Breaking News

Cheaters Club 15

 _*CHEATERS CLUB...*_ 

 _(Babban goro sai Magogin Æ™arfe...)_ 




#ROMANCE

#FICTION

#ADULTHOOD

#SEXADDICTS

#WOMENPOWER


BY

 _SURAYYAHMS_

 _08060712446_


⏯️1️⃣5️⃣



Cikin daren Banda juyi from one end of the bed to another babu abunda hadiza takeyi akan makaken gadonta da babu kowa akai sai ita, ko kadan bata samu halin runtsawa ba dan babu wani sauki a tattare da ita face dan nauyin data ragewa zuciyarta data iya furta ma alhaj kyari irin abubuwan dake cemata rai akansa dazu.


Sedei duk dahakan kalma daya daya furta mata acikin maganganun nasa ya fi kowanne kalma tsayamata aranta wato kalman kara aure dayace zaiyi inyadawo dan ta mugun tsanar kalman kishiya arayuwar ta bana wasa ba. 


Tun tana tunane tunane sama sama har bacci yay nasaran awon gaba da ita gabanin asubah, batawani jimaba ta tashi sake sako wani wankan tayi sallah fajr snn ta tashi ta shirya cikin wata tsadaddiyr atamfa exclusive sheraton dark purple sanan tasauko kasa rikeda wayanta a hannu wanda kallo daya kawai zaka mata kasan cewa sam hanklinta bayanan ajikinta.


Gaban 45 inches royal dinning table dinsu takaraso tana bude hadaddun wamers dake kai dan already maid tai mata wasu lafiyayyun girki kala kala masu armashi, ferfusun kifi ta deba da soyayyen irish  sanan tazuba ruwan tea adan karamin cup tazauna tanafaraci ahankali tanata tunanin kota kira therapist dinta ne kokuma ta kira shema'u susan nayi akan zancen auren nan tunkan ma abun yay nisa.


Aranta tasan alhaj bazai ambaci aure gatsau batare da wata budurwan a kasa ba, dan dama taji ana kishin kishin cewa zaiyi auren jari da wata tantiriyar ex minister of humanatarian services datay kaurin suna wajen fitar da kishiyoynta waje.


Mjiinta was said to have died from heart attack anata zargin cewa itace ta kashesa da baqin ciki da mugunta kuma duk akan kishiyointa ne


yatsine fuska tayi aranta tace "Romon baka bana kwarya bane, hmmm muzuba dai mugani..

zanga yadda zakayi ka auromin wnn tsinanniyar matan.


Lissafi ta cigaba da yi a mind dinta harsaida taci abincinta tai nak sanan ta tashi ahankali tafito babban luxury falo dake gidan tazauna tareda daukan wayarta snnn tamikarda kafafuwanta kan table din din tsakiyan falon tafara kiran layin shemau marafa, yay ringin kusan sau uku bata daga ba, tay tunanin hala ko tana hanyar zuwa wajen aiki sai ta basar.


Text ta turawa wani lamba dan abinciko mata zancen datake zargi akai domin ta samu tabbaci akan neman aure da mijinta yakeyi tasan kuma irin matakin data zasu dauka akansa ita da shemau



Washe gari sassafe nile ya farka yay wanka ya sako wata casual dress data amsheshi yafito a cikin wata shegiyar unbuttoned shirt na givency white wandonsa black color dayamai kyau banawasaba kafafunshi sanye da wani black boot na parco rabanne, ya fito da duster coat sabida sanyi sai wani hadadden kamshin turaren midnight oud yakeyi kaman ka lashe shi..


Zaune yake abakin gado Yanakan daure igiyar takalminshi yaji kamar anbudemai kofa, hakan yasaka dagokai ya kalli yar uwansa dake tsaye agabansa fuskarta ba yabo ba fallasa, ya mata murmushi mai sanyi snn yace "good morning early bird,..wani Karamin Ajiyan zuciya ta sauke jikinta a mugun sanyaye batace maikomi ba har ya kammala saka talkamin shi ya mike tsaye...


hannunta ya jawo ahankali tareda ce mata yane Whats wrong sis".


Kallonshi take dan Gabaki daya ta rasa me zatacemai dan jiya ko runtsawa bata iyayi ba da tunanin yadda zata soma korarsa agidanta bisa umarnin femi daya bata kafin yafita jiya da daddare.


She wonders wher he is been last nite..kuma bata san izuwa karfe nawa zai dawo gidan ba.


Tuna irin tozarci da walakncin dayay ma uwarsa data haifesa yasaka itama takejin tsoron karyazo yaga nile agidan shima ya masa irin haka dan ji take kamr zata iya daurewa akn komi amma bazata yadda a walaknta mata dan uwanta har haka ba.


Gabaki daya ta rude ta rasa me zata ce masa sai inda inda kawai takeyi, Jin ya matsa hannunta acikin nashi yasakata dago kai da sauri ta kalleshi  suma hade ido yana murmushi sosai yace sister vicky am going to be late.

So Tell me...what is it?


Ta lumshe ido..

Kafin ta bude, da muryansa mai sanyi ta ci karo yanamai cewa dont worry abt me ive already gotten a nice hotel yanzu nan zan tafi and I totally understand you sister!!!.


Da sauri ta bude idon nata daya ciko da ruwa a sigar borin masifa tace "what?..u booked a hotel witout telling me..ahankli takai masa maka a saman kirji yace auch sister yanzu fa na girma kuma nasan mijinki is not comfortable with me kuma ke bazaki iya gayamin ba...Zatay maganan ya jawota jikinshi ahankli snn ya rungumota yanamai cewa da sassanyar muryansa "hey hey dont worry abt me...Your peace of mind is actually eveything to me..i swear i will be fine..  Cirota ajikinshi yay hankli tare da tallabo fuskanta da tafin hannunsa yanami kallon ruwan hawaye dake zubowa a idanunta na takaici da bacin ran dokar mijin nata, murmushi yay snn yace "zanna zuwa miki hira a schl, ko during wknds zanzo nan muna hira, or u can even drop by the hotel sumtimes

..nan ya ciro wayarsa ya hau nuna mata komi da komi na detail dinshi harda room numbersa ta gani...lokacin sosai hawayenta yake zuba.


Jikinta a sanyaye sosai tace .."Nile am soo sorry abt this...i seriously dont knw what is wrong with him hakafa yay ma mahaifyrsa ranan..


Murmushi nile yay yace shine kekuma kika maidashi abun kuka?

Is not a big deal okay, he is right gidansa ne da ace gidanki ne dasaidai na fitar dashi badai shi ya fitar dani ba alho i knw u will definatly follow him bcos i can see u love him so much.


Dariya mai tattare da blush tay tana dan tare hawayenta cikin sakar masa runguma,can tasauke ajiyan zuciya ahankli tace Thank u soo much for understanding me bro,..And hey, if u need anything just text me okay?..gyada mata kai yay yana tapping bayanta ahankli yanayin lallamarta hartay shiru ta dena hawayen gabaki daya.



Mikewa tsaye yay snn ya zuba hanayenshi a aljihu ya wuce gaba yana taku daidai kamar Dan sarki tana binshi abaya har suka kai waje..


Mai aiki ne ya zuba masa trolley dinsa a mota driver ya jashi izuwa suite din daya kama acikin ikeja.


Zuciyar vicky babu dadi sam haka ta dawo cikin gidan tahau shiri da sauri domin ta wuce school inda take koyarwa dan kwata kwata batasan ma prince femi ya dawo ya sameta while her blood is hot dan bakaramin bacin rai da takaici take ji aranta ayanzu ba.


As usual cikin hadadden shigarta na manyan mata ta fito ta saka peach colour suit na gucci da wani irin dogon higheel silver colour na kamfanin labourtin to march da jakar data dauka ta rike a hannunta.



Yau bata jira wani driver ba ta dauki latest mercedex benz dake parker a lot ta bude ta zauna aciki, agogon ta ta duba is already 7.30 am ta dan sauke madubin motar ta kaalle gyaran datayma suman kanta dan tsabar sauri yau kamashi kawai tay da ribbon ta gyara tagaban gel bata tsaya ta É“ata lokcinta sosai akaiba.


But she still looks gorgeous as usual nan da nan ta daga glass nan da nan ta ja motar ta nufi pan athlantic university inda take koyarwa.




Ata dayan fannin kuwa

Kusan a gigice shemau marafa ta bude idanuwanta Jin karar Wayarta dake ringing da asubahin fari yanata kara akai aKai Babu kakkautawa Wani doguwar tsaki taja mai cike da uban haushi alaman ranta yakusa Kai kolowa da haushin koma uban waye yake kirar,a fusace ta miÆ™a hannu cikin gigin bacci tana cewa "who's calling me this early morning for God sake..?Jan nityn ta tayi ta dada rufe jikinta da kyar ta zauna ta shiga neman wayar... Kara Jan tsakin tayi ta miqe a yangace dan tagama sawa aranta bazai wuce Mijinta engr mahmmod  ba ne"..wat the hell did he want now? Aranta tace nifa baza a takurani akan wasu tsohuwar banza ba,I can't just be rushing myself eating on d table like a baby,kayita gaishe da mace tana maka Kallon yar iska

gaskiya bada ni ba...I can't take it...inma kara zuwa min bakonta tay yau kam bazan amshe ta ba saidai yasan inda zai sakata.


Sanda tagama bambaminta tsaf snn ta mike a zafafe ta dauki wayar da niyyar sauke masa buhun masifa caraf sai taga number mahaifiyarta ne akan screen da Wani irin sauri ta sake wayar takuma daukawa da sauri hannunta na rawa ta karashi a kunnenta cikin sassauto da muryanta a ladabce "Helo Mamee?


Daga dayan bangaren akace Assalamu alaikum shema'u Ina kika shiga haka kika bar wayarki ya nata kara?


Shemau na sosa kai Tace uhmm uhmmm Mameee, dama ina Ina..Ina..kan shiri


Atsawace Matar tace dakata min shemau

Hala ma ko sallahn fajr bakiyi ba sakaliyar banza wato har yanzu baxaki dena wannn mummunar dabiartaki na baccin asarar bako? ...


Xatayi magana matar ta tsareta cikin fada sosai

Ni karki kawomin Wani bayani tunda ba yau aka saba ba Mutum in yace bazaiji tsoron Allah ba saiyayi tayi Nide gani  ahanyar zuwa kofar gidan ki zamuxo ne da mutumin nan danake so ki tsayamai a kotu saiki fito ynzun nan dan bazamu jima ba.


Cikin sanyin yanayi shemau ta kalle agogon bangon dakin ganin karfe bakwaine da minti 40 yasa tayi kwafa a hankli tace toh Mameee gani Nan fitowa ...Cillo tayi da wayar akan gado ta wuce bathrum ko minti goma batayi ba ta fito daure da towel Sharp tashasshafa mai tasaka madaidaicin gown din atamfa ,Wani hijabin da tun da can take eye service dashi ta rarumo ta zura ajikinta ta tada sallan asubahi Nan ma sallama kawai tayi ta mike a gaggauce bata damu da yin koda istigfari ba ta fito.


Hijabin dogo ne wanda yaje mata har kasa Dan haka dashi kawai zata fita kodan Gudun surutun mameen sun, kalar sa ash colour sai ya mata kyau sosai dake ma Babu lokcin yin Wani shafe shafe sai fuskanta yayi fayau ya fito da innocent dinta a fili..


turaren dake kan mirron ta Dan shafa sama sama ta zura flat shoe dinta cikin sauri ta haura takan step tana saukowa kitchen direct ta nufa ta samu ruwan shayi dayaji kanunfari mai aikinta hafsa ta saukeshi kenan tana jiran ya huce kadan tayi serving dan already itace take yi ma mijin shemaun komi na abinci kuma take kulawa dashi sosai, infact kusan kominshi agidan hafsace kawai take masa sakamakon shemau iriin matayen nan ne da  ko tsinke bata dagawa.


Ita kanta ba taɓuka komi makanta takeyiba bare har ajega tay ma miji dan haka hafsa ce meyin masa komi da komi gyaran gado,wanke toilet hada ruwan wanka, su tashinshi a barci goge mai takalmi,aika, wanki guga, infact evrry little thing hafsa ce keyi.



Kamar guguwa shemau ta faso cikin kitchen din ta bubbude tukunyar a kyamace taga alaman harta yi ma mijinta abinci probably hartagama dashi ya fita, karkada kanta tay cikin yanayin masifa ganin yanzu ne ma take kkrin hada mata nata breakfast din ta dafa mata noodles ta tafasa mata ruwan tea kwan ne ya rage bata soya ba taje dakinta domin daukar wayarta dataji yanata ringing.


Daga kauyensu aka kirata cewa mahaifyarta bata da lafiya sosai tana son ganinta amma tasani da wuyane shemau ta saurareta bare ta barta ta taje gida


Dan tamkar malakal maut haka shemau tazamto mata uwa wata abar tsoro dan tsabar bata ragar mata intaganta awaje bari kawai jikinta yakeyi, ga walaknci ga kuma mugunta gashi bata isa ta huta agidan ba se in shemaun bata nan.



Idanuwanta harna fidda ruwa ta zauna daga bakin gadonta tana jin nakasashen muryan ummanta dake cewa tay kkri tazo ta dubata dan tanaji ajikinta wann ciwon nata bana tashi bane tanason taganta kafin rai yay halinsa


Sosai hanklin hafsa ya tashi ta rasa meke mata dadi tunanin yadda zasu kare da shemau ya hanata sakat ta kasa cewa mahaifyarta eh ko a'a sai kuka kawai takeyi tanamata adduar sauki tana cemata karta mutu tabarta a duniyan nn bata da kowa.


Tin daga bakin kofa shemau take jin dukkan wani abunda suke fada wanda inba wai kanadaa karamcin imani a zuciyarka ba dakyar ne kaji conversartion dinsu jikinka baiyi sanyi ba.



Murya kasa kasa ahankli hafsa tace mama kiyi hakuri anty sheimaun bazata amince ba amma in sha Allahu in mijinta ya dawo zan neme alfarma ta wajenshi naga shi yanada kirki hala ya amince min nazo.


Jin hakan yasaka shema'u gyada kai aranta tanamai cewa ohhhh wato mijina nada hankli nikuma gani mahaukciya ko????..ko uban wayace mata tana ma mijina magana oho..yau nakamata yar iska karuwa kawai.


Fuuuu ta juya a fusace taje kitchen agaggauce ta dauko wuka ganin bazai mata ba ta jefar akasa ,ta dauko muciya shima bai mata ba ta yasar ta dauko wayar wata tuna cewa mum dinta is on her way taga shima bazai mata ba, can ta dawo kan table da niyyar daukar zazzafar indomie taje ta watsa mata ajiki caraf sai idonta ya fada akan tafasashen ruwan shayin

Nan.


Acikin sauri ta zubashi a kofi dan tsabar ya tafasa atake jikin kofin ya dauka da wani irin zafi.


Lkcin Hafsa harta kwantarwa mamanta hankli tana ta kkrin share nata hawayen shemau ta bankado kofar kamar ankarota tana wani huci


Suna hde ido a mugun razane hafsa ta Sake wayar ya fado kasa tayo kanta ta jawota kamar yar tsana Takai mata naushi ke Dan ubanki nine mahaukaciyarki ko?

Aiki ne ya kawoki gidana ko karuwanci so Uban wayace miki kina yi wa mijina magana...


Rudewa hafsat tay jikinta na wani irin rawa tafashe mata da kuka dan batasan ma ta labe taji maganan nasu ba


Hajiya dan girman Allah.



Kiyi min shiru tantiriya yar iska...zaki amsani ne ko saina ci ubanki..nice mahaukaciyarki


Hafsa na kkrin budar baki shemau ta shakureta tare da danne mata bakintan da karfi babu dandanin imani aranta tahau juye mata tafasashen ruwan shayin nan abakinta na dole sauran da basu shigaba  nan da nan suka zuzzuba akan wuyarta suka koñata


Fadin irin azaban daya ratsa jikin hafsa bazai misaltu ba, wani irin radadi tare da azabane ya dinga ratsata kukan razana da azabar datakeyin ma bata san kalarsa ba dan har kololuwar kwakwalta taji zafin ruwan yana tsagawa.


Tuni harshenta ya É—aÉ—e ya kone tasss ta dawo bata ma iya furta kalma ya fito sarari tsabar konewar da harshenta yay ta dawo kamr wata me koyon magana snn duk da ita baka ce bai hana wuyarta yin ja yabi ya kumbura ba.


Bayan ta mata wann azaban a fusace ta jefar da kofin ajikinta tahaura mata da masifa tana memeta mata abunda taji tana cewa awayarta dazu.


Babu kalar zagin da bata sha ba hartace mata ai uwarkin tasan da haka ta turo ki aiki abinni dan haka kice mata bamu bada hutun mutuwa bare na rashin lafiya.


Wallah wallah kika kuskura kika budi shaddar bakinki kika ma mijina magana akan wata personal issures dinki saina kasheki anan gidan hafsa ki gwadani ki gani....


Fuuuu ta fice ta barta anan hafsa tanata kuka rike da bakinta dayakan mata radadi duk ta dukunkune ta rasa inda zata aje kanta taji sanyi


Ko numfashi bataja ba taji muryan shemaun daga waje tana cewa 

Kin fito kin hada min breafst koko kina jirana nazo na karyaki awajen


Da sauri ta miƙe jikinta na rawa sosai tanata kuka a sanyaye, rike da bakinta ta isa kitchen din ta soma harhada mata komi akan tray kamar yadda ta saba



falon kasa shemau ta sauko inda ta samu har ummanta ta iso sunyi cirko cirko atsaye cikin shigarta na brown colour hijab dogo har kasa sabida normally dama mahaifiyar sun haka take dressing dinta a nitse kasancewarta kamilar mace me addini sosai.


Kallo daya mahaifyrtata ta mata sann ta dauke kai tabi ta hade ranta


Shemau Tana karasowa cikin falon ta rusuna har kasa kamar mutuniyar kirki ta hau gaida mahaifyartan wanda take amsata ciki ciki Dan jiranta datasa sukayi ya matukar bata haushi Wai ace mace kamar shemau bazata farka tun asubahin fari ta fuskance hidiman dake gabarta ba? Yo metakeyi agidan mijin? ..Wani uban tsakin takaici taja sanin cewa tun asali laifinta ne da bata musu tarbiyan haka tun Suna yara kanana ba dan lokacin da ubansu yakeda matsayi yanada babban mukamin gwamnati girman gata kawai aka basu,toh yau gashi Babu uban Babu muqamin kuma yara sun riga sun fandare gaskiyar bahaushe dayace icce tun yana dan karami ake tankwarasa basai ya girma ya bushe ba.


Bayan sun gaggaisa shemau tafara yima mutumin da suka zo dashi din wasu tambayoyi tana recoding awayarta dan dama case din rape ne akan uba da Æ´arsa amma ana zaton kawai sharri yarsan ta masa bisa umarnin wanda ya mata aika aikan


Bada jimawa hafsa ta leko ganin sunyi baki yasakata koma kitchen din da sauri ta hado musu shayi suma ta taho musu dashi.


Bakaramin ja idanunta sukayi ba ta sauko tana tafiya ahankli kamar batada laka ajiki 


Sussunkuyar da kanta kasa take sabida kar aga konewar da wuyarta yay da ruwan zafi ga bakinta dayay wani irin jaaa yadan haura har labbanta yana nunawa.


Kafafunta dake bari mahaifyar shemau ta dinga kalla tana mamkin tsoron me kuma yarinyar takeji hartake É“ari haka wanda da alamu batamasan jikin nata na rawa ba.


Sallama tay muryanta wani iri dan kalmomi basu fitowa abakinta da kyau bisa konewar da harshenta yay tace "atata lekum...nnna ikwana?

Ta rusuna tana gaishe su mamaki ya cika masu jin magananta wani iri kmr na yara.


Shemau sai watsa mata muguwar kallo da gefen idonta takeyi akanda tay sauri tabar wajen kar mum dinta ta fahimce wani abu..


Acikin sauri hafsa ta zuba musu shayin ta juya zata haura sama kenan mahaifyar shemaun tace "ke zonan?..


Da sauri hafsa tajuyo kanta na kallon kasa


Kirjin shemau yahu dukan tara tara


Kare mata kallo matar tay sosai Batace mata uffan ba ta dubi shemau tace "ya naji muryanta haka ko dama haka take magana ne???


Dariyar yake shemau tay tace "ohhh ai bebiya ce mameee haka maganan ta yake baiya wani fita.


Matar Tace ohhh toh jeki


Cikin sauri hafsa ta bar wajen shema'u ta sauke

Boyayyen ajiyar zuciya.


bayan  yan wasu lokuta na tattaunawa kadan shemau ta kammala deban rohoton mutumin tare da tabbatar masa da cewa zatayi iya bakin kkrinta wajen ganin an kwato masa gaskiyarsa.


Daga nan sukayi sallama

Ayayinda take rakasu mahaifyarta take kara mata nasiha akan zaman aure dan duk gabaki daya yanayin data kalle hafsan a wahale kuma a firgice aranta sam hakan baiyi mata wani dadi..


Da can harta turje mata tace sam sede akira hafsan ita zata tambayeta taji matsalarta amma haka shemau ta yi kutunktun tahana hakan yuwa


Anan ma ta sauya fuska kalar mutuniyar arziki ta hau tabbatar ma mameentan cewa yanayine kawai na yaranta amma hafsa bata da wata matsala agidan face missing din kauyensu datakeyi acewar shema'un  wai aure kawai hafsan ta saka aranta shiyasa batason ta zage tayi aiki, gashi kuma mahaifiyarta tana fama da jinya  akauye danda kudin aikintan dashi suke siyan abinci da magani..


Seda ta karkatar da maganan a wann sigar kafin nan mahaifyartan ta kyale zancen tare da ce mata ta dinga kkri wajen nitsar da hafsan sosai.


Wajajen karfe 9 saura suka wuce gida tana dawowa cikin gidan ko karyawa batay ba tay wanka ta zuba uban kwalliya tare da sako wata tsadaddiyar turkishi abayanta mai kyau baka 

Tabishi wedge shoes na kamfanin zarah da jakarsa. Wasu iri dokoki ta zubawa hafsan as usual kafin nan ta bar gidan tana Allah Allah ta isa anguwar lekki domin ta ji damuwar hadiza dan ganin miscalls dinta datay dazun tasan bana lafiya ba.



Fannin meenal kuwa gabaki daya bawani jin dadin rayuwarta tayi ayau din a office ba duba da babu fadila awajen aikin yasaka abubuwa suka dan soma cirke mata dake fadilan itace yawanci take daukar aiki

Mafi yawan tanayi a memakonta koda kuwa tananan.


Gashi dama fadilarce kawai tay mugun kwarewa wajen iya aikin tare da iya bida jama'ar dake shige da fice yau da batanan sai abubuwan gaba daya suka rikice ta rasa gane kan komi


Tsabar takaici batama jira lokcin tashinta ba ta tattara kafafuwarta ta wuce gidan halisa nanma tun daga bakin gate malam liman ya sanar da ita cewa sun fita da jasmine a mota baisan inda suka nufa ba


Da dumbin takaici tabar wajen, nan ma tazo ta tarar da wani takacin daga wajen mijinta dr khaleel dan wani sabuwar sarar da ya samona shareta musammn intazo masa da wani complain dinta da babu kai babu gindi.


Yauma ko kula zancenta akan fadilar datakeyi bai yi ba ya fice agidan cikin sauri sauri yanamai duba agogon dake makale a hannunsa da alaman ana nemansa urgently awani waje.


Bude motarsa yay ya shiga yana zaunawa ko kunnata baiyi saiga sakon text message ya shigo atake ya bude yagani an rubuta masa


Location: _NISA Premier Hospital in Lagos located at 2/4, Afolabi Awosanya Street, Off Road 12, Lekki Phase 1, Lagos._

Team: Dr Asim khan(ccc)

           Assistants Dr  khaleel hasheem and Dr surayyat usman Adetunji

Client: Miss Halisa roberts mansa.

Duration:12 months.

Acikin yanayin sauri ya aje wayar harya kunna motarsa zai wainata ya fita kamar an tsakureshi cikin dakatawa yay sauri ya dauki wayar ya sake duban sakon da kyau. Dede wajen dayaga an rubuta"Halisa mansa Ya kure da idanu,tunowa da cewa halisan dayasani ne yasakashi jan wata kakkaurar tsaki tare da cewa shitttt!!!..dan ko kadan basa shiri da aminiyar matarsa wato Halisa roberts mansa.

AYI SHARING PLEASE


SURAYYAHMS 08060712446

No comments