Breaking News

Dare Daya Complete Hausa Novel

 [1/29, 6:39 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): 🏅🏅🏅🏅🏅

  DARE. DAYA

🏅🏅🏅🏅🏅


             Na

Hafsat.   (Hapsy baby)



10&15




 




Nurayya nacikin bacci taji saukar ruwa masu sanyi jikinta  tayi firgit tatashi a firgice tabude idonta saitaga gwaggo tsaye bisa kanta . gaggwo cikin fusata tace  don ubanki baki San safiya tayi bane ki kwanta sai bacci kike shegiya tashi maza kisha re man gida da kuma gidan tumaki. Ko kuma nayi miki shegen duka.  Tahaure da kafa   nurayya cikin sauri tatashi  natafara shara bayan tagama ta ibo ruwa tayi  tayi Alwalar safe domin ta makara bacci yadauketa domin da asuba Baffa

 kedata shikuma ya nufi massalaci batasan abinda yahana yatadaba ita kuma bata tashi ba.  Bayan tagama sallar  tanufi daki gwggo  da durkusa gwggo Ina kwana  ta harereta tace daban kwana ba dakinganni  gwagggo Ina kalacina tawurgo Mata wani kofi kingin kadan yazube hannuta  saiki dauka gayanan  kokone tsururu babu kauri ko kadan     atare dashi gashi babu sugar ko kadan  hakanan nurayya tahau shanshi. Bayan tagama tadauraye Kofi takaishi maajinsa. Tanufi hanyar soro domin tadubo lafiyar Baffa   tayi sallama dakin ya Amsa Mata yana kwance. Yace nurayya tace naam Baffa Ina kwana yace lfy lau kintashi lfy tace lfy lau Baffa najika shiru yau har na makara  sallar Asuba domin kasaba tadani. Baffa yace Ayya!! Nurayya tunjiya banajin dadin jikina shiyasa kikaji jini shiru wallahi zazzabi da mura kedamuna. Tace sannu  Baffa. Allah sawakkka. Yace Ameen yar Albarka. Kinyi kalacine Tace Masa nayi Baffa  yace to. Nima naji sauki yanxu zantashi infita nima.




ABUJA


 Wata kyakyawar matace bazata wuce  36 years zaune  kan kujera tayi tagumi salllama ake batajiba  saidai taji antabata saudat!! tayi firgit tagoge hawaye  da suka zobomata Amma tayi late, yariga yagani saudat sai yaushe zaki rage sa damuwa cikin ranki ne tafashe da kuka tace sai ranar danaga  Meenat Alhaji bansan araye takeba ko mace  shekara 12 haryanxu shiru babu labarinta  duk da Allah yabani wash yayan Amma Meenat  takibari raina. Yace kiyi hakuri saudat komai rubbbatce daga Allah zaga ganta tana Raye. Insha Allah. Nan yarrrasheta tayi shiru.



"NURAYYA ce  ke tafiyarta cikin natsuwa  zuwa Aiken da gwago tayi Gidan delu dillayiya," kawai taga mutum Gabanta ta tadago fuskarta a firgice  taga Ilu ne  cikin  muryasa ta Mashaya yace waike meyasa kincika girman Kai?? Anunamaki Anasonki Amma saiki  ta  wani kaucewa ko taja wani  tsoki ta tofar da yawu tace Allah  sawwake nayi soyaya da kazami mashayi,

Dakai  tajuya tayi tafiyarta,



"Bayan tadawo   daga Aiken gwaggo saidatasha rankwashi wai tadade bata dawo ba.

       BAYAN KWANA BIYU


Dadddare nurayya ce kwance bayan ta idar da sallar isha'i  wani yaro yashigo wai Ance nurayya tazo  wajen kafin ta motsa har gwaggo tafito Zane rike da hannu waye ke Kiranta tane yaro yace Ilu ne dan Gidan malam garba sarkin noma,

"Gwago tace  muje wajen bada jimawa tadawo ,

Nurayya!! Don ubanki  bakiji Ana kiranki bane munafuka kina fitowa ko saina biyoki cikin dakin  nayi miki shegen duka,

Dasauri nurayya tatashi tanufi Hanyar wajen tafito taga Ilu  Ansha dan duwala  sai tashin kamshi nurayya ta kalleshi tace  waikai Ilu saunawa zanfadamaka ka kyaleni ko Ana soyaya dole ne tayi tsaki tashige ciki,tanashiga gwaggo tace munafuka har kin koroshi saboda bakin halinki KO??takaimata bugu nurayya takauce.

,

[1/29, 7:08 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): 🏅🏅🏅🏅🏅

DARE D'AYA

🏅🏅🏅🏅🏅       

         Na

Hafsat ( Hapsy baby)


1&5


Dasunan Allah mai rahama mai jinkai


Masoyana nacanza salon book dinan daga so Gamu najini zuwa Dare D'AYA dafatan kuna tare Dani luv you All masoyana😘😘

Muje zuwa.











     'Nurayya!!! Nurayya!!! "Naam gwago ganinann fitowa",cikin fushi Gwago dake zaune akan tabarma tace" karma kifito, kiyi ta zama" Nurraya  dake tsaye cikin d'aki kaya sawa tane a gabanta tama rasa wani kaya zatasa yabuda ma jikinta domin duk sun tsufa sai faci dake garesu, Can tajawo wata tsohuwar atamfa wadda keda dama- dama tasa ta d'auko wani tsohon hijabi duk saman anyi, masa faci tasa. Tafito tazira takalmata da duk suka sha d'aurin leda. Tanufi inda gaggwo take cikin natsuwarta tace "gani Gwaggo nagama" Gwogo ta  wurgamata harara sannan  tace  "sai yanxu kika damar fitowa don ubanki? Nurraya ta sunkuyar dakai tace "kiyi hak'uri dan Allah"  Gwaggo tace " ga gyadar nakuma samiki, saura kuma  kik'i saidowa kiga yadda zanmiki  shegen duka!  kuma bazan baki abincin yau ba kowaye yatsaye miki kuwa, dauki maza kije kisayar man da gyadata kidawo inajiranki" .  Nurayya cikin sanyi jiki  tana k'okarin  daukan faranti gyada wani uban rakwanshi taji akanta wanda yasata tsala kuka saboda azaba,  Gwaggo tace" yimin shiru munafuka kiyimaza kidauk'a kitafi ko saina jawo Kara nayimiki shegen duka?"   Nurrayya tad'auki  faranti tanufi waje tana matsar kwallah.


   

      Tana cikin tafiya tagamu da Hanne k'awarta tadauko dankali nan suka nufi rumfar Bobo inda suka Saba zama in sundauko tallah.  


   Bayan sun saida  sukatashi suka nufi Gida sunatafe  suna hira    Hanne kecema nurrayya iro yakusa  Aikuwa gidansu  domin Maganar bikinsu. Nurayya tace " Allah yanuna mana lafiya" Hanne tace Amin tana murmushi, ahaka suka cigaba da hirarsu harsuka rabu kowa yai kwanar gidansu.


     Tana shiga  Gida tayi sallama  Goggwo ta wurgo mata wata harara tasan maganar, cikin sauri taje gaban gaggwo tazube  ta mik'a mata  kud'in  ciniki datayo  gwaggwo takarb'a ta k'irga taga sun cika daidai tayi dariyar mugunta sannan tace "Allah ya taimakeki suncika" Nurayya cikin rawar murya tace "Gwaggo Ina abinci na?" Gwaggo  tace "sai kije gayacan bakin kitchen"  Nurayya cikin sauri tanufi wajen kitchen domin wata azababiyar yunwa takeji, tana budawa taga wani dan guntun tuwo sai uwar miya datasamata, hakanan tajawo tafara ci tashanye miyar tatashi tayi Alwallar  sallahr  La'asar sannan  tashiga dakinta.


     Dakin kamar bola domin cike yake da shirgin  gwago babu matsaka tsinke, Nurayya tanufi  inda yagyalar tabarmata  take ta shimfida Abin sallah wadda Baffa yabata shima duk ya tsufa ta tada Sallah.


  

    Bayan ta idar  da sallah ne  tazauna tana lazimi  can taji gwago nakiranta  tayi zumbur ta mik'e tafito gwaggo tace "wanke- wanke da ibo ruwa waizai miki? Da zaki shige daki munafuka, cikin sanyin jiki ta nufi wajen   tulu  ta dauk'a tanufi rafi tafara  jido ruwa sai data cika komai na Gidan  tazo tafara wanke- wanke, ba ita ta gamaba sai daf da magariba tayi sallar magariba bata tashi daga kan salayar ba   sai datayi isha'i  tadan kwanta nanfa cikin ta yafara kukan yunwa tarasa yadda zatayi,


   Har bacci yafara daukarta  taji  Anhakali Ana kiranta "Nurayya!" Firgigit ta tashi saitaga Baffa ne Yayi maza ya mik'omata wata bak'ar leda yace "maza  tashi ki cinye, karta gani" Nurraya ta tashi tana mitsika ido ya juya yatafi dasauri  ita kuma tazauna ta buda leda saitaga rogo ne,  nantafara cinsa hannu baka hannu kwarya, take ta cinyesa ta tafito ta lallaba tasha ruwa takoma  ta kwanta  a ranta tace " Allah sarki Baffa, shikadai kesona  ko Ina nahaifiyata?  domin nasan ba  gwaggo ce ta haifeniba! Da wannan sak'ake-sak'en bacci me nauyi ya d'auketa.

[1/29, 10:17 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): 🏅🏅🏅🏅🏅

DARE DAYA

🏅🏅🏅🏅🏅


      Na

Hafsa(Hapsy baby)



20&25






Nurayya ce daki kwance tana tunanin irin bautar datakesha Hannu gwaggo to wai ita Wacece ita,

In Baffa maihaifinta ne Ina mahaifiyar ta domin tasan ba gwaggo bace mahaifiyar ta,


Tayi nisa tana wannnan tunanin taji" Baffah yanacewa nurayya firgit tayi tatashi tace Baffah yaushe kadawo ne,


"Yace nurayya kikara hakuri nasan kina,cikin matsi daga wurin jummala da bauta babu yadda zanyi Amma kikara hakuri kinjiko,


" Nurayya ta dukar, dakanta Baffah dama cewa zanyi wai Ina mahaifiyata??? domin, nasan gwaggo ba ita tahaifeni ba,


"Baffah yayi shiru yace kikara hakuri nurayya zakisan komai Nan gaba kadan kinji ko.


"Nurayya ta gyada Kai shikenan Baffah,yace yauwa,

Bari nakoma. Dama nashigo naduba lafiyarki danasan batanan Bari nakoma,






Gwaggo ce zaune da kawarta delu nurayya tadawo daga tallar gyada cikin natsuwa tashigo talkma duk sun katse sai qulin leda ga Atamfatar duk ta qoqe,



Tadurkusa taba gwaggo kudin  gyadar gwaggo saidata kirga kudin "tace Allah yataimakin kin kawoman kudina. Daidai,

Dayau nadakamaki shegen duka,


Nurayya cikin murya mai sanyi tace gwago Ina Abincina,

Tace bandafa sai kisha eyes .


Nurayya tatashi tatafi dakinta


"Delu kawar gwaggo tace  wai ke yamaganar Auren 

Diyar nan   mai suffar Aljanu da  Ilu, ne,


Kinsan yalikeman yace sai ita yakeso zai Aura kuma kinsan babu Abinda nakeso irin farin cikin  Ilu,


"Gwaggo tace kawata sha kuruminki  indai wannan munafukar diyarce naba Ilu,ta 



Kawai kicema mallam ya Aiko Anyi Magana,


 

"Nurayya dake  daki tace  Ilu za aban Aure wallahi bazan Auri Ilu, tafashe da kuka,


           Bayan kwana biyu



Nurayya ce kita jido ruwa daga rafi yunwa duk ta isheta,


Tazo saidai shigowa taji Abba yanacewa  Haba jummala bazaki duba Amanar Allah dayabamu  


Nurayya tasaurara bata shiga  cikiba,


Kisani nurayya Amanace Allah yabamu bamusan ko waye mahaifantaba Amma kita Azabatar da diyarnan.


Shinema bama danasani ba zaki zaatoroman su malam. Garba maihifinn Ilu  Akan maganar Aure, 


Tuss sukaji  fashewar wani Abu  suka waiwaya suka nurayya,

"Cikin kuka nurayya tace Baffah 

 Dama bakai kahaifeniba

Waye mahaifina to"

[1/29, 11:43 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): 🏅🏅🏅🏅🏅

     DARE DAYA

🏅🏅🏅🏅🏅

        Na

Hafsat(Hapsy baby)


30&35







_Baffah_ _dama_ _bakai_ _ka_ _haifeniba_ to _waye_ _mahaifina_???

 


"Baffah yamatso kusada da nurayya tashi nurayya kiyi hakuri yanzu zakiji komai,


"Gwaggo tace don ubanki sai kin biyani tuluna ji yadda kika fasheman shi babu wani sauran moruwa dazaiyi,


Baffah Hannu  nurayya. Yaja kawai yayi suka nufi  Hanyar dakin shi,


Yazaunar da itah yace kiyi hakuri nurayya da Abinda Zan fadamaki ki tabbas tsintar kiyi nayi Ahanya tadawo Gida 


Kinga kayan dakeji jikinki yatashi yadaukomata kayan 

Yan kati pink masu kyau,


Yace natafo dake na niyyar nakawo ma jummala ta raineki tunda Allah bemamu haihuwa ba,

Amma jummala taci Amanar da Allah yabata,

Kuma inhardai da raina baza'ayi miki Auren dole ba,


Tashi kije Allah yayi miki Albarka,


"Nurayya tafito tanufi dakinta 


Tafashe,da kuka Ashe ni yar tsintuwa wace baasan mahaifana ba, menayi ma mahaifiyata harta yadani haka, wayyo Allah nashiga ukku,!!!



      BAYAN WATA UKKU




NURAYYA  tanacikin matsala bacin gwaggo takara takuramata Arayuwa sai tunanin wacece ita,



Nurayya ce zaune tana wanke wanke sallama taji ta Amsa  saitaga Atallabo Baffah cikin sauri tamike Baffa!! Gwaggo! Gwaggo tafito meye kike kwalamn Kira Kamar wadda tayi sata! 


Ganin A tallabo Baffa tace meyasa meshi bayinAllah  haka,


Suka yana Aiki A gona ne maciji yasareshi,


Amma Anbashi magani


"Bayan Anje Baffa ne nurayya tazo kusadashi sannu Baffa,



  

Cikin Alamun yanajin jiki yakadamata gwaggo ta ingije nurayya munafuka tunda be lafiya sai ki kyaleshi KO,


Bayan sati daya 


"Baffah yana jin jiki nurayya ce tashigo dakin sannu Baffa cikin karfin hali yace yauwa,



 ""Yace nurayya ba tabbas bane tatashi Ina rokon Allah yahadaki da iyeyenki,


Tari yasarka shi yace nurayya bani ruwa da gudu tafito tanufi wajen ruwa tabuda ta ibo takawomishi 


Baffa yace nurayya kowani hali kikasami kanki karki saida ,mutunchi ki kinjiko,


Nurayya tace Baffah sannu 

Amma Ina  Baffa Kalmar shahada kawai yake,


Dukkan mai rai zai zama gawa Baffah ya Amsa kiran mahallichi



Wata Kara nurayya tasaki daidai shigowar gwaggo  Domin fitar take babu ruwanta,

Ta Afko cikin dakin taga

Baffa kwance dasauri ta isa wajensa mallam!!

Amma yaki motsi dasauri  shikenan malam ka mutu wayyo Allah na,


Nan dai Akayi ma Baffah wanka Akaishi makwancin sa na gaskiya,

Nurayya Tasha kuka kamar me 

Amma gwaggo Anatafiya kaishi suka dasa gulma,

(Allah yashirya)


          Bayan Wata Biyar



Komai yafara wucewa bautar nurayya da tallar datake sai Abun yakara gaba 


Yauma kwance take tana tunanin, mutuwar Baffah gwaggo ce tashigo dakin munafuka sai kitashi Ilu nakiranki, konayi miki shegen duka, kuma natsaida bikinku Nan da sati biyu tunda babu shirin dazanyi nidai 


Damasu sun shirya, nisuke jira


Nurayya tafito wajen Ilu yace Amaryata cikin fushi tace wacece Amaryaka yace kemana  Nan da sati biyu,


Tsoki nurayya tayi takoma cikin Gida Amma labewa tayi taga gwaggo batanan sannan tashige dakinta,

Tazauna dabas

"Tace wallahi daayiman Aure da Ilu gwara nabar garinan dama Baffah kadai kesona kuma ya mutu,


Tadasuri tatashi ta kulle kayanta

Tafito salab salab 

Har tafito tana fitowa tadinga gudu kamar zaa kamata,

 

Tanufi Hanyar Gari


Ina  nurayya ta nufa??

[1/30, 3:09 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): 🏅🏅🏅🏅🏅

     DARE DAYA

    🏅🏅🏅🏅🏅

           Na

Hafsat (Hapsy baby)


40&45







Nurayya gudu take Hanyar ta tafita Daga kauyensu, 


Marece yayi Tasha kawai tanufa tagarinsu Daga babu motoci sai daya kawai dazata Kaduna, 


Tarage kingin mutum daya yarage dasauri tashige kartaga ma wadda yasanta,


" Sukafara tafiya ta kwance kullum kudin ta wadda Baffah yakebata taga. 950 da hamsin ne,

 


Akafara Amsar kudin mota naira 900 duka nari 900 nurayya ta mika  sai naira Hamsin da ta tsira da ita,



Sun iso Kaduna lafiya Aka sauke su Tasha, kowa ya tafi inda zashi,


Nurayya kuma tsaya tayi tana kallon garin domin vataba shigowa birnin ba tarasa inda zata nufa,


Fitowa tayi Bakin titi inda taga kowa nafita,


Taga motoci sunata wali bisa titi gashi ita kuma bata 

Iya ketara titi hasalima,

Bata taba ketarawaba,


Dagudu tanufi titi zata ketara ganin wata mota ta tafo ta dawo da gudu Amma inah dawowar dazatayi,


Wata mota tatafo garam!!

Tabanke nurayya, 

Kan Ayi haka sai jini tabaki 

Gashi duk taji ciwo bisa kanta,

Na cikin motar da sauri,

Yafito nan mutane suka taru,

 Wadda yafito Daga cikin motar yace sun Santa  

Sukace basu taba ganinta ba santa,



Dasauri ya sunkuce nurayya data suma yasata mota suka nufi Asibiti,


Bayan sun  isa  Akabata Gado 




Akayi dinki wurin dataji ciwo,

Dama bataji ciwo sosai ba buguwa ce,


Kawai tayi tana farfado taga ganta bisa gadon Asibiti,


Kagakuma wani dattijo kusa da ita zayakai shekaru 50,


Tabuda idanuwanta  wadda yabanketa yace ya matso gadon datake yace sannu baiwar ki farfado??


Inane inda iyayensuke naje nakirasu don su San halin dakike ciki??


Nurayya  tafashe da kuka.

Yace baiwar Allah meyasameki kike kuka ne??


"Nurayya tace ni bani da 


Iyayen bansan kowacece niba,


Mutum yaja Numfashi yace Allah mai iko, 


To inazaki danaganki Har tsautsayi yasani nabankike??


Nurayya cikin kuka tabashi labarinta wadda tasani,.


Yaja Numfashi yace  yace Allah yabayyana iyeyenki,



Yacemata sunana Alhaji  Lawal

Inada Mata daya da yayyya Ukku,


Mahmmad shine babba sannan. Lubna ikram,

  


Zan daukeki natafi dake gidana domin duk wadda yataimaki wani Allah zai taimakeshi,


Doctor yace zaibaki sallama yanzu saboda baki Ji ciwo sosai va,


Nurayya tace nagode Baba,

Yace babu. Damuwa yata,


Alhaji lawal yace dauko kayan ki sai muje KO, 



Nurayya tasabi kullin kayanta sukaje office din doctor yabasu sallama.


Sukazo Alhaji yaja mota suka nufi gidanshi,



Iluv masoyana😘😘

[1/30, 4:33 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): 🏅🏅🏅🏅🏅

DARE DAYA

🏅🏅🏅🏅🏅


        Na


Hafsat (Hapsy baby)



50&55






Bayan sun shiga mota sun tafi


Isarsu Gidan Alhaji Lawal 

Alhaji yaja hannu nurayya Har ciki Gidan ya iske.  

Lubna da ikram falo,

Suka tashi cikin murna dady kadawo


Amma ganin  bakuwar fuska taredashi kuma yar kauye  nan suka Fara yatsina Fuska,

Daddy inakasmo Almajira ne??


Daddy yace ba Almajirabace Ina Momyn Ku?? 


Ku kiranman ita saiga Hajiya

Saratu tafito Abban mahhmad me Akasmu ne Akace Akirani ne,


Yace zoki zauna sai kiji komai,


Itama Hajiya saratu kallon wulakacin tabi nurayya dashi,


Alhaji yayi gyaran murya yace nasan zaku ganni  da bakuwar fuska Baku sannan kowacece ba,


Nan yabasu labarin nurayya kamar yadda tabashi,


Yace inafatan zaku kulata da ita sosai, kamar ya' nadauketa wajena,



Lubna tashi kinunama nurayya dakin nan da bakomai cikinsa, 


Gobe  zanfita da ita tazabi Abinda take so,


Lubna cikin. Yauki tatashi tanunama nurayya daki,


Nurayya taga daki tsaf ga Gado ga komai,


Ta aje kayanta bisa Gado,

Lubna tace banan Ake Aje  kayanba cikin wadrope,


Dama tsiyar bakauye kidahumanci,


Komai dady yagani zai kwasoman nake,

 Mswwtt



,nurayya tayi shiru batace komai ba,


Lubna ta harareta kawai tayi tafita,



Washe Gari




Alhaji Lawal da family dinshi suna zaune Suna break fast,

Alhaji Lawal yace banga nurayya ke!!

Ikram tashi kikrata tazo taci Abinci,


Ikram tatashi domin tun labarin da dady yabata na nurayya taji tana tausayin Hanyar kofa daki nurayya tayi,


Tatura kofa ta iske nurayya zaune takure,


Tace nurayya dady yace kixo muyi break fast,

Nurayya tace meye Break fast,


Ikram tayi dariya tace bakisan ma'anarshi ba  



To karin kummalo,


Nurayya tatashi tabi bayan ikram,.

Suka nufi dinning,


Muhammad dake cin Abinchi, yadago fuskar da sauri yakware ganin kyawu Irina nurayya  Dady yace sannu sha ruwa,


Yace nuryya yakika shige dakine zo zauna kiyi kakaci 


Kizama kamar yar Gida kunji KO,


Bayan sungama break ne dady yace Ammm nurayya wannan jiya baki Ganshi ba KO,

To shine Muhammad babban Dana,.

 

Nurayya tadago fuskarta ta kalleshi,tamaida,







Haka rayuwa taitafiya dady yasaka nurayya makaranta tafara Daga primary 5


Masha Allah nurayya tana gane karatu,


Amma tanashan wahala wajen lubna da Hajiya saratu domin basu kaunarta kokadan

  


Wasa wasa yauga  nurayya.

Tana shirin zana exam din kammala jinour section,


Zaune take tana karatun exam din kawai saiga lubna tashigo ta watsa Mata kayan wanki.

Tace tashi maza kije ki wankesu kuma wallahi inbasu fita ba sai kin Kara wankesu, tsintartar mage,



Nurayya tatashi tasabi wanki tafito tana fitowa tayi cin Karo da Muhammad 


Muhammad "yace nurayya inazaki da kayane tace Aunty lubna tace nawankemata,


Muhammad yashiga kwalama lubna Kira  saiga tafito


Yace bahanaki bama  nurayya wanki ba Ina Amfanin mai wankin dake cikin Gidanan Maza Amshi kayanki bazata wankeba,


Ba baiwarki bace Ai 



Hajiya saratu tafito cikin sauri Daga daki tace Ahhh mezan gani babana meyafaru,.


Muhammad yace Momy lubna taba nurayya wanki Kamar baiwarta 


Momy tace meke Amfaninta dama???

Shine kake ta mike wuya zaasa nurayya Aiki kul nahaneka wallahi


Maza ke wuce kitafi ki wankemata kayan,



          Bayan shekaru ukku,




Wata kyayawar budurwa nahango tana wanki gindin famfo,


Tulin kayane gabanta sai wankewa take,

Can nahango wata budurwa babbace domin tafi wadda ke wanki,

 Tanufo wajen ke don ubanki Ina kikaiman,

Wayata cikin sauri  tadago fuskarta razana nayi ganin nurayya ce tayi wani kyau,


Tace wallahi Aunty ban daukar miki wayaba,


Ikaram ta iso wajen haba lubna meyasa kika tsani nurayya ne  metayimiki 


Dazakice tadaukar miki waya kodan kinga brother   bayanan,


Lubna tsoki taja kawai tabar wurin 


Ikram tace kiyi hakuri kinji

Nurayya Allah yanatare cake


Ikram tace Amshi wayanan brother yanason magana dake, 


Nurayya takarbi wayanan tasa kunnenta 


_Assalamu_ _Alaikum_



Muhammad yace  walaika salam kanwata kina lapiya,?? tace lapiya lau yaya Muhammad


Yace ya karatu tace yaya Ai mungama sati daya dayuwuce sai jiran result,


Yace wai na manta ikram tafadaman,


Yace inafatan baki kula kowa  nayi miki miji danawo zaizo wurin dady Ayi magana 

Tace yaya nida bana fita sai inzani isalamiyya,

Yace yauwa kanwata nagode,

Sai anjima KO,

Tace Allah yakai mu lafiya

Ta mika ikram waya ikram tashige tana waya,


Nurayya Cikin. Ranta. Tace Allah sarki yayana,yaceman kingin wata biyu yadawo Ai naga wani miji yazabamn ne


Ta cigabada wankita sai bayan mangariba ta idar,






Yau Gidan suntashi da murna domin yau Muhammad zaidawo Daga tafiyar dayayi kasar England,

Karo karatu na shekara ukku,

 Adafa wannan  Asauke Kamar  zaayi baki goma,



Karar mota sukaji da gudu  sukaji da gudu lubna da ikaram suka nufi waje


Nurayya kuma tana lekensu ta window ganin wani handsome guy yafito Daga motar ne yasa nurayya Kara murza ido badai yaya Muhammad bane  yakara kyau haka


Sunji hayaniyarsu tayi sun shigo falon itama yasa , tafito, sallama tayi 



Muhammad yadago fuskar yaga wacece mai zazzakar muryanan.

[1/30, 11:23 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): 🏅🏅🏅🏅🏅

     DARE DAYA

🏅🏅🏅🏅🏅


         Na


Hafsat  (Hapsy baby)



60&65


® *P* *W* *F*







Nurayya tayi sallama tashigo,



"Muhammad yadago fuskarta yaga wacece wannan mai zazzkar murya

Shagala yayi da Kallonta harta durkusa tana gaidashi 

Besani saida ikram" tace yaya  nurayya tana  gaida



Sannan, Muhammad yadawo firgit yace kanwata,  Aibanganekiba  kinkaba kinkara girma,


Momy takatseshi tace Babana. Banason yawan surutun dauki Abinchi kaci,


Kadawo Daga tafiya sai surutu ko ruwa  bakasha,


Momy ta wurga ma nurayya wani Kallo  dasauri tatashi zata bar wurin,

Muhammad yace inazaki kanwanta??




"Momy takatseshi Ina ruwanka da inda zata,?? Ne 





Muhammad yasaddadakai kawai,





Dadaddare zaune suke falo harda dady,

Yadawo Daga. Abuja kiran da  maigidansa yayi masa,


 Harda Muhammad dady yake cema Muhammad to  An idar dakaratu sai shirin Anje.  Iyali KO??


Muhammad Sosa keya kawai yayi yatashi yabar wurin.






Muhammad yadawo kullum sunatare da  nurayya 



Amma badasanin momy ba 


Yauma zaune suke yakecewa kanwata kishirya Gobe zakiga wadda nazabamiki, Amatsayin miji



Nurayya murmushi kawai tayi tace Allah yakaimu yayana,


Nan sukaci gabada fira Amma  motsi kadan sai Muhammad ya kalli nurayya,




 


Nurayya tafito daga Cikin dakinta Muhammad yakira ta  da wayar daya bata batare dasaniba kowa,



Tanufi ;Garden inada yace ta iskeshi yanatare.  Da wadda yazavamata,



Tayi sallama tace yayana gani Ina bakon dakace


Mohammed ya juyama nurayya baya yace ni ne nan Bakon kanwata ni nake son nakasance uban yayanki,


Har A bada


Nurayya Cikin figici tadago fuskarta tace yayana.....




I LUV MASOYANA INASONKU FIYE DA YADDA KUKE SONA LUV YOU😘😘

[1/31, 9:34 AM] Hafsat ( Hafsy Baby): 🏅🏅🏅🏅🏅

    DARE DAYA

🏅🏅🏅🏅🏅

          Na

 Hafsat (Hapsy Baby)



®P. W. F




70&75








"Nurayya tace yayana kasan Abinda kake fada Kuwa??


