Waminal Hoob 18
Mom Aydah??: 18
Sai da Aliyu yayi
xaxxabin kwana biyu ko kofar parlor Bai fito ba nooriyah itace Mai jinyar haka duka ya kashe wayoyinsa,
dakinsa ta tare ana jinyar tare .da dare yayi xata hau kan doguwar soofa dinsa dake dakin tayi kwanciyarta ,shi Kuma Yana kan bed arana ta ukku ne ya samu sauqi har ya samu damar fitowa cikin parlor ta kasance Ranar talata Aliyu Bai fita aiki ba,
Nooriyah na kitchen tana shirya masu
lunch,sukaji ana buga masu door Bell har ta fito xata nufi kofa ya dakatar daita Yana fadin taje tayi aikinta xaije ya duba,Bata yi musu ba ta koma cikin kitchen din,Yana bude kofar sukayi ido biyu dashi tana cikin shigar riga da wando da bakin glass a idonta,sai Dan karamin veil da tayi Rolling kanta dashi Wanda Rabin gashin dokin da tayi Kari dashi duka a waje tamkar ba musulma ba,tana jayeda Yar karamar trolley ware masa ido tayi ta saki trolley din Hannunta ta wani shige jikinsa ,
Tana fada masa tayi kewarsa sosai.jin shuru yasa Nooriyah fitowa daga kitchen ta nufi kofa turus ta tsaya gabanta na mugun faduwa mugun ganin da tayi ,Juyawa tayi batasan lokacin da hawaye suka fara Rolling Akan kyakkyawar fuskarta ba,badai Aliyu bin Mata ya farayi ba??”ita kuma wannan kyakkyawar baturiyar a Ina ya samota.”Juyawa tayi ta koma kitchen Haka hawaye Basu daina xubar Mata ba,haushin kanta take ji meye Kuma na kuka??”wata xuciyar ta fada Mata tana son Aliyu waxeer haka tana kishinsa baxata iya kallonsa da wata macce ba,da sauri Aliyu ya rabata da jikinsa ya shiga dube-dube kar Noory ta gansu girman da take gani nasa yaxube a idanunta,da murnar Areefa Mansoor ta nufi cikin parlorn ta xauna acikin fararen soofa,shi dae Aliyu Yana tsaye ya kasa xama .Areefa ta kallesa da mamaki tana fadin”Banga kana farin ciki da xuwana ba baby??”kayi Rashin lfy ko ka sanarmin ta waya”.
a wajen laylah na samu lbr.”kasan Saboda Kai kawai naxo kasar Nan ,yanxu haka exam’s muke bana fahimtar komai sabida ciwon ka,Amma akwai wacce ke rubutamin exam’s din.”ta karasa Maganar da murmushi tana kallonsa.”You are so careless Areefa kuna exam’s shine xaki tsallake karatunki kixo.”Ta turo Baki tana fadin ,nidai ya wuce tunda na riga da naxo din yanxu ka fara bani Abinci yunwa nakeji.”xuwa Nan nayi wanka mu fita yawo, na riga dana Nasha barci acikin jirgi. Juyawa yayi ya nufi hanyar Kitchen xuciyarsa na bugawa bai san mexai fadawa Noory ba Kai tsaye xae fada mata budurwarsa ta kawo masa xiyara tun daga kasar Egypt………Yankan Albasa kawai take hankalinta baya kan Abunda take,hoton Aliyu waxeer da kyakkyawar baturiya ke dawo Mata,batayi aune ba taji ta datsawa kanta wuka,Karar axaba ta saki gamida wullah wukar gefe dai-dai lokacin Aliyu ya karaso cikin kitchen din da sauri ya nufeta ,
Yana rike hannunta Yana kallonta cikin taushin Murya yake fadin”bakya bin komai Ahankali meya kaiki yankewa mekike tunanine Haka??”Hawaye taji suna ciki Mata ido hannun ya Tara a famfo Yana wankewa ,runtse ido tayi shiya yimata dressing hannun,ya kalleta yana fadin”muna da bakuwa ki shirya Mana lunch nasan kin gama ,kallonsa tayi tamkar ta tambayesa wacece?”sai Kuma ta share ,Juyawa yayi Yabar kitchen din tabisa da kallo xuciyarta na narkewa Ahankali da wani irin sonsa,Haka ta jera komai a table Areefa sai kallonta take cike da kishi Bata san meyasa ta kishinta ba,ko gasar sauraniyar kyau xasu fito tasan itace kan gaba,tafi Nooriyah kyau wayewa, kudi ,komai da komai ta fita Amma batasan meyasa taji Nooriyah din Bata yimata ba karon farko da ta ganta kenan. Idan farhaan ya Aureta duk dadin da Yake Bata xai maidasa ne Akan Nooriyah??”wani irin kishi taji ya taso Mata ,batasan tana kishin farhaan Shagari har hakaba sai da taga Nooriyah agabanta a matsayin wacce Yake tsananin so da kauna……..tasan Bata da matsala akan Aliyu waxeer miskilin gaske ne ba komai ke burgesa ba haka yarda tasan halin Aliyu waxeer tasan tsarinsa,
Xaiyi wuya yaso nooriyahkasancewar ta bakar macce. murmushi tayi na gefen Baki,tare dukan su sukayi lunch Areefa sai baiwa Aliyu labarin karatun ta take ,sauran 6 month ta gama komai da komai na karatunta harta project nata.sai Maganar Auren su.”Jin Maganar Aure yasa Nooriyah ta shiga tari da karfi ,da sauri Aliyu waxeer ya cika glass cup da ruwa ya Mika Mata Amsa tayi tana fadin”Ta gode,ta rigasu barin dinning Area din Areefa Mansoor tabita da wani shegen kallo ,da gudu ta nufi dakinta gamida Rufo kofar kukane taji Yana xomata Wanda Bata shirya tarbarsa ba,wannan kenan itace Areefa Mansoor itace budurwar Aliyu waxeer.”itace Yake da burin Ya Aura,dole Aliyu waxeer yaki kallan kowace ya’h macce a dunia ,gaya da Areefa Mansoor ko ita dake matsayin macce ta yaba kyawun Areefa Mansoor da jar fatarta,wani irin kishin Areefa Mansoor taji yaxo ya rufe Mata xuciya,xamanta tayi a daki.kusan minti talatin sai gashi ana buga kofar dakinta,shuru tayi tamkar baxata bude ba sai Kuma ta bude kallon cikin idanunta Yake,kafin yace meya samu idon naki.?””Bata kallesa ba take fadin babu komai ta juya ta koma cikin room din tabarsa Nan tsaye ,karasowa yayi cikin dakin Yana kallonta.kiyi hakuri ku xauna daki daya da Areefa kwana biyu kawai xatayi yanxu ma tana so tayi wanka,taxo ga dakin Nan ni xan koma boysquaters.”tayi Maganar cike da wani irin kishi.babu bukatar ki koma acan Idan bakison takura sai ta xauna a dakina ni Kuma na dawo naki dakin??”haka yayi maki,daga Kai tayi tana kallonsa shurunta yasa ya juya Yabar Mata room din ,
Sai gata ta biyo bayansa da sauri Areefa na kasan stairs tana kallonsu,kabarshi muyi using nawa.”da Haka ta juya ta koma dakinta,sauka kasa yayi Yana fadin muje kiyi wankan a dakin Nooriyah .”lokaci daya Areefa Mansoor tayi mugun hade Rai tana kallonsa da mamaki take fadin”dama idan naxo gidanka Raba daki mukeyi??”ki fahimce ni Areefa bamu kadai bane a gidan Nan .Haka ko muna kwana daki daya ae ba waje daya muke kwana ba”Baki wangalau ta saki tana kallonsa,
Saboda itane xaka canja???”Bana son musu plz Areefa kaina na ciwo,xai dauki bag dinta tayi saurin dakatar dashi da mugun fushi take fadin”plz kabarsa muje ka saukeni gidan laylah baxan iya hada daki da wannan kaxamar ba.”wani iri yaji da ta Kira Noory da kaxama,car key ya Mika Mata Yana fadin taje daga baya xai sameta.”kallon mamaki kawai take binsa dashi duk yabi ya canja tunda ya Auri wannan yarinyyar……Amma koma minene xata dau mataki,karbar key din tayi ya subbaci goshinta Yana fada mata anjima kadan xai shigo ,har mota ya rakata sai da yaga fitar ta ya sauke wata irin ajiyar xuciya Mai nauyi ya koma cikin gida,shima nashi dakin ya shige Dan yin wanka…….sakin Baki laylah tayi tana kallon Areefa Mansoor,wani irin murmushi Laylah tayi ta Bata hanya ta shiga cikin parlorn tabita tana fadin”Yaushe a gari naxata fa wasa kike ??”barni nayi wanka na kwaso gajia ,da Haka laylah ta daukar Mata bag dinta xuwa dakin dake kasan parlorn sama Wanda ya kasance Nan ne dakin da suke saukar baki.wanka