Breaking News

Diddigar Kaya 15


 DƘ


15


Yana durkushe kan kafan shi É—aya, É—ayar kuma kanta ne a kai hannunshi na patting kumatunta yana cewa

"ke! Ke!!"

Sede ina bata ma san yana yi ba.


Mammi tace 

"yi sauri ɗauko ta mu tafi asibiti Faizan Farhan na da hannu a wannan abun kuma wallahi se sun ga bacin rai da basu taɓa gani ba, wani irin shashanci ne wannan?"


Da sauri ya ɗauke ta yadda yaga ran mammi ya ɓaci be so ta bi su asibitin ba don yanzu suka dawo sbd kafar ta da ya matsanta mata se kuma suka tarar da wannan, haka ta ƙi shiga gida suka juya asibitin tana kiran Baba Prof a waya.


Ba irin faÉ—an da likitoci basu yi ba, aka samu aka shawo kanta aka yi mata dressing ciwukanta, lokacin baba prof da Baba Alhj da jadda suka iso.


Tana kwance kaman wata innocent, sossai Jaddah ta zub da hawaye tana zagin su Farhan inda take shiga ba ta nan take fita ba, Baba Alhj bazaka ce ya wani damu ba haka nan oga kwata kwata Faizan tunda nurses suka karÉ“eta ya samu wuri yayi zaman shi ba don mammi da tayi magana ba ma wayanshi yake ta operating, Baba prof ne yace 

Duk su koma a kawo ko zaliha ne ta kwana da ita tunda allurar da aka mata ze jima be saketa ba.


Tun suna kan hanya ya kira Farhan da Faraj akan su same shi parlornshi, suna isowa duka nan suka yi, tun kan su zauna babu zato ba tsammani ya saukewa kowannensu zazzafan mari, duk a razane suke Kallonshi ranshi sossai ya É“aci yace 


"baku da hankali ne? Kuna Tunanin duk rashin hankalin Fauza ya kai wadda kuka yi? Irin wannan duka ko a hannun hukuma iyaka tana mace in kuka yi mata illa fa? Ina ce seda na ce muku kar kowa ya taɓa ta sbd abunda ya faru? Kun tambayi dalilinta? Ko don tana da yawan neman tsokana se aka ce a komai ma ita ke da laifi?"


Babu wadda ya taɓa ganinshi yana faɗa haka, yayi sossai da sossai sbd yadda ya ga Fauxa, jadda ma ta karɓa harda Allah ya isa tayi musu, mammi ma Seda tayi nata sossai ta kuma ɗauki fushi da dukkansu, Faizan dae da Baba Alhj en kallo suka zama se daga baya baba Alhj yayi ta ba jadda hakuri.


Tace 

"me ya faru É—azu É—in?"


Baba prof da ya zauna ya É—an yi shiru yana Samarwa kanshi natsuwa kan yace a tausashe 

"Duk abunda ya farun laifin Fauziyya kaɗan ne Dukda dae ni shi ya fi daga min hankali ba wani faɗar da suka yi ba, da farko dae ni na janyo don na san halin Fauxa na Haɗata da wata yarinyar makota a nan farkon layin ganin kullum tana wahalan samun abun hawa, to wai Fauziyyar sau biyu bata rubuta paper ba tana fita wani ke rubuta mata a madadinta, to ranan sai bata dawo da wuri ba shine yarinyar ta fara zagin ta har ta kai kaina se fauziyyar ta fasa mata baki a mota kaman yadda driver ya bada nashi bayanin, to bayan nan ne suka haɗu da ƙawayen ta wai zasu dake ta shine tayi musu dukan kawo wuƙa iyayensu kuma suka kawo min hukuma sun kuma aibata ni sun yi min kazafi wadda na Barsu da Allah zasu bada shedar shi ranar gobe"


Shiru parlorn ya É—auka kan Jaddah da ta zabga tagumi tace 

"yau na shiga uku da yarinyar nan, to ina take zuwa? Da wa take fita kuma?"


Baba prof ya kalli babanta da yayi shiru hawaye na shirin zuba mishi yace 

"kar ka yi mata kuka Sulaiman, da ni da kai duk É—aya ne haka yaranmu don an zo kamani a madadin mahaifin Fauziyya ba'a yi kuskure ba, a yinin yau na yanke hukunci akan Fauziyya wadda nake so duk ku sheda, bana bukatar shawarar kowa bayan na mahaifiyata, na yanke nan da watanni biyu zan É—aurawa Fauziyya Aure da Faizan..."


Ɗib haka parlorn ya ɗau shiru, Faizan dae yi yayi kaman be ji ba don ya san kila karan jirgi ya fara taɓa mishi kunnen shiyasa ba ya ji da kyau, ko a imagination baze taɓa kawo wannan hadi ba bare a zahirin gaskiya.


Mammi tace

"Allah ya sanya Alkhairi, wannan haÉ—i shine daidai"


Baba Alhj yace 

"A'a yaya, ya zaka fara wannan kwamachalar? Taya zaka fara HaÉ—a nitsaste kaman Faizan da fits...."


"Akul Sulaiman, in dae ba kana so ka nuna min bani na haifi Fauziyya bane babu ruwanka naka idanu, Faizan na ba Fauziyya kuma ya riga ya zauna.."


Ba don kar ace yayi rashin kunya ba da se ya tambayi baba wai wani Faizan ne yake referring to, kanshi gabaɗaya ya dau hayaƙi in kuwa baba yayi hakan ba karamin cutar shi yayi ba, me ze yi da sauran wasu? Me ze yi da ƴar giya?


Jaddah sossai ta nuna amincewarta da shawaran a haka suka tsayar kan su Faraj suka yi ta ba baba hakuri yace ba shi zasu ba wa ba Fauza zasu ba kuma biyar da Faizan ya kashe a asibiti su tabbatar sun biya shi, a haka aka watse aka bar Faizan a zaune a wurin.


Seda baba ya kula da Sam kaman baya hayyacinshi ne ya tashi yaje ya É—ibo ruwa masu sanyi ya kawo mishi 

"karɓi ka sha!"


Ya kalli kofin kan ya É—aga ya kalli baba da rinannun idanunshi yace 

"na koshi"


Baba yace

"karɓi mana ai ruwa rayuwa ne"


KarÉ“a yayi ya kafa kai ya shanye tas kan ya É—ago ya sake kallon baban, murmushi shimfiÉ—e a fuskanshi yace 

"karka ɗaga hankalinka Faizan, a yadda na sanka da natsuwa, kawaici da hangen nesa kaman mahaifiyarka ina so ka cigaba a haka, na zaɓa ma Fauziyya Kaine sbd Kai ne Allah ya sha nuna min a duk istikhara na, da kai hankalina ya fi kwanciya, na san bazaka taɓa tozarta abinda na baka ba"


Faizan yayi shiru kaman ruwa ya cinye shi

"baba fa watana kwata kwata uku ne da aure"


Yace

"na sani, Fatima da mahaifiyarta masu fahimta ne na san zasu fahimta"


"baba mahaifiyarta bata taɓa ƙaunata ba, ko gaisuwata bata taɓa buɗe baki ta amsa ba"


Yace 

"na sani wannan duk ba wani abu bane ba lallai kowa ya so ka a duniya ba, daga kan Annabawa har Sahabai zuwa malamai babu wadda bashi da maƙiya"


Yace 

"Baba Fauziyya da Fatima basu taɓa shiri ba taya zan iya haɗe kansu su zamar min tsintsiya madaurinki daya kaman yadda ka zamarwa iyalan ka?"


