Breaking News

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 22

 _~*BossLadiesWriters*~_



           _*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_




~Middle step~

          


              _The Prisoners E22🔥💫_




*Daga alƙalamin Boss Bature*




_UMMIN AMERICA🔥🔥🔥_




A hankali ta zuro ƙafarta ɗaya daga cikin motar wow, high hills ne launin army green sanye a ƙafarta, sunyi bala'en yi mata kyau, Launin fatar ƙafarta ka ɗai abun kallo ce, kai kace hasken rana bai ta6a shafarta ba, tsabar kyan fatar da salƙinta.


   Tun kafin ta Æ™arasa fitowa sojojin suka sassauta fushin fuskarsu, Jikin kowan nan su yai la'asar Æ™amshin shu'umin turaren jikinta ya daki hancinansu har cikin maÆ™oshin su fragrance din ya ratsa, Tabarakallahu ahsanul khaliÆ™in, gaba É—aya ta tafi da imanin su, basu san sa'adda Bindugun hannunsu suka faÉ—i Æ™asa ba, Ta yi matuÆ™ar tafiya da hankalinsu, wani irin mayataccen kallo suke bin surar jikinta da shi kamar zasu kai mata hari.

    

Black american ce, A zubin halitta tana da tsayi da jiki, Launin fatarta Chocolate colour ne, Bodycon ce a jikinta, long sleeved gown dai dai gwiwa rigar ta tsaya mata launin Army green, daga ganin ta kaga ƴar duniya hayaƙin taba, baƙar a shana ƙona gari, Irin Ruƙaƙƙun karuwan nan ne Waɗanda suka amsa sunansu A harkar Bariki,Wannan da kuke gani bakowa bace face UMMIN AMERICA, hamshaƙiyar macace mai zaman kanta, Idanuwanta A tsaitsaye suke, Bata da mutunci, kuma bata da kunya ko misƙala zarratin,Tun daga kan shigarta zaka shaida fitsararta, Gaba ɗaya rigar ta bayyana tsiraicinta, boobs ɗinta sun cika faffaɗan kirjinta, tamkar zasu fasa rigar su fito waje don atakure suke an matsesu.


Flat tommy É—inta tamkar ba'a saka abincin acikinsa tsabar É—amewarsa, ga Uban qugu dake gareta tamkar É—aura mata shi akayi saboda faÉ—insa, ko kofi aka É—aura a tudun mazaunanta tsaf zai zauna batare da ya faÉ—o ba.


Wani irin daddaɗan ƙamshine ke fita saƙo da lungu na Jikinta.


 

Round face gare ta,Tasha Uban make up, tamkar an zanata don kyau, Ga eye lashes da akayi mata fixing masu tsayi, dogon hancinta Na manne da Nose ring mai kyan gaske, Haka yatsun hannunta na dama na sanye da knuckle ring, long nails din yatsun hannunta fixing dinsu akayi.


Sumar kanta tasha gyara, sai dai daga gani hair wing ne ta daura ba asalin sumar kanta ba, amma zai wuya mutun Ya iya ganewa.


  Hankalin maza fa ya tashi haiÆ™am, gaba daya sun rasa natsuwar su, sai faman haÉ—iyar yawu suke yi kamar zash lashe ta.


    Muryarta tamkar ana busa sarewa ta furta"Zan Iya shiga Ciki"? Har suna haÉ—a baki wurin bata amsa da cewa"You're welcome" 


shu'umin murmushi ta sakar masu, har dimple din gefen fuskarta Ya lotsa, juyawar da za ta yi, mazaunanta suka girgiza gaba daya sojoji suka zabura tamkar zasu tallabe mata shi.


  Komawa Cikin motar tayi, kafin ta rufe motar, wani daga cikin sojojin yai saurin datse mata murfin, A tsanake taci gaba da yin driving ta nufi cikin head quarter din.


  Ta tafi tabar su da jarabar kallon surar jikinta da su ka yi, ba zasu iya jurewa ba ai ko da sauri suka nufi cikin head quarter din donsu samu damar Æ™are mata kallo ko sun rage raÉ—aÉ—in da zuciyarsu ke yi masu.



  Bayan tayi parking É—in motar, ta fito hannunta ruÆ™e da i phone dinta, Hankulan sojojin dake Zarya a headquarter din gaba É—aya ya dawo kanta, kamar sun samu talabijin, Matarce akwai Iya jan hankalin maza da surar jikinta, duk idan Tayi taku É—aya jikinta sai ya girgiza hakan ba Æ™aramin hayaÆ™a maza yake yi ba.



     All eyes on her, Sojojin Tamkar zasu kai mata hari, sai dai ba damar Yin hakan,Wani irin Æ™warjini gareta, A fuska bata da wasa, Zazzafa ce, Me zaman Kanta.


 Ta wutsiyar ido take kallon masu É—ago mata hannu da masu yi mata alamar suna son yin magana da ita.


Ko kallo basu ishe ta ba, jefi jefi takan ɗan wurga eye balls dinta akansu, da gangan take kashe masu ido ɗaya ko ta ciji lower lip dinta da harshe, ɗabi'arta ce Yin hakan, duk don ta ƙara hayaƙa su.


Kaitsaye ta nufi hanyar da zata sada ta da office din commender domin amsa kiran da yayi mata, tasan ko'ina na headquarter din, don ba baƙuwarta bace, Ba yau bane rana tafarko da ta fara shigarta.


  Tun kafin Æ™arasowar ta, tuni Anyi mata iso wurinshi, jiranta kawai Yake yi, yana daga zaune saman chair, acikin katafaren office dinsa, komai na cikinsa army green ne, hatta desk din gabanshi, dake dauke da computer dinsa, da wayar hannunsa tare da flag and map, daga jikin bangon office din akwai book shelf, da jerin hotunansa da awards dinsa, bashi kaÉ—ai bane a office din hada Major.


