Breaking News

Tayi Min kankanta 10


10*

Murmushi mummy tayi ta dafo kanta tace “É—iyata sauÆ™i yasamu kenan?”
Murmushin itama zahra tayi ta sunkuyar da kai ƙasa,
Daddy ne ya Æ™araso gurin ya zauna sannan yace”dama wannan lokacin nake jira kuma gashi Allah ya kawo mu,zamu so ki sanar damu ko ke wace ce,dan musan taya zamu taimakeki ki koma ga danginki”

Hawayene ya zubowa zahra tasa hannu ta goge,sannan tace”ni bani da dangi,baffana yayi hatsari ya mutu,innata Æ´an bindiga sun kasheta,tade taÉ“a shaidamin muna da Æ´an uwa a gombe,kawu modibbo amma sun bar gomben kuma batasan inda zata gansu ba”

Kallon kallo suke tsakanin hajiya da Alhaji,bakinsu har rawa yake gun jefo mata tambayar”ya sunan innar taki na Aynihi?”

“hauwa’u sunanta”ta basu amsa.

Rungumota hajiya tayi jikinta tana hawaye tace”tunda nake kallon fuskarki naga kamar nasanki,amma na kasa gasgata hakan,ashe ko ikai fuskar hauwa nake gani ataki fuskar,Allah mungode maka”

Daddy sosai yake murna da ganin É—iyar Æ´ar uwarshi,hotunan inna nada ya nunawa zahra ayko murmushi take tana faÉ—in”innata ce wannan dama kunsanta”

Daddy ya gabatar mata da kanshi da iyalinshi a matsayin dangin nata yamata bayanin komai,ayko itama kuka tasa najin daÉ—in ganinsu.

Shide Muhammad abun koma masa yayi kamar a film,daga neman shawarar akaita gidan mahaukata shikenan abu ya juye ta komo Æ´ar uwarsa.

Basu bar falon ba se da dare yayi sosai anata hira,sosai daddy yasaki jiki da zahra wacce yake kallo amatsayin sauran danginsa da suka rage masa a duniya.

Washe gari da safe bayan muhammad ya duba zahra,cire safar hannunshi yayi ya janyo kujera ya zauna yana fuskantarta,ita de tunda ta fahimci shine ke dubata kunyarshi takeji,da ƙyar take iya haɗa ido dashi.
“zahra kin bada labarin komai naki,amma baki sanar damu wanda kuma ya miki fyaÉ—e ba?wanda a matsayinmu na Æ´an uwanki zamu so musani”muhamnad yace cikin tattausar murya.

Hawayene ke biyo idonta a hankali tace”na barshi a matsayin sirrina,don Allah karka kuma tambayata”ta faÉ—i cikin kuka.

TaÉ“e baki yayi sannan yace”bazan kuma ba,amma kisani in ni baki faÉ—a min ba dole zaki faÉ—awa mijinki ay”yana kaiwa nan ya fice daga É—akin.

Hankalin zahra yayi ƙololuwar tashi jin furucin muhammad,tabbas dole zata sanar da mijinta wannan mugun labarin,duƙar da kanta tayi ƙasa tana kuka me tsuma zuciya.

A haka mummy ta shigo tasameta,sosai hankalin mummy yatashi janyota tayi jikinta tashiga tambayarta abinda yafaru,cikin kuka zahra tace”mummy yanzu rayuwata a haka zata Æ™are kenan,bazan taÉ“a aureba,in ko zanyi auren dole sena cewa mijina anmin fyaÉ—e? inde hakane nida aure har abada”ta Æ™arasa maganar cikin kuka.

Tausayintane ya kama mummy ta shiga rarrashinta da duk wata kalma me daɗi,da ƙyar tayi shuru.

Mummy É—akin daddy taje tasameshi yana shirin fita,ganinta cikin yanayin damuwa ne yasa ya nemi guri ya zauna yace”hajiya lafiya kuwa?”

Cikin damuwa tace”Alhaji yarinyar nan na cikin damuwa gameda fyaÉ—en da aka mata, baka ganin akwai buÆ™atar a binciko ko waye a hukuntashi sannan asa shi dole ya aureta?”

Shuru Alhaji yayi na É—an lokaci sannan yace”nemo ko waye beda wani amfani,fyaÉ—e de anriga an mata,ba abinda ze sauya hakan,kuma ni modibbo inde na isa da Muhammad to tabbas shine ze auri Zahra,dan shi kaÉ—ai ze rufa asirinmu”

Mummy itama ta gamsu da bayanin na alhaji,dan haka kwarin guiwa ta ƙara bashi kan ƙudirin nasa,sabida Allah yasani tana tausayin zahra matuƙa.

Alhaji be samu zama da Muhammad ba seda dare bayan ya dawo daga gun ayki.
Lokacin daya sanar dashi hukuncin daya yanke akanshi da zahra muhammad kaÉ—anne beyi fitsari a wando ba sabida firgici,bakinsa har rawa yake yace”daddy don Allah kayi haÆ™uri kabar maganarnan,nifa bana sonta,gaba É—aya zahra nawa take da har zaay batun aurenta,ni tayi min Æ™anÆ™anta daddy pls”
YafaÉ—i kamar zeyi kuka.

“muhammad ba shawara fa nake nema ba,hukuncin dana yanke nake faÉ—a maka,wannan duk raayinka ne,ba nawa ba,nan da wanne lokacine zahra zata iya warkewa gaba É—aya” daddy ya buÆ™ata cikin haÉ—e rai.

Jikin Muhammad a sanyaye yace “wata guda”

“nasa lokacin auranku nan da watanni biyu masu zuwa,na É—auke maka komai,kaje ka fara shiri”daddy ya faÉ—i sannan ya miÆ™e yabar gurin.

Muhammad na zaune kamar wanda aka dasa,yama rasa me zeyi yaji sanyi aransa,da ace ze iya kuka to ba shakka kukan ze ta rusawa.

A Hankali ya miƙe ya nufi ɗakinshi jiki a sanyaye ya faɗa gado yana nazari,shide gaskiya tayi mishi ƙanƙanta a aure to in ya aureta yace ya auri wa?shi fyaɗen da aka mata ba damuwarshi bane kawai de shi yafi son mace ƙatuwa ne.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 
*TAYI MIN ƘANƘANTA*


*Zahra Surbajo*

No comments