Breaking News

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 15

_~*BossLadiesWriters*~_



           _*KURKUKUN ƘADDARA*_



          


  _The Prisoners E15🔥💫_


    

         *Daga alÆ™alamin Boss Bature*



~Middle step~ 




Lokacin da ta É—ago daga sujjadar fuskarta jaga jaga da hawayen, Tafin Hannayenta ta É—aga sama ta soma ambaton sunan Allah tana Yi mashi kirari, Hakan Ba Æ™aramin ruÉ—ar da likitocin yai ba, shi dai Gabriel sai murmushi yake saki yana dubanta, Bayin Allah su kaÉ—ai suka san Wahalar rayuwar da suka fuskanta Dole suji daÉ—in wannan Ranar, Ta jima tana addu'a, 


   Sam takasa miÆ™ewa daga zaunan da take, Hawayen fuskarta tamkar zasu Æ™are Sai sintiri suke yi saman kuncinta


  "Angel pls stop shedding ur tears" Gabriel ne Yai mata maganar, Cikin shessheÆ™ar kuka ta É—ago ta Kalle shi da rinannun idanuwanta waÉ—anda suka kada jawur da su


  "Gabriel dole in yi kukan farin Ciki, kai ka sani irin wahalar da muka sha, munyi rayuwar kulle tamkar dabbobi har Æ™wara ni akan sauran Æ´an uwana tun suna jarirai, wannan ne karo na farko da zasu É—anÉ—ani rayuwar Æ´anci acikin Æ´an uwansu mutane, Iya cuta an cuci rayuwarsu mun tsira amma raunin dake acikin zukatanmu na har abada ne, saboda akwai abubuwan da muka rasa wanda nayi imanin baza su ta6a gogewa a tarihin rayuwarmu ba"


Hankalin likitocin ba ƙaramin tashi yai ba ganin yadda take kuka tana surutu gashi ba su fahimtar abunda take cewa, sai dai sun gane akwai abunda ke damun su wanda yai silar haifar masu da ciwon damuwa da baƙin ciki


 Gabriel da ke a tsaye tuni shima ya fara zubar da hawaye.


   Gabanta ne Ya É—an faÉ—i Jin kukan Jemimah, Nan take shessheÆ™ar kukan da ta ke yi ya dakata, Dr. Laura ce ta shigo ÆŠakin hannunta É—auke da Jemimah Tsabar jaraba ta runtse idanuwanta sun yi suntum saboda kuka, Sunan Genie kaÉ—ai Take furtawa, jikin Angel na rawa Ta yunkura ta miÆ™e da sauri ta nufi dr. laura Hannu biyu tasa ta kar6eta sosai ta rungumeta a Æ™irjinta, hannunta hada cannula da aka sanya mata.


  "Angel" Muryar Batul ce ta ratsa kunnuwanta, da sauri ta É—ago tana kallonsu, A jere su ke shigo É—akin kowan nan su Yasha kuka Idanuwa sunyi luhu luhu, doguwar suman kawu nan su A hargitse kamar waÉ—anda aka koro daga gidan mahaukata.


Kowan nan su Na sanye da light blue uniform da aka sanya masu, hannayensu sanye da cannula na drip da aka sanya masu.


  Batul ce ta farko, Bayanta Parveen ce da hannah, Sai mazan Javed da Naufal, da gudum gaske suka Æ™arasa shiga É—akin gaba É—aya suka Æ™anÆ™ame Angel kamar zasu kada ita Æ™asa.


Al'ajabi Ya hana Likitocin cewa komai, Sun saki baki galala suna kallon Ikon Allah, Aransu suna Mamakin ƙaunar da suke yi ma ƙaramar Yarinyar da su ke kira da Suna Angel.


  Farin Ciki kamar zai kasheta, DaÉ—i take ji tarasa ina zata tsoma ranta, Sun lullu6eta suna yi mata kuka, ko numfashi daÆ™yar take Iya fitarwa


  "Angel ina ne nan? Wanene Ya kawo mu? Wlh tsoro muke ji, munga wasu mutane da bamu saba gani ba, kada su cutar damu Angel, sai kallon mu suke yi kamar zasu lashe mu" Su parveen ne ke kora mata jawabi

  "Ko dai mafarki muke Yi ne? Mu dake acikin Daji Ya akai muka tsinci kanmu a wannan wurin tare da wasu mutane masu fararen Kaya, Angel ko dai Aljannace da kike bamu labari? Idan mun mutu zamu shiga" Maganar Batul tayi matuÆ™ar bata dariya, DaÆ™yar ta samu suka saketa, Ga jemimah ta Æ™anÆ™ameta Jikinta sai kerma Yake yi.


  Azeeza tana maÆ™ale da Gabriel Sarkin tsoro, Ta kasa É—auke idanuwanta daga kan faces É—in Likitocin dake a tsaitsaye cirko cirko suna kallonsu.


  "Angel mun shiga ku, Sai kallon mu suke yi," Hanna ce ta yi maganar

  Muryar dr. Laura ce ta katse masu Hanzarinsu cikin harshen turanci ta ke yin maganar 


"Ku kwantar da hankalinku, babu wanda zai cutar daku, Anan inda kuke Asibiti ne, mu kuma da kuke gani likitoci ne da nurses haƙƙinmu ne kula da Lafiyarku, Za mu taimaka maku don ganin kun warware daga lalurar dake damunku, Muna so ku ɗauke mu tamkar Ƴan uwanku, idan ku ka yi hakan munyi maku alƙawarin zamu share maku hawayenku, Zamu gatanta ku mu baku kyakkyawan kulawa har izuwa lokacin da zamu miƙa ku ga Iyayen ku.


 Tun da tafara Yi masu magana kowannansu Ya natsu yana sauraronta, da alama sun fara fahimtarta


  Matsowa Kusa Dr Brown Yai daga gefenta Ya tsaya"duk wani abu da kuke buÆ™ata zamu yi maku shi, ku É—auka tamkar kuna a gidan Iyayenku ne, burin mu shine ku bamu haÉ—in kai, Ku daina Jin tsoron mu"

    Muryar Dr Jack Ce Ta janyo hankulansu ga dubanshi

  "Mun haÉ—a ku wuri É—aya ne saboda mun fahimci ba za ku ta6a sakewa damu ba, idan har ba Kuna atare da Ƴar uwarku Angel ba, Muna fata Yanzu hankalinku zai kwanta, ga ku ga Mamanku Angel" Da zolaya yayi masu maganar, murmushi Angel ta saki tana kallonsu, daga gani suna da mutunci.


  "Masoyiya Angel faÉ—a min me ki ke yi wa Yaran nan naki ne? Don na lura ba Æ™aramin Æ™aunar ki su ke Yi ba" Dr Brown ne yai magana haÉ—i da É—aga mata gira É—aya, Sunnar da kanta Æ™asa Tayi dariya takeso tayi sai da takasa.


  "Yaushe kika haife su ne? Sannan Ina Mijin naki"? Kunyace ta rufe Angel da sauri ta É—aura Kanta saman sumar kan Jemimah dake ruÆ™e a hannunta.


    Dariya Dr. laura ta saki"Wow Kunya take ji, To ko dai Matashin saurayin nan mai bacci ne mijinki? Wannan kyakkyawan don naji kamar kina ambaton sunanshi" gaba É—aya sun sanyata jin Kunya ji take kamar ta nutse ga farin Ciki da ya lullu6eta.


