Breaking News

Ameenatou 10

 *_AMEENATOU_*

_Mamuhgee_

#Arewabooks@Mamuhgee

#ZafafaBiyar


10


ASHNA BEAUTY SKINCARE 

Free class free class  

Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta 

Carwash 

Airfreshner 

Liquid soap 

Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058

Karku Bari wannan damar ta wuceku


**********

Zuciyar Omar sosai ta sosu ganin rayuwar da Ayshatu Indo take ciki Dan haka take ya Yanke shawarar mayar dasu cikin gombe sbd rayuwar 'yayanta ta inganta hakama mijinta Wanda take ya amince Dan Daman Yana fita binni yan kasuwancinsa na siyarda dabbobi.


Lamarin masu abin duniya Babu Bata lokaci a ranar suka juyo suka baro sai washe gari da asuba suka iso gombe.


Lafiyayyar tsadaddiyar hotel din Daya sauka anan aka saukar dasu Ayshatu da yayanta da mijinta Jamaal kuwa acan sama ya sauka dakinsa daban sbd rashin lfy sosai ya rufesa.


Amina ma kanwar mijin Ayshatu sosai take ta amai da zazzabi me karfi Daya Saka dole aka sanar da Omar yasa aka kaisu asibiti take aka Bata gado.


Lamarin kaman wasa saiga Jamaal ya kwanta ciwo Shima Dan haka a ranar yabi jirgi ya shida Aron suka koma Lagos.


Suma su Ayshatu jinya sosai sukai asibiti ta Amina wadda taji jiki sosai sbd Bata taba fitowa binni ba.


Koda aka sallamosu asibiti anriga an samu gidan ansiya lafiyayye daidai su an Saka musu furnitures daidai misalin masu rufin asiri sbd bayason ya sakar musu kudi sosai yanason sufara sanin rayuwar garin idan zasu iya tukuna.


Duk wannan abin da akeyi Jamaal da idonsa baiga mutanen da Dad Omar yaje Gani a kauyen ba bare wainda yazo dasu.


Abinka da mutanen kauye da karamci da son mayarda alkhairi Kai tsaye Babba yayiwa Omar kyautar Kanwarsa dayake so fiyeda komai a duniya wadda yafisonta akan 'yayansa Daya haifa da cikinsa.


Ita kanta Ayshatu Jin tayi tayi Naam da Hakan Dan haka ta roki Omar akan ya amince.


Shiru yayi tareda kallan budurwar yarinyar da akace an basa din tana zaune a tsakar gidan tana alwala cikin nutsuwa da sanyin jiki.


Fara ce sol kamanta da Yayanta Wanda yake kaman ubanta Dan ya Isa haihuwan nata kaman an tsaga Kara,

Ba qazama bace tanada tsafta sosai shiyasa haskenta yake fresh a Koda yaushe duk da tana kauye kwata kwata Bata aikin wahala sbd idan akwai abinda Babbah ya tsani Gani a rayuwarsa shine ganinta tana wahala shiyasa baiyi wata wata ba yayi kyautarta inda zataje tayi rayuwar Kwanciyar hankali.



Kawu Nuhu Wanda matarsa da yayansa harma da Amina da Yan kauyensu da yawa suke Kiransa Babbah Ya taso a baida kowa a rayuwarsa sai Kanwarsa da mahaifiyarsa ta bar masa bayan ta rasu gurin haihuwarta,

Amina sunan mahaifiyarsu ne data rasu ya mayarwa Kanwar tasa,


Masifaffe ne shi Kuma mafadacin da baida sauki hakama baisan kowa ba sai kansa,

Babu abinda yake girmamawa da ganin mutuncinsu idan ba kudi ba,

Yana girmama kudi,

Yana Basu girmansu,

Yana ganin kimarsu fiyeda kowa Dan kowa zindir yake kallansa idan har baida kudi,

Masu kudi kawai yake saukewa hula ya mutunta,

Duk duniyarsa Amina ce kadai abinda yafi so fiyeda kudi,

Itakadaice abinda take sakasu rissinawa idan ya kafe akan Abu,

Ko Mai garin kauyensu shakkar rashin arzikin babba yakeyi sbd Baya shakkar kowa hakama kauyensu da zagayen ansan Amina ce kadai abinda yake Saka zuciyar babba girgiza Amma ko Barayin dabbobi na shiga gidan kowa a kauyen Amma basa shiga gidan babba Dan Shima kiris ne ya rage masa ya zama Dan ta'addan idan har zaiyi kudin Dan haka Daman dama Kawai yake Jira ta barin kauye sai gata Allah ya kawo.


Kafin Ayshatu yayi aure so biyu suna rabuwa sbd suna kuntatawa Amina sai da ya auri Ayshatu ya Bata matsayi me girma a ransa sbd tsananin son da takewa Amina na tsakani da Allah tin daga zuciyarta Kuma ta riqeta tamkar yarta data Haifa har itama ta haifi nata yayan biyu duka Maza daga Nan haihuwar ta tsaya har suka fara girma.


Duk yanda babba ke tsananin son Amina nata son datake masa yafi Hakan Dan ita sbd shi ta zabi zama kimtsatsiya muka kamilar yarinyar datafi kowa nutsuwa a kauyen tareda mutunci Dan kuwa Bata fita ko kofar gida ko ganinta sai dace ake ganinta Dan kwata kwata Bata fita koyaushe tana cikin gida killace.


Tana tsananin son Dadah da Babba kaman sune suka haifeta Dan haka ko yanzu da suka Bada aurenta ga Wanda Bata taba ganiba bare sani Bata musu ba kaman yanda Shima Omar din kawai ya karbeta bayan ya karanceta cikin qanqanin lokaci.


Bai buqaci komai daga garesu bayan matar kaman yadda suka basa ita Dan haka Kai tsaye ba wani biki ko wata hidima auren kawai aka dauka bayan wata Daya da dawowansu gombe kenan Dan haka Kai tsaye ya tafi da ita Amma Saida babba ya rakota har gidanta yaga duniyar da suke ciki ya koma Yana hawayen rabuwa da Amina.


Ansaka yayan Ayshatu makaranta hakama babba an basa jari kasuwanci yakeyi ba laifi Kuma Yana more rayuwarsa a binni Dan idan ya fara yawo ko gajiya bayayi ita Kuma Ayshatu kasuwancin cikin gida takeyi itama na Yan kulle kulle.



Matar Omar Bata daga hankalinta akan aurensa ba sbd Jin wacece matar daga kauye ta fito,

Hakama su mamman mamakin auren kawai sukayi ta yanda mutum kamarsa da duniya ake respecting da shaawa ace ya auro yar kauye yarinya Kuma,

Shi Alh lameenu hankalinsa tashi yayi da auren sosai Wanda gaba Daya zuciyarsa yaji tana kasa samun nutsuwa ya Kalli Alh mam a lokacinda yake sake Jin damuwar auren yace,


"Mamman me kake Gani zai iya biyo bayan wannan auren na Omar?

Yaushe ne burin shekara da shekaru zai cika?

Wannan burin daf yake da zama tarihi idan har Omar zai fara aure aure."


Wayar sake hannu Alh mam ya ajiye gefen tsadaddiyar Turkish Royal sofa din Dake palon dasuke Yana dagowa ya Kalli Alh lameenun yace,


"Kana tinanin wannan burin ko shi Omar din zai iya hanasa cika?

Idan ban mallaki dukiyar Omar ba har abada bana kallona Mai arziki Duk kuwa abinda zan Tara din....


Katsesa Alh lameenu yayi da cewa


"Hankalinmu na kwance ne duk shekarun Nan sbd Omar Bai taba samun haihuwa ba,hakama acan Baya mun Jira ne mr and Mrs Jaden su mutu dukiyarsu ta taru ta zama ta Omar din kafin mu dauko mataki

Yanzu dukiyar ta zama tasa Kuma gashi a kusa damu yanda muke so Amma Kuma yanzu yaqara aure

Baka Tinanin zai iya samun haihuwa idan har yaci gaba da auren Nan??


Shiru Alh mam yayi zuciyarta na daukan nauyi ahankali Dan kuwa basajin zasu iya tsayawa jiran Omar samu haihuwa,idan ma ya fara samun haihuwar to idan yayan dari zai Haifa sai sun kawar dasu gefe sbd Babu wani Rai da bazasu iya janyewaba akan buri da kudirinsu dayafi shekara da shekaru tin suna matasansu.


Tinani suka shiga dukansu musamman lameenu da hankalinsa gaba Daya shi ya tashi akan auren shi tin kafin wani abu ya shigo gabansu yaji Yana buqatan a cire matar da Omar din ya auro daga lissafi.



Rayuwar Amina a gidan mijin data kasa sabawa da shi sbd rayuwarsu akwai banbanci tazarar sama da kasa Amma Kuma sbd masu aikin da aka zuba mata da Mai kulawa da ita da koya mata abubuwa da yawa sai tafara Dan sakewa tana koyan abubuwan da dama Wanda Bata dauki lokaci ba mijinta kuwa ya amsheta amatsayin matarsa.


Zamansu Daya ya Saka soyayyarta da tausayinta masu karfi shigar Omar

Ita kuwa Daman tini ta kamu da sonsa kawai tana kama kanta ne sbd ganin kaman yafi karfinta.


Sabuwar rayuwa sosai suka Bude ta sabbin ma'auratan da suke cikin sabuwar soyayyar juna,

Gogewa tafara yi ta zama matar gidan mijinta Dan kuwa sosai take kokarin kulawa da mijinta kaman wadda tayi boko ta waye sosai.


Shi kuwa sanyinta da nutsuwarta tareda tsananin nutsuwan dayake samu da ita ya saka zuciyarsa kamuwa da Sonta fiyeda yanda yayi tinani gashi ita din yarinya ce sosai take narke masa tana sakashi Jin kansa tamkar sabon saurayi duk ta gama kame gangar jiki da zuciyarsa.


Jamaal ma yaji dadin zama da ita sosai fiyeda yanda yayi tinani duk da batajin turanci shikuma ba sosai yakejin hausar ba Baya ma iya doguwar Hausa duk kame Kame ne,


Jamaal ya koma gidan Dad dinsa sedai  Bai wani jima ba ya koma sbd hutunta Daya qare na makaranta.



*********Kaman yanda ake cewa kaddara ta rigayi fata kwatsam sai ga ciki a jikin Amina Wanda ya girgiza duniyar Alh Omar Jaden seelah,

Ya girgiza sosai sbd Bai taba Saka ran zai haihu din ba,

Yanada ciwo a zuciyarsa na shekaru akan rashin haihuwa Kuma ya Riga ya cirewa haihuwar Rai shiyasa bayyanar cikin ya girgizasa matikar gaske.


Ita kanta Amina Bata Saka ran samun haihuwa ba sbd ta Riga ta yaddarwa kanta zata zauna dashi ahakan ba haihuwa so itama samun cikin ya Sakata mamaki me tsananin gaske da farin cikin gaske duk a lokaci Daya.


Tinda ta samu cikin ya daukesa suka bar kasar kusan watanninsu uku kafin suka dawo lokacin cikin yakai wata shida Babu Wanda yasan dashi bayan shi da ita sai masu aikinta da suka Saba da ita sosai suke mata biyayya.

#MAMUH#

#JAMAAL JEEY SEELAH

#DEEP

#HAROON SEELAH

#LOVE

#CRAZINESS

#ZAFIN KAI

#AMEENATOU


ASHNA BEAUTY SKINCARE 

Free class free class  

Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta 

Carwash 

Airfreshner 

Liquid soap 

Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058

Karku Bari wannan damar ta wuceku


*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

_Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments