Waminal Hoob 8
Asmy Mom Aydah❤️: *_Waminal Hoob_* 8….
PAID BOOK
Free page.
_Asmy b Aliyu_
Yau laraba ta kasan ce yauce Ranar da xaa saka Nooriyah lalle itada Aliyu a kaidar xuri’ar waxeer amarya da Ango xasu saka fararen kayan,A samu fili babba ayi
decorating din wajen,a rubuta sunan Amarya da Ango,dangi amarya da na Ango xasu xo daya Bayan daya su shafawa Amarya lalle hakama Ango a hannuwa da kafafuwa ,hadin lallen xaayi na musamman xaa xuba turarruka aciki.idan angama familyn Ango xasu xaunar da Amarya ta buda babban mayafinta su rika xuba mata kyauttukka,da xarar an gama xaa kawo Abinci Wanda uwar Ango xata dafa da hannunta Ango ya ciyar da Amaryarsa,ana daukarsu pics ana yimasu vedio ,da angama wannan daya daga cikin dangin Amarya xasu tsaya tsakkiyar fili da Amarya,shima Ango yaxo ya tsaya sai ta hada hannayensu wuri daya tace ga amanar Yar uwarta nan tabasa ,yay mata Alkawarin sai mutuwa xata rabasu .shima mahaifiyarsa ko Yar uwar mahaifinsa ,
Xatace sun dau Alkwarin bbu Abunda xai rabasu sai mutuwa….idan Angama wannan kanwar mahaifin Ango xata dauki amarya na kwana daya,tayi mata wanka da Ruwan lalle,
Ta Kara fahimtar halinta shin yaronsu ya dace da mata ko akasin haka,sauran Abunda xai biyo baya event’s ne idan kana da Ra’ayi xaka iyayi….sai Kuma Ranar daurin Aure da an daura aure wakilin Ango xaa kawo masa Amarya ya fiddo da sarkar xinari ya baiwa Ango ya sakawa Amaryarsa ,shi kenan ta xama daya daga cikin xuri’ar waxeer ,Wanda in har aka auri macce acikin xuri’ar waxeer xaa ganta da wannan sarkar ta xinari ,duk hidimar da xaayi baa canja sarka itace dai xaa gani a wuyanta,
Sai idan acikin gidanta tayi ra’ayin canja wata Dan yiwa mijinta kwaliyya,amma in har xaa yi wani taro acikin xuri’ar waxeer dole ta saka sarkar xuri’ar waxeer ta Aure….
A gidan yayan mahaifinsa xaayi event din saka lalle,wato gidan kabeer waxeer ,Wanda shi kadai ya rage masu namiji sauran matane su biyu ,hajia Ramla waxeer sai Fatima waxeer wacce itace auta Kuma dukan su suna da Aure da ya’yah Ramla a sokoto take Auren wani hamshakin Mai kudi,sai Fatima dake Aure a zamfara gusau itama dai babban Dan siyasa ne take Aure,Wanda idan suka xo basa sauka gidan yayunsu maxa,gidan iyayensu suke budewa su shige suda Yayansu,sai dai kawai suje su gaisa da yayunsu. Wanda kusan iri dayane da na Yaran,Babu Abunda bbu ciki na Rayuwa….
“Ya kamata yanxu ace Amarya ta iso hajia Amina ta fada wacce itace matar kabeer waxeer ,itama tana da manyyan ya’ya maxa da mata Wanda matan sunfi yawa.”ummi toh ki Kira Ammah a waya Mana.”daya daga cikin yaranta ta fada Mai suna Fauxiyya itama baa dde da aurenta ba har ga albarkar ciki,
Hajia Amina tayi dialling lambar Ammah,bugu daya ta dauka,na jiku shiru ne Ammah lafia kuwa??”gamu nan xuwa kin San halin yaronki shiya Bata Mana lokaci,acan bangaren Ammah kuwa wata kawarta ta Kira agefe hajia saudah tace mata taje a matsayin yayar uwar Amarya ,da mamaki hajia sauda ke fadin ita Amaryar Bata da dangine??”cikin sanyi murya Ammah ke fadin marainiyya ce saudah xan warware maki komai idan aka gama,sauke ajiyar xuciya hajia sauda tayi ita ta fita da Amarya har xuwa compound din gidan katuwar jeep dake fake a wajen ,ita ta budewa Amarya ta xauna itama ta xagaya ta xauna driver ya jasu,Kusan gidajen manne suke da juna,
Mutane har sun fara taruwa sai kade-kade akeyi ,ganin mota na shigowa Yammatan gidan suka nufi motar da gudu suna shewa kowa so Yake yaga matar Aliyu waxeer……Ummi ce ta bude bangaren da Amaryar take ta fito daita Ahankali ,nan suka gaisa da hajia saudah wacce ummi ba kowa ta sani ba ko acikin kawayen Ammah ,Dan haka Bata shaidata ba.Su suka rika Amarya har xuwa maxauninta,Bata Dade da xama ba saiga Aunty’s din Aliyu waxeer shima sun rakosa,wato kannen mahaifinsa.shima yana sanye cikin shadda fara Kal ,Amma kallo daya xakayi masa kasan baya farin ciki da wannan Auren sai yanxu yake da ya sanin biyewa Besty yasan Yarda Auren gidan waxeer yake.Aunty Ramla ce ta bude fuskar Amarya sai fadin take “Masha Allah Allahumma barik Alaekhi” .Aliyu ka iya xaben macce har taso tafi matar Khalil kyau fari kawai xata gwada mata.daria akasa Banda Aliyu da ya wani dakune fuska,
Nan akaxo daya Bayan daya ana shafa masu lalle,
Laylah waxeer ce karshe,Aliyu yana kallon yarda take wani babbata rai da alamar tana taya kawarta kishi,murmushi kurum yyi yana ganin irin kallon da take bin Nooriyah dashi,Bayan Angama saka lalle ta xauna ta buda mayafinta aka rika saka mata kyauttuka harda kyautar mota,Nasir waxeer ya Bata Wanda shine babban da awajen kabeer waxeer.laylah bakin ciki tamkar xai kasheta ,itama A aurenta kyautar mota yayi mata,russunawa Aliyu yayi dai-dai kunnenta Yake fadin”karma ki fara Jin ddi duka amshe gifts din nan xanyi,ae fake marriage ne.murmushi Nooriyah tayi tana fadin ,Nima basa gabana Mr.Aliyu waxeer inhar xan rayu tare da Farhaan Dina acikin Aminci.”na yafe wannan kyalkyalin”.daure fuska yyi yana fadin xan Aure ki Kuma kike fadin wani naki. A gabana “Ya fada da wata irin murya da mamaki take kallonsa,sai ya dauke kansa,haka aka cigaba da hidimar saka lalle har akaxo Wurin da Ango xai baiwa Amaryarsa Abinci abaki.dakyar ta yarda yabata sabida kunya,haka aka rika daukarsu pics,wasu suna ganin kunyarta ta burgesu ,wasu Kuma akasin haka.suna ganin Rashin wayewa ce kurum sai Kusan 2 Aunty Ramlat ta tafi daita bangaren da suka sauka,Ruwan wanka ta hada mata masu hadin turarruka na musamman,da Ruwan lalle aciki tayi wanka ,tana fitowa daga wanka tana tsane jikinta da towel sai ga Aunty Ramlat ta shigo dauke da katon tray ta aje a tsakiyyar carpet ,wata irin kunya ta rufe Nooriyah ganin yarda Aunty Ramlat ke kallonta tana sakin wani irin blushing ita har ga Allah taji tana kaunar Nooriyah tun farkon ganinta,Bata San meyasa take Jin kaunar yarinyyar kamar Aliyu waxeer ba.tana son macce Mai natsuwa da kunya ,sabanin matar Khalil waxeer Wanda idonta ya gama budewa da wayewa.tana ji ajikinta Aliyu yyi dacen macce ta gari a wannan bangaren,wasu irin mayyuka Aunty Ramlat ta turawa Nooriyah agabanta tace ta shafa ,bbu musu ta rika dibar mayukkan tana shafawa ,sukan su wani irin sirrukkan kamshine acikin su.Bayan tagama Aunty Ramlat ta Mika mata wata plain gown kalar sararin samaniya ,juyawa tayi ta nufi toilet da sauri Aunty Ramlat ta dakatar daita.ki saka abunki Anan Nooriyah Sam -sam ban yarda ki daukeni matsayin suruka ba.kin ji kou.”daga yau ni kawarki ce kuma Auntyn ki ,xaki iya fada min dukkan damuwarki karki ji komai keda Aliyu duka ya’yana ne ,ko acikin ya’yan Yan uwana Aliyu shine Fav Dina …..Kaunar da nake masa Mai girmace plz kibasa dukkan farin cikin da Yake nema,kinyi dace sosai da samun miji irin Aliyu watarana da bakin ki xaki rika yaba kyawawan Halayen Aliyu believe me noory.”Aunty Ramlat ta fada tana kallonta da murmushi a fuskarta,
Jikin Nooriyah lokaci daya yayi sanyi ,ta rasa mexata fara tunani akai tana ganin yarda mutanen nan suka dauki Auren Aliyu waxeer da muhimmanci fiye da komai ,Ranar da Kuma Auren su da Aliyu waxeer ya kare batasan ya xasuji ba”.kenan xasu rusa dukkan farin cikin su,musamman mahaifiyarsa xasu koma gefe Kuma su cigaba da Rayuwa.juyawa tayi ta koma toilet Aunty Ramlat na kwala mata Kira Bata saurareta ba,
Kiran Aliyu waxeer ne ya shigo a wayar Aunty Ramlat,juyawa tayi tabar room din tana daga wayar lokaci daya tana fadin my fav….”
ASMY#❤️
Team#NooryAli forever#
Post a Comment for "Waminal Hoob 8"