Breaking News

Zarrah 55-56


55-56*_

 

Jikinta ne ya qara matuqar sanyi wasu hawaye suka cika mata ido tabbas Allah yayi gaskiya daya ambaci ya mace a matsayin halitta me rauni a hankali ta miqe ta debe kayan abincin takai kitchen ta dawo ta dauki wayarta kamar jira akeyi wayar tayi ring ta daga tare da cewa tun dazu nakeson kiranki mu tattauna Dr Aseem ya jima yana rainamin hankali ashe duk haukan da mukeyi na aljani ne ya aureni shine qaton aljanin da yake lalubeni cikin dare tabbas yayi wasa da hankalina matuqa nayi niyyar jansa a qasa amma iya yau zuciyata ta karye kamar bazan iya ba shidin suffar hankaka ke gareshi in kaga baqinsa ma zaka dawo kaga farinsa”
Dariya Jiddarh tayi tace “kawai kice kin kamu da soyayyar wannan handsome guy din tabbas akwai alamun hakan to kibada kai mana bori ya hau kinganshi can naga tun dazun ya shigo asibiti amma ya kasa fitowa a mota nifa Asmah inda nice nake da miji irin naku wlh bazan barshi da damuwa ba koda kuwa ni zan cutu” wani abu taji ya caki qirjinta yana taso mata da batasan meye ba a hankali tuna irin yanda ya rinqa mu’amalantata da rashin tausayi da jinqai da kuma gadara da izza inajin kamar bazan iyayi masa wata alfarma ba a gaba” fasali Jiddarh taja tace “kidaiyi qoqarin zama a matsayin da Sheikh Wakil yake fada mana kullum a makaranta shima ba fadarsa bace fadar ubangiji ce idan mutum ya cutar dakai ma’ana yayi maka laifi ka rama gwargwadon abinda yayi maka idan bazaka iya hqra ba amma hqrn shi yafi alkhairi sannan kullum Inna tana fada mana mu kasance kullum a tsakiya kada mu fara cutar da mutum mu zamo masu yawaita yafiya da kuma kawaici akan laifukan da akayi mana Asmah mijinki ko bai fadawa duniya ba duniya ta shaida yana matuqar qaunarki kuma yana shakkarki”

 

Numfashi ta sauke me nauyi ta furzar da iska tare da cewa “ok na gde sai kinjini” kashe wayar tayi ta rungumeta a qirjinta wasu hawaye masu dumi suka zubo mata takai hannunta ta shafa cikinta wani tausayi da qaunarsa tana kwaranyo mata ta kwanta tana sauke numfashi itakam tana tunanin ta inda zata fara yafewa Aseem wadannan abubuwa gima gima da yayi mata ranar yini tayi tana juyi a gado bata tashi ba sai biyar tayi wanka ta sheqa kwalliyarta cikin wasu riga da skirt na English ta hade sumarta ta daure bata bata fuskarta ba normal hakanan yanda fuskarta take haka tabarta sai white lips da tasa tayi kyau sosai ta fito ta nufi kitchen ta dauki macaroni tayi jallop dinta da taji kifi banda ta dora farfesun kayan ciki bayan ta gama ta diba takai part dinta ta zauna tana gyara qumbarta.
Tashi tayi tayi sallah ta sake wanka ta sake kwalliya ta kwanta a kujera ta hau duniyar sama hankalinta gabadaya ya tafi kan lecture da akeyi a group din DOMINKI YAR GATA tanajin dadin lecture saboda ba qaramar qaruwa takeyi a cikin lectures dinba bataji shigowarsa ba sai ji tayi numfashinta yana daukewa ta bude idanunta a cikin nasa bakinsa hade da nata ajiye wayar tayi ta sanya hannunta ta bayansa ta rungumesa ta sake saqalo harshensa.

 

Narkewa yayi a jikinta yanajin yanda take tsotse lips dinsa tana zuqo harshensa tallafo kanta yayi tare da daukar dayan hannunsa ya dora a cikinta ya tura cikin rigarta yana shafa cikinta yana wasa da cibiyarta wani abu taji ya taso mata zuciyarta na tariyo mata abubuwan da suka faru a baya ta kuwa janye da sauri ta miqe ya riqo hannunta yanajin wani felling dinta nayi masa dirar mikiya, hada idanu sukayi idanunta ya ciko da ruwa ta fincike hannunta ta shige dakinta da sauri ya miqe yabi bayanta yana kiran sunanta. Zama tayi a gefen gadon ta rushe da kuka hankalinsa yayi mugun tashi ya zauna a gefenta yace “OMG Asma’u don Allah ki taimakeni kiyi hqr ki daina kukannan pls ki tausayawa mijinki mana……”

 

Janyewa tayi ta kwanta tana jan zuciya tana kallonsa miqewa yayi jikinsa a sanyaye ya nufi bathroom yayi wanka ya dauro towel ya fito ya tsaya jikin mirrow yana kallon kansa itanma kallonsa takeyi a kaikaice tana yaba qirar halittarsa.
Tana ganin ya juyo ta kawar dakai ya sanya rigarsa doguwa ya haura gadon ya dagota suka kalli juna yasa hannu ya goge mata hawayenta yayi kissing lips dinta yace “muje na nema mana abinda zamuci inajin yunwa” sunkuyar da kanta tayi ta janye ta nufi falon ya biyota ta tsaya a dinning din ta fara bude abincin tana zuba masa yanata kallonta harta gama hadansa abincin taja masa kujera ya zauna ya faracin abincin jikinsa na karbar saqon dandanon abincin me ratsa zuciya yana yabawa da baiwarta ta wajen girki ita komanta me dadi ne.

 

Kafin ya gama ta shige daki ta shiga wanka ta fito tasha magungunanta tasa kayan bacci ta kwanta koda ya gama ya dade a zaune yana tunanin ko zata fito yajita shiru miqewa yayi ya murda handle din yajishi a rufe ya girgiza kai kawai ya shiga nasa dakin ya kwanta. Hakanan sukaci gaba da rayuwa shikam yanashan wahalar rayuwar duk wani nauyi dake kanta na kula da duk abinda ya shafesa zata sauke masa hatta dakinsa bata fasa shiga ta gyara masa ba amma taqi bashi damar ya kusanceta duk shisshige matan da yake da rara gefen da yakeyi tana kallonsa amma taqi bashi hadin kai.
A cikin kwanakin ya gama musu komai na tafiyarsu Mimee tanacan shanye da baki tana jiran yaje ya bata hqr wai ita matar so ya dauke matarsa suka daga sukabar qasar, aikuwa ranar da taji lbrn tafiyar tasu bata iya bacci ba kira kam takira wayarsa yafi sau dari bata shiga dole ta hqr a washegari kuwa Naja’at qanwarta tayi mata jagora gurin bokanta sukaje ta baje masa komai kamar gaske yayi surkullensa fuskar Aseem din ta fara fitowa cikin Madubin nasa sannan Asmah kwance a cinyarsa daure da drip wani baqin kishi ya tasowa mimee ganin yanda yake wani shafa cikin Asmah tace “nifa mal cikin nan nakeso ya fara lalacewa inyaso bayan ya zube itama sai a kadata ta kama gabanta shikuma a dasa masa qinta yanda ko uwarta zata yanka ta bashi bazata burgeshi ba”

 

Dariya bokan yayi ya mayar da hankalinsa ga surkullensa ya dago ya dubesu yace “abu daya zai yuwu biyu bazai yuwu ba” da sauri suka dubesa ya sake kecewa da dariya yace “zasu dawo gida a warware bazasu dawo tare ba zaa rabasu amma bazamu iya cire masa sonta ba saboda ba son faraddaya yayi mata ba a hankali sonta ya zaga jininsa da bargonsa idan kinga ya rabu da qaunarta to ya rabu da rayuwarsa ne abu na biyu bazamu iya taba wannan ciki ba domin kuwa ya rubutowa kansa manyan qaddarori da idan mutum ya matsa ganin bayansa to shi zai fece ya sanqama lahira babu shiri”
Gumine ya karyo mata ta miqe da sauri tace “aa nifa indai ukunnan bazai yuwu ba to duka abarshi saboda rabasu ba shine muhimmim abuba rabasu da qaunar juna sannan ni nasan indai shegiyar yarinyar nan ta haihu a gdannan to kashina ya bushe yanda Aseem keson haihuwa ruwa ma saida umarnin danta zanshashi a wannan gidan Boka ka sake dubawa dai idan akwai wata mafitar ayi amfani da ita” tana fadin haka ta fice ya dubeta ya kece da dariya yace “shegiya tsinanna mara albarka wacce ta kwashe kayanta daga gaban ma’aiki bazan rabasu dinba hakanan kawai saina rabasu bayan da bakinki kikace yarinyar tasha wahala a baya” sudai basu tsaya ba suka dunguma suka shiga motarsu driver yaja kowanne zuciyarsa babu sanyi wata uwar ashar Mimee ta saki tace “wlh ko zanyi yawo babu pant saina tarwatsa rayuwar Asma’u a gdan Aseem koda nima zan rasa nawa farin cikin”…………..

 

 

_*Oum Hairan*_
[29/06 4:41 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_

_*Fauziyya Tasiu Umar*_

_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

No comments