Breaking News

Zarrah 9-10


Tunda Asma’u ta koma gida take zumbure zumbure Matan gdan Babu Wanda ya kulata Inna kuwa ba ido ba balle tasan matsalar yartata haka tayi wanka tayi sallar azahar da La’asar ta zauna tsince wake bayan ta gama ta dora musu abinci tana girkin tana qunquni da haka ta gama ta zuba ta zauna tanaci bayan ta gama ta shirya ta tafi islamiyya sai shidda ta dawo lkcn uniform dinta ya jiqu ta wankeshi ta shanya sai lkcn ta jirge ta zauna tana bawa Inna lbrn abinda ya faru.
Sosai Inna ta nuna rashin jin dadinta da abinda yartata tayiwa Aseem tare da rufeta da fada daga baya ta dawo yimata nasiha to ta danji a lkcn ta miqe tayi sallah ta kwanta, washegari da wuri ta fice saboda so takeyi yau suje makarantar da wuri cikin saa ta tarar da Jidda ta shirya suka tafi suna tafe suna Hira Jidda tace.
“Nifa jiya kin kullemin Kai Asma’u waike bakida tsoro ne baki tsoron kada mutumin nan ya sanya yan sanda su kamaki?” Tsaki tayi tace “kuma saboda Ina tsoro saina bari yaci mutumcina na qyaleshi ko?”

 

Kada Kai Jiddah tayi tana Shirin yin magana wata mota tazo ta giftasu kawai sai sukaga taci burki a gabansu hankalin Asma baa kan motar yake ba har zasu gifta taji Jidda tace “mun shiga uku Asma’u mutumin jiya ne fah” da sauri ta kalli gurin suka hada ido ta galla masa harara ta qarawa tafiyarta sauri saboda Inna tace idan ta sake kulashi sai taci mutuncinta.
Murmushi yayi cike dajin tsanar yarinyar a qasan zuciyarsa yaja motarsa ya qara gaba ta gefenta ya wucce shuuu taja fasali tace “kaci arziqin Inna ta hanani kulaka wlh yauma dasai nayi maka rotse sakarai Wawa”

 

 

Duk da Aseem baiji abinda ta fada ba Amma ya fahimci dashi take murmushi yayi ya qara bawa motarsa wuta tabbas sai yayi maganin rashin kunyar yarinyar nan da take ganinta daidai dashi saiyabi ta kowacce hanya yaga ya koya Mata hankali saiya sanya Mata jin cewa Ashe ita ba kowa bace a rayuwarta tunaninsa yanzu ta inda zai fara gudanar da aikinsa kisan mummuqe yakeson yimata batare da wani ya gane qudurinsa ba yakeso ya baje tarihin rashin kunyar Asma’u,
Yana tuqi yana murmushi Yana maimata sunanta yanayin yanda ta harareshi dazun yana Masa gizo yanajin wani nishadi da Allah yasa yarinyar ta siyar Masa da qasar wasan dole akwai badaqala zai ganar da ita kurenta na shiga sharafin daba nataba. Koda yaje asibitin ya fara duba marasa lfyrsa bayan ya gama ya wucce nasa private hospital nanma yayi abinda zaiyi sannan ya shige office dinsa ya zauna yana juyi a kujerarsa cike da zumudin ganin yamma tayi Zahran ya gama aikinsa ya daukeshi suje su nemi mahaifin Asma’u kamar yanda ya tsara kafinnan Saida ya sake tura wani yaronsa yayi masa binciken tsaf inda anan ne yaron nasa Uzairu yake sanar dashi ai Mal Husaini yasa gdansa a kasuwa zaiyi auren yaransa uku sukuma iyayen zasu koma qauye da zama wacce bazataba Kuma tasan inda dare yayi mata.