  Da biyu likitocin suke zolayarta, Yana daga cikin aikinsu kwantar da hankalin Mara lafiya musamman su da suke son su saki jiki da su, Ta hakanne zasu samu bayanan da suke so daga gareta.


  "Mun fahimci Masoyiya Angel bakinta ya mutu, saboda An sosa mata inda ke yi mata Æ™aiÆ™ayi, Yanzu faÉ—a min me kikeson Ci ke da Ƴan uwan naki mu kawo maku" Cikin kulawa Dr. laura ke yi mata magana.


  Kallon sauran Ƴan uwan nata tayi


"Ko ba ku jin yunwa ne"? Shiru suka yi ba wanda Ya bata amsa, idonsu akan Angel, Dariya doctors É—in suka saki

  "Oh Baku Iya magana sai da izninta, to ke masoyiya Angel FaÉ—a mana me kikeso akawo maki keda Ƴa'Æ´an naki don bama son barinku da Yunwa"


  Cikin Jin kunyarsu Angel ta furta"komai muka samu zamu ci" Jinjina kai Dr Laura Tayi kafin ta juya ta kalli Sister rebecca"A shirya masu lafiyayyan abinci da Kayan sha" amsa mata Tayi da toh da sauri ta juya ta fuce.


  Dawo da dubanta tayi akan fuskokinsu

  "Yanzu zamu tafi mu baku wuri Pls Idan an kawo maku abincin Ku tabbatar Kun cinye min shi duka kaf, zanji daÉ—in hakan,' dr Laura davis Na rufe Maki Dr Mark Yace"Zamu dawo Da Anjima, Kyawawan Æ´an mata, dole in za6i É—aya daga cikin ku, irin wannan Kyau haka" 

  Dr Bown Yace"ai ba kai kaÉ—ai ba mutumina, Ni ruwan ido ma ya hanani zabar É—aya, ta ko'ina Kyau nake gani musamman Masoyiya Angel ta tafi da ni" Dariya ce ta kubcewa Angel da Gabriel

  Harara Dr Laura davis Ta watsa mashi"bazaiyiwu ba, Duk na riga ku, Nima nayiwa Æ´a'Æ´ana kamun matan aure a Cikin su' NishaÉ—i sosai suka sanya su.

  "Zamu tafi Masoyiya Angel, Amma kafin nan Ki kula mana da Æ´a'Æ´anki, Ki lallashesu su daina mana kuka dake kanki bama so kuna zubda tsadaddun hawayenku" Cikin sanyin murya Angel ta amsa mata da toh, Sallama suka Yi masu atare suka fuce daga É—akin suna masu santin Kyawun Yaran acikin ransu.

  Fitarsu keda Wuya Ange Ta fada saman Gadon rungume da jamimah tana tiÆ™ar dariyar Farin Ciki tana faÉ—in"ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN" 


   "Kuyi Farin Ciki mana, Ina Tayamu murna Mun ku6uta daga Kurkukun Æ™addara, Mun zama masu Æ´anci" Su Batul sunÆ™i sakin jiki har yanzu basu fahimci Ta ya ya akai suka tsinci kansu a wannan wurin ba.

  Gabriel ne yai Æ™oÆ™arin fahimtar da su abunda Ya faru zuwan Sojoji Dajin.

 Wayyo Allah daÉ—i Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskokinsu, Bakunansu sun kasa rufuwa Fararen haÆ™oransu tamkar Gonar auduga

  "Gabriel kana nufin Yanzu mun bar kurkuku da daji? Muna acikin Mutanan duniya" Fuskar Gabriel da murmushi Ya amsa masu"Æ™warai kuwa, Babu ku babu zubar da hawaye baÆ™in ciki da kunci sun Æ™are" Tsabar Farin Ciki Suna kuka suna dariya, gaba É—aya suka Haye saman Gadon Angel, suka kwanta a jere da ita sai daÉ—i suke ji saman ceilling É—in É—akin suka Æ™urawa ido kowa Yana tariyo abubuwan da suka faru a rayuwarshi jin shessheÆ™ar kukansu ta cika É—akinne Yasa ta soma yi masu magana cikin lallashi

  "Dan Allah ku daina, Yanzu lokacin farin ciki ne, Godiya yakamata Muyiwa Allah, a koda yaushe shi mahaÆ™urci mawadaci ne, yau gashi dai mun shaida hakan Allah ya kar6i kokenmu yaji Æ™anmu ya raba  mu da Æ™angin rayuwar da muke aciki, A yau mu masu Æ´an ci ne zamu shaÆ™i Iskar duniya son ranmu batare da wani yayi mana Iyaka da ita ba" Murmushine Ya bayyana akan fuskokinsu 

  Cikin shessheÆ™ar Kuka Azeeza ta soma magana tana fadin"Ni Æ´an uwanmu nake tunanawo waÉ—anda muka rasa acikinmu, tare da Salsabeel da ya taimaki rayuwar mu, nasan dole su kashe shi idan suka kama shi Yana acan kurkuku Suna azabtar dashi"



  Naufal ya É—aura da cewa"babu Deeja! Babu Mubeen Akan idonmu ya yanke jiki Ya faÉ—i, a lokacin muna aga6ar barin kurkuku....." Kasa Æ™arasa maganar Yayi saboda kukan da ya ciyo shi.


  Javed ya dasa daga Inda ya tsaya"Mun rasa tsohuwa tamira! Mun rasa Eve da Yasmin sannan mun rasa Hibba da Rubina, da Sarah! " tunkan Ya rufe Baki Angel ta É—aura da cewa"Allah Sarki Unaiza Ƴar gidan daddy, da Majnoon Bayin Allah ban ta6a tunanin zamu tsira ba tare dasu, Muna Æ™aunar Æ´an uwanmu sosai, Sai dai mutuwa tayi mana Yankan Æ™auna, Ta raba mu da su, In sha Allah zamu haÉ—u da su agidan Aljanna inda babu kurkukun Æ™addara babu duk wani mugu, Allah sarki tsohuwa tamira da Salsabeel waÉ—annan bayin Allahn Har duniya ta naÉ—e bazamu ta6a mantawa dasu ba, saboda Sun kafa tarihi acikin zukatanmu In sha Allah a koda yaushe zamu dinga binsu da addu'a, sannan zamu Cika masu burin su na ruguza tarihin KURUKUKUN ƘADDARA. 




Abubuwa da dama suke tariyowa na rayuwarsu na baƙin Ciki da farin Ciki

 "Angel Danish fa har yanzu bai farfaÉ—o ba, Haris kuma Bashi da Æ™oshin lafiya nurse ta faÉ—a min abunda ke damun shi ni nasan silar deeja ne, Amma tace Ciwon nashi bazai jima ba, Zaiji sauki"

  Jin wannan maganar yasa gabanta faÉ—uwa, A hanzarce ta miÆ™e zaune saman mattress É—in, su Batul ma suka mimmiÆ™e suna kallonta, sun sha kuka fuskokinsu sunyi jawur dasu abunka ga farare, Ita dai Jemimah tunda ta lafe ma angel hankalinta kwance bata da sauran damuwa.