Muhammad yajoyo yace nasani mana nurayya 


Kobazaki soni ba??

Nurayya tace yayana kafi karfina kyau daidaini marar iyaye nifa tsintaciyyace bansan kowaye iyayena,


Kyau kaje Gidan marayu kasamo man daidai Dani 

Amma nibazan iya soyaya dakai ba.


Tajuya tagudu tashige ciki tana kuka,




_ABUJA_



wata yarinyace bazata wuce  12 years ba tashigo daki dagudu mamy kinga  Afnan ya Amshema chocolate wadda dady yayoman tsaraba,


Amma wadda Ake Kira mamy batasan tana iyiba,

Takurama wani photo na Hannu ta ido tana kuka,


Yarinya takara matsawa kusada ita tace mamy sannan tadago fuskarta tafara tsiyayar Hawaye  tace yesmeen yaushe kika shigo ne,??



Tace mamy inatayimiki magana bakiji kin kurama wannan pic din ido wacece ita tacikim photo??


Mamy tagoge fuska tace  yayarkuce Meenat wadda tabata shekaru   16 dasuka wuce tana yar shekara 2 tabata haryanzu babu labarinta,


Kiyi Addua intana Raye Allah bayyanata kinjiko

.

 Domin jikina yanabani meenat tana raye kuma takusa bayyana garemu,



Toro kofar Akayi  Da Amsa da Ameen Hibba, 



_can_ _baya_ _nakirata_ da _Saudat_ _mistake_ _dafatan_ _zaayi_ _man_ _Afuwa_





Mamy tajoyo taga mijinta tane uban yayanta ya Amsa Mata  da Ameen,


Tace Alhaji inaji  A jikina Meenat ta kusa bayyana gareni, domin Ina mafarkinta kwananan tanakuka Alhaji yace Allah yatabbatar mana da Alkairi to tace Ameen.






Abangaren nurayya kuma tana shiga ta iske babu kowa falon dagudu tashige Cikin dakinta,


Tafada bisa Gado ta fashe da kuka tace wayyo zuciyata nasan kina son Yaya Muhammad Amma yafi karfinki, kinfara sonshi tunranar dawowarshi daga England,

Amma yaya Muhammad ba Ajina bane, yana da iyenyenshi,

Tafashe dakuka  tace ya Allah kafiddaman yaya Muhammad Cikin raina,


Kadda  ciwon son yaya Muhammad yakamani kamar yadda Yakama saffeya  Akan Dr Ahmed,






Wasa wasa duk yadda Muhammad yaso su hadu da. Nurayya Abun yafaskara wayar  dayabatama ta kasheta ta Aje,


Abun yafara damun  Muhammad yarasa yadda zayayi su hadu da nurayya,



Yauma zaune yake   yayi tagumi

Kawai sai wata shawara tafado masa da sauri yatashi yashiga Cikin ya iske  momy tare da ikram da lubna Suna Kallo yace ke ikram kiraman nurayya tagyaraman dakinna


Momy batace komai jin wahala zaasa nurayya,

 

Ikram tatashi tashiga dakin nurayya tafadamata sakon Muhammad


 Nurayya tatashi tafito Muhammad yanaganin tafiyarta yabi tabaya ya isketa


Nurayya tana tura kyauren dakin wani kamshi yaziyarceta taga daki tsaf babu inda yayi kura 

Tajuya tacema ikram kodai ba gyaran daki yasaba,

Kawai tayi kicibus da Muhammad dasauri takoma ciki Cikin tsoro,


Muhammad yace kisameni A garden inbahaka Zan biyoki har dakin ki yajuya yatafi,





Nurayya tabi bayanshi suka isa  garden  Muhammad yace " nurayya meyasa kike guduna??


Nurayya batace komai  yace  kisani fa babu Wadda yafi wajen Allah sai wadda yafi tsoronshi,


Nurayya son tsakanida Allah nake miki har Cikin zuciyata, Amincewarki kawai nake bukata da dady yadawo nasanardashi nasamu Mata,



Nan Muhammad yakashe nurayya da zafafan kalamai  har ta Aminche tana sonshi,






    BAYAN WATA BIYU






Soyaya tayi nisa tsakanin Muhammad da nurayya babu Kama Hannu yaro 

Amma haryanzu momy batasan Sunayiba.




Yauma zaune suke garden inda suke haduwa suyi firar love dinsu,


Muhammad yawaigo yakalli nurayya yace Amaryata, 

Ta sunna Kai Cikin kunya,

Muhammad yace kidaina jin kunyata domin nakusa mallakarki yau dady zai dawo Zan fadamasa,






Dadadre dady ne zaune da  iyalensa Anata  fira   saiga 

Dady yace wai Ina  nurayya tunda tayiman sannu dazuwa bangataba,

Lubna kiraman ita,


Lubna Cikin kumbere kumbere  tatashi takira nurayya,


Dady yace nurayya lafiya tunda kikayiman sannu dazuwa banjikiba tace  lafiya lau  daddy yace Ina fatan babu matsala ko tace 

Eh,


Muhammad ya shigo Cikin sallama,

Nurayya tatashi zata  tafi  dady yace dawowar ki nurayya Ayi firar dake,


Nurayya tadawo Cikin kunya  tazauna,


Muhammad yace dady nasamu matar Aure fa,

Dady yace mai babban suna 

Inakasameta??


Muhammad yace nan Cikin  gidan

Wato nurayya


Zumbur hajiya saratu ta mike wa kace??

[1/31, 5:06 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): 🏅🏅🏅🏅🏅

      DARE DAYA

🏅🏅🏅🏅🏅


          Na



Hafsat ( Hapsy Baby)




80&85





® P. W. F.









Zumbur hajiya saratu tamike wakace nurayya ??


Itazatama uwar yayanka tsitatar magen wadda baasan Asalinta itace kake fatan tazama matarka?


Dady yace ya isa saratu zauna,



Momy Cikin fushi takoma tazauna tana huchi,



Dady yajuyo wajen Muhammad yace Mai babban suna  nurayya kakeso yace 

Eh dady,



Kanemi yarda tane??


Eh dady ta Aminche 

Dady yace tashi kaje zamuyi magana,


Muhammad yatashi yafita,

Dady yajuyo wajen nurayya jeki kema daki

Yakalli su   lubna yace kuma  kutashi kutafi,



Dady yace. Saratu meyasa kike wannanan maganar gaban yarinyar nan 


Don basan kowaye maihaifinta  shine kike Aibata Haba saratu kowaya taimaki wani Allah zai taimakeshifa 


Momy tayi shiru  domin bataji wannan  sai kada  kafa take,


 Tace Alhaji bazan yarda ba ya Aure ta fa yarinyar dabaasan Asalinta ba  wayasani ko shegiyace batada uba yake neman hada kanshi da ita,



Dady Cikin fushi yatashi yabata wuri domin yaga batajin maganar dayakemata,







Nurayya kuma tanashiga daki takara fashewa da kuka tace Allah kabayyana man iyayena insuna Raye,

Adainayimani gori, Rashin. Asali,


Tanawannan tunenen har bacci yadauketa tayi mafarkin wata mata tatafo gareta  tana buda Hannu taho yata nadade ina kewarki A tare Dani,

Nurayya taruga dagudu kingi kiris ta ida kaiwa ga matar nan kawai tafarka firgice tatashi,


Tace Allah kabayyana man mahaifiyata idan tana Raye,


Tayi Addu' takoma ta kwanta.



Washe Gari



Anyi break lafiya lau dady yatafi office shida Muhammad,


Momy tashigo dakin nurayya tace fito  munafuka makira,


Algunguma, nurayya tadiro daga kan Gado jin muryar momy ta iso 


 Momy tashigo har inda nurayya tajawo ta keyy!! Har waje 


Tace uban mikakayi ma dana ya likemakine??



Tahau jibgarta kamar jaka nurayya tafara Ihu,


Saiga lubna tafito itada Ikram,


Lubna tana ganin Nurayya ce Ake bugu kawai koma daki tayi 


Ikram kuma gaban momy tazo tace momy don Allah kiyi hakuri ki kyaleta,


 Momy tasaketa tana numfashi tace,


Muzuba nidake inhar kindage sai Muhammad wallahi kin gamu da wahala Kala Kala,


Har sai Kince kin hakura,


Kuma kitashi ga  wanki can kiyiman, danawa Dana su Ikram,


Banza tsintaciyar mage,

Marar Asali 

Nurayya Cikin kuka tatashi  ibe kayan wanki tanufi, waje 




Dady yadawo dadddre yatarasu baki daya yace Muhammad nabaka nurayya nanda wata daya insha Allah zaayi bikinku,


Nurayya Cikin kuka tace nidai dady banasonshi,

Yanemi wata,ya Aura,


Dady yace ke nurayya banason maganar banza nariga nasa saidai kinuman iyakata,


Nurayya tatashi tashige daki tana kuka,


Momy tamike tace wallahi bazata sabu ba bindiga Aruwa muzuba mugani fuu tashige daki,






Muhammad yanafita yakira wayar nurayya saidayayi Kira ukku bata dauka yana na Hudu tadauka.


Tayi shiru,

.


Muhammad yace nurayya,

Tayi shiru yace nurayya  pls kiman magana,


Cikin sheshekar kuka tace mezance yayana don Allah muhakura da juna tunda momy, bata so 


Yace kull nakarajin wannnan  zance,


Nurayya ruwa ko iska bazai rabani dakeba,


Nan yakashe ta zafafan kalamai itama taji babu Abinda zai rabata da Muhammad itama,






Nurayya  tanashan wuya yanda Baku zato masu karatu wajen momy da lubna da dady  da Muhammad sunfita 


Zasu Fara sata bauta, 


Su duketa Abinsu San ransu kuma momy tace tasake tasanar da dady tana shan wani duka wadda yafi wani,





Wasa wasa yau bikin ki  nurayya da Muhammad  kingi sati daya duk wani Abun da  uba zai  ma diya dady yama  nurayya,



 _ABUJA_




Alhaji sadiq ne zaune da iyalensa falo yajuyo wajen Hibba matarshi yace mata 


Kishirya jibi zamu bikinki dan Alhaji Lawal  mai Kula da company na Kaduna,


Hibba tace Allah yakaimu lafiya wallahi Alhaji kanafadin kaduna gabana yafadi yace kiyi Addu'a to






Dady ne zaune falo yana rarrraba  invitation na biki 

Hajiya saratu sai kumbure take tabi duk yadda zata Hana wannan Auren yaki yiwuwa dady yace takara magana Bakin Auren ta,


Shiyasa tayi shiru Amma badon ranta yasoba


Dady yadago yakaleeta yace Gobe 


Yallabai zaizo bikin Muhammad,


Kuma nan zasu sauka,


Momy tace Allah shi kaimu,




Washe Gari



Nurayya ce cikin kitchen sai girki domin momy tace baki zasuyi kuma manya taki Abinchi marar dadi taji duka wallahi,




Nurayya ta idar da girki tana jerawa bisa dinning,

Taji karar mota 

Momy tafita dasauri tatarbo  su 


Hajiya Hibba ce ta Iso 

Domin Alhaji yace tafara yo gaba Anjima zai tafo, 

Wani Aiki  ya tsaidashi office


Momy tataro Hajiya Hibba,

Cikin murna,


Itakuma nurayya tashiga ta hado juice,




Daidai fitowar wata Hajiya Hibba suka shigo,


Tas!!! plate Hannu nurayya yafadi domin Gabanta yayi wata muguwar faduwa....





Love you masoyana 😘😘

[2/1, 5:12 AM] Hafsat ( Hafsy Baby): 🏅🏅🏅🏅🏅

      DARE DAYA

🏅🏅🏅🏅🏅


         Na


Hafsat ( Hapsy baby)



90&95


LAST PAGE







 

Tas!!!! Plate yafadi daga Hannu nurayya domin gabanta yayi wata muguwar faduwa gani fuskar Hajiya Hibba,



Momy tace  to marar Asali halin naki zaki nuna gaban  mutane,


Tsintatar mage,


Hajiya kinga wadda  

Muhammad yalikemawa 

Zai Aura batada Asali kokadan,


Alhaji daga tsintar ta yarakitimana ita,


Har Muhammad yagani yalikemawa zai Aura,


Hajiya Hibba tajoyo wajen Nurayya 


Kawai itama gabanta yawani yanke yafadi,

Tace Meenat!!


Nurayya tace sunana nurayya ba Meenat ba,


Hajiya Hibba tamatso kusa da nurayya tace  yakikaji dakika ganin??


Nurayya tace naji wani sonki da Kaunarki dabantaba yima  wata Arayuwata jinake 


Hajiya  Hibba tajawo  Hannu nurayya 

Suka zauna tace bani labarinki nurayya

Nurayya tafara bata labarin  yadda Baffa yabata,

Taceyaceman ya tsinceni A katsina Hanyar zuwa kwado,


Dasauri HajiyaHibba tamike tace wallahi Meenat ce yata Allah Nagode maka, yau kanunaman Meenat.


Dasauri tabude jaka tazaro waya hello Alhaji yau Addu' a ta karbu naga Meenat gata kusadani


Alhaji Sadeeq yace ganinan Bisa Hanya,


Momy ko mutuwar tsaye tayi tarasa Abinda zatace ne,


Itako hajiya Hibba tarike  nurayya kam kamar zata gudu,



Bayan Alhaji Sadeeq ya iso  shida Alhaji Lawal suka shigo,


Tare da Muhammad 


Hajiya Hibba tamike Alhaji kaga Meenat yau 

Allah yagwadamana Meenat 


Allah nagode maka yau ga meenat gabana,


Alhaji Sadeeq yace Hibba samu wurin muzauna naji komai,


Nan suka rankaya suka zauna 


Yacema nurayya  tasake bada labarinta,

Nurayya tabashi kamar yadda taba Hajiya Hibba



Alhaji Sadeeq yace tabbas ki yar muce,


Nurayya domin mu da maifiyarki 

Yan Asalin Garin katsina ne


Unguwar   Gafai 


Nida mahaifiyar ki makotane 


Muntaso muna son junan mu 

Har Allah yahada Aure mu,


Shekaramu daya  Allah yabamu ke 


Mukasamu miki Meenat


Ranar da Allah yayi zaki bace kuma


Munje unguwar kwado nida maihafiyarki Gidan Abokina


Munazaune muna fira harkika fita bamu Sani  sai can maihafiyarki ta farga bakinan 


Aka fantsam nemanki 

Baagankiba 

Aka Kai cigiya Gidan radion ta television,

Amma baadaceba,


Maihafiyarki tashiga wani Hali,

Na rashinki Ana haka Nasamu Aiki Abuja muka koma,


Nan Allah yabudaman  nagida company Kasar wajen danan Cikin Garin Kaduna Alhaji Lawal shine manager,



Ashe da rabon zamu sake ganinki 


Alhaji Lawal Nagode Babu Abinda zance face,

Nagode Nagode sosai



Alhaji Lawal yace babu damuwa Dana kowane 

Ai 


Momy Kuwa  da lubna 

Jiki yayi sanyi,


Yau DARE DAYA Allah yahada nurayya da iyeyenta  


Kuma karkashin iyeyenta suke cin Abinchi,


Nan Hajiya saratu tanemi yafiyar Nurayya Akan tayafemata,duk Abinda tayimata,Nurayya murmushi kawai tayi tace tayafemusu duk Abinda sukayi Mata itada lubna,





Adaura Auren Muhammad da nurayya Anyi hidima Alhmdlh saiga hajiya saratu tana lalllaba nurayya, 

Ankai nurayya Gidan Muhammad,


Masha Allah Gida yayi kyau

Sunatasha love,



Ga Nurayya yau gaban mahaifiyar ta da maihaifin ta suna nunamata soyayya kamar ita kadaice yarsu,

Sundawo Kaduna kusada ita,




         Bayan shekara daya




Nurayya ce nahango takara kyau sosai, takarazama babbbar mace, tana shayar da diyarta kairat,

Wadda ta Haifa,


Can Muhammad yashigo. Shima yakara kyau da girma,


Khairat tanaganin maihaifinta tadinga bangala dariya,





Dadyn nurayya sunje kauyen tsanyawa, inda Nurayya tatashi,  yagina musu masallachi babba tare da rijiya,


Nurayya suka shiga Gidan Gwaggo,


Gwaggo takoma Abin tausayi kafa ta rufemata sai tsotsi take, gashi babu mai taimakonta,


Nan tanemi yafiyar Nurayya.

Nurayya tadauki gwaggo takawota Asibiti Ayanke kafar,

Ilu kuma yahaukace saboda shaye shaye,




Anyi Auren ikram da lubna domin yanzu lubna tana ganin girman Nurayya sosai

Hakama hajiya saratu Abu kadan tace Nurayya,domin yanzuma Dadyn nurayya ya mallakama Muhammad daya daga cinki company sa na kano,


              Bayan shekara biyu




Sallama ce Akayi dagudu khairat taruga tataro dadyn ta ya sabeta,


Suka shigo ciki 

Yazauna kusada Nurayya maman khairat fushin ne Ake Dani to don Allah Adaina taso kiji wata magana,


Ya rugumenta Ajinkisa yace 

Taso mushiga ciki Asamarma khairat Kane

Nan nakawo karshe dare daya




ALHAMDULLAH👏🏻👏🏻



Iluv All masoyana😘



Jinjina gareku bisa kaunar

Dakukeman masoyana Nagode😘😘ALLAH YABAR KAUNA

No comments