Wata karuwa 41-42
41-42*
Wata ajiyar zuciya taja me Æ™arfi daga nan kuma numfashinta ya É—auke gabaÉ—aya bata dawo hayyaci ba sai washegari ta fara buÉ—e idanunta abubuwa na dawo mata ta sauke idanunta akan wani dattijo da ya zuba mata idanu yana sharar hawaye tare da yunÆ™urawa zata miÆ™e Abdu ya riÆ™eta ta lumshe idanunta hawaye ya zubo mata tace “Da gaske ne Abdu Baba da Mama ba sune suka haifeni ba dama da gaske yaya Hasina ba Æ´ar’uwata bace ta jini Abdu amma meye yasa suka riÆ™eni a matsayin Æ´a meye yasa Baba bai taÉ“a nunamin wata alama da take nuna bashine ya haifeni ba meye yasa yasoni ya nunan kulawa fiye da Æ´arsa ta cikinsa meye yasa bai yarda na sani ba sai yanzun?”
Ji tayi an kama hannunta ta buÉ—e manyan idanunta ta saukesu kan wata dattijuwa dake tsaye gabanta matar ne cikar kamala da nutsuwa tayi mgn cikin yarensu na Nufe tace “Mun daÉ—e muna tsumayi tare da addu’ar dawowar mahaifinki cikin ahlinsa ashe shi tuni ya tsaye a madakata kece zaki dawo mana Tabbas Hafsat É—ana Hamza yayimin alÆ™awarin Indai ya haihu sunana zai sawa Æ´arsa ya cikamin alÆ™awari ina alfahari dashi sannan inayi masu addu’ar samun rahamar Allah shi da Mahaifiyarki Hafsat na godewa Allah daya zamana kece kika zo a jikata kuma matar jikana ki kwantar da hankalinki zaki samu kulawa a wannan dangin kiyi hÆ™r da abinda Allah ya tsara miki har Æ™arshen rayuwarki”
Jinjina kai tayi zuciyarta na karyewa tare da wani kuka me ciwo tace “BantaÉ“a zata ba ban taÉ“a tsammata ba haka Allah yake tsara komansa cikin rayuwar É—an Adam ina gdy daya kasance ban samu cewa Ni É—in ina cikin mutane marasa nasaba ba sannan ina gde masa daya kasance ya jefoni cikin dangin da suka kasance masu cikakkiyar daraja….”
Saita kuma fashewa da kuka Abdu ya kamo hannunta yace “Amma yanzu babu inda keyi miki ciwo ko?” ÆŠaga kanta tayi ya shafa gefen fuskarta yace “to muje gda ki huta baby na ma ya huta” gabadayansu suka É—unguma suka tafi gdansu saida suka rakata har sashinta sannan suka koma tare da Abdu suka gyara sashin suka zauna zuciyarta duka babu daÉ—i kewar Baba na damunta lkc zuwa lkc tana zubar da hawayen rashinsa da haka komai ya fara huccewa tana rainon cikinta.
Cikinta yana da watanni bakwai wani sabon rikici ya bullo na auren da Abdul ya tattago sarai hankalin Aneey ya tashi da auren nasa duk da cewar batasan wace zai aura ba amma tayi bakin ƙoƙarin dannewa duba da cewa iyayensa duk sunƙi karɓar mgnr auren nasa shi kuma ya dage wannan tasa ta sanyawa zuciyarta dangana.
Sosai Mom take yaÆ™i da wannan aure amma Abdul ya dage Aneey da kanta taje ta samu Mom ta Bata hÆ™r tare da nuna mata babu komi Indai don itane abarshi yayi aurensa badon Mom naso ba ta haÆ™ura ta zuba masa ido yanata rawar Æ™afa akan auren har biki ya rage sati biyu bai kawo matar da zai aura angani ba wanda a al’adarsu tun biki saura wata É—aya ake kawo amarya ta gaisa da uwargidanta da kuma dangi
Shikam yayi mursisi yaƙi kawota Aneey ido ta zuba masa ita a yanzu ba shine a gabanta ba burinta kawai ta rabu da abinda ke cikinta lfy, abinda yake bata mamaki yanda yake kafkaf da duk wani abu da zaisa ta gane wani abu hatta katin bikin bai bari a gdanba saboda kada Aneey ta gani to itama dake ba abinne a gabanta ba ko mgn batayi masa ba harkokinta kawai takeyi.
Ana gobe É—aurin auren ne da dare suna kwance aka kirashi a waya ya mike ya fita kamar ance ta tashi sai ta tashi zata zaga bayi abinka da me tsohon ciki kawai sai taga wata Jakar wasiÆ™a ajiye da takardu a ciki tasa hannu ta zaro É—aya taga IV ne na biki tayi murmushi ta fara dubawa sunan mijin nata ta fara gani takai dubanta ka sunan macen _Hasina Ibrahim Garko_….. Ai bata gama karantawa ba ta sulale a gurin sumammiya tsabar tashin hankali hakan yayi daidai da shigowarsa yaganta cikin halin neman agajin gaggawa ta
Ya nufeta da sauri yana jijjigata baiga alamun zata miÆ™e ba Hakan yasashi É—aukarta sai asibiti tashin hankali suna zuwa likitan yace sakamakon faÉ—uwar da tayi saidai ayi mata aiki a cire mata babyn inba hakaba za’a iya yin biyu babu juyawa yayi cikin tashin hankali ya sanar da Mom abinda ke faruwa itama ta shiga É—imuwa ta kira Granny ta sanar da ita suka É—unguma sukayi asibitin a ranar akayi mata aikin bata farfaÉ—o ba sai washegari karfe goma da rabi lkcn saura minti talatin a É—aura auren Abdul-Ahad da Hasina koda ta farfaÉ—o da abinda ya buÉ—e baki kenan Mom dake da ita ta zubanta ido cikin faÉ—uwar gaba tace “Hasina kuma Aneey wacce Hasinan?” Kama hannun Mom tayi tace “Na shiga uku Mom Ni nasan watan barina gdan mijina ya kama wlh Hasina bata Æ™aunata da Abdu tayi alÆ™awarin ko zata rasa komanta saita rabani dashi Mom kiyimin wani abu kada ta rabani dashi wlh inasonsa…..”
Rufe mata baki tayi tace “Ƙuddun ubancan dama shine yasa yaÆ™i nunata a dangi aikuwa zai gane ya yaudareni ya munafurceni itama zata gane kurenta haba wannan wanne irin munafurci ne da cin amana….
Kuka ta kuma rushewa dashi tace“Wlh Mom ba ita taci amana taba nice naci amanarta….” ÆŠaga mata hannu tayi tace “nasan komai bakida laifin komai Æ™addara ce ta rubuto hakan kima daina damun kanki ki kwantar da hankalinki ki kula da Æ´aÆ´anki” miÆ™a mata yarinyar tayi tace “Ki bawa yarinyarki nono tasha ki manta da komai”
Yanda Mom ta rinÆ™a kwantar mata da zuciya yasata samun nutsuwa”
Ta zubawa babynta idanu kyawun yarinyar yana fusgarta tana sauke ajiyar zuciya tanajin wani farin ciki me gauraye da baÆ™in ciki farin cikinta na samun lfyrta da kuma ganin Æ´arta a hannunta baÆ™in cikinta kuma tunanin yanzu mijinta ya zama nasu su biyu ita da Hasina? Hasinan da take kallo matsayin shaÆ™iÆ™iyar Æ´ar uwarta ta jini yanzu itace kishiyarta?”
Ta jinjina girman al’amarin amma ta barwa Allah ikonsa tasan zai shiga lamarinta ya dafa mata.
Kwanansu uku a asibitin sannan aka sallamesu wani abin mamaki tun ranar É—aurin auren da safe har zuwa ranar da aka sallamesun baije asibitin ba wannan abu ya girgiza duniyar Aneey matuÆ™a musamman data samu labarin amarya ta tare ta girgiza gabanta ya rinÆ™a faÉ—uwa da Æ™arfin addu’a ta samu zuciyarta tayi sanyi, suna komawa babu kunya ya fito daga sashin amaryarsa ya shiga sashinta tana kwance da babynta a gefenta ta lumshe idanunta taji É—umin hannu a goshinta ta buÉ—e idanunta akansa ya lumshe nasa tare dayi mata murmushi yace “kiyi hÆ™r ban dawo ba wlh Æ´ar’uwarki ce tunda aka kawota batada lfy so kuma kinsan bata saba da mutane ba Gara ke kinga a cikin danginki kike…..”
Murmushi Aneey tayi ta yunÆ™ura ta miÆ™e zaune ta zubansa idanu sai taga duk ya rame tayi ajiyar zuciya tace “Babu komi” yanda tayi mgnr yasashi saurin kallonta tayi Æ™asa da kanta ya sunkuya yasa hannu ya É—ago kanta yace “ya Salam meye kuma na kukan?” Janyewa tayi ta kwanta tana jan zuciya yace “kinga don Allah kada kisa wannan abin a ranki kinga kinada heart problem wlh Aneey inasonki a duniyata bazan taÉ“a son wata mace kamar yanda nake sonki ba nifa tsoron halin da zaki shigane ya hanani sanar dake Hasina zan aura amma yanzu ai komai ya wucce kuma ina sanya ran insha Allahu lfy lau zaku zauna domin naja kunnenta akan banason fitina idan tanason kwanciyar hankali na to ta zauna dake da Æ´aÆ´anmu lfy idan kuma bataso to tayi duk abinda taga dama kuma kema nasan bazan samu matsala dake ba”
*Ki tausaya karki fitar mana dashi in kin siya ,Inkin san siya zakiyi don kiyi sharing don Allah karki siya mun hutashsheki,Haƙƙin mallakar marubutanne su kaɗai,Ki tausaya masu plz ,Inkinga wani pages na yawo to na sata ne ki runtse idonki karki karanta ki biyo ki siya ,Mungode*
•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*WATA KARUWAA* Na kuÉ—ine ,Zafafa ne Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU✨ MASU HASKAWA* Da suke zuwa maku daga alÆ™alumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haÉ—a da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA’AWA* Daga AlÆ™alamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauÆ™an farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *ÆŠaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800
_Manyan mata kuma Æ™asaitattu ba’a barku a baya ba,ganaku kaÉ—an cikin tunjimin aljihunku_
*ÆŠaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000
•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_Zaki biya ta wannan Bank account É—in_
0255526235
_Fauziyya Tasi’u. GTbank_
Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932
Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265
•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265
♡♡ “`Sai munjiku Masoyan Amana….ShareShareAnd ShareHabibties Allah ka barmu da masu sonmu“`♡♡
*OUM HAIRAN*
[12/28, 6:04 PM] Oum Hairan&Affan:
Post a Comment for "Wata karuwa 41-42"