Breaking News

Yanci da Rayuwa 23


Arewabooks; hafsatrano

Page 23

***Duk yadda taso ta danne bacin ranta sai da ta gaza, haka ta daure suka koma gida ta kira Hajiya Maryam tace ta bata address din gidan zasu daukowa Rafeeq matar sa, address din ta tura mata hade da number Noor din sannan tace zata isa gidan itama yanzu.

***Noor na zaune ta hada tagumi saboda tunanin tafiyar da zatayi, kayanta ne a cikin wata yar madaidaiciyar akwati da Baban ya bayar aka siyo mata a jingine a gefe, kamar almara haka ta dauki maganar auren sai gashi ta tabbatar har yanzu ana maganar tafiyar ta, Salajnmatu ce ta shigo dakin rike da sabon mayafi ta mikawa Noor din sannan tace

“Ki cire Hijab din nan ki yafa wannan, sannan ki saki ranki kinga kar ki tada hankalin mahaifin ki, ki daure aure ba mutuwa bace ba, rayuwa ce zaki yi ta, ta yanci da jin dadi in sha Allahu ”

“Bana so na tafi na bar Babana, shi kadai ne fa ba kowa.”

“Sanda bashi da lafiya ma shi kadai din yake zaune, bare yanzu da ya samu lafiya, ki godewa Allah ba kowa ne yake samun irin wannan damar ba.”

“Ban fada wa kowa ba, amma Hajiyan su bata so na, ta tsaneni.”

“Toh ai naji an ce ita da kanta ta nemi izini wajen Baban, ki tsarkake zuciyar ki kawai karki ma sakawa wani ranki tunani.”

“Toh, amma fa shiru ko kirana be yi ba tunda aka fara maganar nan.”

Ringing din waya ne ya katse maganar da Salamatun zatayi sai tace

“Wayar waye ke ringing?” Salamatu tace tana waigawa dakin jin ringing din waya a cikin kaya

“Tawa ce.”

Dago labulen akayi, kanwar Salamatun ta leko tace

“Kizo in ji Baba.”

Kallon in da jakar take tayi, zuciyar ta na gaya mata shine yake kira, wucewa tayi kiran Baban duk da tana cike da son amsa kiran.

Yana zaune a dakin shi, shi kadai ya birkito wata akwatin shi ya hargitso kayan.

“Baba gani.”

“Yawwa yar albarka, shigo kiga wani abu.”

Karasa shiga tayi, ya dauko wata jaka karama ya mika mata

“Jeki kasa wannan cikin kayanki, ki adana shi sosai idan kika nutsu sai ki duba.”

Hannu biyu tasa ta karba sannan tayi godiya, fitowa tayi sai ga Hajiya Maryam sun shigo ita da jamaar ta, sosai hakan yayi ma Noor din dadi taje ta rungume ta suka dariya a tare.

“Wannan wacce irin amarya ce ido kyamas babu kuka.” Tace tana dariya. Rau rau tayi da idon ta zata fashe da kuka tayi saurin cewa

“Wasa nake miki ba, karki bata fuskar ki ango yace ya fasa.” Dariya suka yi dukka aka zauna ana jiran zuwan su Mummyn. Daga zuwan su Hajiya Maryam din babu dadewa suka iso a wasu shegun motoci tun daga kan yanayin unguwar suka fara mita su Ummita da Aneesa ita kuwa Laila wani irin haushi ne ya turnike ta ganin wai Rafeeq ya rasa ina zai dauko mata sai a wannan ghetto din, wannan ba karamin raini bane ya jawo mata ace wannan ce kishiyar ta gaskia ya zubar mata da aji. Kin fitowa tayi daga motar wani wani lungu da za’a shiga Ummita da Aneesa kuwa suka ce sai sun je sun bawa idon su abinci ita dai Mummy batayi magana ba har suka isa kofar gidan sannan suka shiga kai tsaye.
Da sauri Salamatu ta rufewa Noor fuska da mayafi jin sallamar su, suka shigo suka tadda Hajiya Maryam a tsakar gidan an riga an saka tabarma dama a tsakar gidan sai Mummy da Hajiya Lubabatu suka zauna Aneesa da Ummita kuwa tsayawa sukayi a tsaye dan gaaba daya ji sukayi suna kyankyamin tabarmar Ummita har da matsawa ta faki ido ta zubda yawu.

“Sannun ku da zuwa.” Hajiya Maryam tace cikin farin ciki dan tunda aka fara maganar nan har zuwa yau tana cikin jin dadi ganin itace sanadin wannan alakar shiyasa ma ta tsaya akan komai kuma ta kara yarda da tabbatarwa mummy din yar siyasa ce ta gaske mara duba matsayi ko ajin mutum kafin tayi masa abu. Gaishe gaishe aka dan yi Baba ya fito shima suka gaisa sannan suka ce zasu tafi, Hajiya maryam ce ta tashi ta shiga cikin dakin ta riko hannun Noor din ta fito da ita wajen su idon ta a rufe. Da sauri mummy ta mike ta taro ta jikinta tana murmushi

“Bani diyata Hajiya.”

“Gata nan.” Tace tana dariya, aka saka dariya gaba daya.

Hajiya Lubabatu ce ta rike Noor din, ta kaita har mota tana kuka tamkar ranta zai fita, kusa da Laila ta sakata sannan ta shiga gefen ta, wata motar Aneesa da Ummita suka shiga Mummy Kuma suna tare da Hajiya Maryam sai dayar motar Salamatu da matan da Hajiya Maryam tazo dasu. Sanda suka isa gidan magriba tayi, dakin ta Hajiya Lubabatu ta kaita ta zaunar da ita sannan a hankali ta daga mata veil din data rufe fuskar ta, har rige rigen magana Ummita da Aneesa sukayi saboda abinda basu taba tunani ko zato ba.

“Wannan ce amaryar?”

“Ku fita ku bani waje.” Mummy tace tana ratsowa cikin dakin Hajiya Maryam na bayanta, taji abinda suka fada duk sai mamaki ya kamata amma ganin yadda Mummyn ta shiga nan nan da Noor din sai ta share sukayi sallah sannan sukayi mata sallama suka ce zasu tafi,rike Salamatu tayi ta saka kuka itama hawayen take amma na farin ciki ganin irin aljanar duniyar da suka kawo Noor din, dama ta dade tana ce mata ita din matar manya ce, kuma tana mata fatan wani babba a Abujan ya kyalla ido ya ganta dan tabbas tafi kala da kalar masu kudi. Rarrashin ta tayi da kyar ta kyale ta tana kuka ta fito, har sunzo parking lot mummy tace tana zuwa ta koma ciki. Lokacin Noor din na tsaye bata koma ta zauna ba jar fuskar nan ta daga sosai tayi jawur saboda kuka, ganin Mummy ta dawo yasa gabanta tsinkewa amma sai ta dake tana sadda kanta kasa har ta karaso gabanta.

“Akwai maganganun masu yawan gaske da nake so muyi dake, abu daya nake so ki sani ba zaman mike kafa kika zo yi gidan nan ba, ni na auro mishi ke haka kuma idan amfanin ki ya kare zan saka almakashi na datse igiyar auren ki koma chan cikin talauci da wahala.”

Sai ta sakar mata murmushin mugunta sannan ta juya cikin takun kasaita ta fice. Zama tayi yaraf a kasan carpet din tana sake sakin kukan, kukan takaici da bakin ciki, ya akayi har ta kasa gane cewa plan ne? Ya kamata ta gane cewa Hajiya ba zata taba son ta ba, amma ya akayi idon ta ya rufe haka ta kasa yin dogon tunani akan yadda komai ya kasance? Wayar tace ta cigaba da neman agaji a karo na ba’adadi, da jan jiki ta matsa wajen kayan nata ta kwantar da trolley din sannan ta bude ta ciro wayar da tsabar kiran har b3 yayi ja. Number kasar waje ce ake kiran ta dashi, tana rike da wayar har ta katse wani kiran ya sake shigowa, haka kawai taji bata da karsashin daukar wayar. Sau uku tana shigowa da katsewa a hannun ta sai kawai ta yanke shawarar dagawa, ajiyar zuciya ya sauke da dan karfi sannan yace

“Ina kika shiga?”

“Ina wuni?” Ta gaishe shi sannan tace

“Wayar ce take cikin jaka, sai yau zaka kirani?”

“Ya Allah, kinsan yadda na damu kuwa? Na rasa sim a garin nan kwata kwata gashi wayar ki karama ce babu ta yadda zan iya reaching miki, baki ga yadda na damu ba sai yanzu na samu nayi activating layin shine fa nake ta kiranki.”

“Ok.” Tace sai tayi shiru

“Ok? Ok kawai zaki ce?”

“Toh me zan ce?”

“Kiyi min sannu toh mana.”

“Toh sannu.”

“Yawwa, thank you. How are you? Hope kina lafiya dan naji voice dinki kaman baki da lafiya.”

“Alhamdullillah, kuka kawai nayi.”

“Kuka? Me yasa zakiyi kuka??”

“Bansani ba nima.”

Tace tana jiran taji ya sako mata wata magana da ta shafi auren gaba daya Amma sai taga gaba daya kamar ma be san me yake faruwa ba.

“Yaushe zaka dawo?” Ta daure ta tambaye shi

“Nan da two weeks.”

“Waiii.”

“Yayi yawa ko? Nima yayi min yawa but AJI ne, sai sanda aka gama komai. I promise you muna sauka ke zan fara zuwa na gani, ko gida ba zan je ba zanzo.”

“Allah ya dawo daku lafiya.”

“Amin ya Allah, I can’t wait to see you, akwai abubuwa da yawa da nake so na fada miki.”

“Uhmm.”

“Serious, so just be prepared,.”

Motsi taji a dan corridor din dakin da take ciki, kallon kofar tayi sai kuma ta kalli wayar tana jin motsin na kara matsowa.

“Tsoro nake ji.” Tace masa a hankali

“Tsoro? Why?”

“Ni kadai ce fa, duk sun tafi sai ni kadai a gidan.”

“Ayya, babu abinda zai kama ki kinji? Just pray and sleep.”

“Ok.” Tace still tana jin tsoron

“Ki ajiye wayarki kusa, zan kira ki anjima. Sannan gobe za’a kawo miki new phone, bana so na kara shan wahalar da nasha kafin na samu line din nan, we can chat and keep in touch.”

“Ok nagode.” Tace a sanyaye ta ajiye wayar. Tashi tayi sad’af sad’af ta bude kofar ta leko amma babu kowa a corridor din, fita tayi a hankali tana dan lekawa.
Yana tsaye a tsakiyar falon waya a kunnen sa yana magana, maganar tasa na fita da wani irin sauti me taushi da dan kauri kadan, fada yake wa Saddam da yace su kawo shi ya dau abu a gidan su jirashi yana fita yaga basa nan sun tafi, sosai abun ya bata masa rai shine ya dawo ciki yana kira saddam din ya hau yi masa fada.

“Me yake anan?” Ta tambayi kanta tana labe tana kallon sa tana sauraron yadda yake maganar.

“No ba zan kwana a gidan nan ba, idan ka gama abinda kake din sai ku dawo ku dauke ni.”

“But sir na riga na saki dakin fa.”

“Waya saka ka? Sai ka kama min wani. Bana son jira kuma karka bari na sake kira.”

Sai ya jefar da wayar yana jan tsaki,me ma ya kawo shi gidan ne a wannan lokacin duk da yasan tana ciki. Zama yayi a cikin sofa din falon ya harde kafarsa yana jijjigata cikin yanayi na bacin rai da fushi. Lallabawa tayi a hankali ta koma dakin tana dafe kirjin ta.

_”Ba zan kwana a gidan nan ba.”_

ta maimaita maganar sanda ta koma daki, akan wanne dalili dama zai kwana a gidan nan toh? Toh ko gidan part part ne dashi amma kuma menene ya kawo shi falon nan? Duk yadda taso ta dauke tunanin ta maye shi da abinda take so yaki yiwuwa. Zamewa tayi ta zauna a jikin kofar tana fata da adduar Allah yasa ba abinda zuciyar ta take raye mata kenan ba.
Knocking akayi a jikin kofar, da sauri kamar wadda aka wuntsula ta mike sannan ta tsaya a jikin kofar ta danna karfinta.

“Come out.”

Yace yana daga bakin kofar dan bashi da niyyar shiga, yana zaune zuciyar sa ta raya masa ya ganta yaga kalar zaben da matar da tafi kowa tsanar sa tayi masa, ya tabbata sai ta duba ta dubo wadda tasan zata kara kona masa rai sannan.

“Kina jina?” Ya maimaita yana tsaye rataye da hannun sa a bayan sa yana kallon kofar

“Bana so na shigo, just come out.”

Ya maimaita mata, kallon dakin tayi tana tunanin in da zata shiga ta buya, jikinta na rawa ta nufi wajen closet ta bude ta gwada shiga amma sai taga tayi mata kadan, taba kofar da akayi ne sannan aka turo yasa ta da sauri ta murda kofar toilet ta shige ciki sannan tayi locking dinta ta ciki

No comments