Rainon Soja 29
_________________________
Sosai yake kissing É—in taffaan hannun ta ta baya , wanda ita kanta Bata san iyaka Adadin lokacin da ya É—auka akan ta a hakan ba . Huwwwwmmmm....Saukar Ajiyar zuciya sa da taji ne yasa ta Æ™ara yin lamo tana bin lafiyar Gadon , duk da Zuciyar ta Wani irin bugawa yake da Æ™arfi da Æ™arfi amma kuma a haka ta daure ta kasa motsa koda É—an yatsa bare ya fahimci idanun ta biyu . Wata zuciyar ne take ce mata “ Ma'eesha kika yi kuskuren buÉ—e idanun ki ko kika motsa ki ka tashi daga wannan barcin Æ™aryar da kike yi Wallahi Uncle ya fahimci kinji mene yake cewa sunan “ Sorry , don sai ya karairaya ki . A yanzu
abun da ya kamata ki yi shine shiru ki kama bakin ki , Tom Amma Sauran Æ´ammatan sa duka baya san su ne? Me yasa ya ce dani kaÉ—ai zai yi Rayuwa? Shi kuma Ya Khaleel cewa yayi damu biyu zai yi Rayuwa, amma a zahiri Ya Khaleel shine gatana! Kamar wanda take magana a zahiri wata Zuciyar ta bata amsa da cewa “ Shi Ya Khaleel yana sonki fa sosai , Kuma bai taÉ“a cutar dake ba , Sannan yana San farin cikin ki ne sosai . Shi kuma Uncle so yake ya Aure ki don ku zauna daga ke sai shi yanda komene zai Miki babu mai gani ko yaji. Ohhhh kika FaÉ—a Hannun sa kin shiga uku . Gwara ma kiyi sauri ki karbi soyayyar Ya Khaleel da me son ki tsakani da ALLAH ”. Motsin miÆ™ewar sa ne ya katse mata tunanin ta , wannan yasa ta Yin shiru tana tsagaitawa har taji fitar sa kana ta Fara Ware idanun ta A hankali tana bin bayan wucewar sa Da kallo . Ƙarya kake yi Wallahi Uncle ban taÉ“a ganin mugu irin ka ba . Tun da na taso kake mugunta mun , ba zan taÉ“a bari na Aure ka ba , ina tausaya mawa macen da ta Aure ka , bare kuma Ni da kaina , ai tuni zuciya ta zata buga , ina dai maka fatan Alheri , Allah ya baka mata wacce zata iya haÆ™uri da halinka ”. Komawa tayi tana rintse idanun ta sakamakon kan ta da taji yana mata ciwo , alamun barci nason É—aukar ta . A hankali ta fara sauke numfashi kamin daga bisani ta fara tunanin irin horon Azaban da Uncle Aliyu ke bata wai duk na zama SOJA da Wannan tunanin ne wani nannauyar barcin yayi Awaon gaba da ita ”.**
Hajiya Atika ne ta kalli Rabi kana tace “ Inaso kamin yammaci
a yau Boka Aruguntsu ya Aiko da Aljanun fitina a cikin gidan nan , wanda zai
tarwatsa zaman Lafiyar Auren Hajiya Falmata , a taƙaice ina so Ta ko wani hali
A yau dai Falmata ta bar cikin gidan nan , ita da shegiyar Æ´ar cen nata , dama
duk wani abu da ya shafi nata ”. Tom an gama Hajiya , faÉ—a naki aikatawa na
Aruguntsu......Rabi ta furta tana wani ƙasa da murya irin na makirai, kana ta
cigaba da cewa “ Amma Hajiya KuÉ—in nan sunyi Æ™asa 100k fa , wannan Aiki ai
babba ne kece fa ta Alhaji Adamu, don haka ki daÉ—o wasu yanda kamin faÉ—uwar
rana zaki ga Aikin Aruguntsu . Kai tsaye cike da jin an fangama ta an fasa mata
kai Hajiya Atika ta furta “ Na Æ™ara Miki kamar sa akai masa 200k Ni dai fatana
Aiki ya biya . Wangale baki Rabi tayi kana tace “ Baki da matsala Hajiya Bara
yanzu na falfala don mu ga Aikin mu nan kusa . Yauwa rabi Shiyasa a kullum kike
ta hannun damata ”. Kwasar kuÉ—in Rabi tayi tana ficewa daga falon Hajiya Atika
kana tace “ Wannan kudin babu Wanda zan ba shi sai Basiru, ALLAH ka gani ina
mutuwar son wannan bawa , Allah ka taimake Ni kasa ya Aure Ni ya fiddani daga
Wannan zawarcin da nake ciki, ya kuma cire Ni daga Wannan Rayuwar bautar da
nake yi na Aikatau É—in gidan masu hali ”.
Da Hakan Ne Rabi ta gangara tana barin gidan Alhaji Adamu
Yes and No 😹 kana ta tare mai Adaidaita tana nufar layin da Take samun
masoyin nata wanda Allah ya sa mata Son shi a zuciya , shi kuma a kullum
wahalar da ita yake yi , don irin mazan nan ne yan iska masu lalata yara da
manya , kuma yana da Aure har da yara Amma shi Abin nashi munin yakai . Gashi
kamar baya barin mata haka kurum duk wacce yayi mu'amala da ita , to gaba É—aya
zaucewa take itace mai nemar sa ba dai shi ya nemeta ba . Sauke rabi mai
Adaidaita yayi tana biyar sa kuÉ—in sa tare da nufar layin , da jakar kuÉ—in ta
tuɓi tuɓi .
Post a Comment for "Rainon Soja 29"