Breaking News

Ameenatou 6


 *_AMEENATOU_*

_Mamuhgee_

#Arewabooks@Mamuhgee

#ZafafaBiyar




6

*_ASHNA BEAUTY SKINCARE_*

Free class free class  

Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta 

Carwash 

Airfreshner 

Liquid soap 

Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058

Karku Bari wannan damar ta wuceku



*********

Babban abinda yafara sauyawa sosai a rayuwar Omar shine harshen yare,

Daga Aron har Ahmed dayake musulmi basa Jin Hausa Daman tin farko da dubaru suke magana dashi Dan haka da karfi da yaji yaren turanci ya fara kama bakinsa Dan kuwa ko Ahmed dayakewa kallan nasa ba bahaushe bane yaren igala ne da aka haifesa a Lagos ya tashi a Lagos Dan haka tini Omar ya sake ya fada yaren turanci Shima Yana cabawa.


Sabo da shakuwa dole ya shiga tsakaninsu duk da Yana girmamasu a matsayin wainda suka girmesa su Kuma suna kulawa dashi kaman jininsu Dan kuwa Babu abinda bazasu iyawa Mr Jaden ba ko Yana kasar ko bayanan Dan shine gata da rufin asirinsu da iyalansu.

Mutum ne shi Daya inganta rayuwarsu sosai yanada alheri baida rowa Sam shiyasa suka zama Yan amanansa Dan ya dade a Nigeria shekaru sosai anan yake huldodinsa da yawansu.


******Lokaci yaja Omar tini ya kwana biyu da shiga makarantar da ake kira yaqi da jahilci wadda kusan acan kansa ya qarasa budewa yanzu ba laifi Yana iya abubuwa wa kansa da da sama wainda su Ahmed suka koyar dashi da Kuma iliminsa Daya fara basa,

Shine yake zuwa da kansa yaje ya dawo da mota batareda ankaisa ba hakama Kuma Yana zuwa banki ya cire kudi da kansa batareda wani ya raka sa ba hakama siyayyar abubuwan buqatansa,


A rayuwarsa yanzu abu biyune ya rasa masu damun zuciyarsa kowanne dare shine rashinsu mamman da lameenu a tareda shi sai Kuma rashin Mr Jaden da kusan zuwansa biyu Yana komawa batareda shi ba Amma yanzu Kam da komai nasa na tafiya ya kammala haka yayi bankwana dasu Aron ya tafi yanajin kaman ya rabu da Dan uwansa na jini 

Amma Ahmed dashi suka tafi sbd shi har lokacin baiyi aure ba Bai da iyali sabanin Aron yanada family Dan haka shi aka barsa da kulawa da gidan suka koma Poland kwata kwata.


Da farko yaso ganawa dasu mamman kafin tafiyarsu Amma ba lokaci Dan haka dole Mr Jaden yayi masa alkawarin zaa kawo su Suma Nan Lagos su samu Dan ilimin shigowa mutane kafin akawosu Poland inda yake su hade suyi karatu kamansa.



Wannan alkawarin ne ya kwantawar da Omar hankali Wanda har sai dayayi magana dasu mamman da waya daga can Ashalawa suka basa tabbacin suna Nan tafe Suma sun shirya tsaf.


Farin ciki da nutsuwan zuciyar Daya samu da Jin Hakan ya Sanyashi kwantar da hankalinsa daga Dan tsoron Daya shiga na samun kansa a wata qasar wata duniyar da baisan da ita ba Dan haka gaba Daya yanzu ya kwantar da hankalinsa ya Maida akan  karatunsa dayake Dan cimma buri ya samu dawowa yaje dubo mahaifiyar Kasimunsa da mahaifiyar jamilu.



A bangarensu mamman kuwa wata sabuwar duniyar rayuwar Baji ba Gani suka Bude a Ashalawa Dan kuwa gasu da kananun shekaru Amma Kuma suna cikin yan lamba Daya na rashin imanin Ashalawa da bushewan zuciya.

