Breaking News

Tayi Min kankanta 21


*21*

 

Tsawon kwanaki biyu da farkawar hammad aka sallameshi sabida jikin nashi yayi sauƙi.
Sede zahra ita bata jin daÉ—in yanayin yayan nata,sabida gaba É—aya kunyarta yakeji baya son su haÉ—a ido.

Jameel ne ya É—aukosu a asibitin ya kawo su gida sannan yatafi da zummar gobe ze dawo.

Suna shiga cikin falon zahra taja hannunshi zuwa É—akinshi,sede ita abun da bata gane ba koya suka haÉ—a ido kuka yake ta rasa gane kan lamarin.

ÆŠakinshi ta kaishi,sannan ta juya ta koma nata É—akin domin tayi wanka.

Bayan duk sunyi wanka sun kimtsa ne taje É—akinshi tasameshi zaune ya rafka uban tagumi,zame hannayensa tayi sannan ta zauna akan Æ™afafunsa,hannayenta tasa ta sakalo wuyansa tace cikin shagwaÉ“a”yayana wai kode bakaji sauÆ™in bane?”

Kallonta yayi da hawaye cike da idanunsa yace”Naji sauÆ™i mana”

“to me yasa kake kuka?”tasake masa tambaya.

“tausayin kaina nake shiyasa”

‘to ka kwantar da hankalinka ay ina tare da kai yayana”

“kin min alÆ™awarin duk sauyin yanayi bazaki gujeni ba?”ya tambayeta cikin marairaicewa.

Dariya tayi ta faÉ—a jikinshi tace”yayana kenan to ni da na aureka dan ina sonka to ina zani,ay muna tare har abada”.

Sosai ya tattaro natsuwarshi yace,”to shi soja me ulcer meyasa bazaki yafe masa ba?”

ay kamar wacce ya mintsina,zimbur ta miÆ™e daga kan cinyar tashi,hawaye na bin idonta,tace”ay wannan baÆ™in karen har abada ba yafiya tsakanina dashi,ni yaya don Allah kar ka sake min maganarshi”ta Æ™arasa maganar cikin kuka.

Janyo ta yayi jiki ba ƙwari ta faɗa jikinshi sannan ta saki kuka me sauti gwanin ban tausayi.

rarrashinta ya shiga yi yana É—an bubbuga bayanta gamida hura mata iska a kunne.

Sannu a hankali tayi shuru ta dena kukan,suna nan zaune aka kawo musu abinci daga gurin mummy.

Zubo musu zahra tayi suka ci suka ƙoshi,sannan kowa ya nufi ɗakinshi domin gudanar da ibada.

Hammad zafin da zuciyarshi ke masa yafi gaban tunani,ya rasa ta ina ze É“ullowa zahra ya shaida mata shine wanda yay mata fyaÉ—e,tsoron ta tsaneshi yakeji,shiyasa damuwar tai masa yawa.

Haka suka kwana kowa a É—akinshi,hammad yadda yaga rana haka yaga dare ba tare da ya runtsa ba.

Gari na waye ba,yayi wanka ya kimtsa sannan ya fice a gidan batare da ya mata sallama ba ya nufi gurin jameel dan yazo ya warware masa damuwarsa.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 
*TAYI MIN ƘANƘANTA*


*Zahra Surbajo*

*wasun ku basa da uzuri a rayuwa,nace muku ina tare da mara lfy,to surukatace aka kawomin in kula da ita,tsakani da Allah se in barota inzo inta saku nishaɗi,in na samu lokaci ne ko tayi bacci se in ɗan rubuto,amma kunƙi kumin uzuri*

No comments