   Æ˜asa Æ™asa da murya ta ambaci kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Gabriel Akwai matsala! Wai ni wace Æ™asa ce wannan"? A matuÆ™ar ruÉ—e ta jefa mashi Tambayar, duk budurin da akeyi bata lura da fararen fata bane sai da yayi mata zancen Danish.


  "Ni kaina Angel bansani ba" Dafe kai tayi da hannu É—aya, Yayin da take bin ko'ina na room É—in da kallo, karaf idonta ya sauka akan wani hoto dake manne jikin bango, a jikin shi an rubuta


  SAN ANTONIO TEXAS United states of America


 zazzare idanuwanta waje tayi wuÆ™i wuÆ™i Muryarta Na kakarwa ta soma maimaita Sunan America, tun da take arayuwarta bata ta6a taka kafadarta a Æ™asar waje ba, Iya Nigeria ne, Yau Æ™addara Ta jefo su America a maimakon Nigeria! Hankalinta idan yai dubu toh ya tashi, ta ya ya zasu Koma Nigeria har su samu damar É—auko ruwan zamzam da zasu ba Danish? Don tana Ji aranta Baccin da yake yi bana lafiya bane zaiyi wuya ya farka batare da giant's heart É—insa ta motsa ba, Muryoyinsu AruÉ—e su ke ambaci sunanta"Angel menene? Bamu tsira ba ko? Wani abu zai faru damu"? Girgiza masu kai tayi muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Wlh ba Nigeria bace wannan ba Æ™asa ta bace, America ce Æ™asar turawa, taya akai haka ta faru!?  Nauyayyar ajiyar zuciya suka sauke, don su basu san abunda take gujemawa ba, Lamarin ya girgizata har tafara tunanin dama kurkukun Æ™addarar ba A nigeria ya ke ba? Akwai gagarumar matsala dole su nemi mafita.


  "Angel ae zamu Iya zuwa can ko"? Da sauri Gabriel ya amsa masu da cewa"Eh mana ba wani abu, kada ku damu kanku, Sojoji sunce idan muka basu haÉ—in kai zasu damÆ™a mu wurin Iyayenmu, Idan suka tambayemu sai mu faÉ—a masu cewa Mu Æ´an nigeria ne"


  Kafin wani Ya Æ™ara magana acikinsu, Nurse rebecca Ta turo Æ™ofar É—akin Hannunta ruÆ™e da faffaÉ—an tray na kayan abinci da aka jera masu, A saman table ta É—aura masu, kafin ta É—ago tana dubansu fuskarta É—auke da murmushi tace"Idan kuna buÆ™atar wani abu zaku Iya kira awaya ku sanar dani" Ta yi maganar tana nuna masu wayar dake ajiye saman table, al'ajabi ne ya kama su wai yau sune ake tarairaya? har tambayarsu ake yi in suna buÆ™atar wani abu? Wannan wani irin abun farin ciki ne!


 Har ta juya zata fuce, Muryar Angel ta dakatar da ita "Sister, which country are we in?" ? ta tambaye ta ne don ta Æ™ara tabbatarwa

  Juyowa Nurse rebecce tayi fuskarta da fara'a ta furta"San antonio texas" idanuwan angel luhu luhu ta ce"Thank u" 

  Hankalin Angel YaÆ™i kwanciya, sam bata lura Sun fara Cin abincin ba, gaba É—ayansu sun dawo bakin gadon, Su  parveen banza ta samu, soyayyar kaza mai maiÆ™o ta damÆ™a tana turawa abaki atsiyace take cizgar Naman kazar, Jemimah ta sungumi tsiran nama ita da azeeza, Batul kuwa Soyayyan Æ™wai ta É—auka tana Ci har wani nannaÉ—e shi take yi kafin ta tura abaki, Hannah ko warmer ta É—auka shaÆ™e da Chips tana ci, Ba baka sai kunne, Su naufal an dahi Chicken shawarma, Javed ko Kayan marmari ya damÆ™a yana sha, kamar kwancen Yunwa Sun zaÆ™e suna ci suna Korawa da lemu me sanyi kala kala aka kawo masu, basu san akwai cctv ba a É—akin, Duk wani motsinsu ana kallonsu😂 

  Ita kanta Angel data dubesu saida gabanta ya faÉ—i, Ganin yadda suke cunkusa abinci abakunansu Kamar kuraye, Muryarta na rawa take faÉ—in'pls ku bi a hankali kada ku shaÆ™e" tamkar kurame babu wanda ya dubeta bama su san akan me take magana ba, a dole ta Æ™yalesu ta zura hannu ta É—auki burger tana ci...........

  

*BARI MU LEƘA GIDA NIGERIA*


*A DAULAR OBIE ESTATE*


A Zaune take dirshan acikin Katafaren Bedroom ɗin Obinna, wa'iya zubilla kai kace ɗakin matashin saurayine saboda tsabar haɗuwarshi, An kashe dukiya a furniture ɗin ɗakin komai na cikinsa launin Red and golden ne, Ko sarki Albarka, Tanƙamemen gadonsa Royal state bed irin gadon da ko mutun baijin bacci ya hau sai Ya runtsa, Ga wasu matassan kai launin red da golden jere a gaban headboard ɗin, Dogayen labulaye ne a kewaye da ɗakin, ga wasu bedside drawers masu ɗauke da lamp, daga saman ceilling ɗin ɗakin Haɗaɗɗen Chandeliar ne dake bada hasken ɗakin ga wata zungureriyar Sofa Bayan ita akwai arm chairs masu ɗan banzan kyau, Ga wani ƙayataccen table dake ɗauke da Kayan Ado na ɗaki. Daga jikin bangon ɗakin haɗaɗɗiyar wallpaper ce mai zanan flowers masu matuƙar ƙayatarwa da jan hakalin me kallonsu, floor ɗin ɗakin tamkar mirrored tiles ne Kana Iya ganin fuskarka a cikinsa tamkar madubi, ga wani Jigunannan Dressing mirror Tafkekan gaske Jerin tsadaddun turarurrukane ne asaman shi da sauran kayan gyaran jiki, idan nace zan cigaba da zayyana haɗuwar Ɗakin dattijon arziki tabbas zamu ƙare takun tsakiya wurin fasalta Kyawunshi.


Yana daga kishingiÉ—e saman lallausar mattress É—in gadon, Apple laptop ce agaban shi, Da alama Video call Ya ke yi da wani, É—abi'arsa ce yana magana yana shafa gemun shi wani sa'in har Jan shi ya ke yi.


 Hajiya saratu tayi zaman cin tuwo saman lallausan carpet É—in gaban gadon shi, tana jiran Ya kammala Yin wayar, ta tsare shi da ido babu annuri akan fuskarta, Hankalin shi gaba É—aya yana akan fuskarta, Nazarin yanayinta ya ke yi, kamar daga sama ta tsinkayi muryar shi akanta

  "Saratu kin wuni lafiya"? Ƙara tamke fuskarta tayi"lafiyalou baba, fatan na same ku lafiya" murmushin gefen fuska ya sakar mata"Alhamdulillah, in ce ko lafiya? Naga yanayin fuskarki da 6acin rai, Waye ya ta6amin autata ne yanzu in É—aura É—amarar yin yaÆ™i da shi" murmushin YaÆ™e ta Æ™aÆ™alo, har ta buÉ—e baki zatayi magana yai saurin tarar numfashinta"nasan kinzo gaishe da baban nakine kamar yadda kika saba, Naji daÉ—i sosai mamana, Bari na kira hajjaty A waya ta kawo mana dinner mu ci atare ni da autana" tur6une fuska Hajiya saratu tayi"ba yunwa nake ji ba, Zuwa nayi mu yi magana, kafin barina É—aki sai da nayi magana da masu aiki  nasan sun kai min a É—akina"

  "Ai nasan ba yunwa kike ji ba, Ni nake ra'ayin cin abinci tare da ke, idan mun kammala sai mu yi magana" aruÉ—e take kallonshi, Æ™iri Æ™iri Ya hana tayi magana.

  Ba tare da ya jira amsarta ba, Ya É—auki waya dake saman bedside drawer, Ya kira landline na kitchen, bugu uku aka É—aga kiran, muryar sophia ce ta ratsa kunnansa cikin girmamawa ta gaishe da shi.


  "Ina buÆ™atar Dinner É—ina a shigo min da shi É—aki yanzu" amsa mashi tayi da toh kafin yai rejecting call É—in, idanuwanshi akan saratu da ta haÉ—e rai, kasa jurewa tayi don baÆ™aramin takura tayi ba hakan yasa ta soma magana ba tare da ta jiran umarninsa ba.


 "Baba ni gaskiya ba a kyautamin agidan nan, akan me za'a dinga kushe min Æ´a'Æ´ana ana yabon na wasu, abun yana Æ™ona min rai bana jin daÉ—i, haba dan Allah wannan ba adalci bane, kuma ba girman Yaya Lateef bane da yaya mubarak su zauna suna faÉ—an maganganun marasa daÉ—i akan Æ´a'Æ´ana, ni kaÉ—ai ke ba'ason ya'ya na a family din nan ko dan saboda ban auri jinsin mu bane" Rai a6ace take yin maganar, tun da ta fara magana bai dakatar da ita ba, ya natsu yana sauraronta idonshi akan fuskarta, dama tun kafin ta fara yin maganar yasan meya kawo ta, Yana mamakin Halin saratu, ko irin alkunyar nan babu, idonta ya rufe akan Æ´a'Æ´a da miji, abu É—ayane take jin nauyin yi wato idan tana zazzaga masifa bata bari su haÉ—a ido dashi, murmushine akan tausasan la66ansa

  "Kin gama maganar ko akwai saura" bata É—ago ta kalle shi ba idonta na akan carpet É—in da take a zaune dirshan

 "Hateem FaÉ—a min menene sunan macan da take É—aukar zigar miji"? ras taji gabanta yai mugun faÉ—uwa, A ruÉ—e ta É—ago da ido tana kallon fuskar obinna, Æ™ayataccen murmushine akan fuskarshi, Ji take tamkar ta yunÆ™ura ta miÆ™e ta zuba da gudu don ta fahimci Video call yake yi da Yayanta hateem na Æ™asar Canada, Hakan na nufin duk wata magana da ta ke faÉ—ama babansu akan kunnanshi, Hankalinta ya tashi don ba Æ™aramin jin shakkar shi ta ke Yi ba, duk acikin yayunta tafi fargabar sharafudden da hateem.


 A hankali Obie Ya juya mata Lapton É—in gabanshi don suyi magana da Yayanta, sunnar dakai Æ™asa tayi sam ta kasa É—agowa ta kalli screen É—in laptop nasa

 DaddaÉ—ar muryar prime minister Hateem ce ta ratsa kunnuwanta

 "Ji ra kike in gaishe ki"? Girgiza kai tayi tamkar tana agabanshi, cikin girmamawa ta soma gaishe da shi

"Ina wuni Yayana, Ya aiki Ya iyali"

 "Ki É—ago da ido ki kalle ni Saratu"! Da kakkausar Murya ya furta hakan, Yawu ta haÉ—iya kafin A hankali kamar maijin tsoro ta saci kallon screen É—in.


Tabarakallahu ahsanun khalikin!! Ni kaina da nake rubutawa sai da alƙalamina ya girgiza da ganin Kyakkyawar surar nan mai cikar kamala, gwarzon namiji jajirtacce, kallon ɗaya zaka Yiwa fuskarshi ka shaida Jinin Obinna ne, Yana ɗaya daga Cikin waɗanda su ke kama da babansu, basu baro komai nashi ba, Kyanshi, ɗabi'unsa da halayansa, Fatarshi kaɗai abun kallo ce, yadda kasan da ruwan madara ake mulketa saboda tsabar kyau, skin colour ɗinshi launin na mahafinshi ne, A zaune yake Cikin Katafaren Office ɗinsa dake a Presidential residence Na ƙasar Canada, tsayawa zayyana kyawun Office ɗin da dukiyar da aka kashe masa wurin zuba kayan cikinsa abune da hankali ba zai ɗauka ba, wata'ƙil zamu ƙare Takun tsakiyane wurin zayyana shi, wasu hadaddun tailored suit ne a jikinsa sunbi shape ɗin jikinsa, mutumin akwai ƙira.


  "Bai kamata kiji kunyar haÉ—a ido dani ba Saratu, tunda har kika iya tako Æ™afafuwanki kika zo É—akin baba don kiyi mashi masifa, Ke ko kunya bakya ji? Ki zauna Miji Yana ziga ki Kan Æ´an uwanki? Sara Ba haka nasanki ba, Ni ba haka Æ™anwata take ba, jarumar macace mai hankali da tunani, why kike son bani Kunya"? Maganar Hateem tayi matuÆ™ar sanyata jin kunya, duk sai ta ji haushin kanta ya kamata, tayi danasanin zuwa É—akin obinna, saboda tana matuÆ™ar jin nauyin Hateem, da ace tasan da shi suke yin video call da batayi gigin zuwa kawo Æ™orafi ba.

  "Kiyiwa kanki faÉ—a saratu, Ba girmanki bane, Ƴa'Æ´anki ai namu ne, babu wani banbanci, nasan abunda Yaya mubarak da Yaya lafeef zasu faÉ—i bazai wuci akan Cigaban Ƴa'Æ´anki bane, maisonka shike faÉ—a maka gaskiya duk min É—acin ta, MaÆ™iyinka kuwa sai dai Ya 6oye maka yakamata Kiyi tunani Æ™anwata" Cikin kwantar da murya yake yi mata nasiha, shi kanshi Obinna har lumshe ido yake yi saboda jin daÉ—in nasihar da Hateem Yake yiwa Æ™anwarshi, kuma ga dukkan alamu jikinta yayi sanyi sosai

  Muryarta tamkar zata fashe da kuka ta soma magana"In sha Allah yaya zan kiyaye, bazan Æ™ara biye mashi ba, zuciya ce ta É—ibe ni, Ni kaina nasani kuna son Æ´a'Æ´ana shiyasa kuke yi masu faÉ—a don su gyara, duk wanda ya rasa faÉ—i a duniya yai asara, ina jin daÉ—in Æ™oÆ™arinku akaina da Æ´a'Æ´ana, Allah ne kaÉ—ai zai Iya biyanku" idanuwanta har sun cicciko da Æ™walla

