Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Waminal Hoob 49

15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??: 49…..

Shirye-shiryen dawowa gida Nigeria suke,sabida Areefa ta shiga watan haihuwarta haka har ta haura sati Daya na (Edd)dinta ,noory tana da cikin dan watanni hudu,amma baxaka san akwai ciki jikinta ba sabida tsawon da take dashi,sai ka kulli


fuskarta data canja ta wani irin cikowa,na alamu juna biyu…..Yau tun safe Ammah ke tsaye a kitchen itada daughters inlaw dinta sun sakata a tsaka anata hidimar girke-girke ,itama Xahra gefe daya tana dauke da cikin leel waxeer ajikinta ,sai dai ita bata laulayi bata komai baka ma gane tana da shigar juna biyu idan ba fada maka akayi ba,laylah ta girgixa kai ta kalli Xahra tana fa?in.”ki xauna ki huta dan Allah .”kin san waccan satin sabida motsin da kike har cikin ya fara xuba ko??”Xahra tayi murmushi tana fa?in.”ni narasa keda Khaleel waye yafi kaunar wannan cikin,
Duka muna kaunarsa” ga kujera can gefe jeki xauna ki huta,kin san na matsu naga wannan Aliyun da kowa ke magana akansa,har matar tasa.”dai-dai lokacin Areefa ta shigo Kitchen din dauke da katon cikinta wanda dakyar take tafia acikinsa,da sauri ta kalli Xahra tana fa?in.”waya fada maki Aliyu yana da mata ae baiyi aure ba tukuna,
Wani kallo Xahra ta rikayiwa Areefa mansoor,xatayi magana laylah tayi saurin dakatar da Xahra kar taje ta tona abunda yake binne,
“Ae wannan twins din namu su fito haka ,muyi musha bikin Aurenku keda Aliyu waxeer,ita dai Xahra baki ta bude tana kallon laylah.insha Allahu ,daddyn su kawai suke jira kila ma yau su fito.”daria laylah tayi cike da takaicin Areefa haka tana jinjina karfin hali irin nata take fa?in.”toh Allah ya kawo su cikin aminci yasa su biyo duka kamannin Aliyu Dan yafi ki kyau!”Areefa ta juya ido tana fa?in.”idan ma sun dauko ae uban sune bakiji ance kyan yaro ya gaji ubansa ba.”hira suka cigaba dayi banda Xahra da tabar masu Kitchen din ,ita har aranta ta tsani wannan Areefa mansoor din tunda taji tarihinta, addu’a take su Aliyu su iso lfy da noory taga ya mahaukaciyar xatayi…..A filin jirgin Namadi Azikwe dake Abuja ,ya daga noory sama har zuwa mota ta dunkule kanta cikin jikinsa ganin yarda kowa kebin su da kallo,duk yarda xata hana Aliyu daukarta acikin bayyanar jama’a baya bari abun ya riga ya xamar masa jiki,driver ne yazo daukarsu cikin ferari dinsa back seat ya bude ya sakata ciki ,
Ta bata rai gamida Turo masa bakin ya shafa bakin yana shirin kai masa kiss taja da baya tana wani rufe ido, murmushi yayi gamida shafa kansa,Aliyu ya kalli agogon dake makale da damtsen hannunsa,idan yace xai kwana Abuja Ammah xatayi fada,
Shi kuma yana tausayawa noory sabida zaman jirgi ga na mota kafafunta har sun dan kumbura,ya daga kafafun ya dora kan cinyoyinsa ya shiga danna mata su a hankali,wani irin barci taji yana zo mata
Cikin minti biyar ta samu barci,sai bayan sallar la’asar suka iso Kaduna kai tsaye Mention din Ammah suka nufa,driver har yayi parking ya fita daga motar Noory bata bude ido ba da alamar tana jin ddin barcin,shi kuma baya son tadata Kusan minti biyar,su Ammah duka suna zaune a parlor suna jiransu,
Khaleel waxeer ya shigo Ammah ta kallesa tana fa?in.”ina Aliyu??”shi dai murmushi Khaleel waxeer yayi yana fadawa Ammah yana zuwa ,shafa fuskarta ya somayi a hankali
Cikin barci ta bude ido
Tana kallonsa gamida kara gyara kwanciyarta cikin jikinsa,cikin wani salo da muryar rada yake fa?in.”su Ammah sunata jira wani irin xabura tayi ta bude ido ta xabura da karfi,gabansa na faduwa ya kamata yana fa?in.”komai bakya binsa a hankali ,
Karkije kiyi min illah dan Allah noory…” ya fada yana dan shafa cikinta ,ta buge hannu ta balle karfin motar da sauri shima da sauri ya bude kofar gefensa yasan halinta tsaf xatayi gudu,ya rike hannunta cikin nasa yana fa?in.”ki natsu dan Allah,daga kai tayi a hankali suka nufi Entrance din shiga gidan kowane murmushi kwance a fuskarsa,da wani irin farin ciki Ammah ta kamo hannun noory tana xaunar daita cikin soofa,ta kalli Adama da itama ta kasa boye murnarta Xahra taxo ta bata side hug tana fa?in.”sannu da zuwa sister in-law hakama laylah,Areefa kallonsu take duka with so much shock ,tana jin bayanta na wani irin rikewa lokaci daya.Hannunta na rawa ta shiga nuna Aliyu da Nooriyah,tana jin wani sabon tashin hankali na xiyarar ta tun daga saman kanta har tsakiyyar bayanta,
Aliyu ya karaso gabanta yana fa?in “sannu da gida maman twins hawaye suka balle mata,tana girgixa kai take fa?in.”wa nake gani tare da kai Aliyu??”noory fa dama tana wajenka ta yaya??”tayi maganar tana daka masa tsawa ,Aliyu ya bude mata ido yana fa?in.”a saboda tana matata!””kalmar mata ta shiga maimaitawa ta shiga tafa hannunta tana girgiza kai tana fashewa da daria lokaci daya wacce bata tattare da nishadi,Yaudara ta kenan kukayi dukan ku?””ta fada tana nuna su Ammah hawaye na xubar mata,akwai babbar mayaudariya axxaluma ,munafuka irinki Areefa!”Aliyu ya fada yana katseta cikin tsawa ,na tsaneki na tsani duk wani abu dake manne dake,wlhi tallahi nayi da na saninki Areefa mansoor.”da ana dawo da baya da na koma na goge bakin tarihin saninki,me kika daukeni??”sakarai wawa marar tunani Right??”Bari na fada maki wannan cikin dake jikin ki bana da alaka da cikin sai dai nasan ina da alaka da uban dan dake cikin,
Wlhi tallahi na tsaneki Areefa nayi mugun tsanarki dake da duk halayyar ki,ta fashe da daria tana taba hannunta,hawayen bakin ciki na xubar mata lokaci daya.”ta shafa cikin A hankali kenan ka dawo cikin hankalin ka cikin jikina ba naka bane na Farhaan Shagari ne,ta bude manyyan idonta tana fa?in.”ko kasan nice na saka a kashe min Farhaan sabida xai shiga tsakani na da kai,Farhaan Shagari shine ya rabani da dukkan farin cikina,sabida ka fifita soyayyata da tashi lokaci daya ya kawo maka budurwarsa ka Aura,batareda tunanin komai ba ka amince ka Aureta,kasan ko da gangan na shiga cikin rayuwar Farhaan na fara alaka dashi ,sabida waccan shaidaniyar da ta shiga tsakanina da farin cikina.dama burina na kashe mutum biyu ne a duniya na farko Farhaan na biyu waccan tsinanniyyar,
daga hannu yayi ya xabga mata shegen
Mari jikinsa babu inda baya rawa,kowa na parlorn kallon Areefa yake cike da mugun shock Wai Akan ita ta kashe Farhaan Shagari tana da saka hannu a mutuwarsa,
“Abunda ma yafi mari nasan xan karba a wurinka Aliyu,bari kaji na fada maka.Asiri nayi maka ka karbi cikin nan dake jikina,
Komai nayi ne sabida soyayyar da nake yimaka ban taba zuwa wajen Malamin tsibbo ba sai akan ka Aliyu ta fada tana wani shafa fuskarsa hawaye na xubar mata,da sauri yaja da baya yana kokarin control din temper dinsa kar Areefa ta kure hakurinsa,yasa yayi mata dukan da xata fara nakuda yanxu,lokaci daya noory ta mike tsaye ta nufi stairs wani irin kallon tsana Areefa keyi mata ganin yarda tayi wani irin cikowa tamkar mai shigar juna biyu,Aliyu waxeer
Har yana da karfin halin da xai hada shimfida da wannan kaxamar ,lokaci daya wani tunani ya shiga cikin kanta,ta fisge kanta da rikon da Aliyu yayi mata wani karfi da wani mummunan kishi ya shiga xuciyarta lokaci daya da wani mugun gudu ta nufi stairs lokaci daya ta fisgo noory tayi wani irin shaketa,Ammah ta nufi stairs tana salati tana rokon Areefa da Allah da Manzon sa ta saki noory juna biyu ne jikinta kar tayi mata illah.”karki matso wlhi!”Areefa ta fada tana wani daka ma Ammah tsawa a fusace Aliyu ya nufeta,
Ammah ta sha gabansa cikin tashin hankali take fa?in.”kabi komai sannu dan Allah Aliyu kar tayi mata illah lallabata xamuyi.”duk yarda noory taso ta kwaci kanta daga hannun Areefa ta kasa wata irin shaka tayi mata ,tana jin numfashinta na barazanar daukewa duka,Areefa meye haka??”ya fada cikin tashin hankali yana daka mata wata irin tsawa,jikinsa ko’ina yana kadawa,da kakkausar murya yake fadin idan wani abu ya sami yarona wlhi tallahi sai na kasheki na karar da danginku duka.”tana ganin ya fara taka step ta hankada noory da mugun karfi,wani irin kara Aliyu ya saka ya nufi nooryn,wacce take mulmulowa akan stairs kafin ya cimmata,ta Fadi akan cikin wata irin kara ta saka lokaci daya tana jin numfashinta ya tsaya,
Tsayawa Aliyu yayi cak!!”yana jin zuciyarsa ta daina aeki na sakan daya,
Ammah ce ta nufi nooryn tana dagota a rude suka xaunar daita itada Adama,lokaci daya Adama ta saki kuka tana salati wani irin tsoro ya shigeta,
Areefa ta fashe da daria ta kalli Aliyu tana bu?e masa ido take fa?in.”meya hanaka Karasowa ??”karaso wlhi tallahi duk ka tako kafarka anan kaima sai na kasheka na kashe kaina kowa ma ya huta,wata xuciya na cinsa ya nufi Areefa,lokaci daya ya fisgota ya shiga wankawa fuskarta mari ta ko’ina kafin yasa kafa ya tadeta ta xube kasa ya shiga ball daita iyakar karfinsa,ihu kawai Areefa ke saki Khaleel waxeer ya rikesa da sauri yana fa?in.”pls ka dawo hankalinka baka ganin Abunda ke jikinta,a tsawace ya fisge kansa daga rikon da Khaleel waxeer yayi masa ya fara jan Areefa tun daga saman stairs har zuwa kasa,da wani irin yanayi Areefa ta mike tsaye fuskarta lokaci daya ta canja kala sabida yarda Aliyu ya rika kaiwa fuskar wani irin duka,tana jin mararta na wani irin juyawa lokaci daya ya buga fuskarta ga bango wata irin karar axaba ta saki gamida xubewa a wurin sumamammiya,jini ya ?alle mata a hankali Aliyu ya xube gwiwowinsa kasa hawaye suka fara Rolling Akan fuskarsa,
Ammah ta saki salati ta soma kiran sunan noory da dukkan karfinta,ganin itama jinin ne ke fita ajikinta
A hankali Adama ke bin jinin dake tsiyaya kan marbles ,da gudu ya sunkuci matarsa ya nufi kofa a rude, Khaleel waxeer ya samo security suka rika masa Areefa zuwa motarsa dan tuni Aliyu ya dde da wucewa da noory,yarda ya shigo hospital din waxeer a rude yasa kowa ya saki aekin da yake aka soma binsa da kallo
Ya shiga kwalawa doctor din wurin wani gigitaccen kira,da sauri aka fiddo gadon marassa lafia aka dora noory akai wanda jini duka ya gama bata jikinta……Hade hannayensa yayi duka biyu cikin rawar murya yake fadawa doctor ya ceci ran matarsa da rayuwar dansa xai basa duk abunda yakeso.daga masa kai kawai doctor yayi aka shiga da noory dakin tiyata,Areefa!!!!!!”Ya fada da dukkan karfinsa yana kaima hannunsa wani irin naushi ga bango,hannun ya fashe jini ya fara xubar masa,da sauri Dr.Arhaam ya rike hannun nasa yana fa?in.”mekake yi haka sai kayiwa kanka illah,taso muje ka huta dan Allah.”ya fada yana dagosa duka,duk kokarin likitan ya ceci cikin noory ganin yarda yake hango soyayyar cikin a idon Aliyu waxeer haka ya gagara,cikin ya riga da ya lalace,dole sukayi mata wankin ciki suka fito daita.amma sai dai har yau babu wanda yake da kwarin gwiwar tun karar Aliyu waxeer da wannan mummunan labarin,
Itama Areefa bayan magrib akayi mata aeki aka fiddo mata da kyawawan yaranta duka maza masu kama da Farhaan Shagari sosai wanda kamar fuskarsa aka ciro aka mannawa yaran,sai dai har zuwa lokacin Areefa mansoor bata san wanda ke tsaye akanta ba, Siddiqa mansoor tana rike da yaran tana jin hawaye na cika idonta wani tsoron Allah taji yana shigarta lokaci daya,
Yanxu yaran zasu tashi da tsanar Areefa mansoor A ransu idan
Sukaji itace tayi sanadiyar mutuwar mahaifinsu,haka kuma idan sukaji bata hanyar Aure suka zo duniya ba,Ammah ta rika yaran tana jinjina girma irin na ubangiji.
