Breaking News

Tayi Min kankanta 7


7*

*Bayan shekara É—aya*

“Modibbo É—iyata zata mutu a sansanin Æ´an gudun hijira,kataimaketa!!!! kataimaketa!!! kataimaketa!!!!!!!!!”

A Razane ya farka daga baccin da yake,wani gumine ya karyo masa me zafi,gudun AC dake ɗakin ya ƙaro,sannan ya samu guri yazauna yana tunani gameda mafarkin da yake yi da Hauwa ƙanwarsa,wacce sanadin faɗan da akayi a garinsu yasa ta ɓace wanda sunyi cigiya har sungaji.

To shi wannan mafarkin da yake da ita me yake nufine,yau kusan kwana uku kenan seyayi mafarkin,É—iyarta to dama ta haihune ko ya abun yake,a iya saninshi hauwa nada matsalar rashin haihuwa,kuma mijinta ankasheshi a faÉ—an da akayin.

Haka de yayi zugum shi kaÉ—ai a É—aki yana tunani,to shi wanne sansanin Æ´an gudun hijira zashi,?taya ze iya gano Æ´ar da be san kamanninta ba,?to bama wannan ba shin mafarkin gaskiya ne?wainnan tambayoyi sune ke yawo a kansa da ya rasa amso shin su.

Haka ya kwana be runtsa ba,da gari ya waye bayan yayi sallar asuba É—akin matarsa ya nufa,

Da faraarta ta taso ta tarbeshi,bayan sun gaisa ne,tace cike da kulawa”Alhaji naga kamar kana cikin damuwa?”

“Hajiya kwana biyu ina cikin damuwa,hauwa kullum se tazo amafarkina tana cewa in taimaki É—iyarta,a sansanin Æ´an gudun hijira ni na kasa gane kan wannan lamari wallahi”ya faÉ—i cike da damuwa.

“ka kwantar da hankalinka baban Muhammad,wataÆ™ila akwai wani abu me muhimmanci gameda mafarkin nata nide ashawarata da ka fara duba sansanin Æ´an gudun hijirar kagani ko wani taimako suke buÆ™ata yasa hauwan ke zuwa ma a mafarki”

“kema kin kawo shawara hajiya,zanyi hakan in yaso duk week end na dinga zagayawa guraren da Æ´an gudun hijirar suke,dan abun akwai É—aure kai wallahi”

Haka de suka gama jajantawa modibbo ya miÆ™e ya fice zuwa É—akinshi,wanka yayi ya kimtsa sannan ya dawo dinning suka ci abinci,agurin cin abincin ne yace “Munyi waya da Muhammad É—azu ya shaidamin Æ™arfe biyu na rana zasu iso, kuma hajiya babba jikinta da sauÆ™i,shiyasa ze taho,ki tanaji komai,ni zan fita,zan jima kan in dawo”

murmushi Hajiya tayi sannan tace”lalle Muhamnad yaci saa da hajiya babba ta barshi yataho,ita da tace se ta masa aure sannan ze dawo”

Dariya sukayi irin ta girma sannan yace”hala ta masa matar ne shiyasa tabarshi yataho”

MiÆ™ewa yayi yana kallon agogon hannunsa yace”hajiya bari in Æ™arasa office,zamuyi waya,in kuma naga da lokaci zan É—an leÆ™a sansanin Æ´an gudun hijira dake nan kusa”

A dawo lafiya tay masa sannan ya fice da hanzari,bodygurd É—insa suka mara masa baya.

Ƙarfe huÉ—u modibbo ya baro office,bayan yayi sallar la’asar,kai tsaye wani gidan abinci ya nufa, domin yaci abinci kamin ya wuce sansanin Æ´an gudun hijirar.

A kan idon Zahra motocinsa suka faka,tana can É—ayan gefen titin,da É—an saurinta ta taho tsallako titin dan tasamu tayi bara agunsu ko zasu taimaka mata,dan kwananta biyu yau bata ci abinci ba,agalabaice take ga ulcer ta data tashi,yanzu ko gabanta ya koma ciwo,yana fitar da wani wari me É—aga hankali,ko giftawa kayi ta gunta se kaji warin,shiyasa duk inda tayi ake korar ta,hakanne yasa take samun kan bola tayi zamanta,gudun kar akoreta.

Cikin rashin sani mota tayi ciki ciki da ita lokacin da take ƙoƙarin tsallakowar.

Ƙarar burkin motar ne,yaja hankalin mutane da dama, ciki harda modibbo dake ƙoƙarin shiga gidan abincin.

Da gudu me motar daya bugeta yabar gurin be tsaya ba.
A Hanzarce Modibbo yayiwa bodygurd dinshi umarnin su É—auko wanda aka buge susa a mota,

Hakan sukayi,sede warin da takeyi ne,ya hanasu kuma shiga motar da sauri suka ja baya har modibbo ya ƙaraso.

Warin shi kanshi ya É—aga masa hankali,shiyasa be tuhumesu me ya hanasu shiga motar ba.

Tsayawa yayi shima yana nazari kamin ya ciro waya ya kira matarsa kasancewarta likita,tana É—agawa yace”Hajiya akwai emergency yanzu wani ya buge wata mahaukaciya kuma ya tsere,in kaita asibiti ne zaki je yanzu ko in kawota gida?”

“Gaskiya ka kawota gida sabida muhammad be daÉ—e da dawowa ba bazan iya fita in barshi ba,amma in kukazo naga yanayin lalurar dole se anje asibitin semu tafi”.

Yana kashe wayar ya faÉ—a motar da kansa yaja,da gudu suka shiga sauran motocin suka mara masa baya zuwa gidan.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 
*TAYI MIN ƘANƘANTA*


*Zahra Surbajo*

No comments