Areefa tayi ta saka riga marar nauyi tana gaban mirror dressing tana shafa turarrukanta masu sanyi kamshi,laylah waxeer ta turo kofar Mai aikinta na binta a baya dauke da katon tray ta aje Mata akan rug laylah waxeer ta xauna gefen bed tana kallon Areefa din ,ya naganki da trolley ba agidan Aliyu xaki sauka bane.”sai lokacin Areefa ta kalli Layla ta hade Rai tana fadin”Kibarni da Aliyu da wannan bakar yarinyyar kin San rainin hankalin da sukayi min??” Kan up stairs na hangosu suna magana sunfi minti nawa ,sai gashi ya sauko Yana fadin muje dakinta nayi wanka.”Ta karasa Maganar sounding so very Angry,ni xaya kalla yace naje nayi sharing daki da wannan Yar dajin Yaushe ma tayi wayewar da xan hada daki daita.”Yarda yakeyi tamkar Yana tsoronta tunda na sauka gidan bai wani sake Dani ba,tamkar wata shegiya a rabon gado.”Laylah tayi Rolling eye’s dinta tana fadin “mena fada maki akan maxa,you tell me .”ae kin San Aliyu baxai yaudareki ba,maxa munafukai ne.”tsinannune basa Jin kunyar soyayyarki xasu maki tijara da Rashin mutunci idan suka tashi laylah waxeer ta bude ido tana fadin”ko ki yarda ko karki yarda Aliyu ya fara son yarinyyar nan.”Lokaci daya Areefa Mansoor ta dakatar daita tana girgixa Kai tana fadin”Bata yi isar da Aliyu xai sota ba barantana taja hankalinsa,kidaina fadamin haka laylah xuciyata xata tarwatse,laylah ta taba hannu tana Daria tana fadin”xuciyarki kuwa fitowa xatayi Idan Baki tashi kikayi fighting akan soyayyarki ba,tun farkon kinyi babban kuskuren barin Yarinyyar Nan ta shigo cikin Rayuwarsa ,bakiga yarda family waxeer ke sonta ba suke girmamata tamkar diyar wani Kusan gwamnati.”kin yarda maxa suna iya canjawa lokaci daya??kin yarda Aliyu waxeer ya canja.”kin yarda shi din munafukine Yana cin amanarki bayan idonki”da sauri Areefa Mansoor ta katseta cikin tsawa take fadin ki daina fadin Haka ni nasan Aliyu waxeer baxai taba iya hada jiki da wata macce ba Bayan ni.”kin manta Aliyuna yarda yake da wani irin aji tayaya xai hada jiki da wannan kaxamar,pls Laylah mubar wannan Maganar tana batamin Rai Dan Allah,
Murmushi Laylah tayi tana juya ido take fadin”Idan na kawo maki Evidence xaki yarda Dani??tashi tayi tabar room din Bata fi minti biyu ba ta dawo da Yar karamar camera a hannunta,xaunawa tayi ta fuskanci Areefa mansoor da taga jikinta yyi sanyi lokaci daya , Mika Mata camera din tayi.buda ido tayi sosai tana kallon Aliyu waxeer dake kissing din Nooriyah with so much emotion and Romantic way”……..Wanda ko ita da Yake dating dinta Bai taba yimata hakan ba,kashe camera din tayi ta mikawa laylah mikewa tayi tsaye hawaye na cika idonta lokaci daya Kuma jikinta na wani irin kadawa tamkar Mai Jin sanyi,da gudu laylah ta tare kofa tana kallon Areefa wacce ta fice daga hayacinta lokaci daya,
“Kefa dadina dake bakida Hankali Areefa wani lokacin??”ina xakije haka.”cikin ihu take fadin xanje na Sami yarinyyar saina kasheta wlhi ita wacece da xata hada bakinta da Aliyu waxeer haka ta hada jiki dashi,toh kina tunanin xai barki ki tabata ne??wani kallo Areefa Mansoor take bin laylah dashi ,ae shima yasan waceceni wlhi tallahi yau koni ko yarinyyar Nan,Sai Aliyu ya Bata takardar sakinta Nan da wani watan xakiji Auren mu na dau Alwashin sai na fitar daita cikin gidan sa,kafin nabar kasar Nan……..Laylah ta girgixa Kai tana fadin baxaki iya ba.”key ta sakawa kofar gamida cire key din,ta kamo Areefa din wacce hawaye sun gama Bata Mata fuska jikinta sai kadawa Yake,ki dawo natsuwarki plz Areefa laylah ta fada mata tana kwantar da kanta kan shoulder dinta,
