Breaking News

Cuta ta dau Cuta 35

 *_Typing📲_*










   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*

             _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_Shafi na talatin da biyar_



________


*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥


*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥



*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥



_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_


*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*


*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*


*TSUTSAR NAMA Billynabdul*


*GUDUN K'ADDARA Huguma*


*AMEENATU Mamuhghee*



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA  LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_



___________



......Kwance take shiru akan abin sallar data idar da sallar asubahi. Tayi wani irin fayau da ita da ke tabbatar da ita ɗin amarya ce a yau ɗin. Daren jiya ne ke dawo mata daki-daki tamkar a yanzu komai ke faruwa. A hankali ta sake lumshe idanunta da cije lips ɗinta tana murmushi. Kafin daren jiya ɗauka take duk duniya babu ya Dafeeq a fannin jarumta, sai dai daga daren jiyan zuwa safiyar yau ta tabbatar da cikakken gwarzon namiji abin nunawa tsara. Lallai a baya tanada kundi, kundi mai ɗauke da tarin ƙaddara abar a tausaya mata da rububin son a karanta. Sai dai a yanzu ta tabbatar da cewar sake buɗe sabon kundi mai ɗauke da sabon babin rayuwa, rayuwa mai matuƙar ƙayatarwa da sanya zumuɗi a zuciyar duk wanda zai nazarci sabon kundin nata dan a yanzun ne kam tayi miji mai amsa suna namijin duniya, ba'a shimfiɗa kawai ba har a al'amuran rayuwa duk da kuwa kwanaki biyu kacal tayi da shi a matsayin mijin. “I love you Hamma Abaan”. Ta furta a hankali saman lips nata.

        “I love you too Adda Khadijah”. Aka gwargwaɗa mata cikin kunne. Zumbur ta miƙe zaune jikinta na ɗan rawa, sai kuma ta waro idanunta cike da mamakin ganinsa. Sam bataji lokacin daya shigo ba balle sanin yana durƙushe a kusa da ita haka. Jitai kunya mai tsanani ta sake lulluɓeta. Miƙewa tai da shirin barin wajen shima ya miƙe yana murmushi. Hannunta ya riƙo ya figota ta faɗo jikinsa. Yanda ya rungumeta tsam a jikinsa da shinshinar wuyanta da yake yana sakar mata sumba yasa ta ƙamƙamesa itama batare data sani ba. Sai dai sai ƙoƙarin son ɓoye fuskarta take yi shi kuma ya hanata hakan.

      “Anya bai kamata ace kunyar nan ta raguba kuwa Baddo. Yanzu fa kika gama faɗin You love me, bai kamata kuwa a nuna min love ɗin nan a zahirance yanda zan manta hanyar gate ɗin gidan nan gaba ɗaya ba. Yanda nake ji banƙi ace daren jiya ya sake maimaita kansa a safiyar nan ba koma har abadan. Dan ya kasance dare na musamman a kaf dararen dana rubuta a kundin tarihina da bazan manta da su ba ya gama danne girmansu da cikar nasu tarihin. Khadijah ke ɗin ta dabance, dan kin min ƙyautar da bazan taɓa mantawa da ita ba, sannan kin tabbatar min da mata ma fa suna suka tara. ALLAH yay miki albarka, yanda kika kasance haka cakwai ALLAH yasa rayuwar aurenmu ma ta kasance haka cike da farin ciki da ƙaunar juna koma fiye da hakan. I love you so much alheran”. Ya ƙare maganar yana sakar mata wasu tagwayen sumba a wuya. Jin tsaiwa na neman gagararsu ya ɗagata cak zuwa saman gadon.

      Wani sabon shafin mai cike da tarihi suka sake buɗewa. Yayinda Khadijah ta sake tabbatar masa da itama mace ce fa, dan kuwa ta cire kunya wajen nunama Abaan da gaske tana son shi duk da kuwa tana ji a jikinta dan Abaan ba namijin wasan yara bane. Bayan nutsuwa ta riskesu suka nufi bayi domin tsaftace kansu. Sosai Khadijah ke jin kunya amma babu yanda ta iya dole ta haƙura sukai wankan tare. Dan shi Abaan mutum ne kai tsaye. Baya kwana-kwana akan duk abinda yay masa. Gadon ta sake kimtsawa sannan suka kwanta ramuwar barci tana lafe a cikin jikinsa kamar wata ƴar mage...