 

Fiye da tunani Aseem yaji dadin wannan farin lbr aikuwa hudu da rabi suka fice daga asibitin suka nufi bakin kasuwar sabuwar gandu inda anan Mal Husaini yake zama Nan suka nemi a rakasu ofishin dillalan qasa akayi musu jagora sukaje suka gaisa Zahran yana nunawa Aseem Mal Husaini da yaketa maka hamma da hularsa ko Kari Babu bisa dukkan alamu yunwa yakeji.
Caraf kuwa Alh Bala dillali yace “Idon cin naira da alamun dai yau baa sammaka abin sawa a maqoshi ba ka fito” kamar me jiran kadan ya balle zance kamar Wanda ya qone a tsakiyar ka cewa yake “yo dama wadannan sakarkarun waye yanzu yake sammin abincin Lantana da Lamunde sunce sun daina cida qato Wai auren yayansu zasuyi Amina ce me tausayina take bane to itanma saidai idan wannan ja’irar yarinyar Ma’u batanan amma fir take hanawa tace ai ba Basu nakeyi ba kuma tana ganin lkcn da nake bawa Lamunde nikuma ganin suna fita bara nasan na annabi baya qarewa shiyasa bandamu da sammusu ba gashi anma kasa samun me siyan kangon can nawa bare na Dan murmure kafin bikin nan”

 

Jinjina Kai Aseem yayi Bala dillali ya dubesu yace “Alh Allah gida ko fili ko kango ko haya ake buqata?” Cire hularsa yayi ya maida hankalinsa ga Zahran Zahran ya gyara zama ya karkace yace “gda muke buqata ginin gargajiya anan Tukuntawa zamu zuba shanu da tumaki a ciki….” Yunqurowa Mal Husaini yayi Mal Bala ya dakatar dashi yace “toh ikon Allah kamar Kuma na nawa kuke buqata?” Kallon Aseem Zahran yayi Aseem da sai yanzu yaga samar mgn yace “ba qarami ba ba babba ba duk yanda kasuwa ta Kama munaso idan akwai a nuna Mana abune na urgent da muke buqatarsa tsakanin yau da sati biyu” duba Mal Bala yakai ga Mal Husaini da dama yake jiran abashi dama nan yayi kwance kwance yace “yo Alh Allah muje suga nawa Mana ko Allah zaisa a daidaita tunda qananun masu kudi sun kasa siye sunce zaici kudi wajen gyaransa

 

Tunda ya fara mgnr Aseem ya zuba Masa ido har ya gama murmushi Aseem yayi Wanda shikadai yasan dalilin murmushin nasa yace “ok muje mu gani idan yayi sai muyi ciniki Amma gsky muna buqatar gurin da wuri zamuyi aiki a ciki ne” Babu tunanin makomar iyalai Mal Husaini yace “Haba yaro abinda yake kasuwa ai ko yau kakeson abinka baka akayi indai ka biya nidai fatana Allah yasa gurin yayi maka fitinar zabba’u ta isheni yau ta debo wannan gobe ta kwaso wancan gara na auraddasu kawai na huta sauran kudin naci tsire dasu hhhh koba hakaba yaro…”
Sudai murmushi kawai sukayi suka nufi motar Mal Bala da Mal Husaini suka shiga baya Aseem da Zahran suna gaba a haka Mal Husaini yaketa basu kwatance suna amsawa har suka shiga unguwar tun daga farkonta suka fara Raina kansu asalin uguwar talakawa ce ko Ina kwatami ne yake gudu haka sukayita kutsawa lunguna har suka isa qofar wani tsohon gda ginin jar qasa dako arziqin yabe bai samu ba babu qofa a gidan sai labulan tampol da aka sanya domin sakaye gdan, tundaga qofar gdan Aseem ya qara Raina matsayin Asma’u tare da tsananin mamakin izzarta a matsayinta na wadda ta taso a wannan rubabbiyar unguwa a unguwar ma a gda mafi qasqanci domin shidai iyakar dubansa baiga gdan da yakai nasu Asma’u lalacewa ba a area.

 

Mal Husaini ne ya shiga ciki ya sanar da matansa cewa zaa shigo ganin gda me tankade ta tashi me dakama ta miqe sukayi daki Inna ce dama tana daki a zaune tana lazumi shigowa sukayi suna duba gdan a zahirin gdan Babu uwar da Aseem zaiyi dashi Amma da suka gama dubawa sai ya dubi Zahran yace masa “ina ganin kamar gurin zaiyi ai ko?” Sarai Zahran yasan me yake nufi shikuma sai yace “dadai an nemi Wanda yafi wannan gsky shanun zasu takura” dafashi yayi yace “kada ka damu fashe dakunan zaayi daki biyun nan kawai zaa bari saboda me gadi da abincin dabbobi” da wannan suka juya zasu fita suna Shirin fita kyawawan yammatan na sawo Kai Dijangala ce a gaba sai Zabba’u ita kuwa gwanar ta cake a qofar gda Laila sarkin soyayya ita da Sadiqun ta suna bawa fure ruwa ai suna fitowa tana dago Kai suka hada ido ba itaba shima Saida yaji gabansa ya fadi ya kasa dauke ido daga kanta dake dariya takeyi yanzun sabanin duk haduwar da sukeyi dashi yau saiyaga tayi wani haske tayi kyau kyawawan haqoranta ya zubawa ido da akayi musu kwalliya da siririyar wushirya.
Ganin fitowarsu daga gdansu yasata saurin tsuke fuska kamar ba itace take dariya ba ta kawar dakai daga kallon da sukewa juna ita da Aseem din, sosai Sadiqu ya lura da sauyin nata don haka ya dubeta.

 

Yace “ya akayine jarumar Mata?” Ajiyar numfashi tayi tace “meye ya kawoshi gdanmu?” Da rashin fahimta yace “wafa?” Duban Aseem tayi da ya juya baya jikin motarsa yana waya tace “wancan Mara mutumcin Mana shine fah mutumin da nake baka lbrn na fashewa qafa ko qarata ya kawo gda gurin Mal tab aikuwa zan daku shikuma zai ragargazu Dan wlh hayar tantiran hayin qwari zanyi su rugurgujeshi.
Dariya Sadiqu yakeyi Mata domin ya lura gabadayanta a tsorace take tsinkayo muryar Mal tayi Yana qwala Mata Kira “Ma’ulele ke Ma’u bakijina ne bakiga mutane ba dan qaniyarki irin tarbiyyar da gyatumarki tayi Miki kenan?” Sumsum ta nufi gurinsu duk a razane take a rusuna tace “ina yininku” Zahran ne da Mal Bala suka amsa shikuwa gogan kallonta kawai yakeyi Mal Bala yace “Mal nayi nayi dakai ka bani daya cikin yammatannan naka kaqi da tuni baba nakece maka ga Ma’u ma ta girma abinta” tsuke fuska Mal Husaini yayi yace “yo Banda abinka yaro ai sai yaro kaga wancan kafirin yaron da qaton Kai shine ya zamemin alaqaqai nayi nayi na rabasu sunqi rabuwa harma na hqr basa zanyi suje su qarata”
Dagowa Aseem yayi yace “wai itama wannan din taka ce Baba?” Murmushi yayi yana sosa qeya yace “wlh kagansu Nan kamar yar maraqan shanu haka akayita jeramin su harsu uku gasunan kansu daya ita wannan itace qaramarsu shekararta sha shidda sabodasu nema zan sayar da gdannan” Jinjina Kai yayi cikin jin dadi yana hango nasara yace “a aikuwa ba ayi haka ba kasai da gda baba kaida kake da Yaya Mata kabar gdanka kawai” da sauri ya dubeshi yace “inbar gda fah kace Alh waye zaiyimin auren yayan?” Murmushi Aseem yayi ya bude motarsa ya bude dashboard ya dauka raffers ta dari biyar biyar guda biyu ya bashi yace “karka damu baba ka riqe wannan gobe insha Allahu zan dawo ai kamarka kanada wadannan kyawawan yammatan ba abarka ka tozarta ba” sake miqa Masa wata reffer yayi yace a rabawa matan gdan wannan anan suka qyale Mal Husaini sake da baki da kudi a hannunsa suka dauki Mal Bala suka tafi a mota Aseem ya dubi Mal Bala yace “yarinyar nan data gaishemu ta fanshi mahaifinta indai zai bani auranta na rantse zanyi Masa komai da yake buqata na hidimar aurensu tun daga satin farko har ranar da zaa gama biki ka sameshi ka fada Masa idan ya amince har gdanma zan gyara Masa”……….
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*

_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*

_Bismillahir Rahamanir Rahim_

_Free Page 11-12_

*_Wattpad realfauzahtasiu_*

Telegram

https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7

______________________________
___________________

No comments