Breaking News

Tantiriya a Gidan Yari Book 1 Paga 46-50

 TANTIRIYA 🏫

        A GIDAN YARI




BOOK 1  

              

                46-50



Official


By

AsmaBaffa 



Sadaukarwa gare ki

AIDA MAMAN TASNIM 



Page naku ne


Maman Afrah

Hajjafatty

Oummu Twins

Umu Afrah

My Num

Mom Twins

Ruky



Masu audio ban yarda a juya min novel zuwa audio ba Dan Allah.




Hey lovelies


Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?


Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?


Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?


Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?


Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din


https://wa.link/49vn47





     Direct gidan da Beauty ta basu address aka kaisu dake tayiwa masu gadi da kula da gidan magana suna knocking aka bude musu suka shiga har ciki aka musu iso,gidane na gaske part uku,ko Ina ya hadu sai kallo suke yi suka dauki daki daya su biyu,Beauty me dafa abinci wata yare Sheyi ta kira tace taje gidan anyi baki zata ci gaba da yin abinci,Sheyi sai gata nan da nan,Naila tace amma gidan nan ya hadu gaskiya Beauty suna da kudi wai dankari,Chikar gayu tace Allah ya azurtamu Ameen.

  Wanka Chikar gayu ta shiga tana fitowa Naila ma ta shiga tayi wanka suka fito suka shirya cikin kaya masu sauki sauki,Sheyi tana ta girki sai kamshi ke tashi,Naila tace Ina so na koyi girke girke na gargajiya dana zamani amma bani da lokaci,yanzu idan Spark ya aure ni me zance da shi? Chikar gayu tace wlh tun wuri ki koyi girki da zaman nan haka, me kike yi baki iya ba ai kuwa zaki ji kunya,Naila tace ai yanzu na dinga dan lekawa kitchen wannan Sheyi din ta dinga koya min ko zan iya.

    Ai kuwa lokacin Naila ta shiga kitchen,tayiwa Sheyi magana da turanci Ashe Sheyi ta iya Hausa ta gaske,Naila tace to maganar gaskiya Sheyi Nan da kika ganni hotiho ce,ta gina bata shiga bace ni domin kuwa ba uwar dana iya na girki gashi na samu mijin aure,ki taimaka Sheyi ki koya min su Amala irin taku da Sakwara,da miyar Ugu yake ko ogu oho muku,Sheyi da Ogbono Soup me yauki da dandanon sabulu sabulu haka,Sheyi tace Ogbno soup ce me dandanon Sabulun? Naila tace haka take mana miyar,da banku,miyar Egusi da sauran su,Sheyi tace ba matsala zan koya miki sosai,Naila tace na gode.

   Kamar abin arziki Naila tace ke Yoruba ce? Sheyi tace ae kina Kashi a leda ai ko? to gaskiya ki dinga tsaftacce muhallinki,Sheyi tace ai mun waye tuni wannan sai na kauye,Naila tace haba ko ku fa amma ododuwa ku dinga tafka Kashi a leda ba tsari ku canja hali wlh,abinda kuke yi bakwa kyautawa a kasar irin Nija Mama Africa uwar Africa gaba daya,yanzu dai ki koya min girkinki iri iri,Sheyi tace karki damu kyakyawa,Naila tace Allah me kika ce kyakyawa? Yes nah Sheyi ta sake tabbatarwa,Ya kika ga saurayina zai yaba? Sheyi tace ai ko waye shi karya ne ace bai yaba ba, Naila ta tsaya tana kallon girkin Sheyi tace Spark zan ci kudinka gani nan bisa kansu Ina iyo, Naila ficewa tayi ta tafi zaga cikin gidan tana Shan kallon haduwa,Chikar gayu ta Gani tayi waje ta fice,Naila tace halina da Chikar gayu rashin daraja gidan ubanwa zata je,kafin ta rufe baki sai ga Chikar gayu ta dawo,Naila tace Ina kika je? tace yawu naje na tofar wannan gidan ai yafi gaban a tofar Masa da yawu ko a toilet,Naila tace ke anya kuwa a birni kika girma,duk kyan gida Dan ubansa ki tofar da yawunki Inda kika ga dama amma banda gidan Spark,duk shegen da ya tofar min da yawu ko na juna biyu ne bazai Kara zuwa gidana ba,Chikar gayu ce tace zo muje mu Sha shayin Wiwi,Ido Naila ta zaro tace iskancina bana shaye shaye bane,a gidan yarin kika koyi Sha? Chikar gayu tace ae wasu ne suke dafa mana ta Katanga ake cillo mana da bushashen ganyen Wiwi muna dafa shayi,Naila tace baki da hankali Chikar gayu,kina mace wannan ai na Maza ne,Dan Allah mu Sam me zaku dinga kwaikwayo Kuna koya a rayuwa, Chikar gayu tace iyye ke wata ta kirki ce kin gwamitsa da kartai ba gwara mu ba,Naila tace Chikar gayu ki  kiyayeni aiki na kawoki ki min in kin gama Spark zai biya kiyi abinda ya dace za a biyaki,Chikar gayu tayi dariya tace cinikin biri a sama,dariya suka yi Naila ta furta gaskiya beauty tsakani da Allah tana shanawa Bata da Yaya bata da kani,Chikar gayu tana ji tace yo ai ni da babanta ma zai so ni duk katon cikinsa tarairayar kayana zanyi, Naila ta sheke da dariya,Chikar gayu tace wlh tumbin Baban Beauty bala'i wai gashi da cin tsiya yazo mana visiting watarana Kinga yanda yake cin abinci kamar wani zai kwace kamar ba me kudi ba, inda kisan kura, Naila tace ni bama haka ba sai hakoransa na tsakiya daya cire fafaroma, hakora dai suka fice yo ai ba daya bane biyu ne ko uku ya Ilahi nace da kudinsa ya sa na roba mana,Zo Kiga Beauty yanda take kuka tana ce Masa Daddy ni ka saka hakora wlh idan zaka ce s din nan dariya kake bani,Naila tace ke Chikar gayu da munafunci,to Kuma mu ai kowa kallonsa muke tsaf, ko zaren dinkin shaddar mutum ma sai mun kalla.


   Palo suka koma ta zauna Chikar gayu taje ta dafa shayinta na Wiwi ta dawo da abinta a cup,Naila tace shedan yau aiki zaibi ta kanka Chikar gayu kiyi Bismillah kafin Kisha shayin Wiwi din nan tunda shedan komai za aci sai yazo ya tsoma baki, Maza ki Masa bakin ciki kar ya Sha miki dadi,Chikar gayu tayi Bismillah ta fara kurba tace ai da ta hayakin nake Sha bazan Bismillah ba zan fara zuka sabo da shima shedan ya zooka ya shake a makoshi.


  Chika tana zuka Naila ta kwace ta hankade keyar Chikar gayu tace ke a gidan yarin har wiwi kika koyo sha? Da Allah ku dinga sanin abin kwaikwayo,mene wani Wiwi kina mace dan Allah ki bari ki gama min aiki na lafiya idan yaso daga baya ai Kya Sha abarki,taje ta zubar,Abinci suka ci sannan suka kwanta suna hutawa.

   Zuwa dare Sheyi ta Dora girki ta kira Naila tazo ta koya Naila ta shugo kitchen,tukunyar ta leka tace yawwa ai na gane wannan girkin miyar Egusi ce ko zamu yi,yawwa Sheyi idan kika wanke namanki sai ki watsa a tukunya Yana tafarfasa Yana zabalbala sai ki yanka albasa Sheyi  ki barbada curry da Maggi,Maggi ki samu me karfi yanda zai bada dandano,ki dakko manjanki idan ya daskare ma ba matsala duk daya Sheyi.....Sheyi ce ta tadakatar da Naila tace ni nake koya miki ne ko ke kike koya min? Naila tace kece mana ai practical nake,Sheyi tace ki tsaya ki koyi Abu idan kinki ke zaki ji kunya a gidan miji,Naila tace Allah ba yasa ba bakinki ya biki, yanzu na tsaya nuna min,Ehem haka zaki ce Yan mata,Sheyi ta shiga koyawa Naila girki har suka gama tare Naila ta gane yanda zata yin miyar da tuwo ko Sakwara ko Amala etc.


     Chikar gayu tana Palo tana kallon tashar wakokin Nija,a haka Naila ta dawo ta sameta ta zauna tare da yin shuru ta lumshe Ido tana Jin wakar tace na Lula tunanin Spark gamu can mun fito daga mota mun shiga shopping mall Yana rike da hannuna,gamu can na rakashi Office...muna soyewa a cikin Office,ya dannawa kofar key, yasa key Chikar gayu,gamu can ya kaini awon ciki asibiti mum fito a hadaddiyar mota,ya tafi dani aikin hajji,Gani ga ka'abah,daga can mun wuce America,laaaa snow.....na haihu a can mace na samu,Chikar gayu tana kallonta ta rufe Ido wai tunani take yi,daga Jin kida sai haihuwa Kuma,Naila tace baza ki gane ba,ni nasan me nake ji na rashin Spark Ina zan ganshi? 


    Ranar haka suka kwana Naila tana zancen Spark Ina zata ganshi,washe gari bayan sunyi Kari me kyau Chikar gayu ta dakko kayanta kodaddu jemammiyar atamfa riga da zani dinkin me Fadi ta saka tayi daurin zani me Bakin almakashi gefe ya zobe baya a dangale ta daura dankwali dan kanti, ta fito da kullin kayanta a leda viva ta rungume a kasan hannunta,tace to matar Spark kira Hajiya Tagwadas,Naila tace ai sai ta gane Kuma na fito a gidan yari.


   Nari kiji ta jawo wayarta ta kira Mohsin ya daga tana jinsa suna fada da Hanan ita magungunan basa yi ciwonta yaki warkewa ya maidata asibiti,Naila tace kaga kyale wannan banzar ka kira Hajiya Tagwadas kawar Umma kace address din gidan Mima kake so sun kiraka Abuja akan case Dina,Mohsin yace to ya kashe ya kira wayar Hajiya Tagwadas,tace Dana Mohsin Allah ya Maka albarka Dana Mohsin,Kuma gashi har yanzu naga Hanan taki ta sake haihuwa ko planning take ne?,Mohsin yace kaji gulma a ransa,a fili yace uhm Allah ne bai kawo ba,to Mohsin ko aure zaka Kara? Mohsin yace haka nace miki? a'a wai dama akwai wata ne da nake Maka sha'awarta a makwaftanmu Iklima yarinya me hankali,bana sonta komai hankalinta Mohsin ya furta yace address zaki bani please zanje Abuja an Gayyace ni akan case din Naila ance naje gidan Mima,gidan Ahmad Maleek,Hajiya Tagwadas tace to bari na turo Maka a rubuce ai yafi Mohsin Dan Albarka,yace Ina jira na gode.


    Mintuna kadan ta tura Masa a rubuce shi Kuma yayiwa Naila forwarding,Nan take ta mikawa Chikar gayu tare da kudi 3k tace ko me kika gani ki kirani,Kinga maganin nan dana baki ki tabbatar idan kika ji Ashraf zaizo gidan to kisa Masa a abinci yaci shike nan Hallare Kuma sai idan ni naga dama na tashe ta,Chikar gayu tace an gama zanci uban kowa,Naila tace kiyi ba komai yi nane ni na saki a kotu harda wani zuwa suna Jin sharia suna kallo aka daure ni,Allah ya tsare.


    Chikar gayu ficewa tayi daga gidan ta shiga taxi tabi address har kofar gidan Mima,aka sauketa taje tayi knocking,kofar aka bude ko Ina sojoji ne a gidan suna muzurai suna zare Ido,Chikar gayu ko jikinta tace da Allah yanlabai Wajen Mima aka turo ni,mutum daya ciki yace bari ayi mata magana aji, ya wuce ciki ya Samu Mima a Palo ta hakimce,yaranta duk basa nan sai Misam da ya dawo jiya daga Barikin sojoji, Yana zaune ya harde kafafuwa Yana kallo ba Wanda ke wa daya magana tsakanin Mima da Misam,Misam wani karkada kafa yake irin Wanda Jin dadi ya ratsa shi, fuskar nan a hade Yana ta fushi da alama fada suka yi da Mima,sojan ne ya shigo yace Ma kinyi bakuwa daga kauye tace turota akayi,Mima ta yatsina fuska tace Kai masifa wai ba anyi zakka ba an Kai, me suke nema Kuma?

 Kai kasar Nan tamu akwai masu matacciyar zuciya,let her in,ya fita ya koma,Misam yace Yan uwanku ne dai,au Kai banda Kai? Yace a'a Banda ni wlh na sansu ne,Kai fa baka da mutunci kaima,shuru yayi sai ga sojan ya dawo tare da Chikar gayu,Chikar Gayu tayi sallama tare da zubewa a gaban Mima ta kwashi gaisuwa,Mima ta amsa tana wani cin magani


    Meke tafe Dake waye ya turo ki? Chikar gayu wacce babu digon tsoro a fuskarta tace Hajiya Tagwadas ce tace kina neman Yar aiki Dan Allah Hajiya kiwa Allah ki bani ko me wanke kashin yara ce,ke ko naki ma zan iya wankewa,Da sauri Misam ya rufe baki Yana dariya kasa kasa,sai dai ki wanke na uwarki cewar Mima,Chikar gayu tace Allah ya huci zuciyarki tuba nake sarauniyar dattawan Abuja,Misam ya sake rike dariyarsa da kyar Yana kulle bakinsa da hannu,mikewa yayi ya shiga kitchen ya saki dariyarsa ya dinga dariya Mima tana jinsa taga abinda yake yi,sai da ya gama ya maze ya fito harda daure fuska ya sake zama.


      Mima tace zan daukeki kinci darajar mutanen kauyenmu suna da alheri, amma sai dai ki shiga cikin masu girki,Chikar gayu tace na gode Allah ya Kara girma dama Babana ya sa min albarka, shi yasa duk Inda naje ko badan Allah ba sai an amsheni hannu bibiyu,Misam yayi sauri ya dauke Kai zaiyi dariya,Mima tace zan koreki wlh wai wacce irin yarinya ce ne ke? Ko Yar kunya ta mutam kauye babu idonki a soye,Chikar gayu tace sorry Mima Tsohuwar Yar Wiwi ce ni yanzu Allah ya shiryeni to chajin ne bai gama sakina ba,karki damu na daina yanzu a hankali zata sakeni,shi yasa na fito neman na kaina,Misam Yana ta dariya ya dauki magazine tare da kare fuskarsa wai kar Mima ta ganshi,tasan me yake yi jaridar ta fisge ta kwala Masa a jikinsa tace tashi ka tafi gidan uwarka, Chikar gayu tana zaune tana satar kallon Misam wani kyakyawa da shi hadadden gaske sai kamshi yake, shi Kuma ko kallonta ma baiyi ba,Chikar gayu tace Masa Ina Kwana? Yana kwano ya furta ba tare da ya ko kalleta ba ya mike ya fice abinsa,Chikar gayu da sauri ta bude ledarta ta dakko biro da Dan littafi ta shigar da sunan Misam ciki ma'ana ta rubuta a gaba tace tarbiyya dole Kaine zaka fara karbanta. 

   Mima kallonta tayi tare da Jan tsaki ta mike tace kice a nuna miki wajen Yan aiki ki koma can,Chikar gayu ta sake rubuta Mima a littafinta,Bata tashi a wajen ba Yan gidan suna ta shugowa daya bayan daya ba Wanda ma ya kalleta,ita Kuma sai aikin rubutu take.

  

    Naila kuwa Beauty ta kira tace motarfa? tace bari a kira Daddy ya turo driver ya dinga koya miki Kinga ai zaki San gari sannan ki fara zuba wanka.

  Naila tace an gama,a ranar kuwa driver yazo ya fara zaga garin abuja da ita Yana koya mata sosai,Naila sai murza kan mota akeyi kamar ta Ubanta,ko wanne namiji ta gani sai ta kalle shi tace to ko Spark ne wancen oho.


    Spark kuwa an taho zance wajen Jamilu,Yana sauka drop motar airport ya dauka zuwa gidan yari,Yana zuwa ma'aikata suka dinga murna suna tarbarsa,suka gaisa tare da tambaya oga ya akayi ne wajen wa kazo? Yace Jamilu Tantiriya nayi mantuwa ne a hannunsa,ma'aikatan suka ce tab ai kuwa Jamilu baya gidan Nan ya gudu rannan baka ga abinda ya faru a labarai ba ai yana daga cikin Wanda suka gudu,kuma mun samun labarin ta gudu wlh an duba file dinta ko sama ko kasa an rasa shi so muke aje gidansu a nemota amma abin ya fassakara,ga wani mummunan laifi data yi wai Ashe Jamilu macece,haba ana fada  nace biri yayi kama da mutum, dukkan ma'aikata mamaki suke yi Jamilu ashe macece,Yan gidan yari Maza basa so a fada amma ta riga ta furta da kanta sanda zata bar gidan yari a kunnen wasu ma'aikatan ta furta,yanzu baka San kowa na Jamilu ba? Spark yace Innalillahi wa innailayhirrajun,sai da ya maimaita sau uku yace yanzu Ina zanga Jamilu,na gama sanin nine nan zan taimaki Jamilu ya fita,kash wannan taurin Kai da me yayi kama,sai kaje yanlabai ka ajiye mana number Dinka idan an sameta sai mu kiraka,Spark ko magana baiyi ba ya Bada number ya basu kudi yace duk Inda Jamilu yake a Nemo shi,suka ce ya zama dole ai kotu za a koma a Nan za a bibiyi Inda dangi suke,Spark yasan Naila baza ta kamu ba Kuma baya fata a sake kamata ma, jiki a sanyaye ya juya tare da shiga mota sai airport ransa a mugun bace idonsa yayi ja sabo da bacin rai,Naila sai yau ta taba nata Masa rai a rayuwa,a cikin jirgi sai huci yake shi kadai kowa ya kulashi sai masifa,yace wlh dole sai na aureta ashe dama ba Sona take ba ohhhh ya ja tsaki tare da dafe Kai haka ya dawo Abuja,gidansa ya wuce direct ya kulle kansa a daki Yana ta faman bakin ciki wayoyinsa ma kashe su yayi gaba daya har tsawon kwana uku,Naila ita kanta tunanin Spark take har ta kwashe kwana uku a Abuja Chikar gayu ana gidan Mima ta rasa ma ta hanyar da zata yi maganinsa sabo da su basa ko bi ta kanta,Naila tana kwance a gida,Chikar gayu ta kira waya tace ke naji wata a gidan yau tace Ashraf zaizo,Naila tace yawwa ki shirya ki sa Masa tace angama,sai da aka gama girki tas sai ta dawo kitchen din Mima ta buya,bata Dade ba spark ya shugo duk ya fita a hayyacinsa,sama ya hau wiurin Mima,Yana shiga Mima tace ya na ganka haka kamar baka da nutsuwa? Kamar baka samun bacci ma lafiya Spark? fuska a hade yace ni dama tambaya ce ta kawoni,Mima tace to Dan Jarfa ko gaisuwar ma babu? Yace ni tambaya nazo yi amma dai Ina Kwana? tace lfy Alhmdllh Ina jinka,yace da karfe nawa kika haifeni? da rana,ko dare ko safe? Mima tace menene? Nifa kawai tambayarki nayi please,Mima tace da safe na haifeka Kuma ranar juma'a yace to ya aka yi bani da albarka an haifeni ranar juma'atu babbar rana da safe Bada duhun dare ba Kuma ace ni komai nayi bazai tafi dai dai ba a soyayya,Mima ta kalleshi tace Allah ya shiryeka,yace Ameen a haihuwata kuwa an samu alheri anya? Kuma kin samu kayan barka?dariya Mima tayi tace to haihuwarka tafi ta kowa wallahi Nasha kyautar da har na mutu bazan manta ba,Baki Spark ya tabe yace uhm bada zuciya daya suka bayar ba to,duk yanda akayi cikin biyu akwai Daya ko dai an sa min kayan Haram a jikina ko an ci Dani da Haram ko Kuma ba a yanka min ragon suna ba,idan kuwa anyi min hakika an yanka rago to ragon Nan na sata ne aka siya ba a sani ba,wani ne ya sato ya siyar muku a kasuwa aka yanka min,amma in ba haka ba taya za ayi Jimiluta ta gudu ai na tabbatar tana Sona ta ya za ayi haka,gaskiya Ku bincika ko Kuma Papa gaskiya ya manta baiyi addua ba a daren....Mima ce tace baka da hankali Spark,Ashe ta tabbata namijin kake so da gaske oh ni dai na shiga uku da wannan jarabawar rayuwa,Spark yace ai taki jarabawar kadan ce Mima idan aka hada da tawa ya furta a sanyaye yace ku kunci duniyarku da tsinke mu kuwa har yanzu rako muka yo.


  Kullum sai nayi zazzabin dare, Mima tace ba dole ba tunda kaki aure ai dole kayi zazzabin dare abinda ma yafi zazzabi zaka yi tunda ba mace,Spark yace Kai Mima a dinga sakayawa karki Ganni yaro nasan komai,tace uhm naga alama ai muje to wlh yau sai Kaci abinci a gidan nan ko naci ubanka,yace uhm Mima a daina kalamai haka a gaban yara,kawai Mima ta kalle shi yanda ya juya mata magana Kuma kamar ba shi ya fada ba sai ya fuske abinsa,haka suka fito ta taso keyarsa gaba,tace Dan Allah kayi sauri wannan uban gadarar taka ni bazan iya ba.


  Chikar gayu ta kwalawa kira wai Chika...Chika...tana boye a kitchen tace gashi Nan a dining ya fara dashi kafin na fito,a ranta tace Allah ka bani sa'a a kansa yaci, ta zubo abinci me Dan ruwa ruwa ta zuba magani ta kawo dining ta koma kitchen ta buya,Spark sai gashi sun fito da Mima tana cewa muje muje Kaci abinci wlh ko naci mutuncinka,Spark ba yanda zaiyi yazo ya zauna Mima tace ga wani nan ma dauki Kaci ai kana son dankalin turawa gashi Nan yasha hadi,Spark badan ya so ba yaja plate gabansa ya fara antaya girki a cikinsa,yaji ya masa dadi ya cinye tas yace a karo,Mima taji dadi ta kwalawa Chikar Gayu kira Chika fito ki karowa Dana abinci, Chikar gayu a ranta tace sai kace wani yace dansa ne wai Danta,bari dai naje naga uban waye Ashraf din ne, ta fito tazo gaban Mima,Spark ne ya dago a hankali ya Kalli Chikar gayu itama ta kalle shi,yace ke ba kece ta prison ba? Tace ae nice ba dai Kaine Ashraf ba? Spark yace nine mana Ashraf amma amfi sanina da Spark,Chikar gayu nan take ta fara hada zufa tace a ranta Naila ta kashe Halleren mijinta ta shiga uku,a gigice taje ta karo Masa ta same su Yana bawa Mimi labarin Chikar gayu yanda ya fitar da ita,daga Nan sai taji tana kaunar Chikar gayu,a ranta tace dama ita na aura Maka  ba komai bari na tambayeta naji.


  Chikar gayu Kuma da gudu ta fece daki ta kulle sannan ta kira Naila tana dagawa tace aiki ya Baci.

  Me ya faru ashe Ashraf shine Spark,Naila tace ban gane ba,wlh Ashraf din shine Spark Wanda kika ce na sawa magani Kuma na saka ya cinye,kizo kofar gidan idan ya fito ki ganshi da idonki,Naila tace gani Nan,motar su Beauty ta dauka hannunta ko kwari baiyi ba haka taje har kofar gidan Mima,tana zuwa tayi parking a baya can ta tsaya,sai ga Spark kuwa ya fito driver na jiranshi a waje da mota,gaba daya tunda yaci abincin yake Jin Hallere dinsa tayi kwanciyar mutuwa,shi dai yasan a mike yazo gidan Mima da abarsa managarciya ,haka dai ya shiga mota a gaban Naila,suna tafiya Naila ta kira Chikar gayu tace fito Dan uwarki fito waje Ina jiranki.


   Chikar gayu tace gani Nan ta fito,Naila ta fito daga mota tace Amma Chikar gayu ke ba karamar matsiyaciya bace mutumin Nan Kinsan saurayinane zan aura kika kashe min Hallare yanzu Bado shike nan bashi da Besty, wayyo na shiga uku,,Yar iska mahaukaciya baki da hankali baza ki leko Kiga waye Ashraf ba sai ki sa Masa magani,Chikar gayu tace ah haka fa kika umarceni dama duk marar hakuri da son ramuwar gayya ai Yana tare da haka


   Naila hannaye ta Dora a kai tace Ina mafita Hallare ta shiga jalala dole fa sai na sake Masa magani wannan Kuma sai na ganta da idona,Chikar gayu tayi dariya tace ah ai a dadinkinki ke da kanki zaki shafa mata maganin ko kuwa? tsaki Naila taja ta shiga mota tana furta ta kwabe ba kanta na kashe kaina,sai ta fisgi mota kamar wata gwana tana cewa na kan hanya ya matsa ko azumi sittin ya hau kaina yau.


    Hawaye ta fara tun a mota tana Tausayin Spark dinta ta manta ma da shine fa Ashraf,motar tasa tabi sosai Allah yasa ta hango su ya dauki hanyar gidan Mummy duk da ba wani gane hanyoyi take ba sai da tambaya take iya zuwa waje,gida ta koma a hanyar gidan ma sai data bata,tana komawa kaya ta canja ta zuba sabuwar shaddarta me tsada a gurguje ta saka hular gashi me kyau dogon gashi ta daure da ribbon kamar nata ya zubo kadan a gefen fuska ta shafa powder da jambaki pink dama shaddar pink tayi kyau duguwar riga me aljihu ta Sha dinkin zamani ta dauki takalmi da jakarta silver ta yafa mayafi ta fito tare da Maka glass dinta a fuska ba karamin kyau tayi ba babu Wanda zaice Naila Jamilu ce zaka rantse Yar gidan wani ce,Mota ta shiga da sauri tayi hanyar gidan Mummy ko zata ga Spark a can da kyar ta gane gidan, Parking tayi a waje ta fito tare da yin knocking aka bude,suna Ganinta kamar Yar me kudi sunga tazo Kuma da mota tana karkada key sai masu gadi suka bude mata ana cewa sannu da zuwa Hajiya,Naila hannu kawai ta daga musu ta wuce ciki tana Izza tana karkada key.


    Palon Mummy ta wuce direct taji Muryar Spark Yana cewa Dan Allah ku kyaleni naji da abinda ya dameni,budurwata ta bace na rasa Inda zan sa kaina amma ke da Mima sai zancen wani aure kuke min idan so kuke na bar duniyar ba sai na mutu ba kawai wannan wacce irin rayuwa ce,ko Dan halinku ma wlh a Hana mutum aure,ni nasan halinku ne ke biniyata,Mummy tace nayi shuru tunda Kai sunna ce baka so ka raya,yace sanda zan raya sunnar Kun ma sani ne ni ku rabu dani Dan Allah, wlh in na gaji zan bar muku kasar,To ubanmu cewar Mummy.


   Naila ce ta makale Murya ta koma ta Yan gayu masu yanga tayi sallama a hankali,Mummy tace shugo ta zaci kawayenta ne sai taga wata Yar Gayun,Mummy tace wannan ko Yar film ce ne sai naga kamar na Santa,gaskiya sai dai idan a film nake Ganinta,Baki ta washe tace shugo mana Baby,Naila ta shiga tana kallon Spark da yaki dago Kai ya kalleta kawai waya yake dannawa,ji take kamar ta fada kansa ta cinye shi tayi missing dinsa matuka,wuri ta samu ta zauna,sannan tace Ina yini ta gaida Mummy da ladabi,mummy ta amsa tana ta wani fara'a tace kamar na sanki a wani film, Naila tace Ohhh Ashe kin gane ni tabbas nice cikin wani film YANKAN KAUNA ko? Mummy tace wlh na manta sunan dai ni dai nasan tabbas na taba ganinki a film,Murmushi Naila tayi kadan tace ae tabbas ai sunana Nasiba Yankan kauna Dake a film din nayi tashe duk da cewa nayi films da yawa,Mummy tace ikon Allah kice duk su Alihu kin sansu? Naila tace laaaa ai yau ma aikinsa zamu fita wani film dama location muke nema me kyau to sai muka ga gidan Nan yayi mana to shi yasa nazo neman izini ko kudi ne zamu biya,Mummy sarkin son wayayyu tace nooo ba sai Kun biya ba kuzo ku fara idan ma zaku dinga kwana ba matsala,Naila tace watarana dai ni zan dinga zuwa Ina Kwana kafin a fara film din sabo da na gaji da zama a hotel sai a dinga ganinka kamar baka da mutunci da kima.


    Mummy tace ba damuwa idan da wasu duk ku taho akwai abinci da komai baku da matsala.Naila harda zamewa daga kujura tace mun gode Umma,Ai mummy ake ce min Umma ai sai Yan gargajiya cewar Mummy,Naila tace gaskiya fa sai local mutane Ina yinki uwar dakina,Spark Muryar ce take Masa gizo a kunne sai yaji kamar yasan Muryar,kallon Naila yayi yaji kamar Jamilunsa wlh,amma ai Naila bata waye haka ba,Yana ta kallonta a sace duk ta rufe fuska da gashi da glass ya kasa tantancewa amma wlh kamar Jamilunsa,Mummy ce ta mike tsam tace Nasiba Yankan kauna bari na kawo miki abin motsa baki,Mummy tana tashi Spark ya mike zai fita Naila ta kurawa saitin Hallarensa Ido,kallonta yayi yaga ta kurawa jikinsa Ido,fuska ya daure kamar bai taba dariya ba,yace ke lafiya? Ina Naila ai ta Lula kallon Hallare ya ta koma,yace ke wai baki da hankali ne me kike kallo,Naila tana kallo tace wait sir, are you out of your mind? are you normal? Naila tana kallo tana matsawa tace Sir sorry Ina bada magani baka da lafiya,abarka bata aiki,Spark tsaki ya ja ya juya ya fice Naila ta tsaya a palon tace yaki ya bari a gani amma ba komai dole sai na ganta bari naga gidansa.


   Ko Mummy bata jira ba ta jira ba ta fice ta shiga motar tabi bayan motar Spark amma Ina motarsa ta bace mata gidan Mummy ta koma,tana shiga Mummy tace Ina kika shiga ne? waccen Dan naki Aljanu sun aure shi bazai taba aure ba sai Kun tashi tsaye Mummy tace ke Dan Allah wlh anyi anyi yayi aure yaki baya son ko wacce mace,Naila tace sai an Masa maganin aljanu Kinga ni yae film ce amma Ina Bada maganin aljanu,Mummy tace wlh indai zai warke ba matsala bani da burin da ya wuce naga Spark Dina yayi aure,Naila tace dole sai na tare a gidansa idan ta kama har kakana zan kawo ayi Masa magani,Mummy sun matsu Spark yayi aure suka ce ba komai kawai zan Masa dole ma ya bari ayi Masa magani.


    Naila a ranta tace oh na canja shigar Maza nazo Dan na samu shiga karshe na fada prison,gashi yanzu a banza nazo a Yar gayu sun yarda dani Kuma,Mummy tace idan zaki iya farawa to gobe ki ajiye film din nan Ali nuhu ya canja wata idan ya warke kina da 1million,yanzu zan sa a miki kudi dubu dari biyar a accnt in kin gama aikinki zan baki cikon kudin,Naila tace an gama yo film din banza na fada masa ya nemi wata suyi rawarsu,gobe zanzo ki kaini gidan da kanki,Mummy tace ba damuwa,Naila tace karfa ki Ganni da shiga me kyau wlh bani da wani kudi mu kin san harkarmu ta celebrities haka muke da karya da fake life amma idan kika ga gidanmu kare bazai shiga ba,Kinga Ina Hawa mota na gyara jiki na sa kaya masu kyau to da cuta zata kamani shike nan sai dai aji ana neman taimako a gidan radio,Mummy tayi dariya tace ai mun sani dama.


   Naila ta gama ta fito tace yanzu ta spark nake tukun kafin na dawo kanki,wai dama Ashraf shine Spark amma ba karamin munafuki bane Yana jina Ina nemansa Ashe shine ya min banza sai ya gane kurensa tunda ya raina min hankali bazai taba gane ni Naila bace sai na sake cin tudu biyu a soyayya,tunda ya Soni a Yar gidan yari to yanzu Kuma zai Soni a Yar gayu.


   Ashraf Kuma tunda ya fita yake tunanin wannan yarinyar yace anya kuwa wannan bata da hadi Jamiluna,bari Allah ya hadamu idan da rabon na sake kallon Jamilu timbir ai shike nan,zata gane kurenta duk gashin Nan sai na cire shi in na samu dama ai nasan kalar boobs din nata da can wajen Garejin, ai nafi tantancewa idan na sake gani,murmushi ya saki yace Allah ya sake hadamu wayo zan mata.


    Yau kwana yayi da farin ciki da murna yaga me kama da Jamilunsa,Allah Allah yake su sake haduwa,Naila ma tafiya tayi taji dadin ganinsa Kuma ta fahimci bai ganeta ba,ga kudi zata samu nan take ta bugawa Chikar gayu waya tace ki bar gidan Mima kice za a miki aure ki dawo gidan Mummy ki dinga hada mata tuggu kina gana mata azaba,Chikar gayu ita kaunar Misam tuni ta kama ta ma, bata yin abinda akace tayi iskancinta kawai take a gida,duk abinda akace tayi ba shi zata yi ba ta buwayi kowa ta gallabe su,idan akace ta soya dankalin sai ta soya doya,in akace kosai sai tayi yamballs,kowa yanzu tsoron sata dafa Masa Abu yake sabo da an San ba shi zata kawo ba anyi anyi bata ji,Misam dinma bai san me take ba domin bai cika zuwa gidan ba.


    Chikar gayu tace ni bazan koma gidan wata ba na Saba da Nan gaskiya ni nayi miji sabo da haka a gidan surukaina nake bazan zubar da damata ba,Na hadu da wani cool guy,kije kiji da aikinki nima nawa nake yi, Naila tace ba komai wlh sai nazo gidan na tona miki asiri,Chikar gayu tace ba komai nima Ina ji da nawa ai iya shegen sabo da haka na gani Kuma na yaba,Kuma tunda na kulla Masa sai na aure shi inshaallah,kin fasa basu tarbiyyar? ae na fasa idan na aure shi nafi bashi da kyau ,Misam ne ya shugo gidan sanye da yard me tsada fari yayi kyau,Chikar gayu wayar ta kashe ta kalle shi ya galla mata harara,tace an musulunta ashe yau anje masallaci,ashe kana sallah ai ban sani ba,Rafeeq ne ya shugo Chikar gayu ta gane shi sai yau ta ganshi a gidan tace ai da Gani ba tambaya kaga munafuki dama shima a nan yake,kafin Rafeeq ya kalleta ta mike da gudu ta fada kitchen tana cewa shinkafata zata Kone, ba girkin da take yi,lekowa tayi kadan suka yi Ido hudu da Rafeeq Baki ya bude zaiyi magana ta hau rokonsa da hannu yayi shuru kar ya fada tana nuna Masa yayi shuru da hannu,Baki ya tabe,Misam yace ke kawo mana abinci Yana harararta.


   Chikar gayu ta shige tana dube dube sai ga kyankyaso kato ya  fito daga cikin wani lungu, da sauri tasa tsinken tsintsiya ta tsire kyankyason ta dora a plate ta rufe ta fito kamar abin arziki tace sannunku ta ajiye a gaban Misam tace gashi tana yin kasa da Kai,Misam yunwa yake ji Yana bude plate yaga katon kyankyaso a soke a Jikin tsinke,mikewa yayi Chikar gayu ta mike tare da kwashewa da gudu ya ya bita suka yi waje da gudu,tsayawa yayi yace sai na harbeki idan na sake ganinki Yana huci,ya dawo ya samu Rafeeq ma ya fice shi Yana jinjina rashin Jin Chikar gayu.


    Yau cikin dare Umma ta fara nakuda,Abba dole ya farka daga bacci,Umma tace Ina Jin haihuwa ce tashi ka daukeni na rasa Inda zan saka kaina,Abba yace da wannan uban cikin kamar zai taba kasa ga kibarki ta ya zan iya kalleni fa sai kace kazar mayu,Umma tace wayyo bayana ka daukeni Hashimu kaji na fada Maka,Hashimu yayi yayi ya daga Umma ya kasa,Umma haushi yasa da ciwon nakuda ta mike zumbur ta dauki Abba Dolo cak ta jefa shi a Saman bed tana masifa,Abba yace na zaci ma shillo shilloriya zaki min ai da naji dadina,Wani takaici ya kama Umma tace ni mu tafi asibiti,Abba yace yanzu karfe 1 na dare a fita yanzu,Kai dalla in zaka samo me napep ka samo,Abba ya tashi ya fice ya bugawa makwafcinsu kofa yana da Napep ya fito yace Hashimu lafiya? Wlh iyalina ce zata haihu take ta nakuda shine za a kaita asibiti,makwafcin yace Allah sarki ai da ka iya tuki ma da na baka ka kaita kawai,Abba yace ni da ko Keke ban iya ba bare machine ko wani Napep,tunda kake ka taba ganina a kan Keke Ina tukawa, Ido makwafcin ya zaro yace Hashimu duk kiriniyar Yaya Maza suna yara amma baka iya ko Keke ba,Hashimu yace ai ko kyauta ka bani mota sai dai na siyar bazan iya tukawa ba.


     Makwafcin key ya dakko yace muje amma Kai mace ma ta fika kwazo,Abba yace hmmm rabani da tuke tuken nan bazan iya ba Allah na Gani ai sai na manta na taka birki a matsayin totir ko naje na daga hand break din mota a tsakiyar titi,Makwafcin yace amma ka cika lusari ,yace Kun Dade Baku fada min lusari ba ko Dolo dama ni nace muku ba Dolo bane ni?,Shuru mutumin yayi yace ni Ina mamakin ma da Kubra take iya rayuwa da wannan Hashimu,Hashimu ya shugo Palo yace to taso uwar biyu,taka a sannu,Umma ta mike da kyar ta nuna masa kayan haihuwar data hada tace dauki muje Dan Allah kayi sauri wayyo Allah marata faya ta fashe,Abba yace Allah yasa fafunga ce ta fashe ba faya ba,ko kogi ne ya tsage kin isheni da kwailo, Allah yasa na kusa Kara aure Batoola tana nan dai tana jira,Umma dakin su Hidaya ta leka tace ke Hidaya,shuru,zafin ciwo yasa ta dirkawa Hidaya duka tace tashi ke mun tafi asibiti kuyi min addua ki tashe su kuyi Nafeela da addua,Abba ya leko yace ku hada Dani, Hidaya harda kuka tace Umma zan biku,Abba yace harkar bata yara bace ku zauna ni na isa komai,Umma Mohsin ta kira bugu daya ya daga dama sabo da cikin Umma ya tsufa shi Kam kullum a ready yake,Yana ganin kira ya daga,kasa magana tayi ta rike ciki tace wash,Abba ya karbi wayar yace Mohsin Umma haihuwa ka taho asibiti Maza private Kuma zaka biya,Mohsin yace to wanne? Abba yace asibitin Uba,Mohsin yace banji ba me? Abba yace faya ta fashe faya sauri muke ya kashe wayar.

 

     Umma ce zata ruko shi ya kwace da sauri tare da daka tsalle ya koma gefe yace bazan manta yanda kika kusa kasheni ba a haihuwar Hidaya,muje Ina daga baya baya,Umma ta shiga napep tana wash tana cijewa,Abba ya shiga gaba wai Dan kar ma ta ruko shi taje ta shake shi,Umma ita kadai a baya tana ta Jin jiki,Mohsin zai fito ya saka kaya Hanan tace wlh ba Inda zaka ta rike shi Yana Juyowa ya kwada mata Mari ta sake shi ba shiri yaja tsaki ya fice abinsa ya hau machine ya dinga fyalla wuta,Yana kiran Abba yaji Ina suka nufa Abba sai fada Masa yake Mohsin faya ce ta fashe,Sai me napep dinne ya kwace wayar suka yi magana da Mohsin sannan suka wuce private hospital,kafin suje ma Mohsin ya riga su zuwa har ya biya komai ana kawo Umma Mohsin shi ya rike Umma ya shigar da uwarsa har ciki,ya kira Hanan yace ki shirya zanzo na daukeki,tace ni bacci zanyi sanda na haihu ni waye yazo min,dama nifa gaskiya wayata da aka sace min da kayan sawata Ina zarginka ko Kaine ka kwashe ka kaiwa Hidaya,wayarsa ya kashe kawai ransa a bace,ya kira Hajiya Tagwadas kafin ma yaje ya dakkota har tasa an kawota a Napep dinta da ake mata haya,Abba dake asibitin private ne Yana ciki,ance ya fita yaki yace duk haihuwar matata tare muke yi bazan fita ba.


   Batoola kuwa an daura mata aure Abba bai ma sani ba shi kuwa Mohsin har daurin aure yaje amma yaki fadawa Abba suka barshi Nan Yana jiran Batoola,sun hada baki akan kar a fada masa Batoola tayi aure sai sanda ya koma zance yaji.

   Ana ta jiran Umma ana mata addua Abba yana ciki tare da Hajiya Tagwadas tace Dan Allah Hashimu ka fita ka bamu waje wai me zaka gani ne wannan masifa da me tayi kama Kai ko kyankyammi baka yi? Abba yace gudan jinjina da Rabin raina Umman Mohsin na fita na barta ai bazai yuwu ba Sam,haka aka kyaleshi,mata suna taimakawa Umma ana kokarin fiddo da Baby Hashimu yace kar ku kashe min dana wlh karku soma.


     Allah yasa dai Umma ta haifo yarta mace kyakyawa da ita kamar Yar Mohsin da Naila suna kama,Hashimu bayan an goge jajirya katuwar gaske aka miko Masa yace macece bazan Kalli tsaraicinta ba ku nadeta a zani,haba ai ba tsari na Kalli na uwa na Kalli na 'ya, aka nadeta tare da Mikasa duk ya dame su a dakin,ya karba ya mata adduoi sosai a kunne sannan ya taba kumatunta yace.. Yan... Yan.. Yan kin ganni sunana Abba,Hashimu ne idan kin girma zaki ji inkiyata mummuna wacce baza ta miki dadi ba Hashimu Dolo,Nurses sai dariya suke kamar me, Mohsin Abba ya kawowa Yar Yana cewa kaga kanwarka ya ka ganta katuwa kamarku daya,uhm ansha warin gardawa a ciki da Wiwi Allah sa kar ta samu cutar warin Kashi,irin wannan wari data shaka tun tana ciki sai addua,Mohsin shi kansa Abba dariya yake bashi sai kace a kanta aka fara haifar Masa yara,sai murna yake yace sai nayi sati guda ban siyar da kayan Miya ba sai bayan suna,Mohsin yace Allah ya kaimu shima yayiwa kanwarsa addua sannan yace ya Umman Abba? garau take da ba lafiya ba ai baza ka ganni a waje ba,Mohsin a ransa yace ta wani fannin Uwata tayi dacen miji.


     Naila washe gari da wuri taje gidan Mummy a taxi da katuwar akwatinta zata koma gidan Spark da zama,Mummy tace gaskiya na yarda da gaske kike harkar nan,Mummy ta shirya cikin kana nan kaya matsatsu ta yafa Dan guntun mayafi tace muje,Naila ta zaro ido tana kallon Mummy a ranta tace tab,motar Mummy suka shiga,Mummy ta tuka suka nufi gidan Spark, Yana bacci kasancewar ba aiki yau Sunday, har gidan Mummy ta murza hancin motarta ciki, bayan tayi parking Naila tace nazo gidan mijina gidana,tana kallon gidan tunda take bata taba ganin gidan da ya tsaru haka ba sai yau a gidan spark,gidane Wanda an kashe Masa kudi iya kudi,ko da ya fito daga prison sai da aka sake canja kusan komai na gidan, ga motocinsa Nan masu tsada iri iri, duk Inda ake neman gida to gidan Spark ya Kai,Spark ne ya fito Jin mota ta shugo Masa gida,Sanye yake da gajeren wando baki da Yar tshirts brown ba karamin kyau yayi ba duk kuwa da cewa daga bacci ya tashi.


    Naila ya kalla ta canja glass yau tasa brown ya mata kyau,sanye take cikin atamfa riga da skert sun masifar mata kyau,ga gashin ya yarfo a fuskarta ta yafa mayafi kawai ba dankwali a kanta mayafi ne a Saman kanta,Spark dariya yayi a ransa yace haba yarinya sai dai kiwa wani basaja ba ni Spark ba,yace wannan karya ne Naila ce yace ni da na zauna tare da ita mun kwana bed daya ma lokacin tana Jamilunta,Bata gaji da wasan nan ba lallai yarinyar nan yarinyar nan da taurin hanci take,Ashe da rabon zanyi kallo na biyu kenan,murmushi yayi a fili tare da danne lip dinsa na kasa da hakoransa na sama,ya Bata rai yace wannan fa, good day sir cewar Naila tana wani sirara Murya,kallonta yake sama da kasa murmushinsa ya kasa boyuwa yace ashe dai Yar wanka ce ko Kuma basaja aka dawo yi min,Mummy tace gata nan zata zauna da Kai zata dinga Maka girki,sabo da kana zama da yunwa ko ka dinga yi da kanka Ina raye bai dace ba,shi tun da ya yaji zancen yasan da wata a kasa Mummy ita tasan me Naila ta fada mata,Kuma shi yasan Naila dai zagin Ashraf take zata dauki fansa kenan ya furta a ransa,wow wannan yarinya amma zan bari naga ni me zata min ta dau fansar ita Kuma Mummy idan bata yi wasa ba kwana nan zata shiga prison domin indai ya tabbata Naila ce wannan to wlh ko makawa babu fansa tazo dauka,Mummy Taga Yar gayu ta yarda da ita Kai duniya,da wani bagidajene yazo baza ma ta kula mutum ba,shi sai yanzu ma ya gano bakin zaren,yace lallai yaro yaro ne Kuma mace mace ce tab,zanga ni ya za ayi dani.


   Spark shi bai San tuni ma Naila ta kwantar Masa da Hallare ba yanzu ma magani tazo ta Masa ba tare da ya sani ba shine dalilin zuwanta gidan, shi Kuma yace dole nayi taka tsan tsan da Jamilu yanzu haka ma tunda ta gano nine Ashraf to ta daina so na tabbas,amma bari na gani ya zama dole na kula da me zata yi sannan na dage da addua Allah ya rabani da Sharrin Naila ta shiga bani tsoro,ashe da gaske take, jikinsa ne yayi Sanyi sannan yaji haushin Naila matuka da tazo da niyyar cutar da shi,yace amma ba komai ni Kuma wannan karon indai su Mima sun kawo min matar aure ko wace zan aureta kawai,gaba daya Nan take ya canja kala idonsa ya canja wani tsantsan bacin rai ne kwance a fuskarsa,yace maimakon ta hakura muyi aure kash,juyawa yayi yace zata iya shugowa na amince ta zauna ya wuce kawai ya haura sama.

 

   Naila tasan kayanta ta hango bacin ransa tace hmm baya so shi wata ta rabe shi Allah sarki abin kaunata shi Jamilunsa yake so,Mummy Nan take ta turawa Naila kudin rabi a accnt tace ki kula da shi sosai ina so aljanun su fita kinji,Naila tace an gama,ni daga Nan ma sana'a zan kama na daina harkar film,Mummy tace yanda kika gani amma kin hadu da Jinin arziki zaki ci Naira ki more matukar Spark ya amince da zabin mu yayi aura.


   Naila tana shiga ciki a kasa ta zabi bedroom ta shiga ta ajiye kayanta tana ta murna tace wayyo Allah dadi yau Gani a gidan Spark dina,shi Kuma Spark Yana sama ya zauna a gefen bed yayi shuru kawai mamaki yake wai dama Naila ba sonsa take ba amma ko da zata dau fansa a tunaninsa idan ta gano shine Spark zai ci darajar son da take Masa,tagumi ya zuba hawaye zubo Masa a Saman kumatu,yasa handkerchief tare da gogewa,kasa komai yayi wankan ma kasa yi yayi ya koma ya kwanta kawai,mikewa yayi ya sake zama tare da hargitsa gashin kansa ya furzar da wata iska me huci,yace ni na taba soyayya irin wannan haka tunda nake, akan mace har nayi hawaye.


     Naila kuwa murna take kawai ta fito ta shiga zaga gidan tana Shan kallo sai da ta gama kallon ko Ina sannan ta shiga kitchen Dan girkin data iya kadan ne Dan ma ta koya a wajen Sheyi,Irish ta soya da kwai ta dafa tea ta zuba a flask ta kawo dining tana jerawa,Spark ne ya fito fuskar nan murtuk,Naila tunaninta Bai ganeta bane shi yasa,a hankali tace sannu sir,ga breakfast,Spark yayi zuciya a ransa yace bari na ci idan ta kashe ni ita tayi asara,ya zauna a fusace a kujera tana murmushi ta gyara glass dinta ta hada Masa tea tun daga yanda ta hada Masa tea yasan wlh Naila ce duk abinda yake so ta sani gashi nan, Bismillah yayi tare da addoui yace a ransa idan na mutu Allah na yafe mata sabo da son da nake mata,Allah ka zama sheda,Naila dai taga Yana addua bata San me yace ba,tea din ya dauka ya fara Shan abinsa zama tayi a kujera tabbacin ta Saba da shi gashi shi tsiyar so baya buya,Naila a nutse ta dinga mika Masa slise  bread din Yana karba,sai faman satar kallon juna suke,shi dai baice mata kala ba,amma itace tace Sir abincin yayi? Ko kulata baiyi ba wani haushi take bashi ma harara ya watsa mata tace a ranta bai sanni ba Bai ganeni ba Allah sarki bai San Jamilunsa bace .


    Mima kuwa ganin Chikar gayu bata ji amma Kuma ta shiga ranta sai tace wannan itace daidai da Spark za yi maganinsa,sai ta kirata har dakinta,Chikar gayu ta zo zata durkusa,Mima tace Chika ya sunanki na gaskiya ma kika ce? Suhaila,suna me dadi,Ina so muyi wata magana tace to Ina jinki, zaki auri Dana? Chikar gayu ta zaci Misam ne da sauri tace ae me zai hana ai kina da kirki Kuma tunda na shugo gidan Nan nasan Ku mutanen kirki ne,a ranta Kuma tace karya nake ku ba mutanen kirki bane Yan wulakanci in kuka ga talaka ne mutum, Mima tace Spark nake so ki aura,Chikar gayu wani gumi ne ya keto mata tace a ranta ai Naila sai ta kashe ni Allah ya tsareni da cin Amana,a fili tace a'a Mima kiyi hakuri wlh bazan iya ba dama wani ne a ciki ba Spark ba,Spark ya haramta a gareni,ba Wacce zata ce baza ta so shi ba amma Banda ni wlh kiyi hakuri a canja min wani,Mima tace to kuwa sai dai ki bar gidan nan,Chikar gayu tace gari da yawa ai maye baya cin kansa,dama ni karya nake miki baku da halin arziki yawwa in fada miki gaskiya Ina da gatana,karki ganni a nan kice bani da gata,Mima tace to hada kayanki ki bar min gida,tace ko baki ce ba dama,ta juya ta fice kayanta ta tattaro tayi wanka tun a gidan ta canja kayanta masu kyau  ba Wanda zai ganta ya rainta ta fito Palo tazo ta jefawa Mima Jakarta tace gashi nan dama aro su nayi Dan Allah a kone su ko a kaiwa dangi a kauye.

  

    Kuma bari kiji nafi karfin na muku bauta shi yasa kuka ga Ina muku rashin mutunci iri iri yawwa, danki Kuma bazan aura ba a likawa wata mu bamu gaji cin Amana ba yawwa,ta juya tana murguda duwaiwaka tace ayyiriri mamarrrrrrrrr......ta wuce tana jijjiga jiki tana waka,Mima baki ta rike tace ashe da Karuwa muke zaune.

     Chikar gayu tace Allah ya rabamu da zuriar masu kisan Kai mugun iri,ta juyo ta Kalli Mima tace byeeeeee....


    Tana fitowa Misam ya shugo Allah yayi shi da neman matan tsiya gashi mata suna rububinsa sabo da shima ba karya,Chikar gayu ya Gani ta fito tana karkada jiki zata fita,Bai taba kulata ba sai yau,yace Chik....da iyayi Juyowa tayi ya kalle shi Yana birgeta a rayuwa yanzu Kam tasan yanda tayiwa uwarsa fitsara Ina zata bari ma suyi alaka.

    

     SANARWA


DAN ALLAH YAN PAID GROUP KU RIKE AMANA KARKU BAWA WASU KYAUTA.

ITA TA KASA SIYA KE KIN SIYA KIN BATA TA PRIVATE TASAN BA SIYA TAYI BA DOLE TA BAWA WASU A HAKA ZASU TURA SHI GROUPS DA YAWA.


YAU DA ACE  ITA KADAI ZATA KARANTA TA PRIVATE DA SAUKI SAI KU BAYAR A WATSA SHI A GROUPS


WLH DA AYI WANNAN GWARA MUTUM BAI SIYA BA.

AKWAI CIWO GA WRITER DA WANDA SUKA SIYA.








AsmaBaffa

No comments