Yace 

"kai ɗin jarumin namiji ne wannan me sauƙi ne a gareka, ina me tabbatar maka zaka yi alfahari da wannan haɗi watarana, ka je ka kwanta karka yawaita tunani instead ka raya daren idan ba zaɓin Allah ba ce se ka ga Allah ya musanya mata da alkhairi in kuma ka ga an ɗaura to kaddarar ku a sarƙe take da juna tun fil azaal"


Mikewa yayi yace 

"Na gode, se da safe"

A ladabce kan ya juya ya fice.


Wannan dare haka ya zamarwa Faizan daren tashin hankali don ya kwana yana rokon Allah akan wannan abunda baba ke shirin tinkarar rayuwarshi dashi, duk mazan gidan a rasa wadda za'a lakabawa wannan fitananniyar yarinyar se shi? Yayi nadamar zuwa yola a ranar ya fi sau dubu kila da be zo ba baba be ganshi ba da wani ya zaɓa ya baiwa ba shi ba.


Jadda da mammi dae sun kwana cikin farin ciki yayinda baba Alhj ya kwana yiwa wan shi Adu'a ya tabbatar ba don shi ba da lamarin Fauza yanzu ya kaishi ƙasa, Ammi ya kira ya mata bayani tashi ɗaya ta nuna Allah ya kasheta wallahi baza ta kara Haɗa zuri'a da Mammi ba an yi mata fin karfi a lokacin fadyaa yanzu kam babu wadda ya isa, har gwara faahim sau dubu da Faizan a gareta.


Baba be kula ta ba ya yi kwanciyar shi don in yace ze biye mata se Amarya ta ji kuma yana so ya sanar da ita ta yadda zata fahimta babu cin fuska ko son kai a wannan tafiyar.


Washegari zaliha ta tashi daga baccin da ta koma bayan sallar asuba bata samu Fauza ba, neman duniya da nurses suka mata bata cikin asibitin ko da Baba prof da jadda da kuma Aunty Amarya suka iso ana kan nemanta ne.


Alamu dae sun nuna fita tayi sede ina zata da rauni a jiki?


Ita kuwa tana tashi ta mike zaune tana kallon inda suka bare mata a fatarta da take matukar tattali, ranta yayi baƙi kirin da irin wannan tozarci da yayyun nata suka mata, ta tabbata duk gidan maƙiyanta ne banda mammi da jadda da Amminta, lallai abunda suke gudu se ta sake yi in basu kasheta ba ba su cika mugaye ba.


Dira tayi daga kan gadon ko hijab É—in da ta dauka ganin yadda ya fashe yasa ta cillar, takalmin zaliha ta saka ta fice, abun hawa ta tare se gidansu sakina, ta sa me gadi yaje ya karbi kudin ya kawo mai, sossai hankalin sakina ya tashi da ganinta haka.


Anan tayi wanka ta sauya kaya tayi kwanciyar ta bayan ta ci abinci, duk yadda sakina ta so tayi magana kasawa tayi da ta matsa se ta kawo kuka ta sa, hakan yasa zaliha bare wasu tabs tace 

"sa wannan a ƙasan harshen ki duka biyu ki barshi ya narke da kin yi bacci kin tashi bacin ranki ze kau"


Sawa kuwa tayi ta kwanta, a haka tayi bacci har sha biyun rana kan ta farka abu kam ya fi karfin jininta ga shi ta bata overdose ne, tana tashi ta gayawa sakina duk abunda ya faru ta kuma ce tana so ta kunsa musu bakin cikin da zasu saka wuyan ta gabas su yanka, wayan sakina tayi anfani dashi ta kira Zubair luckily ya koma da yau abunda yake so da ta bashi.


Haka ta diro ko mayafi taƙi sakawa kaman ba ɗiyar musulmi ba ta nufi fita, Sakina da kyar ta shawo kanta akan driver ya maida ta.


A farkon layinsu tace ya ajiye ta don tana so kowa ya kalleta yadda su Farhan zasu kara jin haushi, aikuwa kaman ta kimta daidai.