Duk abinda suke son samu sunata samunsa da nasu da Wanda na karfin hali ne duk sun hada sun mallaka Dan haka suka Tara wata irin danyar dukiya da Suma basusan ya zasu sarrafata ba,

Jini da rayukan da suka tafi Dan Saka hannunsu sunada Dan yawa a ashalawa Dan haka sunansu ya sake habbaka duk da Babu sauran Amma sunan seelahs Kam a Ashalawa yasake samun daguwa.


Basuda niyar barin Ashalawa sbd so suke ahankali ahankali sai sunkai sune manyan Ashalawa da zasu kwantar da Wanda sukeson kwantarwa su take su kashe.,suna son sukai sune manyan da acikin Ashalawa ko digon zinari bazata fita ba batareda izininsu ba da Kuma kasonsu.


Zuciyar mamman da lameenu ta rikide daga seelahs ta koma wata abar daban da babu Wanda ke iya gane Menene a cikinta ba sai su kadai da yanzu sunfi kowa sanin zuciyoyin junansu.


Dukiyar hannun Omar Bata taba fita daga zuciyarsu ba Kona sekan Daya Dan kuwa itace har yanzu a qasan zuciyoyinsu da basajin har abada idan ba mallakarta sukai ba zasu ji abinda yake kirjinsu ya fada.


Duk wani mataki da sukeson takawa a rayuwarsu Dan mallakar dukiyar ne wadda duk yanda suke daukan Rai baa bakin komaiba yanzu suna mallakar zinariya haryanxu Basu samu abinda yayi Koda Rabin na Omar din bane Dan haka suke sake nutso a duhun zuciya.


A ranar da sukai waya da Omar ya sanar dasu kyakkyawar rayuwar dayake gudanarwa tareda nutsuwa da tarin wadata Jin sukai gabaki Daya hankalinsu ya tashi daga Ashalawa ya koma akan samarwa kansu ilimin da zai Basu ikon mallakar abubuwa da dama daga Omar din Dan haka take suka amince da tahowa inda yake din.


Abinda Basu sani ba shine Omar yariga yabar qasar Mr Jaden ya tafi dashi Poland Dan haka bayan isowarsu sunji ciwon Hakan sosai Amma dai sunsan koman Daren dadewa zasu hade dashi Kuma abinda suke son kota halin yayane sai sun mallaka Koda abubuwa da dama zasu faru.


Aron ne mutum na farko daya fara banbance halinsu Dana Omar Dan kuwa su Babu sauki ko kadan a kulawa dasu kamanshi,

Tinda suka zo yaketa iya kokarin kulawa dasu da karatunsu sedai kwata kwata Babu sauki.


Saida suka shafe watanni suna cin banza a mansion din akai musu komai kaman yanda akaiwa Omar tin daga Id cards da passport da acct suka fara wayewa da harkar kafin Mr Jaden ya hadasu da abokan huldansa da lauyoyi na daban suka fidda dukiyarsu me yawan gaske ta danyar zinariyar Akai huldarta anan ne suka Hadu da Mr Owolowo bayaraben da shima ya goge a harkar danyar zinari ta gurbatacciyar hanya Dan haka tini ya janyesu daga Mr Jaden suka koma gurinsa acan suka fara gogewa da karatu da harkar zinari ta hanyar ilimi da wayewa tini suka bar qasar suka gaba Daya suka bisa Angola acan suka fara karatunsu sosai Kuma suna kasuwancin zinarin sosai tareda wasu huldodin na kasuwancin Daya kamata sabaninsa.


Ahankali ahankali Suma dukiyarsu tafara habbaka kaman yanda iliminsu da wayewarsu ke habbaka tareda sunayensu.


Kaman yanda rayuwa ke tafiyar musu daidai haka rayuwa ke tafiyarwa Omar daidai Wanda nasa ilimin yafi nasu zurfi sosai hakama gaba Daya shi tasa rayuwar tamkar Dan gata yake gudanar da ita Dan kuwa Mr Jaden ya zama tamkar uban Daya haifesa sbd tini ya qara masa da sunansa akan nasa Dan ya zama asalin Dan qasar Kuma kaman yanda da yawa basu San Mr Jaden ya taba haihuwa ba sai suke dauka Omar din dansa ne Daya Haifa a Nigeria sbd zaman da yayi acan sosai.


Matar Mr Jaden da farko ta qyamaci Omar Amma da shekaru suka fara ja ya goge ya koma tamkar baturen Shima hakama nutsuwa da tsananin son dayake wa mr Jaden kamar asalin Dad dinsa ya Sakata itama amincewa dashi a matsayin 'da.


Dukiyarsu Babu Haram Babu cuta ba cutatarwa kasuwanci akeyi da ita sosai tini ta qara haukacewa da habbaka ta bangare Daya Omar ya fara tsayuwa sosai a business ga bangare Daya ya musuluntar da iyayen nasa Mr and mrs Jaden Dan haka suka sake samun nutsatsiyar rayuwa.



****Bangaren su mamman rayuwa tayi musu yanda suke so Tako ina daukaka suke sake samu da qananun shekarunsu Dan haka suna cikin matasan Dake tashen arziki me yawa,


An wayi gari abokin huldansu Mr Owolowo ya mutu sanadiyar bugawar zuciya ake tinani sbd jinin da aka samu ta hancinsa Yana fita da kunnuwansa Amma dai baa tsaya wani dogon bincike ba aka rufesa aka bar maganar daga Nan suka tattara suka bar Angola suka dawo Nigeria suka Gina kansu Amma dai basa wani zama suna gurin Omar Wanda gabaki Daya idanuwansu da zuciyoyinsu sake shiga tashin hankali sukeyi idan suka ga rayuwar dayake ciki da irin mugun tashin da arzikinsa keyi.


Shekarar da Omar yayi graduating daga karatunsa tareda su Akai biki na burgewa da Mr Jaden ya hada masa Wanda ya Tara manyan abokan huldansu da families nasu.


Su kansu su Omar din cikin farin ciki suke sosai sbd burinsa ya cika ayau ya samu kansa cikin ilimi me yalwa da Kwanciyar hankali tareda wayewa tamkar bashine me yawon kauyuka da daji ba.


Su kansu mamman sauyinsu a bayyane yake Dan ma sunfisa budewan ido sbd sunfisa yawon qasashe yanzu tinda kusan su dasu ake yawon duk business dinsu musamman yanzu da Babu Mr Owolowo sune akan dukiyarsu da tasa da suke cinye fiyeda Rabi.


A gurin dinner din mamman ya kalla idanuwansa akan baturiyar qasar data dauki hankalinsa Badan komaiba sai Dan sanin mahaifinta akan sunan dayayi akan harkar zinarin kasar Amma ya tsufa sosai yanzu hakama ko gida baa fitowa dashi mahaifiyarta ce Akai itama mahaifiyar tata ta tsufa.


Da farko lamari ne da bazai taba yiyuwa garesa ya samu baturiyar Amma Kuma duba da Shima kudin ne dashi sosai ba laifi hakama yanada iliminsa da wayewarsa tareda kayansa Dake Jan raayin mata da yawa sosai akansa yasa Hakan zata iya yiyuwa.


Babban abinda yabawa kowa mamakin bayan kwana biyu da dinner din shine soyayyar mamman da Aleena wadda Mr Jaden da mahaifiyar Aleena din da Omar sukai alkawarin hadasu aure Amma Omar na ganin yanda mamman ya mutu akanta take ya Hana Mr Jaden sake tada maganar aurensa da Aleena sbd yayiwa Dan uwansa mamman farin cikin samun mace kaman Aleena duk da ba musulma bace Amma zuciyarta nada kyau musuluntar da ita bayan auren abune mara wuya.


Lameenu dayafi kowa sanin zuciyar mamman Baiyi mamakin farin ciki da tsananin son da mamman din kewa Aleena ba da yanda ya ringa sakin dukiyarsa kaman baisan zafinta ba wadda bawai damuwa Aleena tayi da dukiyar ba sbd shi takeso Kuma duk abinda mamman yakedashi tanada abinda yafisa fiyeda a kirga.

#MAMUH#

#JAMAAL JEEY SEELAH

#AMEENATOU

#DEEP

#ROM

#TOOHOT



*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

 _Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments