Breaking News

Tayi Min kankanta 22


*22*

Jameel sosai yayi mamakin ganin Hammad a daidai wannan lokaci,,dan zaton shi ma ko zahran ce ba lfy.

Bayan sun samu guri sun zauna ne,jameel yakai dubansa gun Hammad yace a sanyaye,”me ke faruwa ne abokina?”

Jajayen idanuwanshi ya É—ago ya dubi jameel É—in sannan ya fesar da iska,yace a raunane”captain na rasa taya zan sanar da zahra É“arnar da nai mata abaya,kullum cikin tsinewa soja me ulcer take ina tsoron ranar da tsinuwarta zata bini,so nike in nemi yafiyarta,amma na rasa taya zan É“ullo mata ta fahimceni”ya Æ™arasa maganar kamar zeyi kuka.
Shuru ce ta biyo baya na Æ´an daÆ™iÆ™u kamin jameel ya nisa yace”kuskure de ya riga ya faru,zahra kuma tabbas bazata mance komai ba,sede muyi adduar Allah ya kawo mana abun da sauÆ™i,”

Asanyaye hammad ya amsa da “Amin”

“yanzu muyi breakfast,se kaje ka sameta ka faÉ—a mata komai,sabida zuwa dani ze Æ™ara dagula abun sabida zata ga abun kamar tonon asiri”jameel ya faÉ—i yana kallon hammad É—in.

Haka sukayi breakfast ɗin gaba ɗaya jikin hammad ɗin ba ƙwari,ya nufi gida zuciyarshi cike da tsoro da zullumin me faɗar gaskiyar tashi zata janyo masa

Zahra ko tunda ya fita bata ma san baya gidan ba tana É—aki tana shirga baccinta,shiyasa koda ya dawo gidan beji motsinta a falon ba,É—akinta ya wuce kai tsaye.

Can ya hangeta kwance tsakiyar gado ta ƙudundune da bargo tana baccinta hankali kwance.

A hankali ya taka ya isa kan gadon,zama yayi ya Æ™ureta da ido gaba É—aya nauyi da kunyarta yakeji,a hankali yasa hannu ya janye bargon dake jikinta,a zabure ta mike tana ruÆ™o bargon,kukan shagwaÉ“a tasa mishi gamida faÉ—awa jikinshi tace,”kai yaya bacci fa nikeyi,kuma sanyi nike ji shine zaka buÉ—eni”tayi maganar cikin shirin kuka.

Murmushi yayi sannan ya kwantar da ita akan gadon yabi bayanta yay mata rumfa da faffaÉ—an Æ™irjinshi,yace yana kallon idonta”zahra ta iyayen rigima,to ayi haÆ™uri yayanki yazo kuyi wata magana me muhimmanci ne shiyasa ya tasheki,amma kamin nan maza kije kiyi wanka ki kimtsa kiyi breakfast,gashi can naga mummy ta ayko,se ki sameni a É—akina kinji ko?”ya faÉ—i yana jan dogon hancinta.

Murmushi tayi sannan tace”to yaya yanzu kuwa zanyi duk abinda kace,É—agani”ta faÉ—i tana É—an tureshi.

Ɗagatan yayi ta sauko ta shige toilet,shi kuma ya miƙe ya fice daga ɗakin zuwa nashi,zuciyarshi fal tsoro da firgici.

zahra cikin gaggawa ta kammala komai da yayan nata yace tayi,sannan ta nufi ɗakin nashi harda ɗan gudunta,dan ta ƙosa taji maganar da zasuyi.

Da sallamarta ta shiga É—akin yana kwance akan gado,yayi rigingine yana kallon silin,shigowarta ce tasa ya maido idonsa kanta,

“yaya gani to na gama” ta faÉ—i tana Æ™oÆ™arin zama a gefen gadon,
Hannu ya miƙa mata alamar tazo gunshi,ba musu ta isa kusa dashi ta kama hannun nasa,yajata jikinshi.
Mirginata yayi ta koma Æ™asan sa,shi kuma yay mata rumfa,cikin dauriya yace”zahra ni me laifine agareki,hasalima ni ne wanda ya ruguza rayuwarki abaya zahra in baki gafarce ni ba zahra ina cikin damuwa”ya Æ™arasa maganar hawaye na bin idonsa.

Cike da rashin fahimta zahra tasa hannu ta na share masa hawayen idonsa sannan tace”yaya ka faÉ—amin me kayi min,da har kake neman yafiyata?nayi alÆ™awarin yafe ma insha Allahu”ta faÉ—i cike da tausayinshi.

A hankali ya furta”zahra nine sojan nan abokin jameel wanda yay miki fyaÉ—e acikin bukka ana ruwan sama lokacin da kika nemi jin É—umi daga gareni,zahra nine soja me ulcer da kike kukan faÉ—i lokacin da nike keta mutuncinki”ya Æ™arasa maganar cikin matsanancin kuka.

Zahra jin kanta takeyi yana juyawa,wani zazzaɓi ne me zafi ya kamata nan take,wasu irin hawaye ne ke biyo idonta, duniyar juya mata takeyi,yayinda numfashinta ya shiga yi mata wahalar ja,dan haka runtse idonta kawai tayi ta dena kallonshi,

A jikinshi yaji zafin da jijinta yayi,a tsorace ya ɗagata,yana taɓa wiyanta,zafin da yaji sosai ya gigitashi,ga wasu jijiyoyi da suka fito a goshinta raɗo raɗo,alamun ciwon kai.

A gigice yake jijjigata amma ko motsi batayi,agigice ya kinkimeta yayi waje da ita zuwa mota.

Kwantar da ita yayi a kujerar baya sannan ya zaga ya tada motar ya fincika da gudu me gadi ya buɗe masa ƙofa yayi asibiti da ita.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 
*TAYI MIN ƘANƘANTA*


*Zahra Surbajo*

No comments