Breaking News

Waminal Hoob 14

Waminal Hoob*_ 14

PAID BOOK
_Asmy b Aliyu_

Washe gari bata shiga kitchen taya peter girkin Rana ba ,sharar gidan kurum tayi gamida saka Room fresherner,kwanciyar ta tayi a daki har Bayan sallar la’asar bata fito ba,sai Kusan 5 ta fito parlorn turus tayi tsaye a bakin kofa ganin Wanda ke dinning Area Yana cin Abinci xuwa lokacin yyi wanka ya canja kaya xuwa kayan Shan iska ,wata irin sanyayyar ajiyarxuciya ta sauke a boye.jin motsi cikin parlorn yasa ya dago manyyan idanunsa ya kalli inda Yake Jin saitin motsin ido biyu sukayi daita ,tana sanye cikin doguwar rigar Bahrain baka tayi Rolling kanta da veil din duguwar rigar,a hankali yaji xuciyar sa na budewa da sabon wani yanayi akan Nooriyah din,ta karaso acikin dinning area tana masa sannu da xuwa da hanya,Yana danna waya Yake fadin”kin samu sauqi kenan??”ya fada batareda ya kalleta ba ,”Alhmdullh kurum ta iya fada dibar Abinci tayi ta koma cikin parlor ta xauna tana ci tana kallon Tv.dake aiki a parlorn ,Har akayi magrib Yana xaune a parlorn shigewa dakin barcinsa yyi itama ta shige nata dakin,
Basu Kara haduwa ba sai washe gari da safe yyi knocking a kofar dakinta ,fitowa tayi da alamar Bata dde da tashi barci ba.Kallonta yyi sama da kasa,Yana fadin ta shirya xuwa anjima xasu fita shopping Dan sanyi taji aranta dama Kuma xaman gidan duk ya isheta,sai Bayan axxahar suka fita acikin motarsa.duk inda suka wuce sai binsu ake da kallo, shopping yyi Mata na tashin hankali ,suka dawo gida kowa ya shige nashi dakin.A hankali suka fara gaisawa sama-sama Yana samunta a parlor yaxo ya xauna Yana aiki da laptop dinsa Yana Hira daita sama-sama Yana fada Mata taga Amfanin karatu da yanxu baxatayi wannan xaman banxan ba gayanan sai narka kiba take tana axa wasu kumatu.Yana yawan tsokanarta da fadin”Yar baka kin ga Yarda kikayi haske har kin kusa kaini Haske ,Ashe dama kina Haske har haka cikin sati biyu kurum A kasar London…….”sai dai ta kallesa tayi murmushi a hankali suka fara sakewa da Junan su,duk wannan kiyayyar da Yake fadar yana Mata a fatar Baki ne kawai Bai Kai har a xuciyarsa ba.,,ta dayan bangaren farhaan suna waya da akwai Ranar da farhaan ya Kira Aliyu waxeer Yana tambayarsa meyasa Nooriyyah ta canja masa yanxu kodai Yana yimata wani Abune??”nima ban sani ba ka tamayeta Mana.”sai gashi yau Farhaan Shagari yayi masu xuwan baxata a kasar London,malamar ta Linda Wanda Ammah ta bincika Mata baturiyace Yar Asalin Pakistan ce Amma ko Mai na rayuwarta a London Yake ,,bbu laifi tana Dan fahimtar Linda duk da har yau turancin kasar na balain wahalar daita,tasha yiwa Aliyu waxeer complain akan hakan,budar bakin sa yake fadin bbu ruwansa karta hadasa da Ammah.
Tana kitchen tana hada Abincin Rana Wanda Linda ce ta Bata shawarar ta rika shiga internet da wayarta ta hannu tana serching dishes kala -kala Wanda harda na larabawa akwai Idan ta tsayar da hankalin ta xata iya sosai,ranar farko da tayi hada dinner agidan,wani tsoro ya kamata tun a kitchen ta saka peter agaba yaci yaji yyi ddi cikin harshen turanci yake fada Mata ae tama fisa iya girki,Da Aliyu ya dawo tana kallo yyi serving kansa .har ya faraci ya wani dakune Fuska ,Yana kallonta gabanta taji yyi mugun faduwa shikenan baiyi ddi ba.”yau peter wane irin abinci ne yyi haka??”Yana hango tashin Hankali akan fuskarta,cikin rawar Murya take fadin nifa nayi baiyi ddi bane ??”Yarda tayi maganar tabasa Daria,
Murmushi yyi wanda ya tsaya mata arai,
“Kinyi kokari Yar baka.”Ta hade Rai tana fadin bana son wannan sunan.””Ya wara ido Yana fadin ni Kuma Yana yimin ddi,haka ya cigaba da tsokanar ta tamkar ba Aliyu waxeer ba Mai girman Kai da nuna isa,yau ma haka ta kasance ita ke hada masu lunch tareda taimakon peter taji an danna door bell,ta kalli peter tana basa umurnin yaje yaga waye.”ya fita da sauri minti kadan ya dawo Yana fada Mata oga ne shida friend dinsa.”da mmki take ta maimaita Friend kuma??tunda taxo kasar London Bata taba ganin wani Abokin Aliyu yaxo gidan Nan ba…..tana cikin Maganar xuci ,taji an shigo kitchen din kallo yabita dashi na Kusan sakan biyar wandon Jean’s ne ajikinta da Kuma rigarta da ta sauka har kan gwiwarta,sai hula Wanda ana hango tulin yawan gashinta acikin hular.Aliyu ya karaso gabanta fuskarsa bbu wani Annuri Yake fadin”saboda Rashin sanin ciwon Kai xaki tsaya agaban peter haka??”yyi Maganar cike da kishin da baisan Yana dashi ba,
Kayi hakuri kawai ta iya fada masa,kixo kina da bako tunda kin gayyato min shi a gida bbu sanarwa.”Yana fadin haka ya juya gaba daya yanayin sa ya canja,lokaci daya jikinta yyi sanyi Koda ta fita parlorn Bata ga kowa ba,dakinta ta shige tayi wanka gamida dauro Alwallah tana cikin sallah Aliyu ya shigo dakin ya saka key jikin kofar,Yana tsaye har ta gama sallar.Ya kalleta yana fadin kixo ku gaisa bana son doguwar Hira Kuma da hijab xaki fito,
Da haka ya juya Yabar dakin farhaan yaxo kenan??”to me Aliyu keyi haka.”sai taji duk Bata ji ddin xuwan farhaan ba,kamar yarda Aliyu din ya fada haka tayi hijab ta saka har kasa,ranta duk a jagule ta fito falon tana kallon farhaan din dake xaune cikin soofas ya xuba Mata ido har ta karaso gabansa,a daddare ta xauna dayan soofa ta kwakwalo murmushi tamkar na dole take fadin”Sannu da xuwa ,
Murmushin sa Mai kyau yyi Yana kallon yarda ta canja lokaci daya,ya Dan bude ido Yana fadin me besty ke Baki haka my Noor.”Kallon sa tayi Bata ce komai ba sai dai tayi murmushi ,Hira ya Rika yimata tana binsa da ido .da haka Aliyu ya samesu a parlorn ,
Ganin haka Nooriyah ta Mike ta nufi Kitchen da kallo dukan su suka bita ,dama ta riga da ta gama shirya Abinci ta fito tana fadin Abinci na jiransu ,farhaan sai binta Yake da ido ran Aliyu gaba daya a jagule Yake har suka gama lunch,daki Aliyu yyi shigewarsa itama da hanxari ta Mike xata bar wurin farhaan ya wani fisgota ta fado kansa cike da tashin Hankali take kallonsa xuciyarta na tsananin bugawa cikin rawar Murya take fadin”Farhaan meye haka sakeni Mana,
Ya hade Rai ,Yana fadin me na maki kike guduna?”gaba daya kin canja ya fada da Dan daga Murya a muryarsa,tana so ya saketa kar Aliyu yaxo ya samesu a haka Amma yaki sakinta ,
Xuciyarsa na ta fasa gabansa na mugun bugawa ,kar dai Nooriyah ta fara son Aliyu??”da sauri ya kauda tunanin aransa Dan baxai ma yuyu ba,
Sakinta Yayi ya mike Yabar parlorn cikin bacin Rai ya fice daga gidan juyowar da xata yi sukayi ido biyu da Aliyu waxeer ,kallon da Yake Mata yasa Tasha jinin jikinta.bayan farhaan yabi ,acikin garding ya samesa cikin kujerun da aka kawata awajen ,Yana xaune da fuskar damuwa a fuskarsa.xama Aliyu yyi Yana fadin”meya faru Besty??”iska Mai xafi farhaan Shagari ya furxar da jajjayen idanunsa yake fadin me ya canja Nooriyah haka.??”Mena Mata take wani shareni tamkar Bata farin ciki da xuwana,a baya na maka maganar Noor ta canja baka dauki magana na da muhimmanci ba,,meyasa Mata basu da tunani da tabbas akan soyayya??”na fara shakku akan soyayyar da Nooriyah keyi min.”Ya fada muryarsa na karyewa,
Xuciyar Aliyu na bugawa da wani irin yanayi da sabon Abu dake xiyarta xuciyar tasa Yake kokarin dannewa,ko xaya mutu baxai taba cin Amanar besty ba.”Kai watarana sai ka koma karamin yaro akan macce ka natsu Dan Allah.”xanyi magana daita ,Amma ko kadan Bata maraba da xuwanka baxai xama hujja ba believe me??”
