwa Mami tayi kana ta ɗan kalli ɓangaren da Jidderh take , eh ina da yaƙinin hakan , don tun da yake ban taɓa nuna masa fushi irin na ranan ba.  Humm banda abun Ali haidar Haka akeyi da ganin yarinya sai ka dauka ka kawota cikin a halin ka yanda rayuwa tayi wuya a yanzu.  Shine dai Fa Genar , yaro ne komai nasa kaman bana mutane ba , a wani fahimce yake.  


Mami wacce yarinya ce? . Muryar Jidderh ya katse su , cikin sauri Mami tace “ A'a ba zaki fahimci zancen ba Jidderh kin kammala Assignment ɗin naki ki taho muje kiyi barci . Sauke pencil ɗin hannun ta tayi kana ta miƙe tana cewa “Ok Mami mu tafi , Good night Dad” . Tayi maganan tana Rungume General Saleh Wanda ya manna mata sumba yana shafa bayan ta tare da cewa “ Sai da Safe ” . Janye jikin ta tayi tana yin gaba Mami na bin ta a baya suka nufi bedroom ɗin ta ....Niko kayan jikin jidderh kawai nake kallo.  Wasu irin tsadaddun haɗaɗun English wears ne na barci masu laushi da salɓi yana kama jiki.  Yanayin shigar yarinyar kaɗai zai tabbatar maka da waye iyayen nata . Wandon iya cinya ne sai rigar bata gama rufe mata ko cibi ba . Sai Hular ta .ƙafarta kuma cikin room slippers ɗin ta .....”.


**

Aliyu baka da hankali ne wai abun da nake ji a bakin su Areef da gaske ne , Aliyu magana fa nake yi ka mun shiru...? Khaleel ke maganan cike da nuna damuwarsa da kuma tashin hankali akan babban lamarin da Aliyu ya ɗauko masu.  


Kallon Khaleel Aliyu yayi kana yace “ Ina zuwa Ya Khaleel Bara naje na duba ta na dawo sai kaji yanda abubuwan suke”. Babu abun da zanji....! Khaleel ya katse shi cike da ɓacin rai . Cigaba yayi da cewa “ koma meye ka tabbatar ka maida ta inda ka ɗauko ta ,ba zaka jefa kan ka a matsala ba , ba kuma na buƙatar jin komai daga gare ki kaji me nace maka”. Shiru Ali yayi kana ya ɗago idanun sa yana kallon Khaleel, Murmushi ya sakin masa kana ya Girgiza kai yana cewa “ Ok ai Shikenn Ya Khaleel ” . Yana furta haka ya juya da Sauri don sun samu free period ,wannan yasa shi ɗaukar Hanyar section ɗin da ya kai Ma'eesha. Baya tunanin Masifar da zai dauko ma kan sa.  Bai biya koman ta ba ya kai ta aji ana kulawa da ita kuma baya jin tsoro ko tunanin wani abu . 


Ta window ya leƙa anan ya hango Madam docas riƙe da stick na pointing bord tana gaban allon tare da yi ma yaran karatu . Hango ma'eesha yayi a front seat tana zaune tana kifa kanta alamu barci ta fara ko zai ɗauke ta . Cike da zimma ya shiga cikin class ɗin yana kallon Madam docas tare da ɗaga mata hannu yana yin alaman ta dakata tayi shiru .


Kallon sa Madam docas tayi cike da rashin Fahimtar meyake nufi ,anan ne taga kuwa abun da yake nufi 🤣 don gani tayi Aliyu na bi layi layi yana kwantar da yaran suma wai suyi barci tun da Ma'eesha na barci to kar Madam docas tayi karatu ta tayar da ita , haka sauran ɗalibai suma kar suyi surutu🤐 .



*To jama'a kar ku manta littafin rainon soja na kudi ne regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 080812029232 yan Niger zaku turo katin Airtel na 500f.*

No comments