Breaking News

Ameenatou 33

 *_Arewabooks@Mamuhgee_*

33


Hafiz dayake nesa dasu da sauri ya qaraso gurin Yana bawa Sir Haroon din hakuri tareda sanar dashi Kanwarsace ya dauko makaranta yanzu wucewa zasuyi gida tabar gurin.


Ahankali Haroon ya mayar da Idanuwansa akan Ameenatou din ya kalleta Yana mamakin kalman daukota makarantar da Hafiz din ya ambata.


Ita kuwa bayan Hafiz din ya matsa ta batareda ta iya furta kalma ko Daya ba Dan samun bakinta datai da mutuwa 'dokin zuciyarta na ragewa batareda tasan dalili ba Kila Kuma zuciyarta tafi sonsa idan Yana daga nesa da ita ne.


Magana Jafar yayi mata a hankali wadda ta Sakata Dan fitowa kadan batareda ta kallesaba ta gaidasa cikin nutsuwa batareda tayi tinanin Yana Jin hausar ba.


Shi dariya ma ta basa Dan haka Saida ya saki Dan murmushi kadan kafin ya amsa Yana kallan Hafiz yace ya tafi da ita gida kawai yabar aikinsa zuwa gobe.


Ita kanta kaman tana jiran ya fada Hakan Dan haka ta wuce gaba batareda ta waiwayoba Hafiz kuwa wanke hannuwansa yayi tareda daukan Jakarta data barmasa yayiwa Haroon din godiya yabi bayanta Yana Bude mata umbrella data manta Yana cewa


"Salon ta ishesu da kukan zazzabi zai kashewa Babbah yar budewa ne yasakata biyosa cikin wanna uwar ranar gashi duk ta ruda masa aiki"


Shiru tayi masa Saida sukai Nisa ta waiwayo tana sake kallan Haroon Dake tsaye har lokacin Yana magana akan abinda sukazo dubawa.


Tin a hanya bakinta ya mutu har suka Isa gida Bata wani ishesa da magana ba Dan haka suna shiga gidan wanka kawai tayi taci abinci tafara kokarin kwantawa yasata gaba suka wuce islamiya Badan tayi niyar zuwa lolacinba Amma sbd tanason ringa biyawa ta gurinsa site hakanan ta shirya suke tafi.

Su kansu malaman sunyi mamakin zuwanta batareda latti ba yau din Amma dai dayake batajin hayaniyar Babu Wanda ya takurata da tambaya haka ta wuni makarantar ba hayaniya har suka tashi ta dawo gida tareda Yaya Abdul.


Washe gari ma haka suka biya site ya qarasa aikinsa ta zauna tana bin duk inda Haroon yayi da idanuwanta masu haske da kyau tana Jin kaman tace ya zauna ya Dena shiga rana duk da duk motsinsa biye ake dashi da umbrella sbd Rana karta tabasa.


Tinda take zuwa Bata sake bari ya ganta ba harta gama binsa da kallo tana murmushin su koma gida.


Abinda Bata saniba tinda kwanakin suka fara ja Yana sane da duk zuwanta da tafiyarta kuma ahankali ahankali ya fahimci sbd shine yake zuwan ta dauka bature ne shi da gasken.


Da farko lamarin mamaki da dariya yake basa sbd Bai taba Ganin inda asalin gata da tattalin 'yaya yake ba sai akanta hakama baitaba ganin kauna da kulawa me tsananin gaske ba da yanne kewa kanwa irin Wanda ahankali yaga anaiwa yarinyar.


Tinda tafara zuwa Bata taba tsallaken zuwa ba Saida exams dinsu ta karato sosai suna farawa shikenan ta Dena zuwa kwata kwata sbd karatu sosai da Yaya Abdul ya sakota gaba dashi 

Shi kansa Hafiz sosai yake Bata lokacinsa suyi karatun exams din tare.


Barin zuwanta ya Saka Haroon tambayar Hafiz ko lafiyanta kalau ya sanar masa axams takeyi Kuma dai Bata jin dadi sosai sbd wahalan karatun.


A nata bangaren ahankali ta dawo hayyacinta akan zuwa ganinsa Dan haka Koda suka gama exam kwata kwata Dena zuwa tayi ga rashin lafiya sosai Daya kwantar da ita na kusan kwanaki Dan haka suketa fama da ita anata lallabawa da ita kaman kwai.


Shi kansa Haroon duk tsananin damuwa da quncin zuciyar dayake ciki Saida yazo har gida ya dubata Wanda Hakan ya Sakata Jin dadi sosai Suma su Babbah haka suka nuna masa Jin dadinsa sosai sbd Ameenatoun.


A nasa bangaren yanda ya samu iyayenta da karamci dakuma sake ganin irin so da tsananin gatan da ake nuna mata ya sakashi fara jinta a zuciyarsa sbd kallan datake masa lokuta da dama idan ta zuba masa kyawawan idanuwanta sai yakejin damuwar datake lullube da rayuwarsa kaman tana ragewa Dan haka ya Dan saki jiki da gidansu Ameenatou din musamman Hafiz dayake qarqashinsa.


A bangaren siddeeq kuwa komai na Haroon shine yake basa kulawa da tsaro yanda ya kamata Dan haka Koda yaga Haroon din yafara samun walwala da yar sakewa a cikin Iyalin Babbah sai Shima yaji ya samu nutsuwa da Hakan take Shima ya sake suka fara samun sabo da mutunci dasu din.


A bangare Daya rayuwar Haroon din na cikin matsanancin daci da damuwa tareda rashin farin ciki ko Daya sbd Dad dinsa da suka Saka ido sosai a lamarinsa hakama Babu alaman aikin Nan nasu zai samu karbuwa a inda zasu gabatar dashi Dan haka kowace dakika ta rayuwarsa cikin damuwa da 'daci me tsanani take Dan haka ciwonsa ma keyin gaba gaba koyaushe batareda sanin kowaba sai siddeeq Wanda ko numfashinsa Baya boyewa JEEY.


Shigarsa cikin Iyalin Babbah ya Saka Dan haske da farin ciki shigowa rayuwarsa a duk lokacinda yake cikinsu Dan takai kusan abinci ma wasu lokutan a gidan yake ci na dadah.


Ameenatou Kam zuwa yanzu tagama shiga zuciyarsa fiyeda yanda yake tinani duk da shagwabarta yayi yawa Amma shi Hakan ne ya kashe zuciyarsa ta mutu gabaki Daya akanta ita Kuma a nata bangaren a yanzu dayake tareda su sai ta aje maganan son datake masa ta jefasu a layinsu Hafiz duk da haryanxu kallansa takeyi a Wanda yafi kowa kyau da tsari Bata taba Ganin kamansa ba.



******Su Dad sun dukafa ba ji ba Gani sai barin kudi sukeyi hankali tashe gurin Neman Maryama Dan kuwa suna gap da zubewa gaba Daya Dan haka suka fice hayyacinsu.


BB ma sun haukace Baki ba ganin sunata tsananta bincike da zufafasa akan Maryama wadda daga karshe suka gano kauyensu.


Bayan barin dukiya me yawan gaske su BB Saida suka gano Maryama saigasu da ita har cikin Lagos sedai ko kwana batai a lagos ba Su Mam suka taho har inda su BB suka boyeta da daddare.


Mam ne ya fara tsayuwa akanta kafin Lameenu ya shigo bayan ya kashe wayarsa gabaki Daya daga wayar dayayi ya tsaya Shima yayi mata kallo Daya Yana komawa ya zauna kujeran alfarma dasu BB suka kawo musu na zama.


Shima Mam zama yayi Yana kallan BB batareda Bata lokaci ba Dan baida time na batawan yace


"Tatso mana bayanin komai daga bakinta banason rasa kalma ko Daya komai nakeson Jin a yanda yake dinsa."


Qwayar datake bakin BB ya qarasa hadiyewa idanuwansa na sake rinewa jajir ya miqawa yaronsa Daya hannu ya Saka masa wata mahaukaciyar wuqa da shape dinta kadai abin tsoro ne.

Nufar Maryama din da idanuwanta suke a daure yayi tareda tsayuwa a kanta ya kamo kanta ya Bude idanuwanta ya Saka mata wuqar gaban idanuwanta da sukasha mugun dauri cikin muryansa me kauri da karajin rashin Imani yace


"Ki kalla Menene a gaban idanunki"


Kafin ma taja numfashin tsoro da tashin hankali bare taga wainda ke zaune a gurin ya mayar mata da daurin idanuwan ya rufe.


Mayar da kaifin wuqar yayi akan jijiyan maqoshin wuyanya Kai tsaye yace


"Meya faru a Daren ranar da matar sir Omar ya ta rasu?

Akwai ciki a jikinta koda ranar tazo?

Wata nawa?

Ta haihu?

Me ya Haifa?

Ina abinda ta Haifa yake?

Waye taredaku a Daren ranar?

Ya Akai kika tsira a Daren????


Cikakken bayani zakiyi sbd rashin kalma Daya daidai take da ficewan ruhinki daga gangar jikinki."


Wasu Hawaye masu tsananin zafi ne suka gangaro daga idanuwanta dasuke a rufe zuciyarta na wani irin rawar tashin hankali da tsoro Dan kuwa tasan shikenan nata karshen yazo abinda taketa yiwa gudu sbd tasan Hakan zai iya faruwa wata ran sbd akwai tabbacin asan data tsira.


Sake daga wuyanta BB yayi Yana qarawa wuqar seti har seda ta Dan fasa wuyan jini ya Dan fito.


Zufa take fitarwa sosai kirjinta na wani irin mugun bugawar da kusan Suma su mam din kirjin nasu harbawa yakeyi sosai Dan kuwa a Baya duk zance ne sukeyi Basu tabbatarba sai yau din zasu tabbatarda masifar Dake gabansu tana can tana yawo a duniya batareda sunsan a Ina ba.


Lameenu kuwa har wani zufa yake tsiyayowa hannuwansa na rawa Da matsuwan Jin Abinda zata fadan,


Allah yasa Omar din Bai haihuba zance ne kawai,

Allah yasa suji abinda zai kawo karshen matsalar tasu idan ba Hakan ba akwai babbar matsala da kura a gaba.

##MAMUH#



*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

_Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments