Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Waminal Hoob 9

Waminal Hoob*_ 9..

PAID BOOK
Free page.

_Asmy b Aliyu_

Ajiyar xuciya ya sauke ya gaishe da Auntyn nasa da ladabi yana fadin “.taimako xakiyi min Aunty nasan a kaf familyn waxeer ke kadaice kika fi kaunata ,ni nasan da hakan…”Yayi Maganar cikin sanyi


murya,murmushi Aunty Ramlah tayi tana fadin fadamin me kake so.”shuru yyi na Kusan sakan biyar kafin ya buda bakin sa cike da Jin kunya yake fadin ina son ganin ta Aunty.”wara ido Aunty Ramlah tayi tana murmushi take fadin”wacece kakeso ka gani,tana so ya fada mata da bakin sa Amaryar sa yake so ya gani,cikin kwantar da murya yake fadin ance tana side dinki,kayi min hausar da xan fahimta Aliyu wacece take a wajena.”cike da Jin haushin farhaan yake fadin Noory,ya fadi sunan tamkar yarda yaji su Batool na kiranta ,Dan shi har ga Allah bai wani rike sunan ta ba.daria Aunty tayi tana fadin”Yeaah Yarona ya girma duka-duka yaushe kuka rabu da har xaka fara tunanin kara ganin ta.”cike da gajia yake fadin sako xan Bata.”toh naji ka kawo min sakon na Bata Mana,ya dakune fuska Yana fadin”noo kibarsa kawai cike da Jin haushi a muryarsa ,kowa Yana tunanin da gaske soyayya Yake daita har Yana mugun son ya ganta.kayi fushi kenan?”Aunty Ramlah ta fada tana murmushi,shaye da toka yake fadin”kema ae kin San dole nayi fushi Kuna tayi min yanga kunki hadani da Amarya ta kwana Kuma Nawa ya rage.”Ya fada batare da yasan maganar
ta fito ba ,Aunty Ramlah ta kama baki tana fadin ni dai karkayi min Rashin kunya na baka dama kaxo kaga amaryar ka a minti Ashirin yayi maka.”Yana dakune Fuska yake fadin ni yayi min ma Yawa ,toh naxo yanxu…..”A’ah sai xuwa Bayan magrib tana hutawa yanxu barci xatayi gaba daya ta gaji Kuma baa son Amarya ta rika aikin wahala.”lallai ma ta samu banxa kenan .wato hutawa ma.”Ya fada can kasan Ransa ,kwafa yayi ya fada mata da magrib xai shigo da haka sukayi sallama,
Aunty Ramlah ta koma wajen kanwar ta Fatima dake sakawa Yarta Pampers tana Bata labarin Maganar da sukayi a waya,Fatima waxeer tayi Daria tana fadin”dama kece baki yarda da Aliyu bbu Ruwan sa ba ,jeki gidan sa ki Mike kafa Kisha kallon yarda xai rika tarairayar matarsa ,maybe harda gudowa xakiyi sabida Jin kunya.”waya sani ko da daren xuwa xaya yi ya Dan shafa Amaryar sa,Aunty Ramlah ta girgixa Kai tana fadin toh Banda sharri gaskiyya Yarona ba haka Yake ba.”Fatima waxeer tayi Daria tana gyada Kai,
Kibar samarin yanxu kurum Maman Airah sunfi ma masu Auren sanin wasu Abubuwan,mikewa Ramlah waxeer tayi tana fadin bari ta koma wajen Nooriyah taga taci Abinci ,ta samu Nooriyah nacin Abinci .Yawwa Yar gidana ki saki jikin ki kici Abinci Dan Allah ,idan kin gama ki kwanta ki huta .godia tayiwa Aunty Ramlah ta juya gamida rufo mata kofar…haka ana gafda sallar magrib Aunty Ramlah ta sakata yin wani wanka,sai wani kamshi ke fita ajikinta fatarta sai wani irin glowing take tamkar ba Nooriyah Yar gidan kawu balele ba.bata taba saka ran Rayuwa xata kawota Anan wurin ba,tana xaune a daki har aka Kira sallar magrib .wannan karon Atamfa Aunty Ramlah ta kawo mata ta saka dinki riga da skirt kayan sun Dan kamata sabida ta Dan yi kiba jikinta ya canja,