Ammah ta mikowa Aliyu yaro daya ya jaye tamkar yaga mugun abu,yabar wurin da wani irin yanayi da wani irin kallon tausayi Ammah ta bisa dashi,har kusan karfe goma duka suna a asibiti itama noory barci take tanayi tana farkawa,zuwa lokacin su Ammah sun san cikin noory ya dade da fita Aliyu dai ne bai sani ba,ko yanxu ya hana kowa ya kwana da noory ya fada masu shi xai kwana da matarsa,washe gari da ihu da buge-buge Areefa ta farka ,duk Tayiwa dakin kaca-kaca banda Siddiqa dake dakin da tuni ta gama nakassa ya’yanta anyi anyi ta basu nono taki ta basu,tunda ta farko take buge-buge da wani irin kuka,likitoci ne tsaye akanta suna kokarin gano matsalar Amma basu ga komai a kwakwalwarta ba,
Aliyu ne ya shigo da polisawa biyu fuska a daure yake fa?in.”su tafi daita case dinta mai girmane barin ta acikin su hadari ne cikin rayuwar su ,rokonsa Siddiqa ta shigayi da kuka wani shegen kallo ya rika yimata yana fa?in.”taci bulus kenan??”a saketa ta tafi kikace??”case din kisan kaine akanta,idan kinga nabar Areefa mansoor a haka sai in Rayuwarta Allah ya dauka na fara sharia daita daga yanxun nan,har sai naga a garkame shegiya gidan yari kafin mummunan kisa ya hau kanta,ya fada so pissed up yayi gaba yan sanda suka garkame Areefa mansoor da sarqa suka jata har wurin motarsu, Aliyu.”!!!”Ammah ta kira sunan sa cike da tashin hankali meke damun kanka ne???”baka bari abi komai a sannu ko nono bata samu ta baiwa yaran nan ba,
Baka gani zasu shiga wani hali,da ?acin rai ya katse Ammah.”bata cancanci xama uwa a wurin su ba .xan duba masu wata uwar banda wannan shaidaniyar Ammah.”!
Ya fada da ihun tsawa yana barin Ammah tsaye a wurin,Adama ta kwantar da kai tana fa?in.”kiyi hakuri dan Allah komai xaixo cikin sauqi,hawaye kawai ke fitar mata,ta dafe cikinta tana jin babu komai jikinta,ta kalli Aliyu ta fashe da kuka cikin tashin hankali take fa?in.”bana jin baby aciki na .”taba kaji dan Allah ta fada tana fashe masa da kukan tashin hankali,shafa cikin ya somayi da wani irin tashin hankali,da sauri ya kalli laylah wacce itace ke tare da noory kafin Aliyu ya shigo,kallon da Laylah taga yana yimata yasa ta nufi kofa da sauri wani irin tausayinsu na karya mata zuciya,
Ya riketa sosai cikin tsawa yake fa?in.”kiyi shiru babyn mu yana nan!””ya fada yana kallon cikin idanunta….

Ban yafe maki ba idan kika karanta min book baki biya ba Allah ya isa.!”

Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

Post a Comment for "Waminal Hoob 49"