Breaking News

Tantiriya a Gidan Yari Book 1 Paga 66-70



🏫 TANTIRIYA 🏫

        A GIDAN YARI


BOOK 1


                  66-70


Official



By

AsmaBaffa



SADAUKARWA NE GA

AIDA MAMAN TASNIM



Page naku ne

Maryam Idris Kabir

Ummy Aysha

Lubabatu Mijinyawa

Mmn Nasree. 

Momy FARUK

Oum Aariz

Aeesha

Rukayyarabiuadam123

Reina

Sadiya Muhammad

Hajjafatty 



Hey lovelies


Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?


Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?


Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?


Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?


Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din


https://wa.link/49vn47





    Spark uzuri yayi mata

 yasan taje gida Kuma maybe wayar tana jaka,Yana zuwa gida ya tura mata text message cewar yaje gida lfy,Naila kamar bata gani ba,shuru shuru ba reply ya daure har zuwa dare sannan ya sake kira sai da ya kira yafi sau biyar sannan Naila ta ga a haka ji tayi tayi missing dinsa baza ta iya share shi ba.


  Spark ko da ta daga baiyi complain ba,kawai ya mata uzuri ,Naila a ranta tace wato ma baiji haushi ba bai damu ba,me kike yi? Bacci,amma naji ki fess? to bacci nake ji ni ta furta ,hmm yaji kamar fushi take yi yace alright,Yana so suyi waya yaji Muryarta gaba daya taki bada fuska shi ya rasa me yayi mata,kawai yace good night ya datse wayarsa,ita kanta bata so ba.


  Umma tana kusa da ita tace Ashe kuwa zaki koma gidan miji ba shiri wannan iskancin ba a gidan nan ba,Yana miki magana kina wani share shi, sannu Naila karfa ki manta Yar gidan Hashimu Dolo ce ba kowan kowa ba,a gidan nan baki isa ba wlh.


  Spark kuwa Yana zaune ya tallafe fuskarsa Yana tunani,kwanciya yayi jiki ba karfi yace Spark kwanta karka kashe kanka akan mace,Mace sai ta haukataka,duk yanda yaso ya share amma ya kasa sai faman tunanin Naila yake,gidan gaba daya ba dadi bata Nan.


   Fitowa yayi sanye cikin Kayan baccinsa Silk olive color, a hankali ya nufi kitchen ya dakko lemon gongoni ya zauna a Palo tare da kunna tv Yana kallon American film a zahiri amma a ransa Naila yake tunanin gaba daya,zata susuta shi gaba daya.

   

   Naila ma tunanin Spark take yi a haka tayi bacci,sai asuba ta tashi bayan tayi sallah tare da Azkhar ko bacci Bata koma ba ta fito ta shiga kitchen ta fara hada musu break fast sabo da yara Yan makaranta,tana yi tana gyara gidan, kafin Yan makaranta su gama shiri ta gama komai tana wanke wanke ma,Abba Yana dakinsa shi da Umma ya mike ya leka ta window Yana ta kallon Naila tana aikinta,farin ciki ne ya kama Abba,Umma ya kira yace Yar Inna taso Kiga yarki tayi hankali,Umma ta leka itama tana washe baki tace shi yasa naji karar kwanika hannu ta daga sama tana cewa Allah na gode Maka,Abba yace Alhmdllh ya mikawa Umma hannu suka tafa a hankali ba tare da sauti ya fito ba, sabo da farin ciki da murna, Naila har masifa akewa yara Dan iskanci ku shirya ku tafi makaranta sai Kun makara, ke zarah baza ki Sha shayi ki tafi ba,Ke kuma Hidaya ki hadawa Aslam shayin mana sai Kun makara,Hidaya sanye da Uniform ta hada musu shayin suka Sha tare da doya da kwai da Naila ta soya, Suka karya sannan suka tafi makaranta,ta sake wanke kwanikan da suka Bata ta gyara wajen da dakunansu duk ta gyara,Umma da Abba ma karyawa suka yi sannan Abba ya fice wajen kayan miyarsa Yana mita Yana cewa ni wannan sana'ar ta isheni wlh kullum mutum sai ya zauna a rumfa kayi ta zama a benchi, basir ma ya kamani,ni na gaji gwara a canja min wata sana'ar.


    Naila sai da ta gyara har dakin Abba sannan tayi wanka ta zauna ta karya ga Spark Yana ta aikin kira bata daga ba sai da taji itama muryarsa take so ta ji sannan ta kirashi back,yana dagawa again baiyi complain ba ko kadan uzuri ya sake mata Naila Kuma so take lallai sai yaji haushi,Gashi bata iya Masa rashin kunya,Yana Jin kalau take sai ya mata sallama abin Yana damun Spark sosai.


   Haka ya shirya ya fita Office cikin wani yard me masifar tsada,Kai da ganinsa ba sai an fada Maka ba Tan color,fuskar nan a hade ba fara'a yanda yake asalin Spark kowa ya kulashi sai masifa,Aikin ma ya kasa tsaki ya ja ya shiga Mota zai fita,manager yazo yace sir takardun nan zaka kawo,Spark yace karka dameni da wasu takardu ya ja tsaki ya yace da driver muje, gidan Mummy yaje,ta ganshi ransa a bace yau a spark dinsa yazo,tace kaga karka zo Inda nake bayan rashin mutuncin da kayi mana a gidanka, Spark Ido ya lumshe yace Mummy Ina Kwana? Ban sani ba ta bashi amsa.


    Yace sorry Mummy daga nace zan afka miki shike nan sai ki dauki gaba dani ai idan aka tsine min nake nufi,yanzu Spark sai ka iya afka min? Spark yace idan aka tsine min ba mene bazan yi ba ai tsinuwa ce take aiki,yanzu sai ka aikata? Spark yace me zai hana kuwa,Spark ko wani ka ganni dashi Ina harkar banza da shi ai sai kayi min fada,yace Akan me? Kina Jin dadinki zan miki fada,ke da kika Raine ni Kuma kawai sai na miki fada sabo da kina neman Maza ba ruwan Spark kiji dadinki ai ko Mima ce ba abinda zance,iyakaci na dinga yawo da wandon karfe sabo da kar a biyo ta kaina.


    Allah ya shiryeka yace Ameen wai Mummy ku mata ya kuke ne? Sai a rasa gane kanku sai kace masu Shan kwaya mata haka suke,Mummy tace an fara fada ne? dama wannan marar kunyar ai tukunna nama sai ka saketa da hannunka,nifa ba laifin data min kawai tambayarki nayi sabo da na San rirrin yanda zan zauna da abata lafiya,Mummy tace lallai baka da kunya,ka gama yi mana rashin mutunci a kanta yanzu kazo wai a fada Maka siririn mata, ta kasheka,share zancen yayi,tace ai baka Jin kunya Kai ka gama zaginmu shine kazo yanzu kana wani tambayata sirrin mata ya muke.


    Yau da yamma Mummy ta dauki wanka sosai ta shiga motarta tana Jin kida sosai sai gidan Chikar gayu,tana zuwa ta hango gidan Malam wow tace Kai kai ya zama wajibi na shugo gidan Nan a matsayin mata,Chikar gayu tayiwa waya ta fada mata a bude gate,daya me gadin ne ya bude gate tayi parking sannan ta fito tana baza kamshi, Basiru kuwa ya saka Yar shaddarsa ta sallah Yana zaune a Palo ya hakimce Yana karkada kafa irin me kudin nan,Chika tace kayi fa aiki me kyau,yace za a ga aiki ai ki kwantar da hankalinki,aiki sai ma mun shiga dakin bacci, Mummy ce ta shugo Palo taga yaci kayan alatu sosai shugowa tayi ta zauna tare da furta wow ta zauna,Basiru Yana karkada kafa Yana wata gadara da kyar yake magana,yace barka da zuwa ya Kalli Chika yace my Watermelon Ashe yau bakuwa zakiyi Yana magana Yana kallon Mummy,Mummy ma kallonsa tayi kawai Basiru ya kashe mata Ido daya tare da daga mata gira,Mummy a ranta tace kaiii ya daga min girma murmushi ta saki,ya kwalawa Sheyi kira kamar wajensa bakuwar tazo yace a kawowa babbar bakuwa kayan motsa baki,Mikewa yayi harda zuwa ya rike hannun Chika Yana cewa Watermalone,Chika a sace ta fisge hannunta tare da gasa Masa harara tana ce Masa Banda wannan.


 Amma Ina Basiru a ransa yace tab ai wlh ba a isa ba na fito a miji Kuma ace bazan taba komai ba an San hakane akace ayi film,Sama ya haura yace kizo Ina son ganinki harda masifa irin me gidan Nan.


   Ba yanda Chika ta iya ta bishi sama tace da Mummy Ina zuwa,suna zuwa Sama a palon sama suka tsaya ya Bata rai yace wuce ciki,in wuce ciki in Maka uban me sadaki ka biya? Film kika ce za ayi ai ana kwanciya a Saman bed,ai Hausa film muke yi ba Nollywood ko American film ba cewar Chika,Basiru yace dama kin San ba Nollywood zamu yi ba kika bata min lokaci to wlh Baki isa ba ni Nollywood film zanyi sabo da haka wuce ciki muje.


   Chika tace baka da hankali Basiru Hausa film muke yi na musulmai,Basiru yace ba komai ai Hausa ma suna Waka da rawa a ciki sai munyi rawa da Waka tunda hakane Kuma karki sa Bra kizo muyi girgiza,Chika tace ai ban taba sanin mahaukaci bane Kai sai yau na fika iskanci wlh ta ja tsaki ta juyo wajen Mummy ta barshi tsaye,yace wlh sai nayi Yaudara a film din sai na so kawar taki komai tsufanta.


   Mummy ce tace wannan ne dama mijin naki? Chika tace ae,amma duk kudinsa yake saka shadda me araha haka,to ai wasu masu kudi idan kudi yakai kudi ba sa saka kaya masu tsada,Mummy tace wannan ma gara ne wlh karki sake ya dinga raina miki hankali Yana zaginki ki rama ki zagi iyayensa,haka Mummy ta zauna tana faman zuga Chikar gayu akan taci uban mijinta kar ta daga Masa kafa...


   Chika harda hawayen karya tana fada mata yanda Basiru yake zaluntarta,Mummy tace shi yasa fa wasu matan suke kashe mazajensu wlh ni bana ganin laifinsu ma,ba ruwanka zaka  huta ka shana kayi abinda kake so,Chika zama ta gyara tare da gyara wayarta tace kice yanzu haka ake yi?Sosai ai mata sun daina zama yanzu,Ina ma zan San Inda ake siyar da gubar Nan,Mummy tace zaki samu mana wata kawata  tana siyarwa a sirru,Naila tace idan na gaji zan kawo kudina,Mummy tunawa tayi karta jawowa kanta sai tace ke naji yanzu bata siyarwa amma zan tambayar miki ko ta dawo tana siyarwa.


    Basiru Yana Jin zata tafi ya fice ya rigata zuwa Jikin motar,Chika Bata hanashi ba,Mummy ya Gani tana Masa murmushi,yace bakuwar Alkhairi zaki tafi? Mummy tana wani fari da Idanuwa tace ae sai na sake dawowa,wani zuwan ni zan kawota da kaina,Mummy tace okay bari kaima na baka number ta ko gaisawa zamu dinga yi watarana,Basiru jiki na rawa ya dakko kwakwurar wayarsa yace  Af na manta babbar wayata a bedroom,Kai ai wayarce babba sai ta dinga Maka nauyi a aljihu musamman iphone nauyi ne da su,Mummy tayi murmushi tana karanta Masa number bayan ya shigar tace ko Kai kadai ma zaka iya zuwa gidana ba kowa,yace kasurgumar bazawara ce ne haka? Mummy tace wlh sakin Allah ce ba sakin mutum ba mijina mutuwa yayi kaga kuwa ai sakin Allah ne,Basiru yace sorry sorry harda dafa Kafadar Mummy sorry Yana girgizawa da hannu,Wayancewa tayi tace bari mana Alhaji Basiru kar matarka kanwata ta Gani,yace ke rabu da ita hakuri nake dama da ita ba uwar da take min na soyayya,Mummy ta furta wasu matan sai hakuri wlh basu iya kula da miji ba musamman yaran Nan,Basiru yace habawa bari kedai Hajiya Ina Shan wahala a kasar Nan da kudinka da komai mace ta zame Maka masifa ni sakinta ma zanyi,Mummy tace a'a ka dai Kara hakuri ai gwara kayi mata kishiya tunda gidan kaga part part ne,Kin kawo shawara na gode sai na kawota,Mummy ta shiga mota tana kissima irin kudin da zata samu a hannun Alhaji Basiru.


    Basiru ne ya dawo ciki yace Baby,Chika ta hade rai tace the End film ya kare,ko kwanciya bamuyi ba zaki ce ya kare? Chika tace ya kare gashi Nan rubutu akeyi na karshe dalla mallam kama gabanka bana son raini,tsayawa yayi zai sake magana Chika ta jawo takalminta me tsini ba shiri ya fice.

   Shirye shirye tayi itama na tafiya Kano,washe gari ta wajen Mummy ta biya ta daki cikinta a haka ta samo address din Misam har Office dinsa tace bari na dawo daga Kano nasan ta Inda zan bullo Masa.


      Naila tunda taje Kano ake Bata magungunan gyara da kudinta Kuma tana siyan wasu,Yau zasu je zance wajen budurwar Mohsin,Naila a waya ta kira Spark ya daga Yana fushi sabo da Bata taba kiransa ba idan ya kira ma sai taga dama take dagawa sannan idan ma ta daga baza tayi maganar kirki ba, daga gaisuwa shike nan,abin Yana yiwa Spark ciwo matuka,sai da kiran ya katse sannan ya kirata back ta dauka,tace Ina yini? Lfy Alhmdllh,dama unguwa zanje nace....sai kin dawo kawai ya kashe wayarsa,hankalinta ne ya tashi amma ta danne ta shirya ta zabo atamfa cikin kayan lefenta wata Indigo ta saka riga da skert kamar an aunata,tace wai Lefen Umma har akwati Sha shida aka kawo? Umma tace gashi kin Gani ai sun kashe kudi,tace to ki kwashi wasu mana a bawa su Hidaya da Zarah suma su Dinka,cikin shaddojin Kuma Abba ya dauka,Yaya Mohsin da Aslam,Umma tace wa yace miki haka akeyi? Ai Dan kiyi Masa kwalliya ya zuba miki,to ai dai ana kyauta ki zaba Hidaya da Zarah su zaba a bawa my love Mohsin da Abba ki duba sunyi yawa fa,shike nan zan fada musu an gode.


   Mohsin ne yazo yace fito mu tafi mana,Naila ta fito da Jakarta da mayafi duk sababbi,Umma tace ki gyara mayafin Nan sosai bana son wannan iskancin na yaran zamani mace me aure ba a banbanceta da budurwa bai dace ba, wasu mazan suna tare su a hanya idan mace tayi shigar Kamala ba me tareta yace Yana so,amma yanzu mayafin da wasu matan auren ke yafawa ko budurwa sai taji kunyar fita da shi, Naila an zama matan aure cewar Hidaya tana kallonta,tace ai kuwa Hidaya baki ga sai Shining nake ba? Hidaya tace na gani ai,Naila tace to Hallare ce ta jawo shi yasa kika ganni haka,Hidaya kunya taji tace ke Aunty,Naila tace ah to Kuma baza a Fadi gaskiya ba sai a zauna ana boye boye kamar me bin Maza,Mohsin ne yace Dan Allah muje ko kunya bakya ji naga ranar da zaki hankali ki fara kunya Umma fa tana jinki sharewa takeyi,Naila tace to ai ta San harkar itama gashi nan ta siyo min kayan gyara.


    Suna fita taga mota me kyau Sabuwa wata zata Kai ta 2m,Naila tace motar wa ka aro? yace ke baki sani ba to mijinki ne ya bawa Abba,Abba yace ya bar min ita nine Dan zamani Allah ya tsare shi da tuki,da fa wai siyarwa zaiyi Umma tace wlh ba Wanda zai siyar, Naila tace yayi kokari Spark gaskiya,nayi dacen miji,shi yasa nake sonsa fa,Mohsin dariya yayi ya fara driving,yace Naila na fahimci Baki San Hallare ba shi yasa kike wannan iskancin,wlh na Santa kaji Yaya to bari kaji na Santa sosai sau nawa Ina kare mata kallo,Mohsin yace ai shike nan magana ta wuce,yanzu me zaki siyawa Amaryar? Naila tace a siya mata turare mana,tace Yaya ya Hanan wai? Yau a gidanka zan kwana,Yace kishi take Abba ya fada mata zanyi aure in kika ga haukar da take ya Baci,Naila tace to ya nonon nata? Yace ai yanzu nake kallonsu kullum sai anyi yawo ba riga tun Ina kallo a dadin Rai har sun sire min,yanzu ma ni haushinsu nake ji,kullum Kuma sai an bude,Naila ta dinga dariya,tace duk duniya ban taba ganin Dabba irin Hanan ba,da haka ake birge miji,Mohsin yace uhm ni yanzu na Amarya nake Hange na gaji da nata Abu duk sun Sha iska sunyi Sanyi sun huce,Naila ta dinga dariya tace yau dole na kwana a gidan,yace a satin Nan zamu tare a sabon gida kafin ayi bikin.


    Turarukan suka shiga Shopping mall zasu siya,Mohsin Zai biya kudin Naila tace Ina auren me kudi zaka siyi Abu Ina wajen matsa ni taje ta biya kudin sai gidan su Beauty,Naila taga har cikin gidan suka shiga, tace me zan gani wai? Wannan ai gidan su Beauty ne,dariya Mohsin yayi yace itace amaryar Ashe babanta shine nake zama Masa a shago,gashi ya bani gida sabo part biyu ba Nisa da daya gidan nawa ga Kuma yace naci gaba da juya wannan shagon halak malak,Naila tace amma nayi murna,Ashe Kai na dinga yiwa zance a gidan yari,yace wlh,Naila tace akwai tsiya Yaya Hanan da amarya fa za a gwabzu,Mohsin yace wannan bata fada,yarinya shuru shuru saliha ga iya soyayya ai Hanan sai dai ta zalunce ta.

   Naila tayi dariya a ranta tace zaka ga Saliha ganin idonka.

   

    Beauty ansha gayu cikin Abaya me tsada ta fito suka rungume da Naila tace amma wlh Kun raina min wayo amma naji dadi ko ba komai na nadaki a madadina tunda ban auri Yaya ba yayi Kuskuren zuwa a gidanmu, nasan zaki zama wakiliyata yawwa a adana min shi,Beauty harda Jin kunya wai ita ta gari Naila tace duk fake ne nasan komai yarinya,tafawa sukayi suna ta hira suka bar Mohsin a zaune shuru.


   Ya gyaran Jikin? Beauty ta tambayi Naila,tace Inda kika min kwatancen na fara zuwa tuni ma suna goge min skin sun bani su lotion da sauransu,sai harkar kamshi,sai dare su Naila suka wuce gidan Mohsin.


    Hanan tana Palo kawayenta sunzo sun zauna in banda tsinewa Mohsin da Maza baki daya ba abinda sukeyi suna zugata, wallahi karki sake Amarya ta takaki ko shi ya takaki,Hanan tace Ina zan yarda ai wlh tunda naji zancen nan shi da zaman lafiya sai dai ya Gani a makwafta,masifa da bala'i ya dinga ganinsa kenan.wata a cikin kawayen me hankali tace ni Kuma a shawara ki kwantar da hankalinki Kuskuren da kika San kinayi ki gyara,sannan karki tayar Masa da hankali domin zai sake tsanarki ne wlh,tun Yana sonki zai daina gaba daya,idan kuwa kika kwantar da hankalinki an San akwai ciwo amma daurewa akeyi, mijinki na gari ne ki daure ki lallaba abinki shine kadai zaki siyawa kanki mutunci.


   Ko mutuwa zakiyi wallahi aure bazai fasa ba, Maza basa fasawa,idan kika daina nuna Masa kishi sai yafi Jin kunyarki ,surukarsa zaki zama wlh Kuma zai dinga tsoronki,duk abinda yake ciki akan auren sai kinji labarin ya fada miki,ke ko fada suka yi sai ya fada miki,kece uwar gida amma mu muke Bada kanmu har a kawo wata sama ta Kai tazo ta kwace mijin ko tayi sanadin mutuwar aurenka.....da masifa suka hayayyako mata to sannu ustaziya mu zakiwa wa'azi to baza ta kwantar da Kai ba salon a takata kenan Yar bakin ciki,kawar wacce a cikinsu ma itace karamar tace shike nan Allah ya Bada sa'a,suka ce Ameen munafuka.


     Naila ce tayi sallama kafin ta shugo a palon,da Sauri  Hanan tace kanwarsa ce karku kulata itace ta je gidan yari taje a suffar Maza ta shiga cikin kartai wacce nake Baku labari ta hadu da me kudi ya dinga sex da ita sai da ya gama cinyeta tas sannan ya biya cin hanci suka fito ta bishi Abuja can ta dinga karuwanci yanzu karshe ya aureta Dake Yana da kudi tuni ya kashe case din taci banza, Kuma kisan Kai tayi, wata tace to ki dinga taka tsantsan da ita kar kema ta aikaki lahira,Hanan tace ai yayanta da iyayenta boyewa suke basa so asan zancen Kuma naji labari,Naila ce ta shugo Kai tsaye suka yi shuru basu kulata ba itama Bata kulasu ba ta zauna,tace Hanan? Tsaki Hanan ta ja tana harar Naila sabo da yayanta zai Kara mata kishiya.


    Murmushi Naila tayi tace tare muke da Yaya mun fitar da ankon bikinsa namu zakiyi ko kuwa naku zaki fitar da kawayen naki?  tun yanzu har Kun fara dannar kirjin ne? Ai dai kwa bari bikin yazo,Hanan ta fara dure duren ashar kamar mahaukaciya,duk uban da bai Kara min kishiya ba baya kaunar uwarsa da ubansa,Naila tace ai shi yasa zamu Kara tunda muna kaunar uwarmu da uban namu,Amarya me dadin tuwo da Miya gata da nonuwa lukwi lukwi Yaya idan yayi pillow dasu sai ya makara gasu jajir abinsa,dama shi yasa akace a dinga sirkawa idan uwar gida baka ce sai a Nemo fara,Mohsin ne ya shugo kawayen suka tashi sum sum suka bar gidan ita Kuma Hanan kawai zage zage take yi ba ma'ana ba lissafi.


     Mohsin yace Naila bana son tashin hankali kin sani ko,Hanan tace duk wani matsiyaci dai dai nake dashi wallahi,duk tsiya kafin ayu daram akai kwandi,wallahi ba Dan shegiyar da zan ragawa ko uban da ya haife ki ne,Naila tace Abba kenan? Hanan tace ae,Naila tayi murmushi tace kin San dai me kayan Miya yafi Dan koli nagarta ko?ko a jari ba daya bane,Hanan ta sake tunzura tana zagi,Naila tace biyu da safe biyu da biyu da daddare, Amarya ce sai mun Kara sai dai ki mutu,Hallare dole ayi sharing dinta,idan ya Baki ya bawa Amarya yawwa,ta yayana tafi karfin mace daya lalura dole sai an raba muku ita,Hanan tace Inshaallah sai an miki kishiya in Allah ya yarda,Naila tace kema da za a miki ke kika yi wasa da damarki,ni nawa na isheshi tun Ina karama nake Shan madarar shanu akwai kayan aiki,ko baki ga jikina  bane? Mohsin ne yayi alwala zai tafi masallaci yace Naila bana so fa bakya ji ne wai,Shuru tayi ta kyale Hanan tana ta kumfar Baki.


      Naila alwala tayi ta dauki Sallaya, Hanan ta fisge tace ai ba Yayanki ne ya siya ba ubana ya siya min,Naila tace Hanan karfa ki haukace sallah zanyi,tsaki Hanan ta ja ta Maida sallayarta daki,Naila tace hmm kawai ta shimfida dankwalinta tayi sallah a Kai..


   Jakarta ta bude ta dakko mata wayarta data taba dauka sanda ta fito daga gidan yari tace ga wayarki,ta zaro kayan sawar data dauka a wanke a goge tace gasu nan na biyaki abinki kar na tafi lahira da nauyi,Hanan tace barauniyar banza,Naila Tashi tayi ta shiga kitchen zata zuba abinci,Hanan ta shugo tana huci ta fisge plate dinta,tace ubana ya siya min,kular abincin Naila ta jawo Hanan tace wlh akan kici abincin Dana dafa gwara na zubar, ta kwada flask dinta da kasa sabo dashi, abincin ya watse ,Naila tace ikon Allah haka abin yayi tsamari? ashe haukar kullum shahara take.

 

   Hanan kuwa tana huci ta chakumi wuyan Naila tana zage zage Naila ba karfi,kokawa suka fara Hanan ta hankada Naila Jikin kofa Naila ta bige kafarta,kofa ta ji mata rauni a kafa jini Yana zuba,turo Naila tayi waje tafado kasa,kafarta dayar ta gurde ta kasa tashi,Naila tace wlh sai nayi sanadin barinki gidan Nan sai an sakeki,kin jawa kanki,Kuma baza a sakeki ba sai kin Sha wahala a gidan Nan sannan a miki korar kare shegiya, sai kin koma gidan ubanki,dama ai kin tsufa tsohuwar banza


    Mohsin ne ya shugo ya samu Naila a kasa ta kasa tashi tana ta kuka kafarta daya wajen yatsa Yana ta jini,Mohsin ya dagata da sauri yace sannu nace miki karki biye mata bata da hankali, muje na Maida ke gida,Kinga abinda nake gudu ko,yace yanzu idan na saketa ko na koreta mutane zagina zasu yi ace sabo da zan Kara aure ne,Naila tace karka saketa wlh sai ta kunshi bacin rai,tana dingishi ta dauki Jakarta da mayafi suka tafi,a chemist ya tsaya aka mata dressing suka koma gida.


   Tana kuka tana Bada labari,Umma tace bar shegiya aure ne dai sai ya Kara,Abba yace Naila kema da tsokana ai dole tayi kishi ko wacece, baki kyauta ba ai sai ki kyaleta, Nan ga darasi a gidan nan nace zan Kara aure uwarku wacce hauka ce bata yi ba,Umma tace yaushe nayi haka? Hashimu kaji tsoron Allah,to ai dama ita uwa tana so ace Danta zaiyi aure musamman in basa shiri da uwar gidan Danta, amma idan akace ita za ayiwa to Kuma sai tsiya,Allah ya kiyaye min nayi wannan haukar a kanka cewar Umma.


   Hashimu yace na nawa Kuma,a Hakan ana rainani a haka akayi kuka kina tsoro zan dinga yiwa wata girki,Umma tace to ka karo matar yanzu,yace sai da kika ga nayi kwantai zaki ce na Kara kowa ta gujeni,Batoolar ma ta gujeni, amma sanda Naje zance ai ta iya baza kunne taji Ina koya mata girki,Umma tace au har girki ka koya mata? Kaci Amanata,Abba yace Kinga ki gasawa Naila kafarta ni na riga nayi kwantai Kuma a gari, ya zanyi Kubra dai kullum Kubra kamar masifa,dariya Umma tayi tace Allah ya kyauta Maka Dan Yagana.


   Abba yaji sabon Suna harda sosa keya Yana murmushi,yace Uhum Uhum Uhum...Allah yaji kan Yagana ana lahira,Uhmm ko su Yagana kamanni sun canja oho, su Yagana an mutu ana gulma,sun zaci ni Dolo ne sai su dinga gulmar mutane Ina jinsu ni kuwa in nade tsab a kaina, sai naje na fadawa mutumin da suka yi gulmarsa nace Yagana tace Maka kaza,Naila ta kwashe da dariya tana kuka tana dariya,Babar Hashimu ce guda amma yake fadar haka,Umma tace Inshaallah tana Aljanna Allah zai yafe mata, Abba yace Ina mata addua kullum Allah ya yafe mata amma har ta mutu tana zuwa wajen malamai wai sai ta Kara haihuwa,nace Yagana nima da ya kuka sameni ki fawwalawa Allah, amma Yagana taki ji,kullum baza suyi hirar duniya ba sai zancen wasu,ni Kuwa Ina ji duk na kwashe naje na fadawa mutumin,Ina ta mata nasiha sai ta zazzageni,to yanzu wa gari ya waya? Sai dai nayi mata addua idan Allah ya yafe mata shike nan,idan Kuma bata dace ba yanzu walakiri ya sassaba mata kamanni,Umma tace Dan Allah ka dinga fadar Alkhairi,Abba yace ni na sata tayi gulmar? yanzu haka da za a dawo da Yagana duniya bazan ganeta ba tsabar dukan walakiri.

   Naila sai dariya suke kamar ba gobe.


      Naila tana hawaye Umma ta gasa mata kafa, Spark Yana ta kira,yau bugu daya Dake shagwaba ce har ta daga tana kuka,yace menene? tace uwar gidan yayavce ta kusa karyani,Spark yace amma dai baki karye ba ko? tace ae tana shesheka tana cewa kafata jini take yi sai da aka kaini asibiti yanzu ma Likita yace gobe da sassafe lallai na karya da hantar rago,Spark dariya yayi yace to ai ta kwana gidan sauki indai zaki warke.

   Tace Kuma yace da ice cream da daddare kullum sai na Sha,sai me? Spark ya tambaya,tace da tsire me Laushi,yace wannan ciwon ai da sauki,yace wannan bata da Imani gaskiya,Naila tace ai shegiya sai nayi sanadin sakinta wlh bazan yarda ba,an fasa kawo Maka Amarya Nan da kwanaki kadan sai na dau fansa,Spark yace a'a please Dan girman Allah a kawoki sai muzo tare mu dauki fansa,amma Ina wani kar a kawoki ai bazai yuwu ba,Spark yace ki rabu da ita Allah zai saka miki,ai dama na ganta duk wata ya muka kwana ce,duk ta zama wata Rasss da Kwassss,Naila tayi dariya tace ko tayi kwalliya ma bata kyau,Spark yace ai shine Rasss da Kwass din tayi expire kenan.


   Yace ki rabu da ita a kawoki gidan mijinki yarinya Kisha madarar Nido inji Scoler,dariya suka yi,Naila bata San Hallare ba Sam ta zaci wasa ne,tace Yama sunan style din da akeyi? Spark yace suna da yawa fa akwai su

Snake in the monkey shadow, su Bend down,Naila tace na gane bend down dai kamar zaka Koma shekarar 2001? Spark yace Ehem ashe kin gane, sun Dade suna hira kamar zasu kwana a haka, yau Spark yasha nishadi da farin ciki da wuri ya Sha baccinsa me dadi,Naila kuwa sai bayan sun gama ta tuna ai aji take ja fushi ma take yi da shi.


   Shuru tayi Umma ta fito daga daki tace lafiya? Naila tace nidai soyayya tana cutata Umma idan ya kira sai na manta komai na dinga farin ciki,Abba da yanzu ya shugo ya tsinci zancen,yace ai haka so yake Naila ki tambayi Kubra,Kubra ya sanda aka turani zance wajenki na dinga guduwa Ina Jin kunyarki,Umma tace Dan Allah daga masallaci ka dawo ka tafi Palo a kawo Maka abinci,Naila tana ta boye dariyarta,tace ko Dan Abba ai ka so zaman gidan nan wlh.


   Su Naila ana ta gyaran jiki ba daga kafa ko Ina gyara yake Sha ita da beauty,sunyi kyau sun Kara haske ko Ina suka gifta sai kamshi,Naila har wani kiba ta danyi, Hanan taga biki ya taho ta haukace,Mohsin yayi mata lefe akwati uku Amarya akwati shida amma tace bata so,ta fatalo akwatunan kofar gida sai kwashewa yayi ya Maida su gida wajen Umma,Ya Bata kudi ko zata yi wani abu taki karba ta watsa Masa abinsa,Baban Beauty shi ya zuba musu furniture amma kowacce da kalar nata,Hanan sabo da kishi da tasan zata tare duk tasa almajirai suka fitar da kayan ta kaisu ta siyar da na bangarenta ta dauke kudin kayan ta Kai gidansu ajiya,ta kawo kwararrabarbun kayanta tsofaffin ta zuba a part dinta,gidane hadadde yasha alatu part biyu ko wacce 3bedroom da Palo,ko Ina a tsakar gidan yaji flower da interluck, ga motarsa shi Mohsin lafiya Lau abinsa,Chikar gayu anyi dinkuna sunyi anko har Naila da sauran kawayen su Beauty Naila ita bata da kawaye a birni sai kauye,Kuma sai da ta fadawa kaka a gayyato mata kawayenta na kauye,Kuma an basu alawa zasu zo su hudu. 


    Ana gobe daurin aure ko wanne bangare an cika gida ana shiri har dinner Mohsin zaiyi lafiyayya,Naila da iyayi harda kiran Spark lallai sai an kawo mata motar Hawa sabo da zirga zirga,yo abinka da amarya ana zumudi sai gashi ansa wani ya kawo Mata in ta gama amfani da ita za a zo a dauka.

  Gobe ce ranar Dinner Hanan tace dole taje da kawayenta sai sunga tsiyar da za ayi a can,Naila itace gidan Beauty itace gidansu,gata itace babba  mace a gidan da ita Umma ke shawarar komai,abinci ma duk an Bada kwangilar yi,tukunya ko digo baza a a Dora ba a gidan sai dai a kawo a dire,Naila tace Umma Spark ni fried rice zan basu kar a kawo min wani abinci idan ba ita ba ranar daurin aure zaizo,Kuma zaizo Dinner ma gobe,Umma tace ai dai ranar daurin aure ai za bashi ko? Dinner ai akwai acan,ae ranar daurin aure,Allah ya kaimu.


   Abba an kawo goro da yawa da alawa na daurin aure,sai cewa yake ni ta Hanan nake  so a raba abata nata Dana danginta,ana rabawa cewa yake a fitarwa da Hanan fa nata Dana Yan uwanta.

   Spark shi duk burinsa yazo Kano ya sace Naila a rubibi su kwana a masaukinsa,har Allah Allah yake gari ya waye ya tafi Kano.





A dinga sharhi fans 

Masu Sharhi Ina godiya




AsmaBaffa

No comments