  Shigowarta office din, Tuni sanyin Iskar A.c É—in cikinsa ta gauraya da Æ™amshin shu'umin turarenta.


 Har saida suka shaÆ™e shi sosai a hancinansu.


  Da kwarkwarsa ta Æ™arasa gaban desk dinsa, kamar yadda ta saba yi mashi duk in tazo office dinsa haka yau ma tayi mashi, Ta buga Æ™afa tare da sara mashi, hakan ba Æ™aramin Æ™ayatar da shi yai ba, har sai da suka saki murmushi, tun kafin Ya bata iznin zama, ta zauna saman chair din dake facing dinsa, ta É—aura Æ™afa É—aya bisa É—aya, murmushi ta sakar mashi haÉ—i da É—aga mashi gira É—aya ta kashe mashi ido.


   A wayance ta soma yin magana cikin harshen turanci"fatan na same ku lafiya" lumshe ido commender yai tare da kai hannu ya gyara zaman wuyan rigar kakinsa.


"Lafiyalou ummi, I'm glad to see u, Ina fata kiran da mukayi maki bai taƙura maki ba"?


  ÆŠaga mashi gira tayi alamar eh ba tare da ta furta ba, a mutunce suka gaisa da junansu. Bayan kowan nan su ya natsu, Major Ya miÆ™e ya bi ta Æ™ofa ya fuce waje jim kaÉ—an ya dawo hannayen shi ruÆ™e da mugs na coffee guda biyu ya É—aura su saman desk, ya É—ago da ido Ya kalli Ummi"zaki Iya sha" ta furta okey, kafin takai hannu ta dauki mug din ta soma kur6an coffee din, da alama ya yi mata dadi kusan sau uku tasha kafin ta ajiye mug din, ta dawo da dubanta ga commender"am all eyes"


  "Dalilin da yasa na kira ki ummi, Magana ce mai muhimmanci muke san yi da ke, Ina fata za ki bamu haÉ—in kai kamar yadda kika saba taimakon mu" cikin harshen turanci commender yayi maganar a tsanake.


Hankalin major na akan ƙirjinta har wani ƙara leƙensu yake yi kamar zai zura kanshi cikin rigarta.


  Kallon da Commender ya watsa mashine yasa shi saurin kawar da idonshi ya kame mutuncin kansa


  "Babu takura, ko da yaushe ina maraba da ku, zaka Iya faÉ—in komai ka ke so kai tsaye" 


ta ƙare maganar tana shafa saman boobs dinta da yatsun hannunta.


  Yawu commender Ya haÉ—iya Kutt throat dinsa Ya bada sauti, shi kanshi daurewa yake yi, surar ummin America na neman kwance mashi masarrafinsa.


 "Ina so ki natsu ki fahimce ni kafin ki bani amsa" amsa mashi tayi da toh

   Bayani ya soma yi mata dalla dalla tun daga farkon tsintarsu Angel da su ka yi a Daji, har izuwa kawosu asibiti, da kuma abun da su ke buÆ™ata daga gare ta, tunda commender ya fara labarta mata, ta natsu tana sauraronshi.


  "Muna so ki bamu haÉ—in kai wurin Kula da yaran ki ruÆ™e su tamkar Æ´a'Æ´anki, munsan zaki Iyane shiyasa muka za6e ki, tun da ba yau kika fara yi mana aiki ba, mun yarda dake ummi, burinmu ki tarairayesu ta yadda yaran zasu yarda dake har su Iya faÉ—amaki ainihin abun da ya faru arayuwarsu' ya Æ™arasa maganar idonshi akan fuskarta.

  Lumshe ido ta É—anyi kafin ta waresu akan fuskarshi


   "ta ya ya zaku yi tunanin damÆ™a amanar yara har goma sha É—aya a hannuna? Bayan kunsan wacece ni, Ban ta6a haihuwa ba, kuma ni banason Rainon Æ´a'Æ´a, ban ta6a sha'awar haihuwarsu ba, balle har in iya kula da yaran wasu, Ina mai baka haÆ™urin Cewa Ni bazan Iya wannan aikin ba! zaifi ku samu macen da tasan zafin haihuwa mai kamun kai ku bata rainon su" tana magana jikinta na jijjiga, major duk yabi ya susuce ya rasa natsuwarshi, ba dan commender na akusa ba da ba abun da zai hana ya damÆ™eta ko da zai sha mari ne.


     "Ummi, Ki sassauta kalamanki, Kina yi min magana da tsiwa, Ko kin manta a ina kike ne? Ki duba da kyau ki gani, nan ba club ba ne, ba kuma gidan karuwai bane, sannan ba ga6ar taku bane, Head quarter din sojoji ce" Ya yi  maganar tare da zaro bindiga daga cikin drawer chest na desk din gabanshi Ya daurata saman desk din.


  Tuntsirewa Tayi da dariyar rainin wayau


  "Kai ma ka sani, Ummin america bata tsoron bingida, ni da ni ke yin mu'amala da masu ruÆ™eta, yanzu haka da nake yi maka magana shigowa ta head quarter din nan gaba É—aya na tada masu jarabarsu, suna can waje, wandunan su sunyi masu nauyi' cike da shaÆ™iyanci tayi maganar, ta riga ta gama raina su bata jin tsoron su ko kaÉ—an.


   Cikin kwantar da murya commender yace"is ok, kibar yi min wasa, Muyi magana ta hankali, ki taimaka ki kar6i buÆ™atarmu, kome kikeso zamuyi maki, sannan É—awainiyar yaran da komai nasu mune zamu bada tallafin da za'a cigaba da kula da rayuwarsu, tun daga  cinsu shansu, suturarsu, da karatunsu, Iya taimakon da muke so kiyi mana kija su a jiki ki zama tamkar mahafiyarsu" yamutsa fuska tayi tana faman wurwurga eye balls dinta tace"Kana nufin wai a gidana zasu zauna? Ka san gidana gidan mazane, a koda wani lokaci Ina busy wurin biya masu buÆ™atarsu, how ka ke tunanin zasu Iya samun kulawar data dace? Kuma naji kace yaran suna fama da depression hada me ciwon ciwo, gaskiga ba Æ™aramar É—awainiya bace kula da su, bazan Iya ba commender, kada ka tursasamin, kasan ina girmamaka saboda halaccinka agareni"


    Kallon major commender yayi, hakan ya bashi damar Yi mata magana


  "Ba zamu takura maki ba, amma kafin ki tafi Inaso zan nuna maki hotunan Yaran Ki gansu" 

 

Miƙewa Major yai daga saman kujerar da yake a zaune Ya zagaya ta 6angaren Commender Ya juyo mata da laptop din saitin fuskarta.


   Operating É—inta Ya soma Yi, hotunansu Angel Ya buÉ—o, daga kan hotonta Ya fara Nuna ma Ummin america

  "Sunanta Angel"  Ya ambaci hakan yana kallonta, da alamun mamaki akan fuskarta ta furta "wow she's beautiful sai dai daga ganin bakinta za ta yi tsiwa, ni kuma bana sha'awar Yara masu masifa" ta faÉ—a haÉ—i da yamutsa fuska, still murmushi ne akan fuskar major da commender.


      Hoton Batul ya nuna mata, sai da ta ta6e la66anta kafin tace "tana da kyau, sai dai daga ganin fuskarta bata da masifa, wannan ko yatsa aka sanya mata abaki bazata Iya cizon shi ba" ta kare maganar tana hura hanci.


   Hoto na gaba fuskar Hanna ce, Ummin america tace"har Æ™wara Yarinyar daka wuce akan wannan, taci ka sanyi daga gani babu kuzari a jikinta" yadda take fayyace É—abi'unsu kamar ta ta6a ganinsu.


   Ko da akazo kan Hoton Parveen Ya cika screen din laptop din.


  Da buÉ—ar bakin Ummi sai cewa tayi"yarinyar nan daga ganin kumatuntu mayyar abinci ce, zai yi wuya idan ba asame ta da shegen ci ba, Ni bana so mutun mai ciye ciye" murmushin fuskar Major da commender sai Æ™ara faÉ—ada yake yi, don ba Æ™aramin nishaÉ—i take basu ba.


    Hoton Jamimah Ya nuno mata, waro ido waje tayi hada sanya Hannu ta dafe saman Æ™irjinta.


   "Major, ruÆ™on wannan Yarinyar ai sai likitan mahauka, shi kaÉ—ai ne zai Iya sarrafa ta, ba dai ni ba, Ni ina zan Iya kula da ita, daga ganin bakinta zatayi tsiwa" Major yayi dariya tare da nuno hoton Azeeza, shiru tayi tana Æ™are mata kallo, kafin ta É—ago da ido ta kalli Major"sai naga kamar Æ´an biyu ne ita da Yarinyar da ka nuna min kafin ita, sunyi kama" Major yace"haka muke tsammani, sai dai muna hasashen azeeza tafi Jemimah shekaru kamar yadda É—an uwansu ya faÉ—a mana"


  Yamutsa fuska Ummin america tayi"tana da kyau sai dai daga ganinta matsoraciya ce, wannan ko tsawa na daka mata zata Iya sakin fitsari a wando, gani da tsiwa bansan ya zamu Æ™are da ita ba" ta fada tana ta6a baki tace"wai Iya matane Yaran"? Ta yi tambayar tana kallon Fuskar Major


  "akwai maza" ya bata amsa, a  dai dai kan hoton Haris Ya buÉ—e mata shi.


     "Sunan shi Haris, shine yaron da commender Ya faÉ—a maki cewa Yana fama da ciwon zuciya"


  Ta6e baki tayi"nifa banason namiji mai raunin zuciya, daga gani baya da hayaniya ba laifi yana da kyan fata" ta faÉ—i hakanne saboda kasancewarta baÆ™ar fata, tana son mutun me duhun fata.


    Wuce hoton Haris yai adai dai kan hoton Javed ya dakata Yana dubanta


   "Amma dai wannan Yaron É—an south korea ne ko? 


  Major yace"bamu da tabbacin É—an Ina ne, duka yaran bamu san wani jinsi bane, sai dai sun faÉ—a mana cewa Ƴan Nigeria ne" da sauri ummin america ta girga kai tana fadin"Impossible, babu kalan waÉ—annan a nigeria, may be sun yi loosing memory É—in su ne shiyasa su ka faÉ—i hakan" 


     Hoton Naufal Ya budo mata, lumshe ido ta É—anyi tare da waresu akan kyakkyawan fuskarshi

  "Wow, kaga Namiji, sumar kanshi ta burge ni, Yayi min kyau" ta yi maganar tana hura mashi kiss.



    "Yaro ne" Commender ne yace haka,

  Ummi tace"Ai shi namiji baya kaÉ—an, especially idan abunsa ya ruÆ™a, a wurina wannan ba yaro bane Namiji ne" murmushi suka saki, basu damu da abun da tace ba saboda sun san halinta, bata mu'amala da matasan samari, Sai mazan da su ke da aure waÉ—anda tasan idan ta bibiyesu za'ayi bala'i idan matansu suka kamata.



     Bayan Ya wuce hoton Naufal Ya buÉ—e mata hoton Gabriel, tunda ta kafe shi da ido bata Æ™yaftaba sai faman jinjina kanta take Yi alamar mamaki


    Can dai ta numfasa tare da cewa"Allah Ya yayi halitta, gaskiya idan aka bani rainon yaran nan tamkar kun ba kura ajiyar nama ne, major idan akwai wani hoton nuna mini na Æ™osa na Æ™arasa ganinsu"


  Lokacin da Major Ya hasko mata hoton Danish daga zaune ta zabura ta miÆ™e tsaye tana duban fuskarsa data cika screen na laptop din, duk suna akwance akayi masu hotunan idanuwansu arufe.


     Muryarta tamkar tame Yin raÉ—a ta furta "Speechless! Major Ina kuka samun Kyakkyawar matashin nan mai kama da É—an sarkin aljanu? Anya Cikakken mutunne? Ko dai A cikin Dajin da kuka tsintosu Aljana ta haife shi Ta yada" dariya kowan nan su ya saki jin sambatun ummi dama sai da ransu ya basu zata ruÉ—e idan taga hoton shi.


    Major yace"sai ma kin ganshi a zahiri, ba Æ™aramin kyaune da shi ba"


Ko da ta koma ta zauna, sam takasa ɗauke idonta daga kan fuskar Danish, Yayi matuƙar tafiya da imaninta, aranta har ta fara Ayyana koya surar shi zata kasance a zarihi?


  Muryar Commender ce ta fargar da ita ga dubanshi"dukansu ne muka nuna maki, shin kin canza ra'ayinka akan kula da su ko kuwa har yanzu kina akan bakanki"


   Shiru ta É—anyi tana yanke shawara da zuciyarta, duk sun Æ™agara da son jin amsarta.


    "Yanzu haka case din Yaran mun miÆ™a shi hannun shugaban isod, shine zai cigaba da jan ragamar bincike akansu, jiya muka samu amincewarshi na kar6ar case din nasu, sai dai ya nuna baya buÆ™atar 6ata lokaci yanason ya tafi tare da yaran can nigeria a jet dinsa, a satin da zamu shiga"


 Lokaci É—aya ummin america ta canza fuskarta zuwa 6acin rai, da farko tayi murnar jin cewa Case din Yana a hannun chief na Isod, daga bisani daya furta komawa Nigeria ne taji komai ya fita aranta.


   "Naji kin yi shiru, baki ce komai ba"

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta soma magana ranta a6ace"Idan har kuna so in ruÆ™e Yaran a hannuna, they should stay in America. I will not follow them to Nigeria,"  


  Commender yace"amma meyasa? Ke kanki fa Æ´ar Æ™asar Nigeria ce why baki son zuwa Æ™asar Ki"


  Girgiza kai Tayi still fuskarta da 6acin rai ta furta"Ni ba Æ´ar nigeria ba ce, asalina ne acan, amma Ni black american ce, tun da nace banaso mubar maganar kawai, Ni zan koma gidan idan ka gama maganar ka"


   Yanayin fuskarta Ya canza sosai, 6acin raine tsantsa, sun fahimci kamar akwai wani abu daya ta6a faruwa da ita wanda har yajawo silar barinta Æ™asar, kuma batason Anayi mata maganar komawa can"


  Ganin yadda ta haÉ—e rai babu annuri ko miskala zarratin akan fuskarta, Yasa Commender cewa"Shikenan ki kwantar da hankalin ki, ba zamu takura maki ba, Zaki Iya tafiya" ba don yaso ba ya ambaci hakan, duk basu ji daÉ—in canzawarta ba, muryarta a disashe ta furta"thank u" ta yunÆ™ura ta miÆ™e ta nufi Æ™ofar fita daga office din, Har ta kusa ficewa Muryar Commender ta katse mata hanzarinta"duk da bansan abunda ya faru dake a Æ™asarki ba da har yasa kika tsani jin an ambaci sunanta, da akwai wani abu da nike so in faÉ—a maki ummi" yayi maganar tare da miÆ™ewa hannun shi ruÆ™e da mug na coffee, Ya kur6a kafin ya É—aure da cewa"wannan dama ce agare ki, da zaki koma Æ™asarki a karo na farko ki nuna ma waÉ—anda sukayi silar barinki Æ™asar cewa Kina araye kuma kinsamu cigaba a rayuwarki ba kamar yadda sukayi tsammani ba, inaso ki basu mamaki ummi, sannan zuwanki Nigeri bana dundun bane na É—an lokacine zaki dawo nan da zarar Mun samu nasara akan binciken Yaran, zamu dawo dake nan, saboda mu kanmu ba zamu so mu rasa nagartacciyar mace irinki ba, ke kanki kin sani muna Æ™aunarki kuma muna daraja Æ™imarki a idanuwan mu, ba zamu so abunda zai 6ata maki rai ba ummi, kina da damar da zaki Iya zuwa gida ki zauna ki yi tunani akan maganata kafin ki yanke shawara.


Kalaman shi sun É—an ta6ata, tuni zuciyarta ta fara sassautowa, ita kanta zataso wannan damar ta zuwa Nigeria ko dan taba waÉ—anda sukayi silar barinta mamaki.


  Numfasawa ta É—anyi kafin a hankali ta juya tana kallon commender dake tsaye abayanta, kamar bata son furta maganar tace"babu buÆ™atar yanke shawara, Na amince Zan bi su zuwa  Nigeria, Kuma nagode da karramawarku agareni, da zarar na gama aikin, zan dawo Æ™asata"


   Murmushi major da commender suka saki, Jin abunda tace, har yanzu bata yadda ta kira Nigeria da sunan Æ™asarta ba.


    Sun ji daÉ—in amincewarta, ba tare da 6ata lokaci ba, Commender ya dauko mata kundun dake É—auke da bayanansu Angel, duka takardun akwai Signature dinsu a jiki, saura sanya hannunta suke buÆ™ata, cikin Æ™anÆ™anin lokaci su ka Ƙulla Yarjejeniya ta (guardianship agreement)atsakanin su da ita, sai da ta natsu ta karanta sharuÉ—É—ansu dalla dalla akan irin rainon da suke so tayima yaran kafin ta sanya hannu a takardun, bayan ta kammala sun bata wasu takaddun yarjejeniyar da zata ruÆ™e a hannunta.


  Bayan tayi masu sallama, Ta fito daga office din, tana tafiya Sojoji Na binta da kallo, Yayin da ita kuma hankalinta na akan takaddun dake a hannunta, Fatanta Allah yasa RuÆ™on Yaran da za ta yi da kuma zuwan ta Nigeria Ya zama alkhairi agare ta.


  Tun kafin ta Æ™arasa gaban motarta da ta bari a harabar ajiye motocinsu, ta hango sojoji dadda6e sun kewaye motar suna jiranta, murmushin gefe fuska tasaki har dimple dinta Ya lotsa, ta fahimci tunda ta shiga office din commender suke ta jiran fitowarta don su yi mata magana, bata tsaya sauraron su ba, daÆ™yar ta samu suka Æ™yaleta ta shiga mota, a tsanake ta tada motar, Ta juya sitiyarin da gudu ta fuce daga head quarter din.


*EX-PRISONERS❤*


Tun ɗazu da safe kowan nan su Ya farka daga bacci, sun wayi gari da jin kyakkyawan labarin farkawar Danish, saboda zumuɗin zuwa ganin shi babu wanda ya nemi breakfast acikinsu, gaba ɗaya sun Hallara a room dinsa, tun daga kan Haris, Javed, Naufal, Gabriel, Batul, Hannah, Jamimah, Azeeza, ƙwansu da kwarkwatarsu sun yi tsaitsaye cirko cirkon suna kallon shi, fuskokinsu ɗauke da Annurin farin Ciki, Ɗaya bayan ɗaya Danish Yabisu ya rungume su a ƙirjinshi, kamar sunyi shekara basu atare da juna, Haris hada kukanshi saboda murnar ganin Danish Ya farka.


  Sun tasa shi gaba suna kallonshi kamar zasu lashe shi, Musamman Azeeza da Jemimah, daÉ—i suke Ji Danish É—insu Ya farka.


   Muryar jamimah da shagwa6a tace"munyi fushi ma sai yau zaka farka, kullum sai munyi kukan rashin ka, ko bacci bamu Iya yi abincin ma ba mu ci" Harara Azeeza ta watsa mata"wlh Æ™arya take yi Danish kullum sai taci abinci sau uku, kuma tana Yin bacci" Murmushi ya saki yana binsu da kallo, Haris dake zaune gefen gadon Danish ya ruÆ™e hannunshi a Cikin nashi ji yake kamar za a kwace mashi É—an uwanshi.


      "Meyasa Angel Jiya daya farka baki tada mu daga bacci ba? Bayan kinsan irin Æ™agarar da muka Yi na son ganin shi" Hanna ce tayi maganar, Gabriel Yace"Ni dai ba abunda zance sai godiya, saboda ba zamu Iya misalta farin Cikin da muke aciki ba, Yau babbar rana ce agaremu É—an uwanmu abun alfarinmu Ya farka da ranshi da lafiyarshi" yana daga tsaye yake yin maganar Ya goye hannayenshi saman Æ™irjinshi.


   "Allah sarki Rayuwa kenan, Har na tuna kokawar da Ku ka yi kaida Danish akan nace zan dire taga" gaba É—ayansu suka sanya dariya.


  Batul tace"ai mu bamusan abunda ya haÉ—a su faÉ—a ba"


    Parveen dake tsaye gefen Naufal hannunta ruÆ™e da Ayaba sai ci take Yi, Kunnuwanta akansu ta natsu tana sauraransu.


    Labari Angel ta basu na abunda ya faru lokacin da zata dire taga, ba Æ™aramin nishaÉ—i su ka yi ba.


     Azeeza tace"munyi kuka lokacin sosai, Munyi tsammanin Danish É—inmu zai rasa idonshi É—aya, sai gashi Allah ya dawo mana dashi da ranshi da Lafiyarshi, gaskiya munji daÉ—i" da farin ciki akan fuskarta ta Æ™are maganar, idanuwan Danish akan faces dinsu, ita da Jemamah.


    Parveen tace"ni banaso muna tuna baya, nafi so inji muna magana akan abunda zai faru agaba"


  Jemimah tace"Genie yaushe zamuje gidan daddyn naki? Ni na Æ™osa mu koma can, waÉ—annan mutanan masu jan kumatun, kullum sai sun tsira mana allura a É—uwawun mu" ta yi maganar tare da nuna ass dinta da indext finger dinta, gaba É—aya suka tuntsire da dariya, Azeeza tace"Kai jamimah ki ji tsoron Allah, Jiya fa ba ayi mana allura ba, nurse ta faÉ—amin an gama yi mana ita, sai dai magani da zamu dinga sha na tsawon one month" turo mata baki Jemimah tayi

    Javed yace"Kufa baku gajiya da abun magana, Kun Cika É—an uwanmu da surutu, Ko so kuke yi ya koma  baccin" atare suka zaro ido haÉ—i da É—an buÉ—e baki"A'a wlh bamu so Ya koma bacci,"


    "Alhamdulillah, Tun da yanzu mun haÉ—u mu dukanmu, Yakamata Muyi wa Allah godiya" Angel Ce tayi maganar, Tare da ÆŠaga tafin hannayenta sama, Da sauri suma suka É—aga nasu zasu yi addu'a, Mutun É—aya ne bai É—aga nashi hannun ba, Hatta Gabriel da ya ke Christian sai da ya É—aga hannunshi don su yi addu'ar atare, Don shi a yanzu baida za6in addini, yafi Æ™arfi ta 6angaren musulunci saboda Angel.


  Kallon fuskarshi Angel tayi"danish zamuyi addu'a, ba zaka É—aga hannu ba"

   Girgiza mata kai Yayi alamar a'a, É—aure mashi fuska tayi sai yayi tamkar baisan tana Yi ba

   Cikin sanyin murya Haris yace"Danish meyasa har yanzu baka goyan bayan addinin musulunci"?


  Shiru danish bai yi magana ba, Kuma babu alamun zaiyi ta.

   Damuwace Æ™arar akan fuskokinsu

 "Pls danish just for today ka É—aga hannu Muyi addu'a" Muyar Angel tamkar zata fashe mashi da kuka Tayi maganar.


      Marairaice mashi fuska Azeeza da jemimah sukayi"Bro pls, let pray together," 


   Runtse idanuwanshi Yai, ba tare daya buÉ—e su ba Ya furta"I can't, ku daina yi mini magana akan Inyi, bana so"


  Sai lokacin Batul ta sanya baki"tun da ya nuna bayaso mu Æ™yaleshi, damu da shi duk abu É—ayane, ko da ace baiyi ba mu zamu yi mashi, hakan ma ya wadatar" Angel bata ji daÉ—i Æ™in Yin addu'a da yai ba, addu'oi' ta soma karanto masu suna amsa mata da ameen ameen, idanuwanta sun cicciko tab da Æ™walla, bayan sun Kammala kowan nan su Ya shafa saman fuskarshi, banda Angel maimakon ta shafa addu'ar da tayi saman fuskarta, sai ta shafa ma danish saman sumar kanshi, a hankali ya É—ago da idanuwanshi yana duban fuskarta, harara ta watsa mashi tare da murguÉ—a mashi baki, hakan da tayi ba Æ™aramin Æ™ayatar da shi yai ba, muryarshi Æ™asa Æ™asa ya furta mata"thank u" ta6e mashi baki tayi"kada ka yi tunanin na damu dakai," Æ™ayataccen murmushin gefen fuska yasakar mata, Su Batul sun natsu suna kallonsu.


 Muryar Dr. laura ce ta katse masu hanzarinsu"Congratulation! My lovely Children Ina tayaku murnar farkawar É—an uwan ku daga bacci, banjima da shigowa asibitin ba, dr Harry ke faÉ—amin cewa É—an uwanku Danish Ya farka, wannan abun farin Ciki ne" ta Æ™arasa maganar, a yayin da take Æ™arasowa Gaban gadon Danish. Fararen idanuwanta dake asanye cikin farin glass ta É—aura su kan face dinshi.


  "An sanar dani cewa Baya kula kowa sai Æ´an uwanshi, dagaske ne masoyiya Angel? Tayi tambayar tare da kallon Angel


 Da fara'a akan fuskar Angel ta amsa mata da cewa "Jiya ne amma yau ya saki jiki, zai Iya magana da kowa" 


 Dr laura tace"Anya kuwa? Naga ko kallona baisan Yi, danish Ya jikin naka? Ko akwai inda ke yi maka ciwo a jikin ka"? Tayi tambayar cikin Æ™agara da son jin muryarshi

   Cikin raÉ—a Angel ta furta mashi"danish pls kayi mata magana, sun taimake mu, kuma suna da mutunci" kamar wanda akayi ma dole daÆ™yar ya iya motsa lips dinsa ya furta"da sauÆ™i babu inda keyi mini ciwo,"


  Dr Laura taji daÉ—in maganarshi"ina fata kaci abinci babu yunwa atare dakai"? ÆŠaga mata kai yai alamar eh

 Ta furta"okey, amma meyasa jiya baka ba likitoci damar duba lafiyarka ba"?

  A takure yake yi mata magana"saboda lafiyata Æ™alau, bana buÆ™atar a duba ni," Jinjina kai ta É—anyi tayi mamakin Halinshi, basu ta6a samun patient irin shi ba.


    Muryar Angel ce ta janyo hankalinta ga dubanta"Aunty, mun gode sosai da kulawarku agaremu, Allah ne kaÉ—ai zai Iya biyanku," tayi mata maganar ne don ta mantar da ita zancen yi ma Danish maganar duba Lafiyar Jikinshi.


  "kada ki damu masoyiya Angel, aikin mun e kula da lafiyarku kuma Alhamdulillah, Naga Jiki yayi kyau Allah ya Æ™ara Lafiya," ta Æ™are maganar tare da kallon Azeeza da jemimah"My twins, Ya jikin naku" atare suka haÉ—a baki" da sauÆ™i" kafin ta É—aura idonta kan Parveen da sauri ta 6oye Ayabar dake a hannunta, dariya dr laura ta É—an saki"hmm ai na gani dama kin daina wahalar 6oye mini" duÆ™ar da kai Parveen tayi fuskarta É—auke da murmushi.


  Kallonsu Gabriel Tayi"Ƴan samari, Jiki yayi kyau, badan sister dinku ta matsa akan son komawarku Nigeria ba, da a gidana zan killace ku, In cigaba da rainonku," murmushi kowan nan su ya saki.


  "Zan Koma Office, Ku kula mun da kanku" har ta juya zata fuce Angel tayi saurin cewa"Aunty, har yanzu sojojin basu kira ba naji su shiru basu zo sun duba mu ba"


  Dr. Laura na niyar juyowa don ta bata amsa, ba zato ba tsammani, Suka hango Dr. Mark tare da dr. brown sun nufo Æ™ofar É—akin, Kusan a tare suka shigo.


   Gaisawa suka Yi da dr laura, Cikin girmamawa su Angel suka gaishe da su, Bayan sun amsa masu, suka tayasu murnar farkawar É—an uwansu


  Kafin daga bisani Dr Mark Ya soma Yin magana"Dr. Ke muke nema, Sojojin nan sun Kira Awaya, idan ba damuwa  zamu Iya zuwa office muyi magana"


 Amsa mashi tayi da toh, ba tare da 6ata lokaci ba suka fuce daga É—akin.


  Hankalin Angel yaÆ™i kwanciya burinta taji me zasu tattauna, fatanta Allah yasa su amince da maganar maidasu Nigeria.


   Bayan fitarsu É—akin kaitsaye office din dr Laura suka nufa, kowan nan su ya samu wuri saman kujera Ya zauna suna fuskantar Juna da ita


  "Ina sauraronku, me sojojin suke ce ne"? A Æ™agare ta tambayesu

 Dr mark Ne ya soma kora mata jawabi"Commender dinsu ne Ya kirani awaya, Ya sanar dani cewa Chief na Isod Ya Amince zai kar6i case din Yaran...." tunkan Ya Æ™arasa maganar, dr laura tasaki murmushin farin ciki


  "Bayan haka, sun Æ™ulla Yarjejeniya tsakanin ita ummin american da su sojojin, zuwa Anjima zasu zo asibitin domin shirya yaran, zasu É—auke su zuwa gidanta, sai dai zamuyi kewarsu saboda Commender din ya faÉ—amin next week chief na isod zai bar Æ™asar tare da yaran" ya Æ™arasa maganar idonshi Akan dr laura, mood din fuskarta ya canza zuwa damuwa, ba ta yi tsammanin zasu bar Æ™asar da wuri ba, zaman da su ka yi da su na kwana huÉ—u ba Æ™aramin sabo su ka yi da juna ba, sai dai ta wani 6angaren taji daÉ—i kodan saboda Angel da ta roÆ™e ta akan ta taimaka masu su koma Æ™asarsu.


 "Dr lafiya? Naga kamar yanayin fuskarki Ya canza? Ko baki ji daÉ—in maganar bane"? dr. Mark ne  yayi maganar ganin ta haÉ—e fuska, Murmushin yaÆ™e tasakar mashi

  "No ba haka bane, Na saba da yaran ne, banaso su yi nesa dani, banyi tsammanin zasu bar Æ™asar da wuri ba, inaso zan nemi alfarma abar mana su ko da one month ne su yi anan kafin su tafi"


   Dr brown yace"ba zai yiwu ba dr, da ace case dinsu a hannun sojojin yake zamu Iya neman alfarmar abar mana yaran su zauna a wurinmu, sai dai kash sun riga da sun damÆ™a case din hannun chief na isod, kuma kinsan shi ba É—an Æ™asar nan bane, A Æ™asar shi yake zaune Aiki ne mai muhimmanci ya kawoshi america, tun cikin weekend daya wuce yaso barin Æ™asar, saboda case din Yaran Ya fasa tafiya, yanzu haka da nakeyi maki magana, yana shirye shiryen barin Washinton zai shigo garin mu saboda ya haÉ—a kan yaran ya tafi dasu, mutumin babu wasa a aikinsa, Baison 6ata lokaci.


  Jikin dr. laura ba Æ™aramin sanyi yai ba, tana son su Angel, ganin duk ta damune yasa Dr mark kwantar mata hankali"Tafiyarsu ba yana nufin mun rabu da su ba, Kada Ki manta Sojojin Æ™asarmu ne suka tsince su, bayanan su da komai Yana a hannunsu, kuma zasu cigaba da bibiyar rayuwar yaran, wannan dalilinne ma yasa suka haÉ—asu da Ummin america.


      GyaÉ—a kai Dr Laura Tayi"Ni damuwata depression din dake damun yaran, da kuma Yaron dake fama da ciwon zuciya, Hankalina bai kwanta da Ummin america ba, Shin zata Iya bamu su kulawar da zata sanya su manta da damuwarsu? nafa santa bata da mutunci macace mai izza kuma ta shahara wurin Iya karuwanci....." Damuwace Æ™arara kan fuskar dr laura, idanuwanta tuni sun ciko tab da kwalla.


  "Yaran sunfi buÆ™atar kulawar mace wadda tasan ciwon haihuwa, bawai karuwa ba! Wadda ta saba Æ™wacewa matan aure mazajensu tana fasiÆ™anci da su! Yakamata Kuyi tunani akan hakan, Ni zanyima Commender din nasu magana, akan su canza masu wadda zata raine su, Yara fa har goma sha É—aya za'a damka ma karuwa, gaskiya basuyi tunani mai kyau ba, zata Iya 6ata su" ranta amuÆ™ar 6ace take Yin maganar.


   Cikin kwantar da murya Dr mark yace"ina baki shawara dr, kada kice zaki shiga maganar nan! Tun ranar da major ya kawo shawarar abata kulawar yaran, Kin nuna kuskuren yin hakan, amma sai basu damu ba, saboda sunsan halinta, kuma sunsan zata Iya ne, kamar yadda yace ta saba yi masu aiki, so bai kamata ki damu ba"


  Dr brown ya É—aura da cewa"sunfi mu sanin wacece Ita, Mu sanin da mukayi mata na karuwa ne, su kuma a matsayin ma'aikaciyarsu suke kallonta, ba zasu ta6a damÆ™a mata amanar yaran ba tare da sun aminta da ita ba"


 GyaÉ—a kai Dr Laura Tayi"Shikenan na haÆ™ura, bazan yi masu magana ba, amma inaso zan ba Masoyiya Angel Kyautar waya, saboda inaso mudinga Yin magana da ita akai kai" 

   

"Na fahimci kina son yaran sosai, Ni kaina na kamu da Æ™aunarsu, Har na fara jin kewarsu" acewar dr. Mark 


 Dr brown yace"aini har Æ™asarsu zan Iya zuwa ganinsu idan naso, don haka banda damuwa, muna atare da su"


  Sun jima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani, Kowa ya koma bakin aikinsa.

