Breaking News

Yanci da Rayuwa 32


Arewabooks; hafsatrano
Page 32

***Bude kofar yayi yana kallon Asim din da madaukakin mamaki, sai dai yanayin da fuskar sa ta nuna yasa yayi saurin gane abinda yake shirin faruwa.
Wuce shi Asim yayi zuwa ciki ya tsaya a tsakiyar falon yana kallon ko ina zuciyar sa na wani irin bugu yana fatan Rafeeq din ya wanke kansa yadda zai iya jin saukin tashin hankalin da yake ji a ransa

“Welcome bro, yaushe kuka shigo? Na zata sai dare fa. Ka shammace ni.”

“Zauna mana.” Yace masa ganin ya tsaya a tsaye yaki cewa komai.

“Ba zan iya zama ba, so nake kawai ka fada min gaskiya, wacece yarinyar da ka aura?”

“Ba zan magana da kai kana tsaye ba, idan ba zaka zauna ba fine. Mu cigaba da zama a haka.”

Yace yana crossing kafarsa calmly kamar babu wani abu da yake shirin faruwa ko ya farun ma. Duk da a matsanancin bacin rai Asim din yake, amma dole ya zauna saboda kwarjinin da Rafeeq din yayi masa.

“Good, me zan kawo maka? Da zai saka kayi cooling down naga kana fuming.”

“Please Feeqq, just tell me. Da gaske ne Noor ce?”

Daga masa kai yayi alamar eh, sannan yace

“Me Mummy din ta fada maka?”

“So it’s true.” Yace yana wani irin murmushin yak’e.

“It’s true kam, but not as you think, yadda ka samu labarin yanzu haka na same shi nima.”

“Da gaske? Lallai ma…” Sai ya mike

“Ina maka fatan alkhairi a sabuwar rayuwar ka, data family dinka. But just know one thing, daga yanzu daga rana irin ta yau, ka cire ni a cikin mutanen da kake da alaka dasu ta kusa ko ta nesa, bansan ka ba, bani da wata alaka da kai da duk wani abu da ya dangance ka.”

“This was her plan all along. Ka saurare ni, karka yanke hukunci cikin fushi you might end up regretting.”

“Ba abinda zai saka nayi regretting, infact I regret knowing you, I regret disobeying my mother because of you, ashe baka kauna ta, baka kaunar abinda zai sakani farin ciki. Right from the start ka sani, kasan abinda nake so, but baka damu ba, kanka kawai ka sani, very selfish and self-centered.”

“Asim… Are you out of your mind? Ni kake cewa self-centered? Ni Asim?

“Ban sani ba, wannan shine last time da zan tsaya nayi magana da kai haka, mu hadu a wajen neman hakkin juna tunda yanzu idona ya bude, I will fight for my right.”

“Shikenan, baka bukatar nayi maka bayanin komai, ko nayi ma ba fahimta zakayi ba, but ka sani, for once ban taba son kaina akan ka ba, nayi sacrificing alot akan ka wasu ka sani wasu baka sani ba, but may be one day zaka zo ka sani. Kayi duk abinda zuciyar ka ta fada maka, ina nan ina jiranka, and i will accept you with an open hand.”

Tsski yaja ya buga table din dake gaban sa, ya juya ya fice ya buga kofar da karfin gaske.

Jikinsa a sanyaye ya mike, cikin wani irin yanayi na rashin jin dadin abinda ya faru tsakanin sa da Asim din, basu taba samun matsala ko sabani ba iyakar rayuwar su, ko irin fadan nan da ake tsakanin sakonni basu taba ba. Girmawa da mutuntawa ce tsakanin sa da Asim dan yadda yake respecting dinsa ba wanda zai ce ba wani shekaru bane masu yawa tsakanin su,amma sai gashi yau, saboda wani buri mara toshe na mahaifiyar sa, ta kai shi ta baro dan hanyar da ya dauka ba shi kansa ba, AJI ma ba zai taba amincewa ba.
Tana tsaye a dan corridor din tana hawaye, tunda suka fara maganar tana makale tana jin su har zuwa sanda Asim din ya tafi. Tausayin Rafeeq din da maganganun Hajiyan na jiya suka sakata yin kuka sosai, tun daga abinda ya faru jiya zuwa yau ta tabbatar da akwai matsala a tattare da gidan kuma Hajiya bata son Rafeeq.
Iskota yayi a wajen, ya kalle ta kawai ya shige ciki a tunanin sa saboda Asim take kukan, yana shiga tabi bayansa da sauri ganin yadda ya nuna damuwa sosai.
A zaune ta sameshi ya zabga tagumi yana kallon tiles din kasan yana lulawa duniyar tunanin abinda zai biyo baya idan alakar su ta lalace shi da Asim. A gabansa ta zauna zaman dirshan tana kallon fuskar sa, sai ya saki hannun yana kokarin daidai ta kansa yace

“Kan ya daina cewa?”

“Eh ya daina.”

“Good, bana jin kaina yau, ki samo wani abu a kitchen kiyi breakfast, idan kin fita ki ja min kofar inaso na dan kwanta.”

Sai ya haye gadon yana jan duvet ya rufe kansa gaba daya. Tsaye tayi a kansa tana so tayi masa magana amma ta rasa ta ina zata fara, kusan minti biyu ta dauka a haka kafin ta juya jiki a sanyaye ta fita. Kitchen din ta shiga tana tunanin abinda ya kamata ta shirya musu breakfast very simple kuma wanda zata samu yaci dan ba zata iya jure ganin sa a damuwa haka ba.
A gurguje ta hada musu simple breakfast ta hada a tray waffles da hot milk sai chinese noodles da sausage. Dakin nasa ta nufa ta tura kofar a hankali ta shiga. Akan wani stool ta dora tray din sannan ta koma ta dauko sugar cubes da mugs ta sake dawowa dakin. Yana jin duk motsin ta har ta gama shirya kayan ta sauko dasu kasan rug din sannan ta matsa gaban gadon nasa tace

“Ga breakfast din.”

“Eat, I’m not hungry.” Yace be juyo ba

“Please dan Allah.”

Juyowa yayi suka hada ido, sai ta marairaice masa fuska kamar zatayi kuka ta kara cewa

“Dan Allah, ni ba zan iya ci ni kadai ba.”

“Shikenan shikenan, bari nayi brush.”

Ya sakko ta matsa masa ya wuce toilet yaje yayi brush ya dawo ya zauna a kusa da ita sosai yana manne jikinsa da nata, bata matsa ko hana shi ba dan ta lura so yake tayi wani abu yace ya fasa ci sai kawai ta kyale shi yayi abinda yake so din. Bismillah yayi ya dauki fork ya dauki spoon ya soma ci yana zuba mata idon sa yana kallonta irin kallon ne me cike da kauna. So yake ya gano takamaimai dalilin da yasa yake mata irin wannan son komai tayi birke shi take. Sosai yaci abincin yana jinjina kansa saboda dadi ba zaka ma ce Noodles kake ci ba. Kwashe kayan tayi ta kai kitchen ta wanke wanda suka baci sannan tazo ta wuce dakin ta tana kallon falon duk da babu datti amma yana bukatar sake gyara shi. Kayan jikin ta sauya zuwa wata doguwar riga da ya siya mata ranar me kyau baby pink ta saka hula ta rufe kanta ta fara gyara dakin duk da ba wani datti shima yayi ba, ta shiga toilet ta wanke shi tas sannan ta koma falon, ta hau gyarawa nan da nan ta gyara komai yayi fes ta kunna diffuser. Tana tsaye gaban TV ya fito yana baza kamshi ya shirya cikin kananan kaya soft jeans da coffee shirt fuskar sa fes babu wannan damuwar ta dazu waya a makale da kunnen sa yana magana a nutse har ya karaso wajen da take tsaye ya jawota jikinsa yana cigaba da wayar.

“Yanzu zan fito.” Ya fada karshe sannan ya katse wayar.

“Shine kika gudu kika barni ina ta jiranki.” Yace yana mata murmushin nan nasa me tsada. Murmushin tayi masa ita ma sannan tace

“Shara nayi da wanke wanke.”

Da sauri ya kalle ta, sannan ya kalli hannunta da take maganar tayi sharar sai ya hau girgiza kai

“Ban amince ba, ban yarda ba. Akwai masu aiki a gidan nan hutu kawai na basu ganin bana zama, kuma weekend dinnan zasuyi resuming aikin su, kar na sake ganin kina wani wanke wanke.”

“Shara fa? Dole za’a share bedroom da wanke toilet.”

“Ohh, toh na dakin mu kawai wanchan, shi na yarda kiyi.” Ya nuna dakin sa

“Amma other bedrooms din ki bar musu su gyara, shima wanchan dan kinga ba’a shiga turakar me gida ne ko?”

Nokewa tayi tana boye fuskarta a jikinsa yadda yace me gidan ne ya bata kunya, murmushi yayi yace

“Emana, sai mu dinga gyara shi tare, kinsan na iya irin wannan abubuwan.”

“Tam.” Tace tana gida kanta.

“Hajiya tazo jiya da baka nan.”

“Jiya? Da yaushe?”

“Da rana.”

“Shine baki fada min ba?”

“Bani da lafiya ai.”

“Ok ok, na tuna. Shikenan idan na dawo zzmuyi maganar. Zan je naga AJI, kinsan sun dawo yau har ya shiga office be ganni ba, shine wai yace maza maza na fito amarcin ya isa haka, be san ni ko farawa ma ban ba.”

Ya karashe yana yin kalar fuskar tausayi

“Allah sarki ni bawan Allah.”

Dariya ya bata sosai yadda yayin,ta shiga yin dariyar, abinda ya sakashi farin ciki ganin tana dariya sosai dan be taba ganin dariyar ta haka ba, yadda ya lura da ita wata irin yarinya ce da gane kanta sai ka sha fama,da gaske bata boye abinda yake zuciyar ta, musamman idan bata gama fuskantar abinda yake faruwa ba daxu ya dauka zata masa maganar Asim bayan ya tafi amma sai yaga kamar bata ma gane komai ba. Anya bata da iskokai kuwa? Ya tambayi kansa yana murmushi, zuciyar ta rawa take mata akan zabin da take bata shiyasa har dazu bata gama fuskantar komai ba, zai yi kokari wajen ganin ya goge duk wani abu a ranta ya maye gurbin sa da zazzafar kaunar sa, wanda yasan ko zabi aka bata ba zata taba kin zabar sa ba sau dubun dubata, hakan shine kadai ribar sa a yanzu.
Peck yayi mata a goshi da kumatun ta, yayi mata sallama ya tafi. Zama tayi tana kankame hannun ta, tunanin abinda taji dazu tsakanin sa da Asim da kuma abinda ya faru jiya da Hajiya tazo sai ta shiga auna shi a ma’aunin hankali. Abinda ta lura sam Hajiya bata kaunar Rafeeq, tunda boldly ta fada mata dukkan plan dinta,sannan akwai wani kulli a al’amarin auren su wanda take tantamar idan shi kansa Rafeeq din ya sani. Yadda yayi hugging dinta a ranar farkon da ya ganta a gidan ya isa ta gane kamar shi kansa be yi zaton ganin ta ba, kamar yadda tayi mamakin ganin sa, kamar yadda Asim ma yayi mamaki. Tabbas Hajiya ce ta kulla komai, ita take so ta tarwatsa rayuwar su ta sa su tsani juna tsana me karfi, shiyasa ta shigo da ita tsakanin su, tayi amfani da ita ta rabasu.

_”Sai na baki mamaki, sai na zame miki kadangaran bakin tulu, sai na zame miki ciwon ido.”_

Ta fadawa kanta tana jin kwarin guiwar tsayawa a side din Rafeeq din, ta taimaka masa wajen playing game din da Hajiyar ta fara, zatayi supporting dinsa dari bisa dari ko da babu soyayyar ta a ransa, ko da a karshe zai rabu da ita yace ta tafi gidan su. Ta hakura da Asim har abadah, dan da ace tayi kuskuren auren sa toh tabbas mummy ba zata taba bari ta zauna lafiya ba, tsangwama da kaskantarwa kadai ya isheta ta gudu da kafafunta.

***Ringing daya wayar Baban ta shiga, ta sakata handfree tana adduar Allah yasa ya dauka.

“Assalamualaikum.”

“Babaaaa.” Tace tana jan sunan na shagwaba

“Wa nake ji kamar Noor dita?”

“Baba nice.”

“Lallai sai yau ake tunawa da ni? Duniya ba gaskia yar Baba.”

“Baba na kiraka baka dauka ba, kuma ranar nan ma na sake kira a kashe. Sabuwar waya ce ban iya amfani da ita ba.”

“Shiyasa layin naki baya shiga, na kiraki na fada miki abun arzikin da mijin ki yayi min,ban san me zan ce masa ba wallahi, bansan da wanne bakin zan gode masa ba, na farko ya kaini asibiti aka kula da lafiya ta aka bani magani yanzu kuma ya chanja min gida a unguwa me kyau da komai na more rayuwa Noor, rayuwar mu ta chanja ta, ta koma ta baya wasu shekaru da suka shude. Na cire rai tuni da irin rayuwar nan Noor, dan a ganina shikenan sai gashi ya taimaka ya dawo mana da ita a lokacin da muka cjre rai da tsammani.”

“Baba ban gane komai ba, ban gane Baba.”

“Baki ji ba?”

“Naji Baba, kawai na rude ne. Yaushe akayi haka duk ban sani ba baba.”

“Ban sanar dake na asibitin bane ba kawai saboda yaron nasa da ya saka aikin yace kar ya kuskura yace shine, shiyasa nima kawai nayi shiru wannan abun da ya faru jiya shine yasa na yanke shawarar sanar dake, a kalla ko godiya kyayi masa ai. Jiya tun safe suke chuku chuku har yamma likis sannan aka gama komai, nayi murna nayi farin ciki kuma nayi kukan kewa da rashin mahaifiyar ki, ina ma tana raye, ina ma.”

Kuka ta saka kawai ta shiga rera shi Baban na jinta, fada ya soma yi mata akan me zatayi kuka abin farin ciki amma ita kuwa kukan haushin abinda tayi masa jiya take, haushin kanta da tsanar kanta yasa take kukan. Bayan abinda tayi masa ashe shi yana chan yana son faran ta mata rai, wanne irin mutum ne shi?

No comments