Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Rainon Soja 27

 *🕊️RAINON SOJA🕊️*

*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*

                 27.

*Don Allah kar ki karanta wannan labarin
indai baki biya kuɗin sa ba . Ga masu buƙatar payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake.... Regular group₦500 Vip group₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*


Jiki na Rawa Ma'eesha ta matsa ga Henry tana dai dai ta kafaɗanta da nashi , ba iya jikin ta ba harta Zuciyar ta rawa yake yana Kyarma tare da bugun uku uku ji take tamkar Zuciyar nata zata tarwatse ta watso waje . Cikin Sanyayyar Muryar ta yana rawa ta furta “ Wayyo Uncle ba zan iya ba ”. Wallahi tun yanzu na gaji gajiyar moto ta ishe Ni ban ci Abinci , kuma barci zanyiiiii.....keee rufe mun baki!! Yayi maganan yana ɗaga Muryar sa wanda sai da Sojojin wurin suka shiga taitayin su . Ji kake tsittt tamkar anyi Ruwa an ɗauke . Wani irin jan numfashi Ma'eesha ke yi tsoro duk ya gama rufe ta.  Wannan yasata Fara ganin Jiri Jiri ......tamkar daga Sama take jin Muryar Uncle Haidar yana magana cikin sakewa tamkar bashi ne yanzu yake doka mata Tsawa ba . A'a mutumin kun iso . Yessss cononel da kan sa , Ina Ma'eesha take ne???. Jin baƙuwar murya wanda bata san shi ba kuma yana Tambayar ta yasa ta saurin juyowa tana cikin zazzaƙar Muryar ta ta furta “ Gani nan yallaɓai ta ƙare maganan cikin sanyi da neman agaji tamkar wacce ruwa ya kawo mata Wuya ”. 


Saurin kallon ta Canonel Areef yayi yana Furta “ Ikon ALLAH Girma ba Wuya lallai jiya ba yau ba , give me warm hug...! Yayi maganan yana ware mata hannayen sa , wanda da Sauri Ma'eesha ta nufeshi tana rungume shi tare da lafewa bisa jikin sa , a Zuciyar ta tana faɗin Allah yasa ya ceceni daga Hannun Uncle , Da'alama ya Sanni tun ba yau ba , Gashi da ganin sa zaiyi Rahma kaman ba Soja ba . Maganar take a zuciya kamin taji Muryar Areef yana katse ta tare da Ɗagota daga jikin sa yana furta “ Ma'eesha kenan , ma'eeshan Uncle Aliyu, Yana ji dake sosai na sani, Don a da baya kina yarinya shi yake Miki komai , baya taɓa yarda ko sami namiji ya rungume ki kamar yanda nayi Miki harta Ni kuwa , wanka komai shi yake Miki sosai yasha wahala akan..... It's Okay please! Ya isa Areef , yanzu mu wuce dai daga ciki , sai kaji meke tafe Dani. 


“ Aliyu ya furta yana katse shi tare da maganan yana kallon yanayin fuskar Ma'eesha wacce ta faɗa duniyar tunanin maganan Areef , Anya kuwa da gaskiya a maganar sa , Bai san yanda yake mun bane a yanzu , Da kuma ai abun da ya wuce ne🤗 ta furta a zuciyar tare da ɗaga kafaɗa alamun bai dame ta ba , Maganan ma bata yarda dashi ba . Da A yanzu nike shan wuyar kace i will definitely trust you for that , Amma kace wai shi yasha wuya akai na tabbas ƙaryata ka xanyi don Mami ke kulawa dani sai Ya Khalil . Duk mai Sona yaso ya Khalil shi ke kula dani yake So na sosai ...........“Ma'eesha!!! Muryar Areef ya katse Ta inda cikin sauri tace “ Na'am Canonel ”. No ki rani da Yayanki inda hali ɗauke Ni tamkar yanda kika Ɗauki Hausar i will be happy if you do that for me”. You are always welcome sir”. Ta furta cike da confidence ɗin nan nata . Shikam Ali caɓe baki yayi yana dalla mata harara a Zuciyar shi cewa yake “ See how she did like a brave girl , Amma Sam ba haka take ba, raguwa ce , Common running kasa ta yanzu zata fashe da kuka da yake hawayen basa mata wuyan zubowa ”.  Common baby let go in ”. Muryar Areef ya katse su yana riƙo hannun Ma'eesha tare da fara barin wurin yana nufar Masaukin sa da su . 


Mamaki ne ya kama ma'eesha ganin yanayin tsaruwar Musamman falon Canonel Areef tamkar ba'a wurin training ɗin sojojin yake ba . Ɗaga kan ta tayi sama tana kallon Hoton Areef cikin kakin soja inda yayi ƙyau Ainun, kana ta kalli Aliyu da suke zaune suna ɗan taɓa hiran su . Wow Uncle Areef you look so Gentle man , Kuma kana da kyau kaman ya Khalil 😄 . Murmushi Areef yayi kana yace “ Ko Ma'eesha yanzu a ina kike da karatu ?”. Yanzu ina M.S.U international school , I'm SS 1 student . Wow that's very good. Yayi ƙyau, me kike sha'awar zama a matsayin ki na mace nan gaba?. Yayi maganan yana kallon ta kana ya ɗan gyara zaman sa yana cewa “ No need nayi Miki wannan tambayar ba yanzu ba tukuna atleast sai kun kai SS2 kana hankali ya ɗan fara shiga ko?” . Shiru tayi masa tana ƙasa da idanun ta tare da wasa da dogayen yatsunta . A'a SOJA zata zama! Muryar Aliyu ya katse su . 


Soja? Areef ya furta yana kallon Haidar kamin ya kalli Ma'eesha yana furta “ Amma tsarinta bai kama dana macen SOJA ba . Just forget about that topic , Wani Soja barta tayi karatu har ta kammala secondary You will understand what I'm trying to say now”. Amma Sam bata yi kalan soja ba . Kalli yarinya the most cutest girl kace Wani SOJA ? Ko da yake ban sani ba ko itace ke da Wannan Ra'ayin ?.


“Ɗan kallon Areef Ali yayi kana ya kalli ɓangaren da Ma'eesha take , Yana mai cizar laɓɓansa na ƙasa tare da Ɗan taunawa kana yace “ No nike da Wannan Ra'ayin , Sannan abin da nake so dole tabi layin nan , Saboda Hatta numfashin ta nawa ne. 🤔kame baki Ma'eesha tayi a Zuciyar ta tana cewa “ Me yake nufi? Ai Allah ne mai yi ma mutum numfashi ba wani Ɗan Adam ba ”.  “Alright it's okay . Yanzu ina so ka fahimci Ma'eesha ba zata iya soja ba . Heeeeee!!! Keep standing don't move anywhere! Muryar Areef ya katse ta , yana sauya mata lokaci guda ya koma sojan da ya amsa sunan shi na soja , fuskar sa ya murtiƙe . Kusan mintina biyu tana ƙame kana taji ya furta “ Fara gudu ki dingi zagaye falon nan ina kallon time ɗin da zaki ɗauka har ki gaji, Oya start it now! . Da gudu Ma'eesha ta fara zagaye falon inda kaiwa da dawowa biyu tayi ta zube a ƙasa tana fara kuka tare da cewa “ Wayyo Uncles ba zan iya ba ,kuyi mun rai 😭”. 


Kallon ma'eesha duka suka yi , kana Ali ya kalli Abokin nasa yana mai sauraren Abun da zaice . 


Ka gani she can't be a soja at all , just ka barta a hanyar ta na ƴa mace , ka duba ko gudun minti ɗaya bata iya yi, Wannan zata fi dacewa da....... Enough 🙌🏻 , ya isa haka da ALLAH. Aliyu ya katse shi cike da ɓacin rai kana ya kalli inda Ma'eesha take Yana furta mu wuce masauki na . Yana furta zancen tare da miƙewa yana barin Falon . Kallon Areef Ma'eesha tayi kana tace “ Gaskiya kai me SO nane, thanks to meet you Uncle, ka bani Numbern ka don kana faɗa masa gaskiya ....Ga Wayata! Murmushi Areef yayi kana ya Girgiza kai yana furta faɗa mun number naki i will call later ”. Saurin Amsan wayar tayi tana loda masa nombobin tare da Ficewa da Sauri bayan ta basa Wayan tana bin bayan Haidar ”.

Post a Comment for "Rainon Soja 27"