“Ki xauna a daki yanxu xan Kira Aliyu a waya .xan fada masa bakida lfy yanxo yanxu,,ke kin San yarda xakiji da sauran xan bar maku gidan dama xan fita,komai rintsi kisan yarda kikayi kika rabasu”.haka ban Baki shawarar ki turawa farhaan vedio din Nan ba,kin San mahaukacine shima Alllura ce xata tono garma.”kin yarda da bayani na??shuru Areefa Mansoor tayi karshe rufe idonta tayi mugun kishi nacinta,
Kusan minti talatin da yin wayar,sai ga Aliyu a gidan laylah najin horn dinsa da sauri ta Isa down stairs dama tayi Shirin fita kofar dakin ta tura ta hango Areefa Mansoor a tsakiyyar bed tana xukar sigari,hakan yayi mugun daga hankalin laylah .da sauri ta karaso gabanta gamida fisge sauran ta hannunta ta nufi toilet da sauri tayi flushing dinta,ta dawo cike da masifa take fadin u are very stupid Areefa hakan da kike shi xai canja komai ne.”Idan yaxo yaji room din wani iri mekike tunani??”kina ganin Aliyu tamkar Wawa baisan komai ba,wlhi Yana sane kawai Yana daga maki kafane.”ki daina waya’nann Abubuwan inhar kina so ki shigo cikin familyn waxeer,
Sai ki shirya ga shi can Yana gyara parking da Haka laylah ta juya Rai a bace tabar room din,
Haukan Areefa Mansoor da kishinta na Bata mamaki wani lokaci haka xata tayin Abu batareda tunanin Mai gaba xai haifar ba,
A kofar shigowa yaci karo da laylah ,kallonsa tayi shima kallonta yayi Yana fadin “good evening…….da haka yyi shigewarsa cikin parlor wani banxan kallo tabisa dashi ,har Aranta tana Jin tsanarsa yarda ya xama fav din Khaleel waxeer Ammah dukama familyn waxeer………a parlor ya sameta kwance kan doguwar soofa xubama fararen kafafunta ido yyi kafin ya maida kansa kan fuskarta Yana gani yasan tayi kuka,Abu ga farin mutum.da sauri ya karasa gabanta ya Dora hannunsa bisa kanta ,kalau yaji da sauri ya kalleta da mmki Yake fadin”akace bakida lfy meke damunki Naga idanunki wani iri.batayi magana ba ta Mika masa wayar hannunta,kallon wayar kurum Yake da mamaki.Yasan ko aikin wanene wannan
da mamaki Yake fadin”meya faru Kuma.”cike da mugun Jin haushinsa da kishi take fadin”me kake tunanin kayi Aliyu Yaushe ka xama Maci Amana.”maicin Amanar Abokinsa ,
Yaushe ma ka fara kula yarinyyar Nan ban sani ba???”Yaushe ka sake daita har haka Aliyu da xaka hada jiki daita ,ta karasa Maganar a tsawace.
Cikin tsawa shima ya katseta yana fadin ni yaronki ne da xaki tsareni da waya’annan silly Questions din ,
Sai me Dan na hada jiki daita ban Isa bane ko ban Kai ba,keda ma ba muharramata ba na hada jiki dake barantana ita da aka daura Mana Aure.”da mugun shock take kallonsa hawaye na cika idonta,plz ka fadamin ba gaskiyya bane wlhi xuciyata xata fashe xan mutu Aliyu Idan ka fara kula yarinyyar Nan,Dan murmushin takaici yayi ki tambayi munafukar da ta shirya maki duk wannan Abubuwan ,ya akayi na hada jiki da Noory kwaya ta samin acikin abun Shana,koni dutsene??”yyi Maganar so pissed up ,da mugun mamaki take kallonsa tasan halin Aliyu kaifi dayane baya karya haka baitaba yimata karya ba,Dan Haka Bata ga dalilin da xaisa ya fara yinta yanxu ba,tasan halin laylah da makircinta xata iya fiye ma da haka.juyawa yayi a mugun fusace ya nufi hanyar barin parlorn………
Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN..ta wannan lambar#
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#
ASMY#??
WM#??
Team#NooryAli forever??
Post a Comment for "Waminal Hoob 18"