  


*DAULAR ALHAJI MUSA*


*Dr Shureim❤*



Ƴan kwanakin da yayi a gidan Uncle É—in nasa Rayuwarshi ta fara canzawa, a yanzu dr. Shureim baida matsalar komai, ta kowani 6angare yana samun kyakkyawar kulawa, kullum yana acikin gida, idan ya gaji da zaman É—aki yakan fito ya zagaye gidan tare da zeenatu, yana matuÆ™ar jin daÉ—in kulawar da take bashi, sun shaÆ™u da juna kamar sunyi shekara atare, hatta abincin atare suke cin shi, sai dai akwai wani abu da ya fara damun zeenatu, hoton da yake yawan kallo awayar shi, abun yabi mashi jiki kamar ibada, Idan ya fara kallon hoton baya so kowa yazo kusa da shi, kuma baya son kowa yasan hoton menene yake kallo, duk idan ta faÉ—o É—akin shi yana cikin kallon hoton da sauri yake danna power button na wayar ya kashe ta, ta rasa gane wacece yake yawon kallo? Don ta fahimci ba Æ™aramin so yake yi mata ba, gashi ita kuma Allah ya jarabceta da masifaffan kishi, ba ta son ganin yana kallon hoton, Har kuka take yi a 6oye ba tare sanin kowa ba. 


A KishingiÉ—e yake saman katafaren gadonshi, tun safe bai fita ko'ina ba, ko Æ™ofar bedroom dinsa bai leÆ™a ba, farin short ne ajikinsa, babu riga, gaba É—aya hankalinsa na akan screen din apple laptop dinsa dake ajiye saitin kanshi daya É—aura saman pillow,   


Sam bai ji takun tafiyarta ba, saboda hankalinshi baya atare da shi, wankan swiss lace ne a jikinta, launin ash colour riga da skirt sunbi shape din jikinta, kamar a jikinta aka ɗinka kayan, duk da bata ƙiba kayan sunyi bala'en Yi mata Kyau, Tani da Lami ne sukayi mata Make up, hatta ɗaurin ɗan kwalin kanta sune suka ɗaura mata shi, ziririyar sarƙar wuyanta ta diamond ce, stone din jikinta sai ƙyalli Yake Yi, ta yafa gyale a saman kafadarta, hannunta ruƙe da handbag, fragrance din turaren jikinta mai daɗin shaƙa ahanci.


   Hankalinta ba akwance yake ba, tun kafin ta shigo É—akin tayi mashi sallama bai amsa bata ba, har ta gaji da yin sallamar shiyasa ta yanke shawarar shigowa don ta ga ko bacci yake yi ne

  Tun kafin ta Æ™araso gaban gadonshi blue eye balls dinta suka sauka akan screen din Laptop nasa


  Ras taji gabanta yai mugun faÉ—uwa, zuciyarta tamkar zata faso Æ™irjinta saboda zafin da take yi mata, zeenatu tana da saukin kai sai dai tana da zuciya idan ta hasala, ranta ya 6aci sosai ganin abunda yake kallo, hoton da ta tsana a duniyar nan duk da batasan hoton menene yake kallo ba, ranta ya bata cewar budurwarsa ce yake kallo.

  

Idanuwanta sun makance, bakomai suke hango mata ba face dr shureim É—inta rungume da mace a kirjinsa.


  Runtse ido tayi da karfi ta fasa wata irin gigitacciyar Æ™ara wadda tayi silar firgitar da shi, da sauri Ya miÆ™e tare da wurga idonshi Kanta, tuni ta saki jakar hannunta Æ™asa, Zafafan hawayene suka wanke fuskarta.


   Hankalinshi ba Æ™aramin tashi yai ba, a hanzarce ya sauko daga saman gadon ya nufeta fuskarshi da alamun ruÉ—u ya furta"zeenatu! Lafiya? Meya faru?


  Girgiza mashi kai tadinga yi tana faÉ—in"kada ka matso kusa dani yaya shureim, inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un" gaba É—aya ta gama rikitar dashi"zeenatu ki natsu kiyi min bayani meya faru dake? Ko wani abu ne ya tsoratar da ke?


  Cikin shessheÆ™ar kuka tace"yaya shureim bazan Iya jurewaba, zuciyata zata Iya bugawa, tun É—azu mukayi magana dakai akan zamu fita yawo atare, kace min inje in shirya kafin in dawo kaima za ka shiga wanka ka kimtsa, ashe baka yi komai ba, ko wankan ma bakayi ba, ka zauna kana kallon hotonta saboda tafi ni mahimmanci awurinka, ba tun yau ba kullum ne saina ganka kana kallonta, wai wacece wannan ne? Dame tafi ni? Numfashinta na fita da hucin zafi ta Æ™arasa maganar, tare da juyawa  da gudu ta fuce daga É—akin nashi.


  Hankalin shi ba Æ™aramin tashi yai ba, idonshi akan bayanta harta 6ace ma ganin shi.


 Dafe kanshi yai da hannu É—aya, har cikin ranshi baiji daÉ—in kalamanta ba, baiso yai silar 6ata mata rai ba, duk da bai fahimci inda maganganunta su ka dosa ba, lumshe idanuwanshi ya É—anyi kafin ya ware su a hankali, yayin da zuciyarshi ke tariyo mashi furucin da tayi mashi, yasan bai kyauta mata ba, ta Æ™walla fa rai akan son su fita tun Jiya shi da kanshi yai mata alÆ™awarin yau zai É—auke ta a sabuwar motarshi su fita yawo.


  Cikin sanyin murya ya furta"am sorry my zeenat, " da sauri Ya nufi toilet don yai wanka.




 *Boss Bature✍️ Mu haÉ—u Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun Æ™addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuÉ—in*




First bank




3196407426, 




*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number É—ina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

No comments