Breaking News

Cheaters Club 33

 33

SURAYYAHMS

#CHEATERS CLUB..



Bangaren halisa kuwa tunda suka fice a talba grp of companies meenal bata kyaleta ba daga nan suka wuce gidanta dake herbert marculay way acikin garin lagos..


Dake babu khaleel din yasa halisa ta zauna mata agidan sukadan sha hira, seidei Koda suka haura sama izuwa dakin meenal din anan ne halisa taga yadda take barin koinanta kaca kaca babu gyara..


bakaramin fada tay ma meenal din ba but as usual bata amsar lefinta saima cewa datake wai duk wani kazantar datakeyi agidan lefin mijinta khaleel ne


Hatta Indomie idan aka bata bazata iya girkashi batare da yay tsololon ruwa ba,sede kuma Ta mugun kwarance wajen iya girka magana yaji gishiri da maggi inda ko bakason ka amince da ita dan dolenka saika amince.


Tunda halisa ta isa dakin ko zama bata iyayi ba tahau tattara ma meenal kayanta data jibgasu a kasa acikin dakinta kusan kowanne da mazauninsa. 


Kama daga kan inner wears, jeweries,kai har kan jakuna da takalma cup din ruwa bootles din drinks komi akwai a dakin kamr yar bola jari. 


In kana neman mace ballagaza uwar shirgi toh inka samu meenal talba kazo bus stop amma kuma bazata taɓa amincewa da lefinta ba sede ta dorama mijinta lefin komi..


Haka ta dinga jujjuya magana Tana cewa halisa khaleel ne ya hanata kawo masu aiki sabida mugunta, tace kishin arxkinta yakeyi dan yaga ta kusa finshi kudi, acewarta shiyasa yake neman hanyoyi nason yaga yamaidata full house wife wacce zatazo ta zauna tana haihuwa masa bata da aikin komi, halama yace tabar masa ragamar kamfaninta daga bisani kuma yaxo yace mata ainashi ne.


Babu irin murde murden sharrin da bata laƙa masa ba wanda inhar ace bakasan khaleel ba to tabbas zakayi zaton mugun mutum ne bana wasa ba...


As much as yadda halisa take iya kiyaye yanke hukunci a bangare daya saidai kaunar datakeyi ma meenal aranta ya saka zancen khaleel din yake mugun bata haushi.


Cikin masifa halisa Tace ai kece kika nace saishi..

Nide mamaki kike bani Amina kullum kina complain akan mutum amma kina kan zaune dashi sai kaace ya tsafeki??? Ana dolene azaman auren?


Meenal tace halisa baxaki gane bane. Aure fa ya wuce yadda kike tsammani wata rana zakiyi auren nan bazaki so ace kinfito waje a matsayin bazawra ba

And besides khaleel bawai baya mutuwar so na bane kawai mugun haline irin namiji..as u know maxa sun tsane macen data san kanta take da kudi.


they alwys want us to be below and them above and i refused to be shiyasa kike ganin yana wakalantani... bace musu ake mu mata muna da rauni ba????

He just want to push me to the wall dan ya lura ina sonshi..


Halisa tace i dont really care about all that..nide nasan inhar mutum yana asalin sonka bazai aureka don ya kasance mugu agareka ba...

Wann khaleel din naki sai ahankli dai, tou ynxu dan ba mai aiki agidan nan shikenan akace bazaki zauna acikin tsafta ba...ki duba kitchen dinki komi yay kura hakama sitting rooms and ur room is even worst kai dolene anemo cleaners gobe.


Tace toh naji halsy zan nemosu kafin ya dawo inadai duk lefina kike gani bazakiga nashi ba??? Halisa nakan aikin jera mata shoes dinta tace eh mana bawai nace kina aikin duka gidan ba,keba mace bace? Nufina ur personal space haba meenal ai kyana gyara gado kinadan jera kayan sawa dakanki, Anya ma kina girki agidan nan kuwa??..tace ina yi mana  kefa kika sani a cooking class lokcin da zanyi aure ko kin mantane??


Halisa tace toh ai banga alaman kinayi din ba.

 

Tace tab khaleel din ne zai kyaleni hmm ai Saidai in baiya nan saina ci awaje. 


Kyabe baki kawai Halisa tayi batace mata uffan ba...bayan ta tsaftace mata dakinta tas lokin meenal din tana sallahn magrib taje kitchen ta dan gogge matashi snn ta dafa musu macroni da sardines around bayan  ishai suka xauna suka ci suka koshi sosai.


Aranta tasan rabonta dataci abincin agidanta haka ta manta amma kuma bazata taɓa iya nunawa halisa haka ba gudun karta masifeta.


Itade rainon carpet da carpet aka mata shiyasa tun tasowarta batasan me wahala ba, ta taso ne cikin kazantacciyar gata wanda ko hanyar kitchen din gidansu ma bata sani ba.


Daga karatu sai kallo sai tay kwalliya da sauran ababen nishadi amma duk wani abu daya shafi rayuwar ya mace inba na gayu bane bata taba saka kanta ta iyashi ba.


Zuwan halisa gidansu yasaka wasu abubuwan daga halayyarta na raina mutane suka dan sauya amma dake halisa na neman kudin kanta bata dogara dasu ba yasaka  abun nasu baiyi nisa ba


Meenal always feels like Allah bai halicceta dan ta zauna akarkashin kowa ba...


dik yan uwan ubanta ta koresune da baqin hali da sharri kuma mahaifyrta itace babban me daure mata gindi.


Shiyasa take living life inta in the spirit of feminism. That is, a Women is equal to man in all. Abunda namiji zaai yi itama zatayi, she dosnt even blive in respect or secrifices. Itade Kawai asota snn abauta ma heart desires dinta 


Money, beauty and knowledge are the true powers, and she have all of that at her beck and cour. 


Maza masu ruwan kudi sun bibiyeta adacan amma duk taki zama dasu, dan Bawani abune yasaka ta aure khaleel ba saidan mummunan son shi datakeyi acikin ranta kuma tasan yanada hankli da tausayi sosai infact shikadaine acikin manemantan data amince cewa zai iya zama da ita awann yanayin nata na mesonkai da kuma makirci.


 Koda zatayi aure ma halisa ce tafi kowa shan wuya wajen kimtsata..


Girki, iya zama da mutane da salo salo na zaman auren duk ta kaita inda ake koya amma haryau bata san cewa meenal bata iya aikata komi ba sedei ta fannin sex din intanason tay masa walaknci takan tuno da ababen da aka koya mata wajen motsa sha'awar É—a namiji danta wahalar dashi.


Anata karatun ra'aayin gani take kamar the more namiji yake samun jikinka the more darajarka yake raguwa a idonshi. Saidai ko kadan batay la'akari da cewa a babin aure good and respective sex life kamar gishiri ne mai kara dandano acikin shaanin zamantakewar aure wanda inhar babu shi fatak rayuwar auren zai kasance babu taste babu gardi kamr yadda zaka ci abinci marar maggi da gishiri.


Duk wayann shafukan bata sakewa ta gayama kowa dan tasan raayinta yasha bambam dana halisa..gara gara shemau wani bin yanayin tunanin su akan rayuwarsu yakanzo musu daya.


Ita Gani take kamr halisa da vicky da hadiza duk  wawayene masu karancin wayewa yan son soyayya shiyasa mazajensu suke abunda sukaga dama akansu.


Bayan sun kammala cin abinci da kamar awa guda uztaz ya taho ya dauki halisa suka koma gidanta dake victoria island.


Hakanan meenal ta tsallake kwanukan da sukaci abincin anan falo ta koma dakinta ta kunne computerta ta cigaba da ayyukan dake gabanta as usual khaaleel ya kirata yafi sau akirga amma dake bataga daman katse aikinta ba se bata dauka ba, bayan ta kammala aikin nata anan tay bacci bata nemesa. 



Ata fannin halisan kuwa da kyar ta samu baccin sabida abubuwan da meenal din ta cusa mata a brain dinta ya nugun daga mata hankli

Har wani hawayen tausayin meenal din takeyi sosai


Iya saukin datake samu wani bin shine inta tuna cewa yawancin accusation din meenal akan mijintaa din harsashe ne babu wanda ta kawo mata sheda ko guda daya amma duk da haka ji take aranta kamar dagske ne khaleel din ne mai laifi..



******

Washe gari Early morning wajajen karfe biyar dede

Halisa ta farka tarasa abunyi saita bude mac book dinta data bude boyayyen instagram acct aikuwa nan taga Dms daga wajen Dr khalid har guda biyu ya mata Hi yana tambayarta ko ta san Halisa sabida tarun hotuna masu kyau dayaga ta zuzzubasu a shafiin nata.


 Tana amsashi baifi da minti biyar ba sai gashi nan yay replying inta.


chating suka fara yi dashi in a flirtious way


Tanata wasa da hanklinsa karshe dei ta gaya masa cewa ai ita din sectariyar halisan ce.


Take ta bashi wasu information yana dubawa kuwa yaga hakane...


Nan da nan ya sake jikinshi yanata famar tambayarta akan halisa


Kai tsaye ya gaya mata cewa yana son halisar ne sabida she is beautiful and  a very rich woman mafarkin kowani dan adam. Haka Ya share fage ya zuzzugata da dadin baki atunaninsa sectaryace baisan da ita kanta yake chat din ba.


Yay yay ya kirata waya amma taki, ganin hakan yasaka yace mata ta masa hanya wajen halisan konawa ne zai biyata..wasa da hanklinsa ta dingayi daga baya ta masa alkwarin zata amso masa lambar halisa she assure him in suka soma chatting he will find it easier ya isar da sakonshi.


Suna gama chat din ta kashe tab din cikin mamakinsa sosai.


Duk dama dacan tay tsammanin hakan daga gareshi sabida rudewar dayake inya ganta amma daya tabbatar mata da zargina sai abun ya daure mata kai sosai..


Ta jima akan gado kafin nan tahau watsap, ganin grop dinsu na kawaye biyar tayi cike da sakonni alaman kusan kowa yana online tarasa meke faruwa taga ana ta zubo sakonni babu iyaka.


Tana hawa tabibbi chat din tun daga sama anan ne take sanin abunda ya faru da hadiza harma bata kasar.


Tanayin kasa kasa sai kuma taga hotuna dayawa da hadzan ta turo musu dashi.


Kaf dinsu sai murna suke ma hadiza dan kuwa labarin ashe ba haka bane. Tafiyarta na jiyan ashe babban suprise ne mijinta ya shirya mata a miami acan united state. 


Taje da zimman mijinta baida lafiya amma sai taga ashe ya hada mata gagarumin lovers eve ne

Ya narka kudi yasaka asalin indian  professionals decorators suka decorating wajen aka mata cakes ga flowers, snn ya siya mata huge huge gift boxes me dauke da 20 pieces of valueble jeweries na gold da rubies da emiralds da na diamond guda daya. Sai 10 pieces na other baby girl stuffs kamar su designer perfumes, italian rosale shoes, pret a poter, paris gowns. Flowers and teddys. Her favorites chocolates and drink da wanda aka saka sabbin kudade aciki.


Wajen da aka shirya domin suprise din agefen babban tekune and is all decorated in red and white balloons. Hatta kayan data saka ranar is all part of the suprises rana ne da hadiza bazata taÉ“a mancewa arayuwarta ba dan batayi tsammanin cewa mijinta zai nuna mata cewa ya gane value inta arayuwarsa har haka ba.  He also gave her a beutiful azurfa ring and a sport car na kamfanin mustang snn yace mata wann suprise din nuna godiyarsa ne daya kasance ta zama mace mai amana da nuna masa so na gaskiya badon abun duniyar dayake dashi ba, yace mata samun mace me amana irinta yay karanci

And he promise to value her for the rest of his life.


It was rhe most romantic day of her entire life hadiza tay murnan tay kuka tay godiya ma Allah har babu iyaka.


Ma kawayenta kawai ta iya nuna musu dukkan abunda ya wakana dansu tayata murna.


Dukkansu hudu babu wanda bai mata hawayen murna ba


Shema'u tafi kowa kuka acikinsu dake nata harda na makirci aciki,duk sai da tafi meenal zakewa tanata yabon hadiza tana cewa haqurine yakaita wann matsayin while a zuciyarta it become more reason enuf to hate her own marriege da mahmud.



Sunfi awa guda a grop din anayi ma hadiza son barka. Mijinta yace zata zauna tare da shi for a while tay hutu dan haka bazata dawo nigeria akan lokci ba.


Angama hira lafiya kalau

Masu bata shawara sun kara mata, masu yabonta duk sunyi angama kowa ya fara shirin abunda ke gabansa amma banda shema'u marafa.


She wasted almost 30 min tana sake kallon hotonan da hadiza ta turo musu agrp one after the other tana musu kallon kurel wanda kafin tagama kallonsu gabaki daya nunfashinta ya sauya salo.


Zaune take agaban mirronta taci kwalliya  tanata kallon kanta A raunane ta rike saman kirjinta da hannunta tana wani furzan da huci mai zafi waje.


A mind inta she was Like 

Whaat the hell is she doing here with mahmud.

Gacan Hadiza da bata fita da komi ba ta samu arzikin nan har kaman na banza. Itakenan ta rako mata duniya????duk wann kyanta da kwalisan tan nan saidai ya kare abanza kenan???


Wani irin Lumshe idanunta tay cikin karsashi jin zuciyarta ya raunana ya dawo baqi kirin. Cikin wann yanayin taji an dafa kafadunta qamshin turarensa kawai taji ta kwace kafadarta da sauri snn ta mike tsaye da wayarta a hannu tana masa wani irin matsiyacin kallo.


Mahmud tagani acikin blue pyjamas dinsa ta versace yanata murmushi. Ko kallonsa bata tsayayi ba ta bi ta mugun hade rai ta maida hanklinta kan wayarta.


Tsabar hanklinta baikansa A iska taji muryansa ayayin dayake ce mata good morning my love.


Bata amsashi ba ta nuna masa wayar dede wajen da hadiza ta sako musu hutunan expensive jewries nata ya karba yanata kallo, tsaki take ja up and down tanamai ce masa "see what ur mates are busy doing to thier wives and kana nan kana damuna da good morning my love toh  bazan amsa ba..

TO BE CONTINUED....

*PART 2 DIN SHINE GUNDURIN ROMANSIYYA DA NISHADI TARE DA DRAMAR DAKE CIKIN LABARIN.. ME SON YA SHIGA CIKIN WANN TAFIYA YA MUN MAGANA  DOMIN YIN REGISTER PAID GRP*

08060712446

No comments