Atamfar da kalar mayafinta.Aunty Ramlah tajata agaban mirror dressing tace ta Dan shafa powder ,ta Dan goga man baki a saman lebunan ta.bbu musu tayi yarda Aunty ta fada mata ta taimaka mata ta saka turarruka…….masu sanyi kamshi,muje kina da bako a parlorn baki .gaban Nooriyah ya fadi to ita Kuma wane bakone Yaxo ko dai farhaan dinta ya dawo.”haka tabi Aunty Ramlah har xuwa babban parlorn baki.jin kamshin turarensa kawai sai da gabanta ya fadi,ta daga Kai ta kallesa wannan karon kananun kayane ajikinsa,hannayen sa xube cikin Aljihun wandon sa.Ya karaso Yana yiwa Aunty murmushi minti Ashirin kayi sauri lokacin ka na tafia fa??shafa sumar kansa yyi ,Aunty ta juya tabar parlon gamida Rufo masu kofar.da sauri ya xauna Yana fiddo wayarsa batare da Ya kalli Nooriyah ba ita kuma ta kasa xama cikin parlorn tayi tsaye ,ya dago da wani irin yanayi a fuskarsa yake fadin Dan xaku gaisa dashi a waya xakici uban wannan kwaliyya haka .”Ya fada fuska bbu walwala ,toh jeki toilet ki wanke wannan fuskar .”Kana kaini karshe Aliyu kanka na koyi fada da masifa harma da Rashin kunya duka Kuma kaine ka koyamin , .Kuma waye ne xamu gaisa dashi a waya kake masifar nayi kwaliyya inhar farhaan ne ae kaima kasan ya cancan ci fiye da haka,Babu ruwanka da kwaliyyar da nayi masa.”,maganganun ta sunyi masa xafi sosai baisan lokacin da ya fisgota ba ta fado kansa gabanta ya shiga faduwa ganin yarda idanunsa suka koma Red tana Jin yarda xuciyarsa ke bugawa.A tsorace take kokarin kwatar kanta Amma yayi mata rikon da baxata iyaba.baxato taga ya matse bakin da karfi sai da ta saki karar axaba.ya turata da karfi Yana huci yake fadin” gobe ma ki kara yimin Rashin kunya ,ya daka mata tsawar da ta gigita ta Yana fadin ta tashi taje ta wanke fuskarta duka inhar tana so tayi waya da farhaan.”mikewa tayi hawaye suka shiga Rolling akan face dinta ,tayi missing din farhaan sosai tana so suyi waya akan wannan dalilin shiyasa baxata ki karbar wayar Aliyu waxeer ba.nuna mata toilet yyi dake cikin parlorn nan ta shiga tana wanke face dinta hawaye na xubar mata tana tsinewa Aliyu waxeer ,samun kansa yyi da Jin haushin kansa to shi ina ruwansa idan tayiwa Farhaan kwaliyya “Aliyu meke damun kanka akan yarinyyar nan.”da sauri Ya shiga girgixa Kai Yana fadin ,kawai na tsaneta ne ina kishin yarda besty ke tsananin kaunarta,
Kallon fuskarta yyi ya wani daure fuska yace karaso ki xauna xan hadaku vedio call ,idan kikayi min rawar Kai wlhi xan fasa.”Ya karasa maganar shaye da toka.xama tayi Dan nesa dashi ya watsa mata harara Yana fadin ni xan sameki na Mika maki wayar,Kara matsowa tayi kusa dashi Amma sai da ta tabbatar akwai space tsakanin su,bugu daya farhaan ya daga ,Aliyu ya hararesa Yana fadin ka xama namiji Mana kan macce kana wani Rawar Kai ,marar aji kawai.”Aliyu waxeer yyi maganar Yana hararar farhaan din ya wani hade Rai,minti goma na baku da ya cika xan karbe wayana inada Abubuwan yi a daren Nan tunda ka hadani da wahala”…….Ya karasa maganar Yana mikawa Nooriyah wayar batare da ya kalleta ba ,mikewa yyi hannun sa xube cikin Aljihun wandonsa ya koma can kusa ga window yyi crossing hand’s din shi akan kirjinsa gamida kurawa window din ido tamkar Mai son ya gano wani Abu acikin window din,sai da ta saci kallonsa in a second taga hankalin sa baya kansu. sa’annan ta maida hankalin ta kan farhaan…Sallama tayi masa tana boye dukkan damuwarta ,duk da haka sai da yaga hawaye akan fuskarta .farhaan ya ware ido Yana fadin ”ya Kuma da haka??ta shagwabe fuska cikin muryar son tayi kuka take fadin kawai ina kewarka farhaan ko nemana bakayi ,plz ni ka sayamin waya mana murika waya da tawa wayar kadaina hadani da wannan mutunen Mai fadin rai.”ta fada cikin muryar tausayi,
Murmushi Farhaan yyi
Yana fadin”kece kuwa my love kin ga yarda Fuskarki ke wani irin sheki ,gaskiyya Aliyu yana kular min dake .
Tasha toka tana fadin ni baya wani kula Dani Ammah kurum ce ke kula Dani,Aliyu duka hirar da suke Yana jinta.ba xato taga ya fisge wayar gamida kasheta duka,Fashewa tayi da kuka tana yarfi da hannayenta da mamaki yake kallonta yarda ta bude baki tana kuka tamkar wata baby doll.”Toh ni ka siyamin wayana Mana sai na rika wayar dashi ,ta fada tana Kara volume kukanta…..”kukanta yaji Yana dagula masa lissafi da sauri ya durkusa agabanta Murya kasa-kasa yake fadin “baki da Hankali ne sai kin Sa anji kukanki an xargi ko ina maki wani Abu.”
To kabani nayi waya da Farhaan Dina shi kawai ne ke Sona shi kawai ke sani farin ciki Kuma baya min ihu kamar yarda kake yimin……..”xai riko hannunta yayi saurin janyewa a tsorace mikewa yyi tsaye Yana fadin”ki bari idan kika tare a gidana xan siya maki waya ,sai ku cigaba da wayar bbu takura Amma Banda kwanakkin Nan.wani xai iya suspecting wani Abu,ni Kuma duk Abunda xai taba xuriata bana maraba dashi. Kofar baya ya nufa da sassarfa Yana barin parlorn da ido tabisa har ya bace.
Washe gari bata tashi ba sai Kusan 11 wanka ta farayi sa’annan tayi break fast da axxahar Aunty Ramlah da Fatima waxeer suka yi Shirin maidata wajen Ammah.sosai Nooriyah taji tana kaunarsu ganin yarda suke sonta suke Bata wata irin kulawa tamkar ta fito daga cikin su,da fara’a Ammah ta tarbi su Ramlah waxeer tana masu sannu da xuwa ,
Yan aikin Ammah ne suka fara cika gabansu da kayan motsa baki.da murmushi Ammah ke fadin yanxu nake xancen ku araina,Yan uwan Nooriyah suna so su karbeta .”sai Kuma Ranar da aka daura aure muda sake haduwa daita ,tunda Aliyu ya kafe baya wani event’s .”Da sauri Ramlat waxeer ta tari numfashin Ammah tana fadin shi Aliyu ne ya fada baya son wani Event sai kace marar gata.”Aunty Ramlah ta fada cikin fuskar damuwa.Ammah ta tabe baki tana fadin toh ina Maganar wane event lokaci ya riga ya kure jibine daurin Aure,baxai yuyuba gaskiyya xamu shirya ko mother’s day ne da waleema……Idan baayi ba xai iya xama wani magana.,,Aunty Ramlah ta Kira Aliyu a waya ta fada masa komai yake yaxo Yanxu tana son ganinsa.basu jima wajen Ammah ba suka koma part dinsu ,Bayan tafiar su Ammah ta samu Nooriyah a daki ta xauna gefen bed tana fadin”murja ta riga ta shirya maki kayan da xakiyi amfani dasu a gidan hajia saudah ,na turaki ne sabida gudun surutun mutane.”musamman wannan familyn xasu fara tunanin ina dangin ki da xaki tare anan??”shiyasa nayiwa su Ramlah karya da an daura Aure ni da kaina xanje na dauko ki,baxan bar kowa yaje dauko Amarya ba sabida kananun maganganu………kinga Yarda Rayuwa ta juya maki Nooriyah na yarda dake a koina xaki shiga ki kama kanki.”hawaye taji sun cika idonta batasan dame xata sakawa Ammah ba irin kaunar da ta nuna mata.,har fargabar take Ranar da Auren su na karya xai kare da Aliyu waxeer……daga lokacin kuma Ammah xataji ta tsaneta,Tare da driver da Ammah suka nufi gidan Hajia saudah,da hannu biyu Hajia saudah ta tarbesu dama Ammah ta fada mata ko wacece Nooriyah itama hajia saudah ba karamin tausayin Nooriyah din taji ba,
Ammah Bata jima ba tayi masu sallama har bakin mota hajia saudah ta rakata Ammah na Kara yimata tuni akan Nooriyah ta rika shan tsumin da ta taho mata dashi kafin Ranar daurin Aure ,
Hajia saudah tace insha Allahu…..Ammah tayi mata godia driver yaja motar..

Thank you.

Post a Comment for "Waminal Hoob 9"