Breaking News

Ameenatou 29

 *_Arewabooks@Mamuhgee_*


29

Da daddare Bata wani ci abinci ba furan babbah kadai tasha kadan tace batacin abinci ta koshi,


Rakata wanka dadah tayi sbd Bata iya zuwa bandaki ita kadai da daddare sai anrakata Dan haka tana Gamo wanka doguwar Riga kadai ta Saka ta Kwanta bacci Dan Allah yayi mata baccin wuri Dan haka yawanci Se dare Hafiz ke samun cikakkiyar yanci a cikim gidan daga wahalan Ameenatou da takaicinta.


Dakinta shine a tsakiyar nasu Babbah Dana su Yaya Hafiz din sbd duka duka gidan dakuna uku rak sai bandaki da tsakar gida da kitchen dinsu karami.


AMEENATOU BABBAH wadda kusan kowa ya sani da budurwan Babbah kaf wainda ke garin shedu ne Kuma zasu Bada sheda a koina cewan Babu yar gata Kuma sangartacciyar da gata yayi mata yawa a garin kamarta,


Babbah fadan tsananin son dayakewa yar budurwan tasa bama Mai yiyuwa bane,hakama dadah akanta kowa ya sheda yakuma tabbatarda son da ake cewa ana yiwa auta na musamman ne Dan kuwa kauna da banbancin datake nunawa akan Ameenatou daban yake a ranta akan sauran yayan nata.


Su Hafiz kuwa dasuke yannanta sunfi kowa Bata kariya da tattalin tarbiyanta da kiyaye huldodinta da kowa,

Bata zuwa gidan kowa,Bata yawo baa aikenta komai yimata sukeyi,

Tin tana yarinya sune suke Rakata makaranta su daukota haryanxu data zama budurwan datake nanatawa Rakata akeyi makaranta kuma a koma a rakota gida ko Daya daga cikinsu Kokuma Babbah da kansa Wanda duk manyancinsa babu ruwansa zuwa yakeyi takakka idan aka Daketa a makaranta shiyasa kowama ya gaji ya shafa mata lafiya basa dukanta sbd sharia ce da zance Baya karewa har gaban manyan gari Kona makaranta

 Babbah Sam Sam Baya yadda da laifin Ameenatou Koda sama da kasa zata hade kuwa Baya yadda da tayi lefi Kuma wani lokacin Yana sane da batada gaskiyar Amma Baya yadda sedai idan sun dawo gida yayi mata fadan kafin ya lallasheta daga baya.


Duk da su bamasu hali bane Suna rufin asiri sbd su Hafiz na aikin karfi hakama babban duk da manyanci sosai Yana Dan babbuga sanaar dabbobin Daya Saba Babu wani samu sosai Amma sbd inganta rayuwan Ameenatou Babu Wanda yayi qasa a gwiwan Nema.


Ameenatou Bata rasa komai ba sbd Tako ina Babu abinda take nema ta rasa,

Tana cikin gata gaba da bayanta hakama har yanzu datake budurwanta batasan basu babbanta ne suka haifeta ba kaman yanda a garin kaf Babu Wanda yasan da Hakan,

Har mamakin akeyi yanda sukeda manyanci sosai Amma sunada qaramar 'ya sedai Babu Wanda ya taba kawo tinanin basune asalin iyayen nataba duba ma da yanda suke tsananin jinta fiyeda komai.


Ameenatou duk gatanta da sangartan da Akai mata tanada tarbiya sosai Dan kuwa sun Bata kyakkyawar rayuwa su Hafiz musamman Yaya Abdul Basu bari gatan ya lalatata gaba Daya.


Bangaren Bata ilimi kuwa sai inda karfinsu ya kare Dan kuwa makarantar primary ma ta kudi tayi Bata gwamnati ba duk da bawai kudi Basu yawa sosai ba Amma dai private school ce.


Secondary ma Bata gwamnatin takeyiba yanzu tana shekarar gamawa Dan haka daidai gwargwado tanada iliminta kaman su Hafiz din da Suma sunyi karatun bokon Dana Addini kowannensu nada diploma Amma dai Babu wani aikin bare Dora karatu me kyau da amfani sai suke Yan buge bugensu.


A cikin gidan kauna da shaquwa ce sosai a tsakaninsu da barkwanci tin daga kan babban har Dadah dasu Hafiz,

Sosai suke cikin Kwanciyar hankali da  farin ciki,

Hafiz da Ameenatou akwai shakuwa da rigima sosai fiyeda Yaya Abdul duk da Shima akwai shaquwan da kauna sosai Amma shi Bata renasa ba kaman yanda ta Rena Hafiz.


Duk inda zata makarantar boko ko islamiya ko wani abin daban basa barinta fita ita kadai shiyasama duk irin shirmen soyayyar da kawayenta keyi ita Bata yi hakama Allah Bai Saka mata shaawan soyayyar da sukeyiba kwata kwata batama ganin kanta a wadda ta Isa fara soyayya.


Akwai masu Sonta da yawa sbd kyau da haskenta tareda gatanta da kyan jikinta Amma suna shakkar tinkararta da maganar soyayya sbd kullum tana tafe da babanta ko yannanta hakama gata kaman Me rariya a Baki koka zagaya kaje makaranta kace kana Sonta tana Isa gida take fadawa yayunta ko Babbah azo ana rantse rantse a gaban me gari ace kana bibiyanta shiyasa kowa ya kama kansa da ita duk da akwai Yan nacin da duk masifar Babbah suna Nan kan bakansu.


Tinda dadewa Yaya Hafiz ya daukota daga makarantar boko ya biya da ita site gurin Hafiz yace tinda lokacin tashinsu yayi ya wuce da ita gida shi gurin aikinsa ana nemansa.


A ranar idanuwanta suka ganar mata kyakkyawar halittar da Bata taba ganin me kyansaba tinda take.


Da farko kasa yadda tayi da mutum ne seda ya tinkaro inda suke sanye da baqaqen kayan dasuka fidda farinsa sosai ga Rana tana haskasa sai wani daukan ido yakeyi duk sai Taga su Yaya Hafiz da sauran ma'aikatan gurin sun koma mata kaman wasu halittun daban ba mutane ba.


Bakinta ta sake tana kallan fuskarsa dake sanye da black sunglasses me shegiyar kyau da fcap akansa Yana magana kaman ranar zata kashesa Dan kuwa alamunsa sun nuna Hakan.


Fitowa tayi daga inda take ta nufi inda yake Kai tsaye Dan kuwa idan ba gabansa ta tsaya tayi masa kallan kurulla ba bazata tantance abinda idanuwanta suka ganiba.


Hafiz ne yayi saurin riqeta daidai tana gap da Isa gabansa Yana cewa


"Ke Ina zakije?


Kwacewa tayi tana cewa


"Yaya Hafiz wannan baturen shine oganku?

Kullum ze Riqa zuwa ne??


Tunkuda keyarta yayi ya maidata inda yace ta jirasa tayi wani Dan qaramin ihun Jin zafi tana cewa


"Tambaya fa nayi Kuma baka ban amsaba ai"


Jin maganar mace a gurin ya Sanya JAMAAL juyowa ya Kalli gurin daidai Hafiz na rufeta da bayansa Yana fuskewa.


Ganin Babu kowa yasashi juyawa Yana ci gaba da sauransu bayanin da ake masa ita kuma ta fito tana cewa


"Bazanyi magana ba kallansa kawai zan riqa yi" ta Dora hannunta Daya a bakinta tana zubawa Jamaal din idanuwanta masu haske da kyau tareda yin shiru.


Sautin muryansa me tsananin nutsuwa da kamewa acikine Taji Yana magana Rabi duk turanci Wanda ita bama irinsa malamansu keyiba dasu kansu Dan Wanda suka iya.


Tinda tafara kallansa tana Jin muryansa Yana magana Bata qara motsi ba har Saida ya gama ya juya yabar gurin Bata motsaba sai murmushi takeyi.


Hafiz Daya gama aka sallamesu sbd maigidan nasu Daya wuce kama hannunta yayi yaja suka bar gurin Saida sukai Nisa ta kwace hannunta tana matsowa kusa dashi sosai tace


"Yaya Hafiz Yaya sunansa?

Bature ne ko balarabe?


Suna Isa gida ta bawa babba da dadah labarin Taga irin Wanda zasu Nemo mata a matsayin miji idan zasu mata aure.



Tin daga wannan ranar Ameenatou Babu ranar da Bata maganar baturen ogansu Yaya Hafiz,

Kaf gidan saida suka gaji da Jin kalan kyansa datake fadan kaman Rana zata konasa yanata kyalli.


Haka zalika tin daga lokacin Yaya Abdul ko Babbah suna daukota daga makaranta gurin Hafiz suke ajiyeta shikuma daga Nan yaje da ita gida duk Dan sbd tagansa Amma kuma abin mamaki tin daga ranar Bai sake zuwa ba bare ma ta gansa daga qarshema sai gashi anrufe site din gaba Daya tareda aikin dole suka koma Neman wasu ayyukan kafin idan Allah yasa zaa dawo da aikin sai gashi kuwa kwatsam ance su shirya su koma bakin aikinsu Kuma me gidanma yananan tafe da kansa.

#MAMUH#

#AMEENATOU

#THE SEELAHS



*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

 _Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments