Breaking News

Rainon Soja 28

 


                    28.

*Don Allah kar ki karanta wannan labarin indai baki biya kuÉ—in sa ba . Ga masu buÆ™atar payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake.... Regular group₦500 Vip group₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*

 

________________________

 

Mami~.

Saukowa Mami take yi gaba É—aya hankalin ta baya jikin ta , Haka zalika bata ko kallon gaban ta , a haka ta sauko daga stairs É—in nan . Su duka maida hankali suka yi ixuwa gare ta . Janar Khalil da Kuma Jidder . Cikin Sauri Khalil ya miÆ™e daga tsaye yana kallon Mami kana bakin sa ta furta “ Mami lafiya kuwa? Meke faruwa ne?” . Kallon shi Mami tayi wacce take isowa inda suke.  Kamin ta juya tana kallon direction É—in da Daddy yake shima ita yake kallo tare da jiran jin Menene ke faruwa don babu makawa yasan da AÆ™wai Abun dake faruwa a halin yanzu ” .

“Janar....! Janar Wai yanzu Hajiya Alawiyya ke faÉ—a mun anga Hajara kuma tana Raye!

 

Saurin miÆ™ewa General Saleh Yelwa yayi yana kallon Mami kamin cikin Sauri yace “ Me kike ce ? Hajara fa kike magana an ganta ? Wacce ta bar gida Na Tsawon sheÆ™aru sha shida(16) . Ƙwarai Janar yanzu Alawiyya ke sanar dani, Wai yanzu haka tana Gidan Mahaifinmu Bara na tafi yanzu ”. Tayi maganan tana gyara zaman Keys É—in hannun ta tare da juyawa tana nufar Æ™ofa . Cike da Rashin Sanin Wacece Hajara ? Jidder ta furta “ Mami zan biyo ki , Sannan kin manta baki É—auki mayafi ba”.

 

Hummm Jidder idan zaki biyo Ni bismillah amma mayafi bana takan shi a yanzu . Mami ta furta tana mai saurin ficewa daga Falon .

 

Da Sauri jidder ta bi bayan ta , don itama a yau tana son sanin Wacece Hajara , duk da Tasan Ƙanwar Mami ce , Amma bata san menene yabar da ita gida ba , kuma sannan a yanzu a wani hali take ? Tabbas zata so ganin ta Wannan yasata bin bayan Mami cikin Sauri , Don sau da yawa kafiyar Aliyu da gayunsa ana cewa “ Babu inda yabar Æ™anwar Mami wato Hajara , sai dai ita kuma rashin son jama'a musamman talakawa , sam bata son raÉ“uwa da Æ™aasÆ™antattu , a cewan ahalin Wai ita wayayyace Shiyasa . Bayan Mami jidder tabi inda ita take Driving, Mami ba É“angaren Hannun dama gaba ÆŠaya hankalin ta baya jikin ta duk ta Æ™osa ta gan ta gata ga Hajara , damuwarta na tsawon shekaru ”.

Early in the morning

7:00am......

 

Gudu take yi kaman tare da jijjiga jikinta tana kaiwa da komowa takaici duk ya ishe ta ga zufa dake tsatstsafo mata . Ƙwallah na bin kuncinta . Tun da nake ban taÉ“a ganin mugu irin Uncle Aliyu ba . Ta furta tana kallon can inda yake daga nesa yana kallon yanda take running exercise É—in, shikam Hannun sa ÆŠauke da Wani mug na coffee yana kaiwa bakin sa a hankali Æ™wance ”.

 

Go! go...!!! 

 

Ta tsinkayi Muryar sa daga can yana mata magana ganin ta tsaya , tana hutawa .

 

Da Sauri Ma'eesha ta É—aga Æ™afafunta tana cigaba da gudun tare da kukan zuci dana zahiri . 

 

Fiye da minti talatin tana a haka , kana ta fara ganin Jiri Jiri na É—ibarta .

 

Cak taja ta tsaya tana ganin hazo² 🫨 tana ganin duniyar na juya mata zuwa gida da yawa . Cike da É—aga murya babu wasa ya furta “ Tsayuwar mene kike yi anan , Ma'eesha na iso inda kike ranki zai É“aci , zan zane ki anan Wurin , a haka ne zaki je training É—in Sojan? What kind of nonsense exercise is that? . Zaki Cigaba ko kuwa sai na Æ™ariko nan??? Ya Æ™are maganan cike da Tsawa da ÆŠaga murya mai tare da amsa kuwa na cikakken Gwarzon namiji”. Maimakon ya ga tayi wannan kiÉ—imewar da ta saba yi a duk sa'ilin da taji Muryar sa ko faÉ—an sa amma a yanzu sai gani yayi tayi baya luuuuuuuuui tana zubewa a Æ™asa sharaffff”. Hasbunallahu wani'imal wakeel Innalillahi wa'inna.....Æ™asa Æ™are magana yayi da Gudun sa a matuÆ™ar kiÉ—ime ya nufo inda take yana É—agota cak tamkar bai É—auki mutum ba , kaman Æ´ar tsana ya É—aga....yana mai barin wurin tare da nufar moton sa yana bude gidan baya yana shimfiÉ—a ta , don ya lura Ko numfashi bata fitarwa ,Æ™wance take tayi sharÉ“an wannan yasa hankali a tashi ya fice daga Barikin Sojojin yana nufar Wata asibiti na kuÉ—i (private hospital) dake kusa dasu .

 

A harabar asibitin tun daga saman Upstairs É—in Wannan katafaren Asibitin Nurses da gudu suka fara saukowa zuwa Farfajiyar ajiye moto inda suka hango Aliyu Haidar fuskar sa a kiÉ—eme, haka gumi ke zubo masa . Idanun sa sun kaÉ—a sunyi jah . ÆŠagota yayi tamkar Æ´ar tsana yana saÉ“a ta tare da wani irin manna ta da Æ™irjin sa . Su kam Nurses hango kalon handon jikin sa na soja ne yasa su gudu irin haka , don sun san halin sojoji da bakar zuciya . Ƙarikowa garesa suka yi suna kai hannu tare da Kokarin Amsar Ma'eesha tare da cewa “ YallaÉ“ai kawota mu bata taimakon gaggawa”. Hummmmmm wata irin numfashi ya sauke tare da Ajiyar zuciya mai nauyi, fuskar sa ta sauya , a hankali cike da sarewa da karaya ya furta “ Rayuwata ce! 💔, ku yi mata kallo tun daga nan , idan zaku iya tada mun Ma'eesha na tsaya , idan ba zaku iya ba , na yi gaba na nemi asibitin da suka amsa sunan su ....idan kuma kuka ce zaku iya ,amma kuka É“ata mun lokaci abubuwa suka wuce sai daga baya kuka gaxa... wallahi tallahi na rantse da ALLAH Ma'eesha ta mutu a asibitin nan ko wani Abu ya Æ™ara samun ta kowa na Asibitin nan babu mai fita da rai .😲buÉ—e baki Nurse Zulfa'u tayi kana ta kalli nurse narret tana cewa “ Sister ma'amshe ta.....Saurin katse ta Nurse narret tayi tana kai Hannun ta tare da Amsan Ma'eesha daga hannun Aliyu kana tace “ Cool your mind Sir , everything will be okay ” .kamin ta jira jin mene Haidar zai furta da Sauri ta nufi Emargency da Ma'eesha .

 

Yallaɓai taho ga wuri ka zauna kamin mu fito .

 

Muryar nurse Zulfa'u ya katse Ali wanda yake kaiwa da kawowa , Goshin sa har wata jijiya ya fito masa na tsananin tashin hankali . Kallon banza ya watsa mata yana cigaba da kaiwa da komowa hankalin sa sam baya jikin sa . Baya ma sani Mene yake fadi a halin yanzu , tun daga zuwan sa , baya tsammanin zai dawo natsuwar sa sai idan Ance masa Ma'eesha ta dawo hayyacin sa. Tabbas a yau a kuma yanzu ya fahimci har a yanzu Ma'eesha rayuwar sa ce! Ba wai kallon da yake kokarin mata bane a yanzu , har a yau soyayyar nan nashi da kulawar da ya saba tun daga yarintar ta babu abin da ya ragu . Fiye da mintina talatin yana a haka gumi ya jiƙa shi sosai , don tuni nurse Zulfa'u ta gudu ta bar sa anan , don ta tsorata da lamarin Aliyu Haidar, ita ko a labarai bata taɓa jin na soja irin wannan ba. Zafin ransa yayi yawa ƙwarai .

 

Wannan yasa ta nufar emergency don ayi komai a gaban ta , idan Ma'eesha ta tashi to ta tsaya idan kuwa aka samu akasin haka , tabbas ita zata fara guduwa daga Asibitin tun kan a sanar mawa Aliyu Haidar ”.

 

Shikam Ogan namu Aliyu Haidar jin shiru tsawan mintuna kusan Arba'in yasa Shi fara tunanin nufar emergencyn , dai dai nan Wayar sa ta fara ringing tare da waÆ™ar mum my heart ❤️.  Wannan yasa shi fahimtar mai kiran tun kamin ya kai hannun sa ya É—aga sunan Mami ya bayyana masa . “ Cikin sauri tare da dai daita natsuwar sa yana Æ™aÆ™aro murmushin dole tamkar wacce Mami ke a gaban sa ya furta “ Mami Howfar? How is your day? . Fine HAIDAR where is my baby love ? Ina Ma'eesha na take ? Ta katse shi cike da annashuwa . Ƙirjinsa ne ya buga masa da Æ™arfi wannan yasa shi É—an kai hannun sa yana dafewa kana yace “ Mum she's well , Yanzu ta  samu barci amma zuwa Anjima zan kira ki kiji Muryar Babyn naki.

 

Murmushi Mami tayi mai sauti kana tace “ Alhamdulillah har naji sanyi da ya kasance tana lafiya a yanayin ka ko baka faÉ—a mun ba nasan Baby Ma'eesha tana jin dadin zaman ta anan , Ka kula mun da ita sosai Ali kana jina ?"…yeah...Yessss Mami ya furta cikin É—an kame kame . Cikin sanyi cike da rashin Fahimtar komai Mami ta cigaba da cewa “ Ina SO Aliyu ka kula mun da Ma'eesha don Allah ko bayan Raina, bata da kowa da ya kai ka a rayuwa , ina so ka riÆ™e Ma'eesha ba matsayin Æ´ar uwa ba , ba Æ™anwa nake so ka riÆ™e ta ba , ka riÆ™e mun ita tamkar rayuwar ka! A taiÆ™aice da da hali ka gatanta fiye da kowa ciki har Dani kai na. Ka É—auke ta tamkar Æ´ar da ka haifa ko ma fiye da haka . Idan kayi mun wannan To ka gama mun komai Aliyuuu don Allah ka sauke zafin ranka a kan ta , still now she's a child yarinya ce Æ™arama ka fini sani ka kula mun da ita sosai ko bayan rai na ”. Mami ki daina wannan maganar inshallah nayi Miki AlÆ™awari zan kula da ita ”. DaÆ™yau Haidar thank you my SOJA . 😬 dariyar yaÆ™e yayi yana jan Ajiyar zuciya tare da cewa “ Love You ma'am , bye bye ”....Æ™itttt ya datse kiran yana Fara nufar emergency don ganin halin da Ma'eesha ke ciki .

 

Kai tsaye ya faÉ—a inda yaga Wayan babu Ma'eesha babu labarin ta tamkar ba anan aka shigo da ita ba😱 . Keeee!!! Ya daka ma wata nurse Tsawa inda sai da kayan aikin hannun ta suka faÉ—i Æ™asa . Malama ina yarinya ta take ? Ya furta a zafafe idanun sa suna jajir tamkar garwashi jijiyo na ratso masa ta ko ina . Itace Ma'eesha ko? Ta far...far... farfaÉ—o an kai ta ÆŠakin hutawa”. Ta Æ™are maganan tana inda inda don ta tsorata da Aliyu . Huuuuuuuwwwww.....Ya Jah numfashi mai Æ™arfi kana tamkar ba shi ba , ya furta “ Na gode na gode da kuka taimaka wurin ceto mun rayuwar ta . Zaki iya kaini É—akin da take . Special room muka kai ta sir , amma muje na kai ka yanzu . Thanks....ya furta yana bin bayan ta ”.  Sun fito daga emergency room dinnne kiran taxt massage na mami ya shigo masa inda idanun sa ya fara rawa yana ganin SaÆ™on kaman ba dai dai idanun sa ke gani ba .

 

Ga abun da ta rubuta kamar haka ya fara karantawa .

_Hello Am sorry my son , na manta ban faÉ—a maka duk da Abin na raina , ka tayamu farin ciki mun ga Æ™anwata Hajiya Hajara wacce ta É“ata Tsawon shekaru goma sha biyar . Yanzu haka tana gidan Hajiya , kuma tana cikin Æ™oashin lafiya 🤗 naji a yanayin ka É—azu kamar kana busy shiyasa Nima na manta . But a ko wani lokaci kuka dawo zaku haÉ—u inshallah, please take care of my baby girl , idan ta farka kace mamin ta na gaishe ta ”._

 

Dafe kan sa yayi kana ya tsaya cak yana dakatawa da tafiyar a sarari yana furta “ Mom Hajara fa tace ? Matar da mu kan mu ba muyi mata cikakken sani ba , itace ta dawo ? Mom Hajara matar da tun da ta taso rayuwar ta ba'a Æ™asar nan take yin shi ba , rintse ido yayi yana tunanin to a ina aka ganta? A hankali ya fara tunawa da labarin ta . Kana yace “ Ƙaddara kenan ko wani bawa da kalan nasa life destination. Wannan abu da ya faru da Mom Hajara dama haka yake rubutacce ne a life circle nata . Kallon Nurse din yayi kana yace “ 1 minute please Ina so zan yi kira yanzu.  Yana maganan tare da fara kiran numbern Mami don yaji tabbacin Abun shin da gaske ne ko kuwa idanun sa ne basa gane masa dai dai .

 

Dakatawa da tafiyar nurse din tayi tana furta “ Ok sir ”.

 

**

Special room .

ÆŠago da sexy eyes É—in nan nata tayi tana kallon nurse narret da ke zuÆ™ar Allura daga sirinji Da'alama ita zata tsira mawa . Nurse gaskiya kin iya aikin sosai don kin yi kokarin ceto rayuwata thankyouuuu very much ”. Murmushi nurse narret tayi tana jin lokaci É—aya Ma'eesha tana shiga mata rai . Wannan Aiki na ne . Zaki iya faÉ—a mun sunan ki ?. Yessss ....Sunana Aisha seleh yelwa ,Amma ana kirana da Ma'eesha ”. Wow nice name . Nurse Narret ta furta tana Æ™arikowa zuwa inda Ma'eesha ke kwance .

 

Kinji sauÆ™i sosai ko kina jin wani ciwo a tare dake ?. No. Ma'eesha ta furta tana Girgiza mata kai tare da sakin mata murmushi. GyaÉ—a kai nurse narret tayi kana tace “ AÆ™wai wani Abu da zan taimaka Miki dashi ?. Saurin gyaÉ—a kai Ma'eesha tayi kana tace “ Taimako É—aya Nurse zaki mun , don Allah idan Uncle É—ina ya tambayeki me yasani suma a lokaci guda . Just told him that I can't be a land army , nauyin ba zan iya ba , I want to be a nurse like you . Amma shi Ya nace yana so na zama SOJA kamar shi . But for me I hate it at all , bana son zama soja Æ™wata Æ™wata .  So can You help me for .....is ok dear , kada ki damu na fahimce ki , a farko nayi tunanin yayan ki ne don kunyi kama sosai , kyaun ku iri É—aya . Sunana Narret ki dauke Ni tamkar Yar uwar ki, sannan zan Miki wannan taimakon amma Kema da akwai taimako É—aya da zaki mun wanda bana tsammanin zaki iya.

 

ÆŠan kallon ta Ma'eesha tayi kana tace “ Why can't I do it for you just go direct to the point,Ina sauraren ki .

 

Hummm....Numfasawa nurse narret tayi kana ta fara cewa “ Zan faÉ—a mawa Uncle É—in ki cewa “ Ba ki da Æ™arfin zuciya , ma'ana Abu kaÉ—an yana iya dagula Miki tunani hankalin ki ya tashi , wanda idan aka cigaba da matsa Miki da Abin da bai Miki at any time you can attack with heartbreak, so dole a rinÆ™a baki kulawa ana nesantar ki da dukkan Abin da zai É—aga Miki hankali , daga karshe dai kina buÆ™atar kulawa fiye da komai. Wow you are so wise Sis...😄 . Ma'eesha ta furta tana washe baki tare gyada mawa nurse narret Kai alamun maganar nata yayi mata dai dai .

 

Yanzu faÉ—a mun me kike a gare Ni , wani taimako zan kuma Miki indai bai fi Æ™arfi na ba ”.

 

Ina so kisa ma Uncle É—inki soyayya ta a zuciya🙀”. Ina son shi a kallo É—aya danayi masa .

 

What???🙀🤔 . Ma'eesha ta furta tana waro idanun ta waje kana ta cigaba da cewa “ Uncle Aliyu kike so? Please change .....ki sauya shi , Uncle ba mutum bane , ba zaki iya rayuwa dashi ba. Cox ba dai mutum bane kawai ki fahimce ni . Ban san na jefa rayuwarki cikin haÉ—ari . Zafin ransa yayi yawa bai san meye ma SOYAYYA ba .

 

 

Ya sani...., narret ta furta tana kallon Ma'eesha ido cikin ido . Kana tace daga lokacin da ya kawo ki nan , irin Soyayyar da nagani mai cike da tsafta da kulawa a kwayar idanun sa dangane dake abun ya tsuma Ni , sannan na dade ina neman namiji kamar sa . Komai irin wanda nake so ne na gani a tare da yayan ki ,sannan idan ina so  abu ko ta halin yaya ina samun shi .

 

Kin iya faÉ—a dai ko? Ma'eesha ta furta cike da Yarinta, tana cigaba da cewa “ I see like you're not Muslim are you a Christian? . No I'm not . Ni ruwa biyu ce , mahaifina musulmi ne ,mahaifiya ta ce take Ba musulma ba . Amma addinin mahaifina nake wato Musulunci .

 

Kar ki damu zan yi farin cikin ki zama daya daga cikin ahalin mu . Murmushi narret tayi tana kokarin magana kenan , suka ji motsin kofa da sauri Ma'eesha ta rufe ido tana jan numfashi tamkar mai barci .

 

Aliyu ne ya shigo da wannan nurse din , fuskar sa tamkar ba shi ba a yanzu . Wani sanyi yake ji yana ratsa zuciyar sa . Kallon narret yayi da ta kashe shi da ido yana cewa “ na gode da kukayi wannan kokarin , zaku iya bari na daga Ni sai Ma'eesha ina so na ganta sosai .  Okay sir amma yanzu ta samu barci . Okay . Ya furta yana takawa ixuwa inda Ma'eesha ke kwance kana Narret ta furta idan ka gama zaka iya samu na a Office sai nayi maka bayanin ciwon nata . Ok ya furta yana yin Æ™asa da Gwiwowin sa zuwa gaban fuskar Ma'eesha . Nan su kuma suka juya suna barin room É—in.

Hannun sa yakai yana shafa kyaÆ™yÆ™yawar fuskar ta . A hankali ya fara tuno da Shafa fuskar ta da ya fara yi a rayuwa kamar haka , a lokacin da take hali mawuyaci, na rayuwa ko mutuwa na hannun ALLAH . Wasu irin Æ™wallah ne yaji sun zobo masa suna sauka saman fuskar ta ,inda taji ruwan hawaye na É—igar masa . Lamo ta Æ™ara yi tana yi tamkar mai barci . Jin al'amarin take tamkar a mafarki dama Uncle Aliyu Yana kuka?.  A hankali taji laÉ“É“ansa yana sauka saman goshinta yana manna mata kisss 😘 tare da furta kalmar “ I love you!🥹 Cikin raunanniyar murya ya fara furta “ Na gode ma ALLAH da ya zamana kin farka babu Abinda Ya sameki Ma'eesha na , Tun kina Æ™arama nake Sonki na kuma raineki saboda mutuwar son da nake miki, me zai sa a yanzu na wahalar dake ....Saboda Wancen shashashan mana!!! Ya furta da Æ™arfi yana sauke wuci tare da kiran sunan Khalil da Æ™arfi , yana fara masifar nan nasa tamkar wanda Khalil dinnne a gaban sa . Dole kowa ya bar mun Ma'eesha domin ita din tawa ce ". Kun manta lokacin da kuka guje ta , ciki har da kai Khalil sai a yanzu Zaka ce kana Sonta wannan ba me yiwuwa bane , ba jin son ta kake a jinin jikin ka ba , a taiÆ™aice sha'awar ta kake yi , daga lokacin da kayi archiving what You want from her , shi kenan zaka mai damun da ita abun tausayi, a Kullum mafarki na Ma'eesha ta yi rayuwar farin ciki , daga hakan ne yasa Ni na yanke shawarar zama Abokin Rayuwar ta na har Abada! Ma'eesha ita kaÉ—ai zan Rayu da ita..........ya yi maganan yana kama hannun ta tare da maÆ™ale shi da nata yana É—aura laÉ“É“ansa bisa hannun nata tare da furta kalmar “ i  love you.......!

 

 

*Don girman Allah kar ki karanta in dai Baki biya ba . Regular payment ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 #mamanteddy#mrs usm.😘*

[1/19, 5:10 AM] Real~Mamanteddy: *🕊️RAINON SOJA🕊️*

*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*

 

 

https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS

Subscribe to my channel@maman teddy.

 

 

No comments