       Barci suka sha sosai kasancewar dama yau ya ɗauki hutun zuwa office. Dan sai sha ɗaya suka tashi. A yanzun ma tare sukai wanka tanata noƙe-noƙe. Bayan sun fito yace ta ɗauka masa kaya a ɗakinsa. Babu jimawa kuwa ta dawo da kayan. Da taimakon juna suka shirya tsaff, kasa ɗauke idanunsa yay daga kanta, dan tayi matuƙar ƙyau a cikin atamfar data saka. Ita kam data ɗago ta kallesa suka haɗa ido sai ta sunkiyar da kai tana murmushi. A haka suka fito falo, inda suka samu an gyara ko'ina tsaf hatta breakfast ɗin su nakan dining a tsare. Zaman karyawa sukai da lafiyayyen abincin da Mamy ta shirya musu da kanta. Suna kammalawa sashen Mamy suka nufa gaisheta. Sun sameta ita kaɗai a falo dan Noor da sauran baƙin da suka rage sun fita kasuwa.

      Cike da farin ciki da sha'awa take kallonsu. Yayinda Khadijah kanta ke a ƙasa. Cike da girmamawa ta kai durƙushe tana gaida Mamy. Hannunta ta kamo ta ɗagota, kusa da ita ta zaunar da ita tana murmushi, ta ɗan bata site hug da faɗin, “Daughter kunyar ce dai har yanzu. Nifa mamanki ce karfa kice zaki ɗaukeni a suruka. Da ke da Baffana da Noor duk ɗaya kuke kinji”.

     Kai Khadijah ta jinjina mata tana murmushi. Gaisheta shima Abaan yayi, ta amsa masa da kulawa sannan ya tambayi ina su Noor. Sanar masa sun tafi kasuwa Mamyn tayi tana maida hankali ga Khadijah da duk ta kasa sakewa. Har akai kiran zuhur suna sashen, anan ma ya barta ya wuce massalaci. Fitarsa babu jimawa su Noor suka dawo. Nanfa Khadijah ta sake miƙe ƙafa aka shiga hira. Har akai la'asar. Sai da Abaan yay kiran Noor a waya yace tazo sannan ta miƙe badan taso ba. Noor ta mata rakkiya har sashen nata sannan ta koma. 

       A falonta ta sameshi zaune yana waya. Zama tayi a kujerar gefensa har ya kammala. “Dama haka amarya keyi ta manta da mijinta Baddo?”.

     “Kayi haƙuri”. Ta faɗa a hankali. 

  Kansa ya ɗauke da ga kallonta yana faɗin, “It's ok bani rowa”.

   Tsam ta miƙe zuwa kitchen. Ya bita da kallo yana wani lumshe idanunsa a kasalance. Sai kuma ya ɗan cije lips ɗinsa da sakin murmushi mai ƙayatarwa. Shi kaɗai yasan irin farin cikin da nishaɗin da yake ji a yau ɗin nan. ALLAH dai ya basu zaman lafiya.....



____________★



         Sosai al'amari yay matuƙar tsamari a ɓangaren JJ. Dan tun ana kiranyen Alimah har an haƙura sai addu'oi da aketa masa da neman magani. Matuƙar ƙawanya cututtuka da aka kasa gane kansu sun masa. Gaba ɗaya ya canja daga JJ ɗin nan ɗan gayu ɗan ƙwalisa. Ya rame sosai kamar kai cutar sida. Kullum cikin masa saukar Alkur'ani ake. Tun ma al'amarin na bama mutane tsoro har ya koma bada tausayi.