Xo muje ka shaki iskan kasar London xuwa anjima xan xauna daku ,ko wanen ku xan tambayesa meye damuwarsa.”Dan sanyi yaji aransa tunda har Aliyu Bai fara sonta ba ,xae yi kokari ya gano hakan a tattare da Noor inhar hakan ya kasance baxai taba yafewa Nooriyah ba,Kuma muddin Yana numfashi a dunia Bata Isa tayi xaman Aure da Aminin sa ba,,koda hakan xai sa ya rasata shima.suna tafe a motar Aliyu Kiran Areefa Mansoor ya shigo a wayar farhaan shagari,,wata irin faduwar gaba ya tsinci kansa aransa yake fadin.'”ita Kuma wannan Jarababbar me xatayi masa da take kiransa,Aliyu ya bude ido da mamaki yake fadin ana ta kiranka a waya baxa ka dauka ba ,tsoro da mugun fargaba suka hade a fuskar farhaan Shagari lokaci daya,maimakon ya dauki wayar kamar yarda Aliyu ya fada sai ya kasheta duka.sai Bayan ishaai suka shigo gidan bbu kowa a parlorn sai kamshin Room freshener dake tashi ya hade da sanyi Ac. Aliyu kallon dinning area yayi ,kafin ya maida kallonsa kan farhaan .
Abinci ko wanka??”wanka dai na gaji ,master bedroom din Aliyu ya shige Yana rage kayan jikinsa.kai tsaye ya tura kofar dakin nata, tana xaune kan sallaya, ba sallar take ba,Amma tayi nisa cikin tunaninta kamshin turarensa da taji tayi sauri dagowa gamida xuba masa fararen idanunta ,shima kallonta yayi kafin ya janye idonsa cikin nata .rufe kofar dakin yayi ya karaso ya xauna cikin soofa ya maida hankalin sa kanta,meyasa kika canjawa farhaan Shagari lokaci daya??”Tambayar da taji ya jefo Mata kenan,danne xuciyarta tayi tana fadin shiya fada maka haka.”Ya girgixa Kai Yana fadin Bai fada min ba ,na lura da hakan ne.”ki shirya ki saka hijab dinki kije kibasa hankuri , he’s ur boy friend Kuma shi din abun so ne a wajenki,,ita dai batace komai ba har ya fice daga dakin tabisa da kallo cike da Jin haushin Farhaan akan me xai Kai karar ta.wannan ma karon hijab ta saka ta fita parlor fuskarta bbu wani walawala tana ta Zama a parlor sai gasu sun fito daga dakin,ko wanen su cikin kayan Shan iska kallo daya ta masu ta dauke Kai ta rigasu Isa dinning area .ta xuba Abunda xata iyaci ta fara ci ba tareda tayi serving ko wanen su ba ,Aliyu duk Yana kula da yanayin ta ,cin Abincin ta kawai take duk ranta a jagule ,
“Irin wannan cin Abinci haka ae sai ki kware my luv.”Farhaan yayi Maganar cikin kwantar da Kai hararar sa tayi taci gaba da cin Abincin ta,ta riga su gama cin Abincin tabar dinning area din.parlor ta koma tayi xamanta ,
Aliyu duk yana kula da yanayin ta farhaan binta kurum Yake da kallo tamkar wani Wawa,shima dawowa yayi cikin parlorn ya fuskance ta da dukkan kwarin gwiwarsa Yake fadin Laifin me nayi maki kike gasa ni haka.”
da dukkan idanunta take kallonsa take fadin”Canjin me ka gani a tattare Dani ,meyasa xan canja maka Kuma.”
Yyi murmushi Yana fadin shikenan ya wuce kaina bisa wuyana,.”Besty ya fadamin Ammah ta hanaki xuwa jami’a ke Kuma kika biyewa Ammah ko.”wannan ba matsala bane farhaan meye na sauri ko yanxu akwai damar haka agaba,Idan munyi Aure sai nayi karatun.”Kalmar da ta shiga cikin kunnen Aliyu waxeer ke Nan,
Wannan kalmar ta kusa rabe masa xuciya gida biyu,,kallo daya yyi masu ya dauke Kai da sassarfa Ya nufi dakin barcinsa Yana kokarin danne wani irin kishi da ya cika xuciyarsa,dauriyar duniya Aliyu waxeer ya tattaro yyi lokacin da ya shige dakin barcinsa Yana Rufo kofar gamida jingina kansa jikin kofar xuciyarsa na wani irin tsalle tamkar xata fito daga kirjinsa sunayen Allah kurum Yake fada aransa ko xai samu sassaucin Abunda Yake ji Akan Nooriyah,yanayi Yana duba agogon dake daure a damtse hannu nsa,mintunan da suke tare yake kirgawa Yana Jin sautin dariar Farhaan shagari da alamar hirar tayi masa ddi.”Wata xuciyar ta fada masa karka ga Laifin Nooriyah tana da shiga Rai,ita Kuma ta biye masa ta saki Baki tana yimasa daria kenan ta manta matsayin ta.”Ya fada aransa kishi na cin xuciyarsa,car key ya dauka Yana fadin bari na bar masu gidan kar su konani tun ban gama tafasa ba…..”Farhaan da mmki yake tambayarsa inda xa yaje wannan daren,karya ya masa wani Abokin kasuwancin sa xai gani yanxu gobe xai bar London ,Yana fada masa haka yabar parlorn batareda ya kalli inda Nooriyah take ba,Kusan 9 ta fadawa farhaan barci takeji xata je ta kwanta.tana wucewa dakin barcinta,ya shige Master bedroom din Aliyu waxeer,ya kunna wayarsa saiga sakon Areefa Mansoor ya shigo ,kiranta yyi tana dagawa ta fara xuba masa Ruwan balai tamkar xata canyesa ta wayar.yaushe ka fara yimin karya Besty??””Ya dakune Fuska Yana fadin karyar me nayi maki,
Wata Daria tayi a wayar.ka hanani xuwa Cyprus na Kai maka xiyara ,kaki xuwa ka kawomin xiyara Amma sai gashi kaje ka kaiwa budurwarka xiyara a kasar London.”gabansa na faduwa yake fadin duk waya fada maki haka??” bakin da naji baxai yi karya ba,
Kasan baxan iya jure Rashin ka na kwana biyu ba,baka ji yarda nake ji bane kasan Aliyu Kuma baya son wannan harkar kansa a duhu Yake har yau,
Nayi booking jirgi ka xuba ido xuwa ko Yaushe xaka ganni,
Wannan tafiar takace Kai kadai bata Aliyu waxeer ba.”cikin Tashin hankali Farhaan Shagari ke fadin Baki da hankali Areefa,ni dae na gama magana bana Jin tsoronka karka yimin Ihu!””……Jin yyi ta kashe wayar Yana kokarin kiranta ta kashe wayar gabaki daya,wani irin xufa Yake hadawa yasan Areefa Mansoor ba wani hankali ne daita ba tunda ta fada da gaske xata xo.”Wai meya ma kaisa fara wannan harkar da Areefa Mansoor??”wane irin Rashin hankali ya tafka haka.”sai Kusan 11 Aliyu ya shigo gidan ko kallon dakin Nooriyah baiyi ba,yyi mmkin idon farhaan biyu har lokacin, Ya fara rage kayan jikin sa yana fadin”Baka kwanta ba kenan,yanxu nake Shirin kwanciya ya fada cike da Rashin
walwala a muryarsa,
Tabe Baki Aliyu yyi gamida shigewarsa toilet…

Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN. ta wannan lambar#
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#

No comments