Breaking News

Yanci da Rayuwa 17


Arewabooks;hafsatrano

Page 17

***Da safe tayi ta expecting kiran Asim amma shiru har suka fita asibitin ita da Malam Hamza da Salamatu. Da sauri ta isa wajen Baban ta rungume shi, ganin sa ya dawo mata da abinda ya faru jiya sai ta soma kuka.

“Kinji ki kuma, ke kuka baya miki wahala ne?” Baban yace yana mata dariya

“Tun jiya take yin sa, yanzu da ta ganka kuma shine kukan ya dawo sabo.” Malam Hamza yace yana dariyar shima

“Karki zama sokuwa mana.”

“Baba kafar ta daina ciwo?” Ta tambaya tana goge hawayen da bayan hannun ta.

“Ta daina yar Baba, dama kulawa take so da magani, yanzu kinga da anyi aikin shikenan za kiga na mike na soma takawa shikenan fa.”

“Allah ya sa, Allah ya baka lafiya Baba na.”

“Amin Amin uwata.”

Kiran wayarta akayi ta kalla da sauri, ganin me kiran yasa ta kallon Baban nata, shima ita yake kallo. A darare ta daga tana rage volume din sosai.

“Ina waje.” Yace tana dagaawa

“Nazo asibiti wajen Babana.”

“Bashi da lafiya?”

“Eh za’a yi masa aiki a kafar sa ne.”

“Ok, ki duba shi, I will see you idan kika dawo.”

“Ok.” Tace a sanyaye ta ajiye wayar

“Wacece?” Baban ya tambaya bayan ta ajiye wayar yana karantar yanayin ta.

“Daga gidan aiki na ne.”

“Ok, fatan dai ba tahowa kikayi baki fada musu ba.”

” A ah baba, sun sani.”

“Toh madallah.” Yace yana maida hankalin sa wajen Malam hamza suka cigaba da magana. Tashi tayi ta zuba ma Baban abincin da aka shigo dashi sanda suka zo sannan ta zuba ma Malam hamza yace ya koshi sai ta kara musu akai suka ci ita da Salamatu.

“Wai har abinci suke baku ne asibitin?”

“Eh har kudin abincin suka biya wallahi, ni dai bansan wacce irin godiya zan musu ba.”

“Allah sarki, Allah ya saka musu da alkhairi.”

“Amin Malam.”

Su dan dade a dakin har su Ammar din suka zo, suka gaisa dasu sannan suka fita. Sallama Malam Hamza yayi musu yace zai wuce kasuwa suka bar Noor din kawai sai me kula da Baban da Saddam ne ya samo shi.
Hirar su suke da Baban nata cikin farin ciki hakan yasa ta manta abinda ya faru gaba daya dama kuma tayi alkawarin sai an masa aikin sannan zata fada masa abinda ya faru. Sai da akayi la’asar sannan Baban yace ta tashi ta tafi kar su neme ta, dole ba dan taso ba dan kar ya gano wani abun yasa tayi masa sallama ta tafi.
Daga office direct chan ya wuce dan ya riga yayi niyyar ganin ta a yau din, sai da ya kusa sannan ya kirata yace mata ya kusa, tashi tayi ta shiga daki ta dauko Hijab ta zura sannan taje ta samu Salamatu a kitchen tace mata zata karbo sako a waje. Amsa mata tayi ta fito rike da key din gidan su taje ta bude ta dauko sabon Hijab dinta ta saka. Kiranta yayi yace mata ta fito, ta fita ta hango shi daga chan nesa yayi parking. Jikin ta a mace ta karasa jikin motar ta dan yi knocking kasancewar glass din baki ne. Yana kallon ta tunda ta fito har ta karaso sai kawai ya bude mata kofar yace ta shigo saboda yadda yanayin area tasu take da mutane da suke wucewa hakan yasa ya zama uncomfortable tunda ba sabawa yayi ba. Bata musa ba ta shiga ta zauna a darare sai kawai yayi wa motar key ya hau saman titin ba tare da yace komai ba.

“Ba dade wa zan ba.”

Tace tana kallon sa. Daga gefe ya samu yayi parking ya juyo yana kallon ta sai taga gaba daya kamannin sa sun sauya mata zuwa na Rafeeq a sanda ya fito da ita. Har yanzu fuskar sa babu walwala ba kamar yadda ta saba ganin sa ba.

“Are you alright?”

Da ka ta amsa da eh, ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

“Bansan me yasa ba, I’m just not happy, about abunda ya faru da komai. The worst part of it shine me yasa tun farko baki fada min wace ke ba? Me yasa kika boye min bayan kin gane ni sarai, kika cigaba da playing da heart dina. Ranar nan I waited for you for more than an hour, thinking zaki zo, ashe kinsan komai kika barni a duhu.”

“Kasan yanayi da tsarin gidan, ba zan yi abun da zai jawo min matsala ba, shiyasa na boye maka kaina. Kuma Hajiya bata so nayi wani abu da za’a yi noticing dina a gidan, shiuasa.”

“Yanzu matsalar fasa faruwa tayi?”

“A ah.” Ta girgiza kanta

“Then babu point din boyewa, you should have told me everything. Da zan iya protecting dinki daga banzayen yaran nan marasa kunya.”

“I’m sorry.”

“It’s ok, ya wuce. Karki sake kin daukar wayata, kuma karki sake tsoron kowa, karki Kuma sake yarda kiyi rayuwa mara YANCI irin rayuwar da kikayi a gidan nan.”

“Ba zan sake ba.”

“Just promise me, kiyi min alkawari shine hankali na zai kwanta.”

“Nayi alkawari.”

“Good, ki jirani please. Zan je na karasa wani abu amma zan dawo, zan dawo da magana me muhimmanci a tsakanin mu, for now just wait for me.”

“In sha Allah.”

“Thank you so much.”

Yace yana jin dukkan burden din dake heart dinsa na tafiya a hankali. Har in da ya dauke ta, ya dawo da ita yana kallo ta fita ya zuba mata ido har ta tsallaka ta shige lungun su. Wuta ya bawa motar ya bar unguwar ganin magriba ta karato.

***Zaune suke a falon Hajiya Hindatun manyan kwalayen juice masu sanyi me aikin gidan ta jerewa Mummy a gabanta hade da snacks kala kala, duk ba wannan ne a gabanta ba a yanzu, saboda haka ko da tace zata zuba mata tace ta barshi. Fita tayi ta jawo musu kofar Hajiya Hindatu ta kalleta tana muskutawa kusa da ita sosai.

“Hajiya me yake faruwa me? Tunda naganki na san akwai matsala babba, me ya faru yanxu kuma? Ina fatan ba shaanin siyasar mu bace ba.”

“Ku kusa ko alama, wannan matsalar cikin gida ce, na rasa wanda zan fadawa zuciya ta, tayi sanyi wallahi.”

“Assha, menene ya faru? Ko ke da Rafeeq din naki ne da bakya son daukar wani mataki akansa kullum cikin kara yi miki nisa yake amma kin gaza ganewa. Da anyi magana kice be miki komai ba.”

“Humm, idan ma matsalar Rafeeq ne ai mai sauki ce, Asim ne wannan karon yazo min da abunda zuciya ta ba zata iya dauka ba.”

“Me ya faru?”

“Humm, wai kamar ni Hajiya, da nake da confirmation na zama minister nan da dan lokaci kadan,wai nice Asim zai cewa yana son househelp dita, yarinyar da naki jini na tsana.”

Zaro ido Hajiya Lub tayi ta rike baki alamun maganar ta taba ta

“Ban ji da kyau ba fa.”

“Househelp me aiki me dafa mana abinci, wai ita Asim yake so. Kuma ya kalli tsabar ido na ya tabbatar min da haka. Jiya ko baccin kirki ban ba saboda bacin rai, dama Rafeeq ne yace yana son ta da murna zanyi dan nasan halin ubansu toh tabbas sai sun samu matsala amma Asim fa? Duk yadda nake kokarin kare shi wajen mutumin nan yana ballo da maganar nan zai wargaza komai, yadda yake jin dama Rafeeq ne kawai zai iya kula masa da dukiya kinga ai sai ya kara sakar masa komai da hujja.”

“Lallai ashe Asim din ma bashi da hankali ban sani ba, ina shi ina gayyar tsiya dan Allah? Yanzu sai kawai a ganmu da mutuncin mu a gari munje nemar wa danmu aure a karamin gida? Ina ba zai yiwu ba. Idan har zaki tashi tsaye kiyi abinda zakiyi toh, yaran nan kamar mayu suke in dai suka kyalla ido suka ga mai kudi sai sun shiga ta karfi kin sani.”

“Ai na rasa yadda zan ne wallahi, tsorona maganar ta koma kunnen AJI, kinsan shi sarai akan hakan zai iya tafka mana rashin mutunci ba ruwan sa wallahi. Dama kamar dan dole yake zaune damu amma koman sa Rafeeq dai.”

“Toh kuwa akwai aiki a gabanki, kiyi kokarin dasawa Asim din tsanar Rafeeq ta yadda zai fara goyayya dashi a komai, shekara nawa dududu ya bashi da har za’a ga wannan fikikon, nace shekara daya ce ko?”

“Wata tara ne ma.”

“Toh, shine amma kika zuba ido haka?”

“Ya zanyi toh? Kinsan dai rashin mutuncin mutumin nan ba sai na fada miki ba, duk in da na bullo masa sarai yana sane.”

“Bafa dama ina nufin wai ki samu Alhaji da maganar ba, ki zauna kiyi tunanin abinda zaki, ki raba kansu gaba daya, shine kawai hanyar samun YANCIN Asim a gidan uban sa.”

“Zanyi tunani naga me ya kamata nayi, dole na dau mataki abun ya ishe ni, a aure maka miji kuma a hana yayanka sakat, kai ni wannan mata ta zamar min jaraba, duk da bata gidan amma me ya sauya?”

“Laifin ki ne fa, Amma dai duk yanzu ba wannan ba,kiyi abinda ya dace kawai dan ni kaina na gaji da takaicin nan.”

“Zanyi kuwa, a yau yau din nan zan samu mafita in sha Allahu.”

“Yafi dai kam, kisha juice din kafin su yi zafi, ko a chanjo miki wasu?”

“Ruwa ma ya isa, banga ta zama ba ai.”

Zuba mata ruwan tayi tasha sannan ta tashi zata tafi. Har gaban mota ta rakota sukayi sallama ta tafi.

***Daf da magriba yana zaune a falon hotel din Saddam ya yi knocking ya shigo, waya ce a hannun sa a kunne yayi saurin mikawa Rafeeq din a hankali yace

“Alhaji ne.”

Sai a lokacin ya tuna wayar sa me personal line din sa tana kashe, karba yayi ya cireta daga handsfree din sannan ya karata a kunnen sa cikin girmamawa yayi sallama hade da gaisuwa.

“Kazo gida ka sameni yanzu.”

Yace ya kashe wayar. Mikawa Saddam wayar yayi ya mike. White Burberry shirt ce jikin sa da dogon wando dark ash sai kawai ya zura sneakers dinsa akai ya dauki waya daya kawai dan sai gobe yake son barin hotel din suka fita tare da Saddam din. Suna hanya Asim ya kirashi yana tambayar shi ko ya dawo. A kusan tare suka karasa da shi da Asim din da Mummy kuma dukkannin su part din AJIn suka wuce dan Mummy ma tun tana hanya ya kirata yace ya dawo.
A falon suka zauna bayan sun gaida Mummy ta amsa tana wuce wa bedroom din AJIn, jim kadan suka dawo tare yana sanye da jallabiya irin ta manyan alhazawa, yana gaba mummy na bayansa duk su kuma suka mike saboda kowa yasan shi mutum ne me son respect dan haka ne ma baa jerawa dashi haka baka zama sai ya baka izini. Sai da ya zauna ya harde sannan yace su zauna duk suka zube a kasa Mummy ta zauna a gefen sa tana gyara masa wuyan rigar sa cikin kissa da son nuna ita din ta isa dashi duk da tarin izza da yake da ita.
Gyaran murya ya soma yi sannan ya shiga magana wanda kusan dukka akan maganar da sukayi last da Rafeeq ne domin mahaifin su Laila ya matsa masa da maganar yana so su kulla zumunci duk da abokin sa ne sosai amma hakan ba zai saka shi karbar maganar ba idan har ba Rafeeq din ne ya gaza kawo masa daidai da raayi da akidun sa ba.

“Ya maganar mu ta kwana Madaki?”

Yace yana zura idon sa akan sa yana jiran yaji yace gata, ya fara jero tambayoyin sa.

“Ban samu ba AJI, na bar muku zabi koma wacece.”

“Tohh, madallah. Kai kuma Wakili fa? Ya muke ciki?”

Sosa kansa ya danyi zaiyi magana Mummy tayi karaf tace

“Ai Asim akwai yarinyar da yayi min maganar ta, so nake su kara fahimtar juna daga nan sai na sanar maka.”

“Toh madallah, Allah yasa dai yayi abinda ya dace.”

Maganar ta dan bata haushi amma sai ta danne, shi kuwa Asim zuciyar sa cike da farin ciki a tunanin sa maganar Noor Mummy take yi, hakan yasa yayi godiya kawai ya bi bayan Rafeeq da yayi musu sallama shima.
Suna fita ta sake matsawa jikin AJIn ta shafi gefen fuskar sa sannan tace

“Alhaji maganar Rafeeq, ka bar komai a hannu na kasan ba zan taba yi masa zaban tumun dare ba.”

“Zaki iya? Irin kalar matar da nake son Rafeeq ya aura zaki iya samo ta?”

“Kamar anyi an gama ne ai, kawai a soma shiri dan ba za’a ja abun ba.”

“Shikenan zan bawa Alhaji Mannir magana, idan yaso ko daga baya ne sai ya auri Lailar idan yana da raayi.”

“Hakan yayi, kuma ba zai ji haushi ba tunda ana tare.”

“Idan yaji ma ai shi ya sani.”

Cigaba da abinda take yi masa tayi,dan duk taurin kai da kafiya tasa wuyarta ta soma bi dashi ta hanyar da yake so, yanzu labari zai chanja, hakan kuwa akayi bata baro sashen nasa ba sai da ta tabbatar ta gama samun abinda take so.

_”Tunda nabi ta lallami ya kasa gane illar da taraiyar sa da Rafeeq take a gareshi, na tabbatar idan na yi masa da wannan yaren zai fi saurin ganewa. Shikenan na jefi tsuntsu biyu da dutse daya.”_

sai tasa dariya cikin jin dadin yadda plan din nata zai kasance.

No comments