       Watanninsa biyar cikin tsananin jiyya a wani dare gobara ta tashi da shi wadda ba'asan musabbabinta ba. Sosai anguwa ta ruɗe, dan abin mamaki iyakar ɗakin da yake jiyya ne kawai ya kama da wutar a gidan. Da ƙyar da ƙyar aka samu aka kashe wutar, yayinda aka fiddo JJ cikin wani yanayi naban tashin hankali. Kai tsaye asibiti aka nufa da shi, in da likitoci sukai masa karɓar gaggawa dan gaba ɗaya jikinsa ya gama saluɓewa, hatta da fuskarsa ba'a iya tantancewa. Zuwa safiya labarin wannan gobara ya gama zagaye anguwa har da kafafen sada zumunta. Yayinda hotunan JJ suka fara yawo tare da labarin tsiyatakunsa na baya. Abin yi fa ya samu, dan dama duk sanda irin haka ta faru kakanji bakuna daban-daban musamman a social media. Ka shuka alkairi ma yaya kakare balle sharri. Al'amarin JJ ya zama wani abin tattaunawa a kowace kafar sada zumunta. Yayinda ƴammata da iyaye ke addu'a akan masu irin halin JJ ALLAH ya sake nuna musu iyakarsu. Wasu ma ko a zahiri suke bayyana sunayen waɗanda sukai musu irin yaudarar JJ ɗin. Nanfa rikici ya ɓarke tsakanin ƴammata da samari, kowa na faɗin albarkacin bakinsa akan ɗan uwansa da ƙoƙarin kare kansa. To komadai minene ta JJ kuma ta ƙare ai. Dan halin da yake a ciki babu tabbacin zai sake wata doguwar rayuwa kuma. Ga taimakon da ake nema ma wasu da sun ji tushen labarinsa sai suji ƙyashin badawa. Sai dai kawai idan kaje kaji yanda yake ihun kuka da roƙon likitoci su taimakesa su kashesa dan azabar ƙunar da yake ji zakaji tausayinsa kasancewar ka mai imani.

      Watannin JJ kusan takwas nannaɗe cikin bandage a gaba ɗaya jikinsa sai idanu kawai ALLAH yay masa rasuwa. Mutuwa ce data matuƙar girgiza duk wanda yasan sa a zahiri dama wanda ya san labarinsa da hotunansa a kafafen sada zumunta. Dan yanda hotunan nashi da labarinsa suka dinga yawo a baya a yayin mutuwar tasa ma hakan ce ta kasance. To shi dai tasa ta ƙare kuma ai. Sai fatan ALLAH ya shiryi ƴan baya idan masu shiryuwa ne. Idan kuma bazasu shiryu ba ya UBANGIJI ka fimu sanin miya dace akan azzaluman nan. Ka mana maganinsu ka kare ƴaƴayenmu da ƙannenmu dama mu kammu da ga shiga tarkon yaudararsu. Ya rabbi ka yafe mana kurakuran mu. Ka sanya duniya a tafukan hannunmu ka hanata tasiri a cikin zukatanmu. Ya rabbi ka wajabta mana tsoronka da soyayyar ANNABIN MU tsira da amincinka su tabbata a gareshi shi da iyalan gidansa. Ya rabbi kasa ranar mutuwarmu ta zama ranar farin ciki a garemu. Ya sabbi ka saka gaskiya a harsunan mu, zukatanmu, jikunmanmu da ayyukanmu baki ɗaya🙏😭..



___________


       A washe garin da aka sallamo Kainaat asibiti ta tattara komai nata ta danƙa a hannun Mom ɗin Nadwa da tazo dubata. Dan hatta kuɗaɗenta na banki kaf ta turasu a account ɗin Mom ɗin. Bayan Mom ɗin ta wuce gida ta kammala nata shirin tsaff akan Dafeeq. Dan zama tai a falo tare da ajiye biro da takarda tana jiran shigowarsa. Kusan awa biyu kuwa sai gashi ya dawo. A kallo ɗaya da yay mata ya gama karantar shirinta. Amma sai ya danne zuciyarsa ya ƙaraso cikin falon. Kusa da ita ya zauna cike da kulawa da kwantar da murya ya ce, “Hajjaju yaya dai! Badai jikin bane ko?”.

     Maimakon bashi amsa sai ta miƙa masa takarda da biron data ajiye. Kallonta yake cikin nuna alamun rashin fahimta, kafin yay ƙarfin halin faɗin, “Namiye kuma wannan ɗin?”.

        A gatsine ta ta ce, “Takarda ce da biro. A yau ina buƙatar saki na Dafeeq. Dan bazan iya zama da kai ba Dafeeq. Ka sanya min ciwon sanyi saboda tsabar son zuciyarka. Miyasa tun kafin aurenmu baka sanar min kana da infection ba ne?”.

     Murmushi yaso saki dan harga ALLAH tama bashi dariya amma sai ya dake. A ɗan ɗage cike da gatsen shima ya furta, “Ai auren mu auren zobe ne Hajjaju, babu saki babu yaji har abada. Banda abinki ma k yanzu ina zaki je da wannan abun da ke a tare da ke”.

    A wani kalar razane ta ɗago ta kallesa da faɗin, “Kamar ya?”.

   “Kamar yanda kika ji na faɗa mana. Hajjaju tunda har kin tabbatar na saka miki wannan ciwon bai kamata ai mu rabu ba dan kema zaki iya zuwa ki sakama wani. Kawai muyi haƙuri da juna a haka shine zai fi”.

       Wata irin ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, dan da farko ta zata cikin dake a jikin nata ya gane. Harara ta watsa masa da miƙewa ta jefa masa takarda da biron. “Babu ruwanka da abinda zai faru a rayuwata ta gaba, na baka awa ashirin da huɗu ka saken da arziƙi ko ka sakeni ta wuya.” fuuuu ta wuce rai a ɓace. Murmushi ya saki da kaiwa kwance jikin kujera yana wani cije lips. Sai kuma ya ciro wayarsa da ke aljihu yay ɗan danne-danne da kaiwa kunne. Cikin wata iriyar murya dake nuna tsantsar basanci ya furta, “Doctor aikin ka ya fara.”

    Murmushi mai ƙayatarwa Doctor Giɗaɗo ya saki da ga can, har Dafeeq na iya jiyo sautinsa. Cike da isa ya furta, “Yes Abokina.” 

  Yanke wayar Dafeeq yay yana sakin wata shegiyar dariya harda ɗan bubbuga kansa a jikin kujera irin na na gama cin nasarar nan..


      *_WASHE GARI_*


   Ƙarfe kusan goma na safe Kainaat dake ta shirye-shiryen matakin da zata ɗauka akan Dafeeq ta sakko ƙasa. Kitchen ta nufa neman abinda zata sakama cikinta saboda yunwar data tashi da ita mai tsanani. Tana ƙoƙarin ɗora tukunya a saman gas sabon maigadin ta yay sallama. Daga kitchen ɗin ta amsa masa tana ɗan leƙowa. Ganin yanda yake kamar a ruɗe ya sata tsayawa kallonta. Sai kuma a ɗan tsawace ta furta, “Ɗanjuma lafiya kuwa?”.

        “Babu lafiya Hajiya, dan wasu baƙine gasu can a tsakar gida suna dudduba gidan nan, sune suka ce a sanar muku wai masu gidan ne su suna buƙatar magana da ku masu hayar ciki”.

    “Haya kuma? Wace kalar haukace kuma wannan, kodai ka fara shaye-shaye ne Ɗanjuma? Kai ubanwa ya faɗa maka haya nake a gidan nan?”. Sai kuma a fusace ta nufi ƙofar fita batare data jira cewarsa ba.......✍️




      _Tofa Hajiya Kainaat mike shirin faruwa haka ne kuma?_.


_Amin afuwa da jina shiru kwana biyu, cikin ƴan hutuna ne ta saka bit a hanci gaba ɗaya hankalina ba'a kwance yake ba kwanakin nan🤦._


 ____________



_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_


_KU MARMATSO KUSA...🔊_



  _ZAFAFA BIYAR 2024_


_ZAFAFA BIYAR!!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_


_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_


_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_


 _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA  ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_


_________


         _1_

 *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_


           _2_

*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_


              _3_

*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_


        _4_

*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments