Breaking News

Cheaters Club 22

 _*CHEATERS CLUB...*_ 

 _(Babban goro sai Magogin Æ™arfe...)_ 




#ROMANCE

#FICTION

#ADULTHOOD

#SEXADDICTS

#WOMENPOWER


BY

 _SURAYYAHMS_

 _08060712446_


⏯️2️⃣2️⃣


Da kyar hafsat ta mike snn ta tattara bedsheet dinta lalatar a hannu ta shiga bathrum dinsa dasu,babu bata lokci ta hau wanke jikinta tabi tasaka sabon pant da pad din daya kawo mata lkcin tsananin fargaba duk ya cika mata kirji tanayi hannunta na É“ari dan gani take kamar shemau zata iya shigowa yanzu ta kamata.


Abatasan ya zatayi ba ta zabge jikakken kayan dake jikinta agaggauce ganin ya gama lalacewa da jini ta hadashi tare da zanin gadon sai ta jawo towel din dake wajen ta daura shi bisa kirjinta.


Kayan data lalata ta tattaro a hannunta tana rungume dasu tafito cikin dar dar da jin tsoro ganin He is still not around bai dawo ba hakan ya bata daman falfalawa da uban gudu ta shige dakinta dasu tay sauri  tabi takulle kofar dakin tareda jingunuwa da bayan kofa tanamai sauke nannauyar ajiyan zuciya.


Har Saida ta dan samu nitsuwa snn ta karaso ta gaban jakar kayanta ahankli ta tsuguna ta bude zip din tafara ciro wasu kayayyaki ayan kayan sawarta da kwata kwata baifi kala biyar ba


Wani doguwar rigar kwanjo abaya baki ta jawo ta zurashi ajikinta snn ta aje kayan wankin datazo dasu din agefe sabida zazzabin dake cin jikinta yasa ta kwanta bisa kan gadonta dan kuwa sosai cikinta shima ya balle da azababben ciwon har ji take kamar itama mutuwa zanyi.


After 1hr ta farka jin kanta na mata nauyi duk saita kasa iya budesu gaba daya idanuntan sunyi sanyi sunyi wani luiii jikinta gabaki daya yayi lagwas kamar an tsoma akuya a ruwan sanyi saboda azabar yunwar daya gama nakasa ta.


Tana daga kwance ahakan Batasan anshigo dakin bama bare ta gane ko waye ne ,ji tayi an dan taba goshinta alaman ana feeling tempureture inta wni nishi ta sake sai taji kmr mutum ya zauna agefe da ita. Dada kame idanunwata tay sabida tsananin kunyarsa data somaji aranta, all She can feel is his scent and warmth dan haka taki sam ta bude ido ta kalle shi da kyau.


Waya ya kammala yi da likitan da zata zo ta dan dubata,kafin nan ya juyo, Kallonta yake yi while his face isnt showing any emotion Har likitar tazo ta dan duddubata,iya Allurai kawai akamata snn docton ta rubuta mata magani ta fita.


Nan da nanbbacci me nauyi yay awon gaba da hafsat all she know is hartay nisa cikin bacci yana zaune awajen yana dubata batasan kuma yaushe ya fita ba.



Daga ta fannin Gidan hadiza kuwa yadda kasan anyi mata mutuwa haka ta kasance da bacij rai dan ko Abinci yau bata iya sawa abakinta ba harsaida shemau tazo kafin nan tadan sake jikinta tay wanka harta danci abinci wani karfin gwiwar ya jiyarceta.


Yau daurin auren mijinta da ramatu ex minister dan haka gaba daya bata cikin mood ,shemau ce ta dinga bata baki tana danneta wanda iya kalamanta na sanyayawa  shiyasaka tadanji sanyi harta warware suka tsunduma cikin shirin Abinda zasu yi.



***************


A fannin doctor khalid yau ma still aikin daya wuni yi kenan wato jiran saÆ™on go ahead daga wajen Dr asim akan case din halisa wanda har yanzu bai sameshi a waya ba. Da kyar da wuya yaji labarin cewa  Abuja doctor ya tafi.

yasha matukar mamakin jin hakan saidai aransa atake ya qudirta cewa hala maqiyinsa khaleel ne yakeson ya kwace masa slot din jinyar halisa mansa a wann karon ma, gashi ya riga da ya dora buri mai yawa akanta izuwa yanzu.


Tun bai tabbatar da zancen ba zuciyarsa ta dau zafi da khaleel ya hau jin mugun haushin sa yanaji kamar ya kashesa.



Tsaki ya wuni yi yau a offishinsa, minti kadan zai dau waya ya kira abokansa da suke da alaqa da board sai kaji yana buga kirji yana cewa Khaleel yana kishi da shi.


Last call din kenan daya shigo wayarsa ya dauka ransa bace yace Hello Doctor wasiu... Dagata dayan bangaren wanda aka kira da wasiun yace 


"khalidi why are u calling me like dis naga 10 miss calls dinka wani abu ya faru ne ata wajenku?


Fuskarsa a daure Yace "eh mana.. wani abu mummuna ya na shirin faruwa dani, i just call to let you knw that Dat dr khaleel is  a very wicked man,i swear to god he is evyng me kuma zan dauki mummunan mataki akansa inbe dena shiga harkata ba.


Da mamaki a muryan Dr wasiu yace meyafaru haka what did khaleel do to you now khalidi?hmmmm Acikin watan nan sau nawa kake kawo maganansa arent u tired?


Cikin katseshi da ihu yace " i am not, i cannot be tired this is getting out of hand.. da mamaki sosai dr wasiu yay shiru yanakan jinshi "..can you imagine an bani aikin therapy akan wata babe yaron nan yaje Abuja yanaso yahana Dr asim yay min aproaving just bcos he knws i am better than him in this hospital?a zafafe yace See Wallh yaron nan bai isa yaga bayana ba fa. U ppl shud help me take his matter to the medical board of directors azo ayi mana sharia ya gayamin mena tsare masa da baison ganin cigabana.


yaron nan yasakoni agaba da hassada ni bansan meye tsakanina dashi bafa ...


Doguwar ajiyar zuciya DR wasiu yaja dan yasan ba haka dr khaleell yake ba sam... snn yace is okay naji but u knw what?..



Yana huci Yace what??


A nitse Dr wasiu yace zan kiraka anjima let me first talk to DR ASIM and confirm first.


Yace okay wasiu but you must do sumtin oo cos i knw khaleel is behind His silent, nasan shine yace masa karyay min aproaving aikin yarinyar nan..i just knew it.


Agajiye Dr wasiu yacemai calm down khalidi..will call u later.. 


yana fadin hakan ya katse wayarsa baima jira amsarsa ba,nan shima ya jefa nashi wayar a silent yana mai sakin masa tsaki dan already ya riga yasan shirya maganan kawai yay amma ba gaskiya ba, ire iren gaba da baqin ciki irin hakan is now very comon yanzu a tsakanin ma'aikatan gwamnati.


izuwa yanzu kusan kowa yasani cewa shine yake nuna tsananin hassada da kishinshi akan khaleel boro boro amma sam yaki amincewa da haka.



A fannin vicky kuwa yau tun da isa schl babu abunda yake fado mata aranta face yadda business dinta ya soma tafiyar hawainiya nazarin new stratergy takeyi wanda zai farfado da ita, sede a duk sadda ta fara lissafin hakan sai nazarin zaman aurenta hade da strange email din nan ya dawo mata cikin ranta.


Game da boyayyar email din Suspect dinta na farko students dinta ne sedai  a iya zamanta a makarntar haryau dai babu wanda ya taÉ“a samun private email dinta bare ta tabbatar dan is highly encrypted and confidential irin wanda ba a samunsu a sauki sai insune suka bayar da hannunsu.


Wani zuciyar raya mata yake ko wani babban mutum ne yay mistaken personality yake mata magana batare da yasani ba, ko kuma hala mijinta ne dakansa ya batta da kamanni yake son ya gwadata.


Ta balain jimawa da wann nazarin aranta bata wani samu saida ba saida kirar kaninta nile ya shigo.


Jin wayarta na ringing ya sata sauke Nannauyar ajiyar zuciya sann ta dauka muryanta adan sanyaye tace "Helo nile, whats up, how far?? Hows work today, did u need anything frm me?


Sautin Muryansa mai bala'in dadi da sanyi ta shako yana murmushi dan aduk sadda zai magana sai ya nitsar da kanshi sosai snn yake fitar da kalaman acikin sanyin kasaita da nitsuwa.


Yana murmushi me sanyi yace "hey Sis..im gud sorry i call u at work.


Gyara zamanta tayi tanamai cewa no no ba komi fadi meke tafe dakai..did  u need anything?....


Ahankli Yace no......

shiru yy sai can yace 

Sis its about ur husband.


Tun bai karasa maganan ba cikin tsaresa tace ohhhh yesss i totally forgot dama femi yace min na hadaku.


...cikin datsar numfashinta yace sister vicky hold on Ina fatan bake kikacemai yana kulawa dani ba...


Zata budi baki cikin haderai yace sister vicky i told u am fine Meyasa zakina daga hanklinki akaina,.inyace baison na zauna masa agida ba wani abu bane u dont have to force him to take care of me in return banason abunda zaije ya dawo mana abun raini.


Idanunta dake lumshe ta bude snn tace.."Nile is not what you think okay..i swear to you ra'ayinsa ne. Altho yace min is a way of making me happy please nile ka yadda dani nifa ban gindaya masa komi akanka ba.


Ajiyar zuciya ya sauke yace shikenan to naji amma...cikin katseshi da magiya tace please nile..kayi hakuri ka kyaleshi ya maka abunda yake da niyya din sabida already yafara tunanin ko zakace ya tsaneka and he doesnt want that to affect our relshp..Kayi hakuri nasan kafi karfin ana kulawa dakai amma tunda hakan zai kawo mana zaman lafiya just let him do this.



Tun da tafara maganan nile baice komi ba ya lumshe idanunsa yana lissafin abubuwa dayawa aransa. Gani yake kamar har yanzu basu fahimce  waye shi ba, dan Shi namiji ne dayake bala'in son yaga yana zaman kansa tare da dogaro da kansa wanda hakanne yasaka shi acikin jerin mazajen da sam basuda kwadayin abun duniya arayuwarsu. Duk wani Abu dayakeso na rayuwa yafiso ya sameshi ne da guminsa bada gumin wani É—a namijin ba besides a iya zamansa dayayi a kasashen waje he belive dat kowani dan adam yana da ra'ayin kansa.


Duk abunda Prince femi falana yay masa agidan sa ranar shi baima dauki abunda zafi har haka ba ..


Daurewa kawai yay yabar maganan aransa  badan komiba sai dan sabida samun cikakken kwanciyar hanklin yar uwarsa victoria dan bakaramin kaunarta yakeyi aransa ba.


Ahankli ya bude lumsashun idanunsa jin tanakan lallamarsa, murmushi yay snn yace mata karta damu Bakomi 

Ya amince.


Sosai taji sanyi aranta daya fahimce ta, dan Hira kadan sukayi nan yake sanar da ita cewa mijintan har ya aiko masa estate developers da yamma zasu zaga dashi gari su nunamai gidan da zai kama masa yana zama aciki instead of zaman da zainayi a hotel.


Murna vicky ta dingayi tana ta suggesting masa ire iren gidajen zamanin da suka dace dashi irin wanda akwai enough bedroom spaces,fully loaded kitchen and gym da swimming pools da bar dan tasan mijinta yana da kudi sosai zai iya kama masa kowani irin luxurious estate to his taste.


Shidai kawai binta yake yana azzama hirar dan ta saki ranta taji dadi amma har ransa bason hakan yakeyi ba, muryanta cike yake da xumudi da murna shikuwa a kwakwalsa yagama tsara yadda zai dauko wani abokinsa da sukazo nigeria da shi dan su zauna a gidan tare.


Ahaka har suka kare hirarsu awayan bai yadda ya gayamata abunda yake shiryawa aransa ba sede sosai ya sakata ta kwantar da hanklinta akan maganan kafin nan kowannen su ya cigaba da abunda ke gabansa


*******

 Daf ana kkrin kiran sallah  azahar hafsat ta farka babu wani karfi ajikinta sabida azaban yunwar data kwana ta wuni dashi.


Jin bazata iya daurewa ba yasata sauko kasa rike da kanta dake mata wani irin nauyi da ciwo.


acikin yanayin jiri ta daddafe ta kai kanta cikin kitchen dan sauran Breakfst din data dafa ma mijin shemau da baici ba shi ta dauka ta nemi waje ta tsuguna  tahaucinshi da sanyinshi ham ham tanata Allah Allah ta kammala ci ta cigaba da ayyukanta tun  kan shemau ta dawo ta rutsata. 


Hannu a baka hannu akwarya take tura abincin abakinta kamar wata yar gudun hijira, kafin kace wani abu har zufar hucewar zazzabi tareda gushewar yunwa ya fetso mata a saman goshinta nan da nan tafarajin kanta dama dama.



Cikin dauriya tare da azama ta soma gabatar da ayyukanta data bari, jin gidan ya dau shiru yasata bari aranta cewa hala Ficewa sallah ko kuma wajen aikinsa yaje.


Tunda ta kama bakin aikin babu abunda yake dawo mata aranta sai tausayinta da kuma temaka mata dayau yayi wanda yakamata ace da shema'u ce a matsayinta na mace kuma lawya me kare hakkin dan adam zata kyautata mata haka amma ina sai aka samu akasin hakan agareta.


Tunda take bata taÉ“ayin tsammanin cewa akwai masu kudi irinsa masu tausayi da kula talaka irinta ba, barema a matsayinta na yar kauye wacce batayi karatu ba har ace namiji hadadden kamrsa ya bata lkcinsa wajen teimaka mata, Itade sosai wann abun ya bata mamaki aranta bana wasa ba.. 


a wani bangare na zuciyarta kuwa tsoro mai balain yawa ne ya cikkeshi dan tasan idan har shemau taji wann labarin to hala kasheta kawai zatayi ba zallan korarta a aiki ba.


Dukufa tayi akan aikinta cikin azama da dauriya, dan Iya Tunanin daya debe mata kewa kenan kafin kace wani abu harta dafa musu spaggeti jollof na dede iya bakinsa dan already suna da soyayyen kaza ga kuma kifin sardines dan haka dasu kawai tayi amfani bata wani yi mintu goma ba abincin ya nuna ta saukar.


Fiye da rabin Abincin ta juye masa a warmer da ake serving dinshi takai kan dinning table ta jera shi a nitse.  


bayannan kitchen din ta dawo ta dauki wanda ya rage a tukunyar ta kankare kanzon ta cinye shi a nitse duk da baida yawa amma sai taji cikinta ya cika babu laifi.


Kallon agogon dake kitchen din tay ganin karfe biyune harda rabi na rana,tunanin me zata dafawa shemaun ta hauyi dan tasan izuwa karfe shida na yamma ko takwas na dare zata iya dawowa gida, itade a iya Kallon datakeyi ma tsarin rayuwar shemau sai taga kamar kwata kwata bata dace da mijin da Allah ya bata ba. 


hakan take ayyanawa aranta ayayinda take kkrin kimtsa wajen datay aiki sabida taje ta huta kafin yamma yay ta sake fitowa. Ta kammala wanke tukunyar ta kifa kenan Kakkarfan sautin Gyaran muryansa ya dakatar da ita abazata ta waigo ganinsa a tsaye yasata kusan daburcewa tana me shirin rusunawa cike da ladabi da biyayya tanacewa "san..sannu da dawowa Alhaji.


Tun kan ya amsata ta tsaya a daskare chak kamar wacce akayi freezing tana kallonshi dan ko iya dauke idan ta akan sa batayi ba.


haduwar sa da hasken fatar sa is flawless nd faultless..


Duk a tunaninta yay nisa bayanzu zai dawo gidan ba sai taganshi gatsau acikin wata sabuwar shiga datamai kyau bana wasa na, Sanye yake cikin kassaitacciyar collection din fitted jumfa na voile material kalar cool custard yellow da hadaddiyar hular zanna bukar me laushi a kife akansa duk Alamu sun nuna cewa Suman kanshi is silky black and shiny plain,askinsa low cut ne amma is very carved and stylish dan haka har hasken fatar kan na nunawa sosai..


Hannun sa daya dafa kofar kitchen din ta sake bi da kallo inda ta cikaro da wata xpensive clive cristian watch dake makale a tsintsiyar hannunsa tana wal wal sann kafafun sa sunsha takalman alfarma.


 Tunani tafarayi aranta ko shirin tafiya wani kasar yayi.


Kasa nitsuwa tayi dan gaba daya ya tsura mata idanunsa cikin rudewar kallon tsaf dayay mata for the first time arayuwarsa.


Kanta ta sauke kasa tayi shiru ganin har yanxu bai amsata ba kuma bai dena kallonta ba alkcin ko kwakkarn motsi ba ta iyayi bare tari.


Hafsat karamar yarinyace sosai amma ALLAH ya albarkaceta da jikin manya tana da cikakken hips tare da madaidaitan nonowarta da yanzu ne suka soma fitowa sosai, ita ba fara bace sann bakinta bai shiga wacce za'a ce dashi Baki wuluk ba, 


Daidaituwar shape din Karan hancinta ya samo kyakywan asali ne tun daga Shatin kerarren Sajenta wanda yabi cikakken giranta masu dauke da dogayen eye lashes.


Alkcin kusan Duk abunda yakeji aransa na rudewa haka nan ya kaucar fuska ba yabo ba fallasa yace mata "ya jikinki?


Ahankli ta dada sunkuyar da kanta for the moment tana sauraran bugun zuciyarta duk abubuwan da suka faru dazun ne suka shiga dawo mata daya bayan daya atake taji kunya ya rufeta.


kakkauran sautin muryan shin ne ya daki tsakar kwalkwarta har yasa ta saki siririn numfashi, ji take tamkar kirjin ta zai fado kasa tsaban tsanan ta bugunsa..not withstanding sai ta daure ta amsa cikin sanyin  murya mai tafe da tsoro tsoro aciki tace..jiki na da sauki, Sannu da dawowa.. duk de ta rasa me zatace, sai can yaga ta sulale kasa ahankli bisa kaan tiles cikin sanyin jiki muryanta na rawa rawa tace Alhaji dan Allah kayi hakuri bisa abunda ya faru dani dazu, nasan ban aikata maka daidai ba, ka gafarceni kamini rai karka koreni a aiki na maka alkwari bazan sake ciwo agidan nan ba.


Acikin wata rudaddaiyar kuka ta karashe magiyar duk atunaninta hala zai mata masifa tunda bata tabbatar da cewa acikin masu kudi akwai masu saukin kai da imani kamarsa ba.



Kallonta ya dingayi yanata mamakin furucinta aransa harta kammala rokonta da magiyar datake masa tay shiru baice mata komi ba.


Sai can snn ya hade rai ya soma mata tambayoyi duk dama tanajin mummunar shakkarsa amma bata sake ta gayamai cewa shemau ce ta hanata zuwa duba jikin mahaifyarta ba amma duk wani halin ciwo datake ciki tay masa bayani dalla dalla. 



Binne kanta kasa kawai tay tanata kuka marar sauti jin yadda yake mata fada acikin sanyin murya mai tattare da nasiha aciki. Yaune karo na farko dataji wani mutum mai kudi kamarsa yana mata magana acikin sassaukar harshe batare da hantara da cin mutunci ba.


"Ce mata yake ba a wasa da umarnin iyaye, bare ma uwa da Allah ya daukakata sama da kowa. Snn yaja kunnenta yace mata karta sake boye musu irin wann damuwar idan yana damunta dan itadin kamr Amana ce agaresu shida matarsa tunda duk wa'adin zamanta dasu anan gidan sei Allah ya tambayesu akanta ranar gobe.


Jikinta sosai yay sanyi tanata kuka tana bashi hakuri.


Kamar a wasa taji yace mata inane garin naku..tun bata kammala shako ma'anar tambayar ba, yasake cewa maza ki tashi yanxu ki dauko kayanki driver yana jira awaje ni zanbi na ajiyeki acan saiki dubata.



Jikin hafsa harna bari ta dago ta kallesa da wani irin yanayin tsantsar mamaki da ya mamaye fuskarta dan jin kanta tasomayi kamar a mafarki.


Godiya tafara masa tana sauke hawaye kamar an kunnata itadai godiyar kawai take zubo masa tare da adduoi batare da tasan metake furtawa bama.


bai wani kulata ba ya maida hnklinsa kan lokci ganin karfe uku aka nema na rana.


Ahankli yace mata ina waje. Snn ya fita.


Acikin sauri ta miƙe ta wuce dakinta babu bata lkci tafara tattara kayanta ajaka tana kukan murnan jin zata sake ganawa da mahaifarta ahankli tana kuma murmushin amsa mata adduarta da Allah yayi dan haryanzu bata gama dawowa cikin hayyacinta ba.


Within 10 minutes ta sauko rungume da jakarta ta rufe kanta da wani tsohon mayafi,kallo daya ya mata ya dauke kansa ya bude door din daya daga cikin motocinsa dake paker a tsakar gidan ya shiga gidan gaba snn ya bude mata itama ta shigo ciki.


Basu jima ba suka dau hanyar Aiport bayan tamasa cikakken bayanin inda kauyensun yake acan agarin jigawa, koda suka isa filin jirgi banda kalle kalle babu abunda hafsa takeyi jin kanta na juyawa kamr na wacce zata zauce da kauyanci dan tunda aka haifeta bata taɓa giftawa ta hanyar tashar jirgin kasa ba.


Wani babban office aka kaisu inda wani farin mutum sanye da uniform fari yake zaune, bayan sun gaisa da engr itama ta gaishe sa da sanyin murya gefe taja ta rakube tana daga tsaye tana kallonsu har suka kammala wata yar magana da harshen turanci sann yace mata tabiyosa su tafi, abaya abaya ta dinga binsa har suka kai cikin jirgi..lkcin banda bugawa da karfi babu abunda kirjinta yakeyi har aka kai kan seat dinta aka bata wajen zama,a sudade ta zauna kmr me jin tsoron wajen zaman tabi ta kame jikinta duba da yadda kowa yake mata kallon bakauyiya .


Da kyar da wuya ta iya kakalowa kanta nitsuwa ta sunkuyar da kanta can kasa ganin duk wajen babu wani mai kama da ita. daga nan baifi tafiyar awa da yan mintina ba jirginsu ya sauka a dutse intl airpot inda ya amshi motar dayay booking awajen ajiya suka kama hanyar izuwa kauyen nasu dake da dan nesa da garin jigawa.


Duk dama ransa a cunkushe yake da lamarin shema'u  baisa ya dena tausayawa halin da hafsat din ta shiga ciki ba musmn ganinta yar karamar.


Aransa bai taɓa tsammanin cewa dan hutun daya samu domin yahuta tare da matarsa zai kasance masa a wann yanayin ba sede arayuwarsa bai taɓa yin danasanin taimakon nakasa dashi.



Wajajen karfe hudu na yamma suka iso cikin wata kwarabbiyar hanya mai dauke da jan kasa dake babban jeep yake ja sosai kurar hanyar ta bude jikin motarsa.


acikin dan wani sukukun kauye suka billa wanda baifi a kirga mutanen cikinta ba, hausawa ne da fulanin tashi suke gauraye awajen suna rayuwansu cikeda rashin neman ilimi da tsananin talauci.


Wanda karancin temakon gwamnati da rashin kayan more rayuwa yasaka matayen suke yawan mutuwa ayayin haihuwa,hakanne ya jawo suke da yawan marayu da yara marasa galihu dayawa Wanda basu da uwayen da zasu rainesu daga sunkai shekaru hudu izuwa biyar za'a kaisu aikin gona, ko almajiranci ko aikin bauta irinsu wankau ko mai aikin gida ko na shago,in namiji ne koyay dako ko achaba acan wasu garuruwan masu nisan tsiya danma karsuna gudowa gida.



Zuciyar hafsat har kamar zai zauce da murna tsabar farincikin datakeji dataga kauyensu.


Mamaki ya dingaji aransa ganin duk wani kunyar datakeji ta kawar tana masa jagora ixuwa lungun da zai shiga...


Acan kusan karshen anguwa gidan nasu yake

Dan karamin gidane da aka zagayeshi da karare, tsabar talauci ko darajar samun kofa bataci ba yarwata tsohuwar tsommace data yayyage tay dukundukun aka rufe kofar gidan dashi tun daga waje kana iya hango cikin gidan.


Lkcin Inkaga yadda hafsat take dagokai tanamai washe baki zaka rantse ba itace takecikin matsanacin ciwo da damuwan nan ba.


Sunayin parking agaban gidan A nitse ta juyo ta kalleshi tacemai "Alhaj mun iso. Kallo ya karewa gidan nasu Baice mata komi ya gyada mata kai tareda bude lock din motar sann yace mata ta saukata shiga ciki tukuna zaishigo daga baya...


Batay mai musu ba ta sauƙa da kullin kayanta a hannunta, tanajin kafarta akasa wani irin shaukin son ganin mahaifyrta ne ya lullumeta, nan ta zuba aguje ta nufi cikin gidan nasu da murna tunkafin ya dago kai harta bude labulen nasu ta shige ciki..


Dakin mahaifyar tata ta burmu ciki dan ko labule bai ci darajar samu ba a wangale haka yake a fili.


Tana kaiwa tsakiyar dakin ta hango maman nata yashe akasa akan tabarma jikinta duk ya kangare bata iya motsi bare tay magana ga wani irin warin rashin wanka daya gamutse dakin..


Idanun hafsa na fitar da ruwan hawaye ta soma kirar sunan ta a ragwabe tana karasowa ciki" umma umma hansatu ce

Umma gani nan na dawo


Ahankli Har ta iso gabanta ta rusuna gwiwowinta kasa ta kamota jikinta ta rungumenta sosai iya abunda take furtawa kenan acikin gunjin kuka..


Wani irin tari mai fitowa da kyar umman nata tafarayi tana kkrin tashi jin muryan yar tata kamar acikin mafarki.


"Acikin wata iriyar nakasashiyar murya datay kamar na wance zata mutu ta soma cewa "Hansai?Allahu akbar ashe da rabon zan ganki kafin Na mutu..hawaye ne suka soma sauko mata tanakan tari tace na dauka mutuwa zanyi hansatu hala sede kizo ki kalli kabarina amma tunda kinzo Alhamdullh nagodewa Allah ko aynxu zan iya mut...t...uwa...

Acikin tari me karfi ta karashe maganan. Tana cewa hansatu ki yafe ni, kiyafeni..


Lkcin Jikin hafsa rawa yakeyi tanajin kamar notinan kanta suna ku cewa, wani irin azababben kuka mai kara ta fashe dashi acikin yanayin tsorata da gigicewar hankli me tsanani.


Umma dan Allah Dan Annabi karki mutu ki barni umma dan Allah kiyi hakuri karki mutu..

Wayoo Allah na na higa uku umma in wani lefi na maki ki yafemin kar daga zuwana kicemin zaki mutu..wallh hajiyata ce ta hanani zuwa wajenki na roketa kudin aikina amma tace bazata bani ba, wallh  ba kin xuwa nayi ba umma. Ummana dan Allah ki yi hakuri, dan Allah karki mutu kibarni.



Wani irin raunataccen  Kuka mai kara takeyi tanata memeta wayann maganganun acikin kukan nata,shikansa engr baisan lokcin da kururuwar tata mai cike da gaucewar hankli ya sakashi ya shigo cikin gidan babu shiri ba.


Tsayuwar cak yay daga bakin kofar dakin yanata kallonsu yana kuma jin abubuwan datake fada wanda yaso ya shigar dashi rudewa.


Kenan shema'u ta san da wann maganar amma tay shiru bata turo yarinyar nan gida tazo tay jinyar mahaifyarta ba


Salati ne ya kufce masa tare da shafa fuskarsa dayay ahankli yaname furta innalillahi wa inna ilahi rajiun kasar wuyarsa jikinsa atake tay mugun sanyi..


Cos All he saw was an immensed fear of being alone daya ke tsagawa a cikin razanannen sautin muryan karamar yarinyar nan.


Kukan datakeyi sam ba acikin hayyacinta takeyin shi ba, tunawa da yadda rayuwarta nan gaba zai kasance ne idan aka barta ita kadai a duniyan da ba uwa babu uba.


Take tahau tunawa da cewa itace silar mutuwar mahaifinta hamma Aliyu  a dacan asakamakon  gwagwarmayansa na son yaga ya sakata a makaranta tay karatu. sedei tun burinsa na hakan bai cika ba haka yan uwansa suka ji haushinsa suka taru suka lashe shi a maita.



Da kyar engr ya Tattaro nitsuwarsa ya karaso cikin dakin cikin karfin hali ya bambare hafsa daga jikin mahaifyarta sann ya soma mata tambaya ina mahaifinta yake ko yan uwanta dan taje ta kira masa wani muharrami sabida akai mahaifyata asibiti cikin gaggawa.


"...Dake ba acikin hayyacinta take ba bai dauketa wani mintin biyar wajen fayyace masa halin datake ciki ba.


Tace babana ya rasu da jimawa..yan uwan babana sun gujemu dani da ummah ne kawai muke rayuwarmu,ita kuma bata da cikakken lafiya,shiyasa tabada ni wa magajiya aka kaini legas dan ina aiki ina samo mana kudin rufawa kanmu asiri.


Alhaji Dan Allah dan darajar iyayenka ka taimaka min kar ummana ta rasu wallh bani da kowa a duniyan  sai ita.


Duk ya rasa meke masa dadi ganin rikicewar da yarinyar tay..


Baiyi kasa agwiwa ba ya tayata suka dauko mahaifyartan suka sakata a motarshi.



Fizgar motar yay cikin sauri suka bar kauyen izuwa nearby public hospital ganinsa me kudi

Yasaka aka tarbesu da sauri tarban mutunci aka bata gado tare da saka mata ruwa. Hafsat ke tare da mamanta agefe tanata adduar Allah ya taimaka mata ta farka daga sumewar datayi.


Shikuwa tunda ya fice waje baiyu wata wata ba yakira few contacts dinsa daya sani acikin garin jigawa nan aka masa arranging motar emergency daga general hospital jigawa.


Kafinsu iso daga cikin garin jigawa already har mahafiyar tata ta sha ledar ruwa yakai guda sha shida, agaggauce  aka dauketa izuwa cikin garin direct aka kaita emergency inda za'a ceto ranta cikin gaggawa.


Suna tsaye daga waje hankalinta sam baya jikinta shikuwa yanata satan kallonta ganin ta kasa tsaye ta kasa zanne.


Aransa gani yake kamar bai dace ya mata tambayoyi game da abunda dazun yaji tana cewa ba, wani zuciyar kuwa ce masa yake zai iya yuwa tsoron shemau yasata taki ta gaya masa gaskiyar maganan..inhar yana son ya san menene asalin gaskiya to dolene ya tambayeta acikin wann hali na rauni datake ciki yanzu hala bazata iya boye masa komi ba.



**********

Daga ta dayan bangaren kuwa sai kusan Wajajen bayan la'asar aka kammala daurin auren Alhaj kyari da amaryansa honourable Hajiya ramatu bukar ex minister of foreing affairs wanda ba ayishi a bayyane ba kamar yadda bokarta ya gindaya mata.


Hudu da rabi na yamma nayi aka kawo amarya.


Daidaikun matan ne suka fito tare da amarya cike da nuna tattali,a lokacin hamshakan kawayenta na harkan siyasa da ayarinsu ne suka sauya sautin iskan gidan hadiza da zazzakar sautin gudansu me karfi da zaƙi wanda kamar da gayya sukeyinshi ba.



Amarya har ila yau sanye take da cotton white lace an rufe mata fuska da tsaddaden mayafi mai sheki assorted with expensive swrasvoki stones hannayen ta sunji asalin jan kumshi duk inda suka wulga da ita tana fida wani irin azaban qamshi ahaka har sukayi cikin gidan da ita.


Duka duka Lokaci kalilan suka deba suna xaga wajen dukansu yan kawo amarya kowa yana raha ana sam barka,daga nan Har sashin amarya aka bi aka mata ban kwana cike da farinciki bayan nan kowa ya wuce mota domin a maidasu masaukinsu.


Itace a lullube luf zaune a tsakiyar fankacecen queen sized italian bed din dakin.


Babbar aminiyarta hajiya hasana ta dafa kafadunta cikin wata iriyar rangwadi tace toh Amarya ramatu zamu tafi...Allah ya bada zaman lpya.


Jawota ramatun tay suka dan yi wata magana kasa kasa acikin kunne.

 Cikin jadaddawa hasanan tace toh

Kawata karki wasa, ki dira ma aiki kawai, ki kuma tabbata alhaji yana shigowa dakin nan ko be nemeki ba ke kinemeshi dan aikin boka ya fara aiki akansa sosai, kema kinsan ai bazama ya kawoki gidan nan ba  kifara fidda wancan shegiyar yarinyar yau yau kafin ki share hanyar debar arxiki da matsayi.


Murya kasa kasa ramatu tace "Au har kuma sai kin nanata min ne? Ai ni a shirye nake shiyasa basai anjira dare yayi zamuyi harkan nan ba yana shigowa yanxun zakiga aiki da cikawa. Kin sanni wallh bani da imani, gagararrun mata nawa ne nayi fatali dasu a uwa duniya bare kuma karamar yarinya kamar Hadiza meitama banza da ita kusan sa'ar yar cikina. Kedai kije ki huta gobe zakiji yadda komi ya kasance.


cike dajin dadi hasana tace shegiyar kaya aikinki na kyau, ai dama Babban goro sai magogin ƙarfe tun asali irin gidan daya kamata ace kin kama kenan bana tsoffin stake holders ba.


Tace Kedai bari kawata ai inkinga nabar gidan nan to na sharewa kaina hanyar wata zazzafar siyasace, Ke nifa so nake nan da sati na gaba ya soma sokani acikin harkansa ta man fetur na kasa dan nafara kwashar rabona ina riftawa ciki toh kaf dinku kawayena sai na nema muku wajen ci.



Wani irin shewa hasana tay tabi ta rangwada guda mai karfi suna masu kwashewa da dariyar mugunta 


Heheheheh ramatu kice da zafinki kika zo.


Tace bari kawai kede sai kinjini...


Suna kammala zantar da hakan saiga kanwar ramatun ta shigo yi mata sallama itama, itade Tun isowarsu gidan ta kasa boye damuwarta wajen nuna zakewa da tambayar shin ina kishiyar yar uwa tata take? dake kusan dukan su basu taba ganin ta a fili ba, ita kam ko da sau daya ne tana so ta gan ta da idanunta dan taje gida tabada labarinta ganin Tunda suka zo gidan ba ace musu komi game da ita ba kuma ko yanxu ma ance musu tana nan acikin gidan a sashenta.


Abun ya dan dameta amma dayake anyi bikin agaggauce ne babu wata hayaniya sai ake yawan danne tsegumi,cikin son tada zancen tace Adda ramatu gashi har zamu wuce kishiyarki bata fito ba bare muganta adan gaggaisa,kakkaurar tsaki ramatun taja batace mata uffan ba.


Hasanan ce tace."Yo me ne aciki dan anyi biki har munzo kishiya bata fito ba? rashin fitowar ta ai Alheri ne agaremu.


Zata kara wata maganan ramatu tace ke da Allah kin fiye son gulma uwarki ce da sai kin ganta? Hassana sata agaba ku tafi ni karta batamin rai


Kanwar tata batace uffan ba ta dauki gyalenta tana cewa Allah baki haquri amarya muntafi..


Suna ficewa ramatu ta sauke ajiyan zuciya tare da yaye mayafin kanta tanamai dada bajewa akan gadontan.


Wayarta ta dauko tana duba sakonin bokanta tanamai sake nanata su.

Tsaki taja tare da jefar da wayar agefe duk ji take kamar Alhajin bazai shigo akan lkci ba.



Bayan nan ana neman wajajen shida na yamma saura shi kadanshi ya taho gida yanzu an manyata so there is less need for all fomalities na angonci, shiyasa tun da yamma aka sa masu kulawa da tsare tsaren biki suka sallame kawayen amarya da masu kawota gidan da goma na arziki.


Daga shigansa gidan nasa shashin hadiza ya fara kuskokai dan har saida aka daura aure  kafin nan ya dawo hayyacinshi ya tuna da cewa baima sanar da ita cewa aurensa yayiwu acikin gaggawa haka ba.


Yana saka kafarsa a site dinta kuwa yaji kanshi yayi wani mummunan sarawa sabida warin hayakin maganin hana aikin ramatu ci akansa datariga tayi,wani dishi dishi yake gani inda ya tsinkayo muryan Babbar mai aikin ta wato iya sharifat, a ladabce ta rusuna ta gaishe shi tare bashi labarin cewa hadiza ta bada umarni akan cewa duk wani mai himman ganin ta ya bari sai da safe bata son ganin kowa yanzu.


Har Ya budi baki zaiyi magana wani irin sarawa kanshi ya dadayi sanda ya dafe goshinsa,daga nan bai gane komi shikansa baisan ya akayi ya sallame ta ya juya  yabar wajen ba.


Yana tafiya kuwa iyaaa sharifat ta isar da sakon ta ciki inda hadizan take zaune...


Har tana batar kalma ta durkusa gaban su...


"Hajiya alhajin ya koma....


Lkcin Wani wal wal din walkiyar ababen hannu dana wuya ne kawai yake haska wuyarsu ita da shema'u suna zaune acikin shigarsu ta alfarma.


 Hadizar ce a zaune akan babban kujera na farko shema'u na agefe duk sun yi kyam suna faman shan qamshi dan duk wata hayaniyar guda a kunnensu akayi.


Gabaki daya ran hadiza a dagule yake dan tsabar tsanar datayiwa kishiya fitar da magana ma gagararta yayi.


tsaban iya kaskntarwa ko kallo shemau bata iya maida ma iya sharifat ba bare ta samu amsar ta

Sai Cahn dataga dama sai ta juyo,Maganan ma takanyi shi ne kasan fatar bakin taf kamar bazatayi ba.


tace ke da Allah ki tashi ki bishi ki tabbata ya shige sashinsa bayan yayi mintina goma aciki sai ki dawo ki gayamin.


Da barin jiki tace toh cikin ladabi ta mike ta fice after 11 minutes ta dawo tace musu eh yana ciki..


Gyada kai kawai hadiza tayi suka sallameta ta tafi.


Tana barin wajen shemau tay marmaza ta mike hurjan jan tare da sake mayafin ta cikin azama..tace hadiza tashi  muje ki shirya kanki kema zama bai kamaki ba.


Babu wani bata lokaci Cikin dakinta suka nufa ba Inda shemau ta fito da wata jaka daga kasar gado wanda bata tsaya bude shi complet bama ta zaro wasu fararen yadunan likkafi matsu karfi ta shiga warware su


agabanta hadiza ta tube tsindir ta nade ta da kayan tsaf izuwa dunduniyar kafafun ta.


Cikin sauri Tace "Durkusa acan ta mata nuni da tsakiyar fankaccen gadon ta dayaji jan kyalli daga gani ba tambaya kasan shima na tsafi ne.


A durkushe hadiza tasaka gwiwon ta a tsakiyar gadon inda shemau ta ciro karamin kwarya mai dauke da kwai ta rufe idanun ta tsam tana tofe tofen harufan sihiri aciki.


Bayan minti 2 ta bude idanuwan ta Kwaryan ta aje a tsakar kan hadiza tabi ta rage wutar dakin zuwa dim inda fuskokin su kawai ake iya ganewa.


Wasu ayoyin sihiri da alfa ya basu suka dinga karantowa, A hankali hadiza take maimaitawa Muryanta har na rarrabewa,alamu sun nuna kusan dukkan imaninta tasa take rerawa fuskn ta dauke da yanayi mai nuna matukar yardan da tayi wa abunda takeyin.


Basu tsaya ba har sanda suka kai aya sanda kwaryan dake kanta

Dakan shi ya bule dakin da wani irin hayaki mai raxanarwa..


Kwan shemau ta ciro ta mikawa hadiza tana kamawa ta fasashi acikin kwaryan.


Ganin komi ya kammala sai ta dauko karamin  karrrawa tana bugawa gyelen gyelen a gefen kunnen ta na hagu da dama. Nan suka faffadi bukatunsu akn ramatu


Cewa take ka tafiyar da ita kamar iska mai tsananin karfi da bai da matsaya sai madakatan karshen rayuwar sa.Ta tafi,ta kurmance kar ta tsaya har abadan abada.


sannan duka suka rufe ido suna mai rike hannun juna,Ko secnd basuyi ba Wani iska mai tsananin sanyi ya shiga ratsa su, bat kwaryan ya bace a dakin jim kadan komi ya washe kamar ba ayi komi anan ba.


Cikin sauri hadiza ta sauko suka nannade bedsheet din ta mika ma kawarta shemau


Lkci Shemau take kallo tana cewa toh Nidai baxan fito gobe ba sai ki tsaya kisha kallo.


Hadiza tace toh ai sai kije ki huta goben zamuyi magana 


Shemau tace toh Ni ma zan wuce kedai kisan yadda xakiyi nagaya maki bana son asaka mana ido yi zakiy kamar bakisan komi ba


Tsaki kawai hadiza taja tace wallh bana shayin su Ohon musu tunda ni suka so su taba.


Shemau tace Allah sa tana fita a karo na farko ta mutu.


Hadiza bata ce uffan ba,  har shemau taja mayafin

ta takama hanyar bude kofa,tsayuwar scnds tayi.

Tace..to nidai na tafi sai kinjini,hadiza na amsawa ta rufe mata kofar ta fice mai gaba daya agidan....

No comments