    "Kada ki bari hawayen nan su zuba, Kinsan banaso ko"? ÆŠaga mashi kai tayi alamar eh"Okey yi min murmushin nan naki in gani" Dariyace ta kubce mata, da sauri ta É—aura kanta saman manyan laps É—inta

  "Ya aikin naki? Fatan komai na tafiya lafiya" amsa mashi tayi da"lafiyalou"


 Jinjina kai Hateem yai"Allah ya taimaka" sallama sukayi da ita Obie Ya juya laptop É—in, idon shi akan Hateem

  "Shiyasa nake Ƙaunarku, Saboda ku É—in na dabanne, Æ´a'Æ´ana abun alfaharina, Allah Yabar munku, ubangiji Allah ya tsare mun ku Ya kare munku daga sharrin maÆ™iya da mahassada......"addu'o'i obinna yadinga jero mashi, Yana masa mashi da ameen ameen hada saratu wurin amsawa daga bisani Suka yi sallama dashi

 Rufe laptop É—in yai tare da miÆ™e ma saratu, YunÆ™urawa tayi tare da matsawa gaban gadon ta kar6i laptop É—in ta nufi saman desk É—inta ta É—aurata.


  "Assalamu akaikum" muryar Hajjaty ce ta ratsa kunnuwan su, atare suka amsa mata da wa'alaikum salam shigo daga Ciki, Tura Æ™ofar tayi kamar kullum fararen Kayane a jikinta, Tasha uban ado kamar amarya, sam bata gaji da ca6a ado, Hannayenta  sun sha Æ™unshi na jan lalle.

  Hajiya saratu dake a tsaye tana kallonta, Haushin Matar take ji, ta tsani taga Æ´ar aiki tana É—aukar wanka kamar yar masu gida, zuciya da saÆ™e saÆ™e, sai ta dinga ganin kamar obinna bin jikinta yake yi da kallo, fargabanta kada wata rana dattijonsu ya Æ™yasa, Ƙarasawa Hajjaty tayi cikin É—akin Asaman Carpet ta É—aura tray É—in, sai faman sakar mashi murmushi take yi shima É—in mayar mata da martanin murmushin yake yi, Hankalin Hajiya saratu yaÆ™i kwanciya Tana a tsaye ta ruke qugunta

  "Yalla6ai fatan ka wuni lafiya, tun É—azu nake jiran shigowarka gidan bansan kun dawo daga masallaci ba, ae da tuni na jima da kawo maka abinci" Yanayin yadda take magana muryarta tamkar ana busa sarewa, Æ™amshin turarenta Ya addabi hancin hajiya saratu

  Lumshe ido yai kafin ya amsa mata da"lafiyalou Alhamdulillah, nagode da kulawarki agareni, Kina ji da dattijon nan naki sosai nima na yaba da hakan"


   Fuskar Hajiya saratu a É—aure ta furta"ke! Tashi kibar É—akin nan tunda kin kawo mashi abincin,ya gode sai anjima" miÆ™ewa Hajjaty tayi tare da jiyawa ta kalleta"Ina wuni hajiya"

  "Da ban wuni ba kin ganni, Ƴar rainin wayau sai yanzu kikasan dani aÉ—akin, dallah ni zo ki fuce waje" jikin Hajjaty yai sanyi duk sai ta ji ba daÉ—i


 "Inaso zan zuba mashi abincin...." tunkan ta Æ™arasa Hajiya saratu ta daka mata tsawa"Nace ki fita ko"? Matsawa tayi tare da fusgo hannun Hajjaty taja ta waje, Obinna dake a kishingiÉ—e saman gadon Æ™ayataccen murmushine akan fuskarshi, lamarin saratu sai addu'a ya fahimci kishin mahaifin nata takeyi.


  Bayan fitarsu daga É—akin, a bakin Æ™ofar suka tsaya da tafiya, Hajiya saratu na faman ciccije le6e ta furta"Ni ban yadda dake ba, akan me zaki dinga zuwa É—akin Ubanmu, balallaga dake Ina laifin Ki turo matasan Æ´an matan masu aikin su dinga yi mashi hidima"? Idanuwan hajjaty tuni sun cicciko tab da Æ™walla, ta tsani faÉ—an hajiya saratu, a shekaru kusan tsaran junane amma ta tasata gaba tanayi mata faÉ—a kamar wata Æ™anwarta

  "Ai shine ya za6eni bani nake kawo kaina ba, Yafi so ina yi mashi hidima, kuma ki tambaye shi zai fada maki hakan" Harara Hajiya saratu ta watsa mata"ae dole ya za6e ki, tun da kin riga kin asirce shi da wannan munafukin turaren naki, mace sai kace karuwa, Kin bi jiki duk kin feshe da turare Bakisan haramin bane mace ta fesa turare mai Æ™arfi ba? Ina laifin wanda zaki É—an matsa a hammata!" yawu hajjaty ta haÉ—iya batare da tace mata komai ba

  "Idiot, daga yau karki kuskura In Æ™ara ganin Kin a É—aki babanmu, tun fil azal ni baki kwanta min araina ba, Ina raga maki ne saboda mijina ba dan haka ba wlh da tuni na jima da korarki can Æ™auyanku  na can india,  A tsawace takai Æ™arshen maganar tare da ingiza hajjaty, tai taga taga zata faÉ—i daÆ™yar ta samu ta dafe bango, dogon tsoki Hajiya saratu ta buga kafin Ta juya ta koma É—akin obinna. 


   Jiki asanyaye hajjaty ke tafiya yayin da hawaye ke bin fuskarta, Da mayafin hannunta take share Æ™wallar dake sintiri saman kuncinta, Kalaman Hajiya saratu sun Æ™ona mata rai.


Tun fitar Hajiya saratu daga ɗakinta, Pravin Yana zaune gefen gadon shi, Shi da Tagwayensa zayn da zayn, suna zaune saman sofa, ransu ya 6aci matuƙa babu annuri akan fuskokinsu


  "Yanzu me kuke so ayi"! ya jefa masu tambaya yana mai kallon fuskokinsu

  "Ka sama mana hanyar da zamu bar Æ™asar nan, saboda mun gaji da zaman gidan nan, a takure muke kowa baya son mu kusan kullum ne sai anyi mana Gori" murmushin gefen fuska Pravin ya É—an saki Yana duban ya'yan nashi cikin so da Æ™auna

  "Kun bani Kunya wlh, Why maganar mutane zata dame ku? Har wani ya isa yasa kubar Danginku? Kenan wata rana zaku Iya kashe kanku saboda wani ya 6ata maku rai eye"! É—aure mashi fuska suka yi don sun fahimci uban nasu babu zuciya a Æ™irjinsa, shiyasa bai ganin illar abunda ake yi masu, yafi so su zama masu matattar zuciya irin shi

  "Daddy pls, ka fahimce mu, bama jin daÉ—in zama gidan nan, america muke son komawa da zama" girgiza kai pravin yai"bazaiyiwu ba, ai baku keda kanku ba, Nima ina buÆ™atar ku atare dani, Ku faÉ—i wani abun na daban da kuke so zan iya yi maku shi" magiya suka dinga yi mashi akan ya amince masu su koma america, 

  "Daddy bafa da kuÉ—inka xaka É—auki É—awainiyarmu ba, munsan komai kakeso mommy zata yi maka taimakonmu kawai zakayi mu samu ta amince mana" 

  ÆŠaure fuskarshi yai"saboda ni bani da arziÆ™in da zan Iya É—aukar nauyinku"? Girgiza kai sukayi atare

  Ta6e la66ansa yai"bansan me kuka É—auke ni ba, Ita kanta mahaifiyar taku A yanzu bata kama Æ™afata wurin arziÆ™i ba," kallon Juna su ka yi da mamaki akan fuskokinsu

  MiÆ™ewa yai daga gefen gadon Ya nufi gaban drawer chest, Ya buÉ—e ya zaro atm card, dawowa yai ya zauna yana fuskantarsu

  "Banyi maku Iyaka da kuÉ—in dake acikin acct bank É—ina ba, don nasan har abada bazaku Iya Æ™arar da su ba, a duk lokacin da kukeso zaku Iya cirar kuÉ—i ku biya buÆ™atunku, sannan kuje Æ™asar da kuke so, Farin Cikinku shine nawa"

  Kallon da suke yi mashi kamar basu yarda da maganarshi ba, saboda sun raina arziÆ™insa,

  Still murmushine akan fuskarshi yace"baku yadda da mahaifinku ba ko"? Shiru basu tanka mashi ba, Aransu suna ayyana may be babu ko sisi a atm É—in, idan ma akwai kudi to Na mommynsu ne tunda ita ke da kuÉ—i.


  MiÆ™a hannu pravin yai tare da ruÆ™o wayarshi dake a gefenshi, kamar sakarkaru haka suka tsare shi da ido suna kallon shi, Daddana wayar yayi kafin Ya miÆ™a masu da sauri Zayn ya kar6i wayar Suka haÉ—a ido suna kallon screen É—in wayar, Total balance ne na kudin dake a acct bank dinsa, tsabar firgita har saida suka É—an zabura ganin millions of dollars, wanda a kuÉ—in nigeria Billions ne.

   AruÉ—e suka haÉ—a baki wurin furta"Daddy Numbobi ne waÉ—annan ko kuwa kuÉ—in ne dagaske" dariya ya sakar masu

  "Abunda idanuwanku suka nuna maku, Just ku É—auki atm É—in zan tura maku pin É—insa ta text message," lamarin yai mugun É—aure masu kai,

  Girgiza kai Zayn yai"a'a daddy kuÉ—in sunyi mana yawa, ni tsorona ma kada ace Na mommy ne" MiÆ™a mashi wayar yai

  "Idan har kuka bari na kar6i atm É—in nan kada ku ta6a tsammanin zan taimaka maku!" Kallon Juna sukayi zuciya na azalzalarsu akan su kar6i atm din suyi sharholiyarsu

  "Zayn mu kar6a ko"? Girgiza kai zayn yai"A'a zaid kuÉ—in mommyne fa, idan muka ta6a zata gane ni dai ban goyi bayan hakan ba" 

  "Pls zayn tun da daddy ne ya bamu just mu kar6a kawai"

  "No zaid, kuÉ—in sunyi yawa zasu sa mu shagala mu daina yin sallah ne" Pravin dake kallonsu ba Æ™aramin dariya suka bashi ba.

  "Har yanzu akwai Æ™uruciya atattare daku, kuÉ—in kuke gudu? Ai nayi tunanin idan na baku jiki na rawa zaku kar6a, ban ta6a tunanin kuna da zuciyar Imani akan kuÉ—i ba, Sam baku da haÉ—ama, Ga dama ta samu amma kuna Æ™oÆ™arin yin watsi da ita"! 

  Muryar zayn na rawa ya furta"Daddy zamuyi shawara tsakaninmu, ka ajiye mana atm É—in zamu kar6a" jiki na rawa ya ruÆ™o hannun Zaid suka fuce daga É—akin.

  Ajiyar zuciya ya sauke tare da miÆ™ewa Ya maida atm É—in inda ya É—aukosa, komawa yai gefen gadon ya zauna yana cin abincin Da abla ta kawoma Hajiya saratu


*Dr.Jazz*


  Tun zuwa shi gidan Mommynsa ta ke ta faman tarairayarsa tamkar Æ™aramin yaro, Yana daga kishingiÉ—ine saman doguwar sofa ya É—aura kanshi saman laps É—insa, Sai zuba mata shagwa6a yake yi, yatsun Hannayenta na acikin sumar kanshi Tana yi mashi susa

  Mahaifiyar Dr.Jazz Baturiyar Æ™asar England ce, sunanta na asali Harriet, Silar zuwanta aikatau gidan ta musulunta suka canza mata suna zuwa khadija amma sunfi kiranta da Turai, Farace jawur tana da jiki bata da tsayi launin idonta green ne, sumar kanta launin blonde, A yanzu ba matsayin mai aiki take ba, Matace awurin Sir mubarak, Ya daÉ—e da auranta tun Bayan rasuwar matarshi Hajiya naja'at, Ƴa'Æ´an shi biyu da uwar gidansa gaba É—ayansu ba mazauna Nigeria bane, Suna a Æ™asar canada suna kula da Babban companynsu tare da sauran Æ´an uwansu dake zaune agidan Hateem.

     Turkish dress ne a jikinta, Riga da wando launin red colour, Ta É—aura satin scarve asaman wuyanta, ta zubo da gashin kanta har gadon baya, Allah yayita da ruwan kyau.

  "Jazz sai nake ganin kamar baka yi kewata ba, Meyasa bakasan zuwa ganina? kullum Sai in ni na shiga gida nake samun damar ganinka idan naci sa'a baka tafi aiki ba.

  Fararen idanuwanshi ya daura akan fuskarta,

  "Mommy ba haka bane, Ni just banason haÉ—uwa da daddyne, ya cika faÉ—a, kuma sharri yake yi min yana cewa wai ni mata maza ne, Fisabilillah"

 "Ya faÉ—i hakanne donka Gyara rayuwarka, ni kaina ina mamakin shagwa6arka sai kace wani yaron goye, komai naka irin na mata"


  ÆŠaure mata fuska yai"mommy kina goyan bayansa kenan, yaci gaba da kira na mata maza"? Girgiza mashi kai tai"A'a, Ai nafi kowa jin haushin inji ya kiraka da hakan, Yana ta6a min zuciyana, donni nasan namiji na haifa ba maca ba" murmushi Jazz Ya saki"to kice mashi ya daina"

 "Zan buga mashi warning, kada ka damuwa" maÆ™e mata kafadai yai"Allah mommy ni nasani wasa kikeyi, saboda ke kanki shakkarshi kike ji ba zaki Iya buÉ—e baki ki yi mashi magana akan ya daina ba"

  Jan kumatunshi tayi da hannunta In jiwa ya faÉ—a maka! Ni bana jin tsoronshi awaja ne mutane ke jin shakkarshi, da zarar ya shigo nake juya shi son raina, Har girki yana yi min" Baki asake Jazz ke kallonta

  "Uncle mubarak É—in"! Jinjina masa kai ta yi"Æ™warai kuwa, ae dukkan Namiji bawan matane, 

  Har ya buÉ—e baki zai Æ™ara magana, Wayar Aljihun wandonshi ta soma ruri,  miÆ™ewa yai da sauri ya curo wayar, bayan ya duba sunan mai kiran nashi ya É—ago tare da kallon mommynsa, Wanene ya kira"?


  Bai amsa mata ba sai dai ya sakar mata murmushi, da sauri Ya fito daga falon gidan, Kamar wani munafuki duk faÉ—in gidan bai isheshi ba sai da ya shiga garden tukunna ya dakata da yin tafiyar, Yai picking call É—in jiki na rawa ya kara ta akan kunnansa, Kirari ya soma yiwa wanda ya kira shi wayar tamkar maroÆ™i,

  "Yalla6ai Kajin nan suna nan cikin Æ™oshin Lafiya, Suna samun kyakkyawar kulawa yadda ya dace," dakatawa ya É—anyi da yin maganar, yana sauraron muryar mai magana, 

  "Ana basu hatsi yalla6ai mai rai da lafiya, Yanzu haka idan nagama magana da mama zan tafi gidan gona domin duba lafiyarsu," sai faman sakin murmushi yake yi, aladabce yake yin maganar

  'kasan kajin turawa saida hatsi mai kyau, Gaskiya basu da matsala yalla6ai, biyu daga cikinsu ne kaÉ—ai suke neman gazawa, shi zakaran ciwon nashi Ya lafa, sauran Kajin muna nan muna basu kyakkyawar kulawa, in sha Allah zasu samu lafiya harma asamu nayin farfesun sallah"


 Tuntsirewa dr Jazz yai da dariya hada dafe ciki.

  duk wannan surutun da ya ke yi acikin waya baisan Sir Mubarak na tsaye abayanshi ba, daga shi sai gajeran wando, Da singlet fara, hannunshi É—aya ruÆ™e da Cup na coffee


  Mamaki ne Æ™arara akan fuskarshi Jin dr jazz na Zancan kajin turawa awaya


  "Okey toh, Zuwa anjima idan nashiga gidan Gonar zan Kiraka Awaya" Daga haka sukayi sallama, Juyawar da zaiyi karaf suka haÉ—a ido da sir mubarak, tuni yasha jinin jikinsa, DuÆ™ar da kai Æ™asa yai ido ya raina fata

  "Jazz! Dawa kake magana a waya? Kajin menene naji ana magana akai? Ni dai A iya sanina likitan mutane ne kai bana dabbobi ba" sosa Æ™eya jazz yai, mirya dabarbarce yake faÉ—in"am...umm..dama " Ya rasa ta ina zai taro zancen, 

 Kallon tuhuma Sir mubarak ke jafa mashi hakan yasashi yin saurin fauzewa 

  "daddy, Ni da abokina ne dr fawan muka buÉ—e gidan gona, kajin turawa ne muke kiwo, wasu ne babu lafiya shine ya kira muna tattaunawa game da yadda zamu shawo kan matsalar" 

Ajiyar zuciya Sir Mubarak Ya sauke"Okey, mu shiga gidan" yai maganar tare da miƙa mashi Cup din hannunsa, da sauri jazz Ya kar6a Yana sha atare suka nufi gidan sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi.


*GIDAN ÆŠAN IYA*


Mahboob ne ke ta faman zuba sauri Yana tunkarar harabar ajiye motocin su, ya É—auki wankan shadda, tunkan Ya Æ™arasa idonshi ya sauka akan motar Uncle abdallah, Æ™ura ido yai yana kallon bayan motar sunanta Ya karanta, Aranshi Ya ayyana lallai mutanan nan ba Æ™ananun shaggu bane wannan mota haka mai tsada! saboda almubazzaranci da rashin sanin ciwon kuÉ—i, Ina laifin ko Æ´ar Æ™aramar honda mutun ya saya ya wadatar, mutane sun É—aurewa Æ™aryar arziÆ™i wurin zama, Allah dai ya shirya mu, ae ni wlh ko nayi arziÆ™i ban Iya fidda kuÉ—ina in sayi mota, na Æ™wammace duk inda zanje in taka da Æ™afata, idan ma da nisa ne Æ™wara in biya kuÉ—i In hau motar Haya, Ita ma wannan motar da nake amfani da ita ba don babansu abokina  ne ya bani kyautarta ba kuma ina ganin mutuncin shi saboda ya ji tausayina ya siyamin ganin ina hawa  motar haya yasin da tuni na jima da siyar da ita' Shi kaÉ—ai ya ke yin sambatunsa, Har ya Æ™arasa gaban motarshi Ya buÉ—e front seat Ya shiga Ciki Yana Æ´an dube dube, da alama wani abu yake nema, saÆ™o da lungu na motar yake ta bincikawa, har Æ™arkashin seat, tuni ya haÉ—a uban gumi.


  "Ina na ajiye zoben nan Jiya? Ko dai ban shigo da shi mota bane? fuskarshi a hautsine Ya jefawa kanshi tambayar, zurfin tunani ya shiga yi still bai tunano inda ya ajiye shi ba, A Æ™arshe Ya soma tunanin kodai Ya shigar da shi É—aki ne, 


  Fitowa yai daga cikin motar Ya datse murfin, Jiki na 6ari ya nufi cikin gidan.


   Abie da Uncle É—an Iya ne zaune a saman sofas na palourn tare da Uncle abdallah, Sun nutsa suna tattaunawa dangane da 6acewarsu tajuddeen, Mahboob Ya faÉ—o falon Ko kallo basu ishe shi ba hankalin shi na akan zoben shi da bai gani ba.


  "Wancan ba mahboob bane? Kamar naso na wayi fuskarshi" Uncle abdalla ne yai maganar,


  Girgiza kai uncle É—an Iya yayi Yayin da yake bin bayan mahboob dake Æ™oÆ™arin karya kwana zai nufi sashen É—akinsa

  "Shine, halan bai gaishe ka ba"?


 Murmushi É—auke akan fuskar Uncle Abdalla yace"Tun da muka zo ban yi tozali da shi ba, sai dai naji labarin shi awurin junaid"


  Cikin nuna 6acin rai ÆŠan Iya yace"baida wayau ne ai ni bansan baizo ya gaishe ka ba, bari ya fito daga É—akin É—an rainin wayau, Zahra tafi shi hankali" 


  Abie yace"Ƙuruciyace ke damunshi, Zahra kuma ae tafi shi shekaru baza a haÉ—ata da shi ba"

  ÆŠan Iya yace"babu wata Æ™uruciya atare da shi, Sarai yasan me yake yi sai girman jiki ba wayau" da alama Ranshi ya 6aci da rashin gaishe da uncle abdallah da baiyi ba.


 Kafin wani daga cikinsu ya Æ™ara yin magana Hajiya adama ta fito daga É—aki  hannunta É—auke da baby junaid, tun da ya dawo daga school a wurinta ya wuni ya hanata sakat duk inda za ta je Æ™afarta kafarshi toilet ne kaÉ—ai yake bari ta shiga, Ta canza Kayan jikinta zuwa atampa riga da skirt, Ta yafa mayafi akanta, kafin ta Æ™arasa shiga palourn Mamie ta fito daga É—akin Ummi su biyu ganinta yasa suka nufi wurinta fuskokin kowannansu da fara'a suka soma gaisawa da junansu


  Atare suka Æ™arasa shiga palourn, Kowa ya samu wuri ya zauna, Kafin suka fara gaishe da Mazajensu, miÆ™a ma junaid hannu uncle abdallah yai"zonan kyakkyawan Jikana mu gaisa," da sauri Junaid ya sauko daga saman laps din Hajiya adama ya nufi sofa É—in da uncle abdalla yake azaune Ya haye saman jikinshi yana faman sakar mashi murmushi, shafa fuskarshi yai da tafin hannunshi"Masha Allah mutumina, Ka tashi lafiya? Fadamin meyasa baka je school ba yau? Sannan baka bi mu zuwa masallacin Juma'a ba" Zaro ido Junaid yai haÉ—i da É—an girgiza kanshi muryarshi da shagwa6e yace"nafa je, ae yau da wuri ake tada mu duk ranar juma'a, kuma ni ai ban isa zuwa masallaci ba inji mommy" maganarshi ba Æ™aramin Æ™ayatar da su take yi ba, musamman In ya haÉ—a da shagwa6a,


 "Junaid kaji tsoron Allah, Aneelerh ce ta faÉ—a maka haka? FaÉ—amin gaskiya ka dai san me Æ™arya É—an wuta ne" jin haka yasa shi saurin sanya tafukan hannayenshi biyu ya toshe fuskarshi Yana tiÆ™ar dariya" muryarshi Æ™asa Æ™asa ya furta"ba ita bane, ae malaminmu ne yace mu Æ™ananu ne bamu isa É—aukar zunubi ba" gaba É—aya suka saki dariya, bayan sun tsagaita da yin dariyar ne, Uncle É—an Iya yai masu gyaran murya hakan yasa suka dawo da dubansu gare shi.


  "Dama yanzu nake shirin aikawa a kira mun ku, don mu haÉ—u duka muyi magana, Kafin mu shiga cikin zancen Ina Æ™ara yiwa baÆ™inmu barka da zuwa fatan kun wayi gari lafiya" da fara'a Hajiya adama ta amsa mashi a mutunce


 Mami tace"tun É—azu da safe take son yin magana mun fara sai nace ta bari idan kuka dawo daga masallacin juma'a zaifi mu haÉ—u mu duka mu tattauna tunda abune daya shafi kowannanmu da buÆ™atar aji shawara daga bakin kowa" 


  Jinjina kai Abie yai"hakane, Yanzu Ina aneelerhn take"?


  "Tana a É—akin zahra, Bari na shiga na kirata" kafin ta mike muryar junaid ta katse mata hanzarinta.

  "Ni zan Kirata" Bai jira amsarta ba, Ya sauko da gudu Ya nufi ÆŠakinsu, uncle abdallah ne ya É—an É—aga murya yana yi mashi faÉ—an ya daina gudu kada ya faÉ—i yaji ciwo, Jin haka yasa shi dakatawa da yin gudun ya soma yin tafiya a tsanake

  

A lokacin Aneelerh da Zahra suna zaune saman gado kowa ya dafi waya suna fira suna chatting, sun É—auki wankan dogayen riguna

  "Ba zaki leÆ™a wurin surukar taki ba? Kin barta a É—aki ita kaÉ—ai" acewar zahra

 "ÆŠazu da safe na shiga na gaishe ta, har ma na tarar da mami zaune suna tattaunawa shiyasa ban tsaya ba,"

  "Gaskiya aneelerh ki godewa Allah, surukarki tana da mutunci ta iya magana ga faran faran da jama'a, Ni wlh ba Æ™aramin burgeni take yi ba, Inasonta sosai, da ace tana da wani É—an Bayan Yaya uzair Allah dana aure shi" har cikin zuciyarta take yin maganar,

 Aneelerh na murmushi tace"Chief Owais din fa? Ko kin fasa"! farfari Zahra Tayi mata da ido

  "shi wannan na dabanne, idan ana maganar Æ™arauÆ™arau ba a maganar Zinari, My dream man inaji araina ma ya kusa dawowa Æ™asar jiya har mafarkinsa nayi"

  Murmushin gefen fuska Aneelerh ta saki

  "Allah Ya cika maki burinki zahra, Ni na Æ™osa inga fuskar Owais É—in nan, har tambayarki nayi hotonsa kinÆ™i ki nuna min, bansani ba ko rowa kike yi min" dariya Zahra tayi"Ina jin fargabar zuciyarki ta buga silar ganin kyakkyawar fuskarshi, kuma kinga ke matar aure ce bana son ki kalli haramun" Sakin baki aneelerh tayi yayin da take kallonta, tama rasa bakin magana

  "Fuskarshi tsadane da ita, idan har zaki Iya biyan farashi sai muyi ciniki in nuna maki" fashewa da dariya aneeleeh tayi jin wani zancen abakin zahra.

  FaÉ—owa ÆŠakin Junaid yai tun abakin Æ™ofa yake faman Æ™wala mata kira"Mommy!mommy!" a hanzarce ta kai idonta ga Æ™ofar

  "Babyn mommy lafiya kake ta Æ™walamun kira" tai maganar tare da sakowa daga saman gadon ta nufe shi, hannu biyi tasa ta É—auke shi tana kallon fuskarshi

  "Mommy ana kiranki, ki zo inji su abie" 

  "Sune sukace ka kira ni"? ÆŠaga mta kai yai alamar eh ya Æ™ara da cewa"ke kaÉ—ai banda Zahra" 

  Harara zahra Ta wurga mashi"aiko sai naje É—an baÆ™in ciki, so kake kayi mun buÆ™ulu wata'Æ™il Æ™udi ne za'a raba mana,

  Saukowa tai daga saman gadon ta É—auko masu mayafi a closet ita da Aneelerh ta yafa mata akanta, atare suka fuce daga É—akin zuwa palour


Hankalin Mahboob Ba ƙaramin tashi yai ba, ganin babu zoben a ɗaki, duk yabi ya birkice ɗakin, ya tarwatsa komai, Hatta zanin gadon shi da fululluka duka yayi wurgar dasu saman tiles, ya zazzago da jerin ninkakkun kayansa na cikin wardrobe kaf dinsu Ya bazasu saman gadonshi, zufa ta ko'ina, Bawan Allah shine har ƙarkashin gado neman zobe, Cikin drawer chest, da laundry basket, kanshi harya fara yi mashi ciwo, ya tsani asara a rayuwarshi, a haukace ya tura ƙofar toilet dinsa ya shiga ciki Yana neman zoben, gaba ɗaya ya fara zaucewa, ganin babu zoben a toilet ɗin ya dawo ɗakin, yana haki zufa sai tsastsafo mashi take Yi, Idanuwanshi sunyi jawur dasu luhu luhu yakai maƙura tamkar zai rushe da kuka, jiri ne ya fara ɗibarshi a hanzarce ya koma gefen gadon shi ya zauna tare da sanya hannayenshi biyu ya tarbe kanshi Takaicin duniya ya ishe shi, bakomai yake tunawa ba face kuɗin da Aka sayi zoben, har zazza6i yai daya miƙa su dubu goma sha biyar. Ahakama kuɗin bada guminsa ya same su ba, Abokin shi ne ya siya mashi zoben saboda ya nuna yana so kuma baida kuɗi.

  



*Boss Bature✍️ Mu haÉ—u monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun Æ™addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuÉ—in*




First bank




3196407426, 




*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number É—ina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

No comments