Waminal Hoob 16
Waminal Hoob_* 16
PAID BOOK
_Asmy b Aliyu_
Kallon Aliyu tayi tana fadin muje kar dare yyi ,Yyi murmushi Yana fadin”ga saurayinki Nan shi xai saukeki,hade Rai tayi tana fadin”Idan baxa kaje ba kabani car key din peter ya saukeni .
Mika mata car key din yyi tana gabda ficewa daga parlorn farhaan ya wani irin fixgota Yana kallon fuskarta ,
Kokarin fisge kanta take ya riketa sosae Yana girgixata a tsawace yake fadin”Kara ki fito fili ki fadamin kin tsaneni kin daina yina yanxu sai na San matsayina a wajenki da wannan munafurcin da kike min,fisge kanta tayi tana fadin”kaje ka fara tambayarka Farhaan
Kaje ka tambayi kanka meyasa alakarmu ta canja.”ka sauya gaba daya tamkar ba farhaan din da Yake sona a baya ba wannan daban ne ,,da wanda na sani,wata irin Daria farhaan din yyi wacce Bata tattare da nishadi acikinta,
Ta gefen sa tabi xata wuce ya Kara fisgota Yana fadin,Ina kike tunanin xakije da wani kato……”!komawa tayi parlorn tana kallon Aliyu waxeer dake kallonsu tun daxu tamkar ya samu Tv.,Yanxu Kai nake Aure ba farhaan Shagari ba,kayi min ixini fita Dan Allah naje gyaran Kai…….”Tayi Maganar da rawar Murya,kalllonta kurum Yake Yana karantar yanayinta nishadin da takeyi xuwan farhaan ya kawarda shi kije kawai Allah ya kiyaye.”Ya fada Yana kallonta fisgota farhaan yyi ya xabga Mata Mari akan fuskarta Yana huci Yake fadin”ni xaki rainawa hankali ,Aliyu waxeer ya daka masa tsawa Yana fadin”Ka fara shaye-shaye ne??”Kai waye da xaka mareta ??”’ka fitar min a gida tun kafin rayukka su baci,ya kalli Nooriyah da hawaye sun gama wanke Mata fuska tana kallon farhaan din,wuce daki.”da gudu ta nufi dakin barcinta tana barin parlorn farhaan ya karaso gabansa Yana kallonsa a xafafe Yake fadin”Ae ni ne dai silar wannan Auren kou.”To ka saketa ynxu kabani takardar sakinta ,,ni da Kai ae kasan mun San hakan,kawai ka saketa ni xanji da sauran nagode da dukkan Karamci ,duk da wata xuciyar tana fadin ka fara cin Amanata shiyasa Nooriyah ta tsaneni, murmushi Aliyu waxeer keyi Wanda ya tsaya iyakarsa labbansa,xuciyarsa ta girgixa akan kalaman da suka fito daga bakin farhaan Shagari sai dai Bai nuna hakan a fili ba,Auren shekara daya kabani ba Auren wata daya ba,macce ce xata shiga tsakanin mu Besty Kuma ka yarda da hakan???”Abokantar shekara talatin tana neman ta rugeje sabida macce.”Ba Kai bane Besty wannan ya canja,Kai kana tunanin xan iya son Abunda kake so.”wani murmushi Mai ciwo yyi Yana fadin” hakan kakeso?? sakin Nooriyah inhar hakan xai sakaka farin ciki kabani wata daya xan fara shawo kan Ammah.”kasan ciwon da take dauke dashi ,xan iya rasa komai Banda mahaifiyata ,Idan wani Abu ya sameta baxan taba yafewa ba.”farhaan yyi murmushi xuciyarsa na tafasa Yake fadin”meyasa baka fada Mata contract marriage bane,akan me xata damu da Nooriyah har haka.”batareda Aliyu ya Kara kula sa ba ya dauki laptop dinsa ya nufi dakin barcinsa da sassarfa ,dauriya kawai yake agaban farhaan da ya ambaci kalmar sakin da ta Kusan tarwatsa xuciyar Aliyu waxeer a wannan lokacin,da ya runtse idonsa maganganun farhaan Shagari ke dawo masa cikin kunnuwan sa,hannu biyu yasa ya dafe kunnuwan sa Yana sauke wani irin numfashi……..A bangaren farhaan kuwa dakyar ya Kai masaukin sa,fridge ya bude dake gefen bed dinsa kwalaben beer ne masu tsadar gaske aciki ya fito da kwalba daya,ya cire marfin ya kafa a bakinsa sai da yaji bbu komai ya sauke haka ya tada kwalbar beer guda ukku da alamar ya Saba Sha sosai ,Amma har ynxu fuskar Nooriyah Yake gani agabansa.watsi da komai na Room din ya shigayi kafin ya xube Akan bed ya shiga surattai.”wlhi tallahi baki Isa ba bbu Namijin da kika Isa ki so sai farhaan Shagari,ni kadai xaki so da ni kadai xaki rayu,bbu namijin da ya Isa ya soki bayan ni!””…….Sai ga hawaye na xuba akan fuskarsa……..saloon din da ba samu xuwa kenan ba har washe gari basu sake haduwa da Junan su ba,kowa da abunda ke cin xuciyarsa .A bangaren Aliyu ya xabi akan ya rage mu’amala da Nooriyah hakan ne kadai xai samu ya rage Jin Abunda Yake ji akanta,duk da xuciyarsa ba karamin axabtuwa take da hakan ba,baisan shi so ba ruwansa da wannan ba .”sabida xuciya an halicce tane da soyayyar Mai kyautata mata ,Yana daukarka minti daya kacal kaji kana ra’ayin mutum,xai iya daukarka kwana daya kaji ka kamu da xaxxafar soyayya Amma Kuma xai daukeka tsayin Rayuwa kafin ka manta wannan soyayyar,cikin sati daya ba karamin axabtuwa Aliyu waxeer yyi ba yarda ya kauracewa nooriya ko abincinta ya daina ci ya daina xama a duk inda take xama,ko gaisuwarta ba ya amsawa cikin kwanakki kalilan nooriyah tayi wani irin Rama ta ban mamaki,
Kasar London gaba daya ta fice Mata arai,
Ko gaisuwarta Aliyu ya daina amsawa,Wanda Linda ta lura da haka, Abubuwan da take ko yamata ta rage fahimtar ta,akwai ranar da ta tsareta da tambayar meke damunta.”Hawaye kawai ke xuba a idonta ta kasa baiwa Linda Amsa,ganin haka yasa Linda ta fada Mata bara ta Bata hutu na sati daya kafin ta dawo natsuwarta,godia tayiwa Linda.tana kwance a dakinta kamar yarda ta Saba,
Wayarta ta fara ring kurawa wayar ido tayi
Har tagama ta katse sai ga wani Kiran ya Kara shigowa tasan shi da mugun naci a Kusan karo na biyar ya sake Kiran ta daga Amma batayi magana ba,ina kiranki a waya baxaki daga ba Wai mena maki Noor kinbi kin tsaneni??”Farhaan Shagari yyi Maganar cikin kwantar dakai,
Hawaye na xubar Mata take fadin bakai na tsana ba Farhaan halinka ne na tsana duk kabi ka canja,ka juyamin baya haka ma Aliyu tun ranar da abun Nan ya faru na nemi farin cikin da nakeyi a gidan sa na rasa ,sai da nace kar ayi wannan Auren gashi yanxu tun baaje koina ba Kai da kanka kakeso ka lalata komai……….”ni na fada maka da bakina ina son Aliyu waxeer ne??”da xakayi min irin wannan mummunan fahimtar ,shuru yyi Yana sauke ajiyar xuciya maganganun ta kurum sun kwashe Rabin damuwar da Yake ciki. Haka Kuma yayi nadamar abunda yyiwa bestyn shi.ina sonki baxan iya rasaki ba wlhi.”Shuru Nooriyah tayi xuciyarta na bugawa da wani irin yanayi.ka kula da kanka ina son na kwanta kaina na ciwo.”Ta fada hawaye na xubar Mata tana mamakin Hawayen da basa gajia da xuba a idanunta tausayin farhaan takeji,Ashe da can baya haukan banxa takeyi akan son da take yiwa farhaan yanxu take ganin banbancin hakan da son da takeyi wa Aliyu waxeer.tana Jin lokacin da Farhaan ya fada Mata Kalmar ina sonki fiye da son da nake yiwa kaina……”Batace komai ba har ya kashe wayar,tana ta kwanciyarta a daki har Kusan karfe 2 na Rana kasancewar week End ne,a hankali ta Mike tsaye tana Jin jirin da takeji tun safe ,tana alakanta hakan da Rashin cin Abinci da baxata iya tuna Yaushene na karshe da taci Abincin ba,lemu da ruwa da bescuit sune Abun shanta Idan suka kare xata koma store ta kwaso wasu,fitowa tayi a falo tayi ido biyu dashi cikin kananun Kaya na Shan iska,
Da mug a hannunsa batasan menene aciki ba.wani irin faduwa gabanta yyi shima dauke kansa yyi xuciyarsa na wani irin Rawa,tana dawo masa da sabon ciwon da ya kwana biyu da mantasa ,duk da xuciyarsa ta kasa cire Nooriyah daga ransa,
Har aransa Yana Jin da gaske ba son Nooriyah yake ba kyawawan halayenta kawai ne yakeso ba ya Mata soyayyar Aure Yana sonta kamar yarda yakeson Batool waxeer.saurin mikewa tsaye yyi gamida daukar car key da alamar fita xaiyi tayi saurin shan gabansa hawaye na xubar Mata da rawar Murya take fadin”me nayi maka kabi ka tsane ni??”Kamo hannunsa tayi tana fadin ka manta Amintakar mu??”meyasa xaka biyewa shirmen farhaan ka yarda da maganganun sa kenan,ganinta kurum Yana ruguxa masa duk wani shiri da yyi axuciyarsa musamman da yaji tattausan hannunta cikin nasa,Xare hannunsa yyi cikin nata idanunsa na juyewa da wani irin yanayi,xamuyi magana wani lokacin inason xama ni kadai.”Ya fada da wata irin murya,ki shirya Mana Abincin dare ya fada Yana barinta tsaye a wajen Dan sanyi taji aranta ,ya fara saukowa kenan har xaice ta hada masu Abincin dare.
Ranar farhaan ya kirasa yafi sau goma Amma Bai daga ba,
Suna da exam’s baxai iya barin Cyprus ba da yaxo har kasar London ya basa hakuri ,shima abubuwa sunyi masa yawa ,Mami ta kirasa an Kai kudin Aurensa da ya ruguxa sauran hope dinsa,da ba Mami ce maihaifiyarsa ba waya Isa yyi masa wannan Karen tsaye da shisshigi acikin Rayuwarsa , sunyi waya da Aunty Nafisa wato yayarsa ita ta tabbatar masa da hakan,haka tace yakira xahra a waya tana ta korafi baya kiranta haka itama Idan ta Kira Bata samun sa,su basu sani ba ya dde da yin blocking dinta,Koda rantsuwa nawa xaiyiwa Mami akan xahra azeex Ali Yar hannuce baxata taba yarda ba,xata iya cewa sharri yayi Mata dama ya nuna bayason Auren tun farko
Bbu Abunda Bata Sha na kayan maye ,,haka tasan maxa kala-kala a rayuwarta shi baxai iya Aurenta ba wlhi ,yadai gama karatun Ya dawo gida ya fuskanci Mami.Shima exam’s kawai Yake Amma hankalinsa gaba daya yayi gida Nigeria……..da murnarta ta shiga kitchen Bayan la’asar har sai da peter yyi mmkin hakan,Tuwon shinkafa Mai Rai da lafia tayi masa,Wanda kafin ta gama kamshi ya cika koina ,tana gamawa ta hada masa coconut juice Dan tasan Yana sonsa,Wanda ta lura Aliyu ya fison juice din gargajia fiyeda na kanti,Ana gabda sallar magrib ta jere komai a dinning Area,Koda ta koma dakinta Kusan 5 miss call ta gani duk daga farhaan,wanka ta shige .tana fitowa mayukkan ta kawai ta shafa masu sanyayyen kamshi ta nemi riga marar nauyi ta saka ta tada sallar magrib tana cikin sallar taji rurin motar Aliyu da alamar ya dawo.kusan bakwai da rabi ta fito daga room dinta cikin shigar doguwar rigar Abaya kalar maroon Mai ratsin Baki ajikinta sai veil din da tayi Rolling kanta dashi,Bata samesa a parlor ba tasan Yana bukatar wanka da gabatar da sallah,xamanta tayi a parlor gamida kunna tv.tana kallon program din da suke na tashar larabawa,sosai ta maida hankali suna fada cikin harshen turanci Wanda ta fahimta tana rubutawa a takarda ,Wanda Bata fahimta ba xata nunawa Linda tayi Mata bayani,tana cikin rubutun sai Gaya ya fito,yyi wanka har ya sauya kayan jikinsa.
Wani irin sanyi nooryn taji lokacin da taci karo da kyakkyawar fuskarsa,shima a wurinsa hakan ne sai dai dukan su bbu Wanda ya nuna hakan a fili Kai tsaye dinning Area ya nufa,ita tayi serving dinsa da yarda ta lura ya natsu Yana cin Abinci tasan yamasa ddi,ke baxaki ci Abincin ba.”Yyi Maganar da sauti marar Amo.,,sai lokacin yyi Mata magana tun xamansa ,Bata kallesa ba take fadin sai xuwa anjima.sabida saurayinki na fushi dake shine xaki kashe kanki da yunwa.”wannan karon da Dan daga Murya yyi Maganar Kuma akwai wani yanayi na kishi acikin muryar tasa Wanda baisan Yana dashi ba,ta girgixa Kai tana fadin ba Saboda shi bane bana son naci Abinci banyi sallar ishaai ba ,farhaan yanata Kiran ka a waya kaki ka dauka “.dan Allah kayi hakuri cikin fushi yyi hakan.”kallonta kurum Yake da wani sabon bacin Rai acikin fuskarsa,tambayar kansa Yake Yaushe suka shirya suka Jone kansu wuri daya.”kenan shine mahaukaci sun ware kansu gefe suna faranta ran Junan su ,Jin yyi Abincin ya fice masa arai sabida kishi mikewa tsaye yyi
Ta kallesa da mamaki
Tana kallon Abincin da iyaka Rabi yaci ko coconut juice dinsa Bai shaba,bar Mata wurin yyi batareda ya Kara kallon inda take ba ,xuciyarta na bugawa take binsa da kallo.tayi tunani iya tunani Bata hango Kalmar da xa fada Dan ta Bata masa Rai ba,kodan tace sai tayi sallar ishaai xata ci Abinci shine yyi fushi??”har aranta Bata Jin Maganar farhaan xata Bata ransa lokaci daya…..Kusan 9 tayi fito wanka kenan Dan tana so ta kwanta da wuri yau ,taji ana knocking kofarta da sauri ta xura hijab tana basa umurnin ya shigo ,Kai tsaye ya sanyo kansa cikin room din da sallama a bakinsa cikin Italyn suite bakake da sukayi mugun karbarsa.yyi kyau har ya gaji kallonta yyi daga dama har kasa ,
“Ki shirya yanxu xaki rakani wani wajen.”da haka ya juya Yabar kofar batareda ya Kara kallonta ba, murmushi ta shigayi ita daya Aliyu waxeer Yana da wani irin good personality da ba duk maxa suke dashi ba,
Tukish gown ce a jikinta kalar mint green Wanda tayi Mata kyau sosai,itama kallon kanta ta shigayi a madubi turarrukan da take amfani dasu ta saka da Wanda Aunty Ramla waxeer ta Bata tace ta rika using dashi duk lokacin da xata kasance tareda Aliyu waxeer,tana fada Mata turaren Kusan 50k ta sayeshi Yana mallake xuciyar maxa,baa fi sati da sukayi waya ba ta Kara tambayarta turaren da tabata tana amfani dashi kuwa Yana da kyau.”kunya yasa ta fada Mata Yana da kyau,Alhalin Bata taba amfani dashi ba,tasan ba Auren gaske bane.”Amma kasancewar xata fita da Aliyu waxeer yasa taji tana son amfani da turaren ko kadan ne,maybe yace Yana son turaren ko ya yaba kwaliyyarta,Babu wani tunani ta bude Yar karamar kwalbar tana jujjuya sa a hannunta Wai wannan shine dubu hamsin?”kadan ta xuba a hannunta tabi koina ajikinta dashi har akan dogon wuyanta.cover shoe ta xura a kafanta Wanda sukayi shige da gown din jikinta,A hankali ta tako cikin parlorn Yana xaune cikin soofa yyi crossing leg’s dinsa Yana danna waya,kamshin turarenta yasa yaji tsikar jikinsa na wani irin tashi catching breath dinsa ya shigayi tamkar Mai Asmaa,wani irin tari ya shigayi da sauri Nooriyah ta nufi kitchen Dan dauko masa Bottle water,Mika masa tayi ya amsa sai da yyi rabi ya Mika Mata sauran dawowa tayi gabansa tana jera masa Sannu ,mikewa yyi ya nufi kofa turarenta na Kara saka sa cikin wani yanayi Bai taba Jin irin wannan kamshin ba rabonsa da Jin haka,tun ranar da aka daura Auren su.”meyasa yanxu xata saka,Jin yyi tamkar ya fasa fitar Amma yasan xaisha korafi wajen Khaleel waxeer,yau Yake birthday a gidan sa laylah waxeer ta hada masa Party,Abokan business dinsu duka ta gayyacesu.Haka Ammah ta matsa masa Akan laillai yaje da Nooriyah,A mota ya dubeta da idanunsa da suka fara canja kala,Yake fadin meyasa kika saka wannan turaren bana Jin ddin sa.da sauri ta kallesa gabanta na faduwa,,Amma Kuma Aunty Ramlah ta fada Mata turaren Yana da kyau,meyasa shi baiji ddin sa ba.”shuru kurum tayi masa tana ganin yarda Yake tukin motar duk baya cikin yanayi Mai ddi sai Tasha jinin jikinta tana da na sanin sakawa…….
Waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin Wayar MTN.ta wannan lambar #
09060259200
Shidar Biya ta wannan lambar
08086207764#
_Duk barauniyar da ta karanta min book Bata Biya ba ban yafeba.”_??
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??: *
Post a Comment for "Waminal Hoob 16"