Farhan, Faizan, Faraj, Baba Alhj baba prof da polisawa ne tsaye ana batun yadda za'a samo ta shi Faizan kaman dole ce kawai aka mai na shiga case É—in zuciyarshi na bashi wurin watsewarta tayi don mashayi daga ranshi ya É“aci abun shaye shayenshi yake nema ya rage zafi.


Yana cikin wannan tunani ya É—an kalli hanya har ya É—auke idanu yayi saurin sake mayarwa ya zuba mata su yana kallo, tun daga nesa zaka san a make take mankas, so yake ya janye hankalin baba Alhj sede yana juyowa yaga duk suma sun zuba mata idanu, ga bandage a jikinta ta sa wani riga da da kadan ya sauka kaurinta, hannunta duk a bayyane gashin kanta a Parke cikin loose bon, Baba Alhj ne ya tafi ze fadi, Baba prof yayi saurin tare shi yace 


"Menene haka Sulaiman? A kanka aka fara jarrabawa? Kana so se ka É—aurawa yarinyar nan abunda ya fi wannan?"


Su Farhan yayiwa kallon duk wa ya janyo? Ba ku ba? Kan ya saki baba Alhj ya fara tattaki zuwa gareta.


Maganganu take maras kan gado tana faÉ—in laifin babanta ne da yayi mata baki kullum yake kiranta fitsararriya gashi fitsara ta bita, ba su Farhan sun ce zasu mata abunda bazata kara marmarin rayuwar banza ba? To gashi ta kara su sakata gabas su yanke yanzu yanzu zuwa tayi don su gani, Kaman Faizan ze yi kuka don tausayin kanshi yanzu da abunda Babanshi ze HaÉ—a shi kenan?


Har É—akinta ya kaita a sashen Jaddah tare da taimakon ta ta shimfiÉ—ar da ita se bacci, duk idanu suka zuba mata.


Jaddah tace cikin karfafa mishi gwiwa

"Adu'ar mu baze taɓa faɗi ba professor, ka kwantar da hankalinka abunda kake shirin yi in shaa Allah shi ze zama silar warakar komai, Allah maji roko ne me jin ƙai ka fini sanin cewa baya taɓa juyar da Adu'a sai de in ya musanya da abunda ya fi alkhairi, ya kuma amsa ta hanyar da tafi kowacce daidai, sadaqa maganin masifa ne, haka kuma Qur'ani waraka ce, Adu'a kuma takobin mumini ne duk bamu daina akan Fauza ba kaga kenan muna da yakinin Allah ze karɓa ko ba daɗe ko ba jima"


Yace 

"hakane mama, bana kokonto akan Hukuncin Allah sede a duk sadda zan É—aga idanu na kalli yarinyar nan jikina yana bani wani abu na daban mama, gani nake ana zaluntarta amma ban san ta ya ba, tausayinta ke ratsa zuciyana har na kan zubar mata da hawayen tausayawa in na kalleta, ba ni kaÉ—ai ba sau ba Adadi Aisha ta min magana makamancin haka akan yarinyar nan"


"komai ze tafi daidai professor in shaa Allah auren da ka HaÉ—a ze zama sanadiyar warwarewar duk wasu al'amuran É“oye"


Mikewa yayi ya fita bayan ya tofe ta da wasu Adu'o'i, ko da ya dawo ya nemi Faizan ya rasa don barin garin yayi.


Satin shi uku da komawa Fatima ta sake É“arin cikin wata guda.


Wannan karon har gida ta zo sbd yadda duk ta É—aga mai hankali, ta kasa fahimtar komai na Allah ne.


Shi kam ya ma tafi chan wata ƙasa ne hakan yasa dole ba yadda ya iya ya barta ta koma gidan, a gidan bayan mutane shiddan nan har yanzu babu wadda ya san da maganan auren na Fauza da Faizan, a fakaice Jaddah ke mata gyara ba tare da ta sani ba, asalin gyaran shuwa Arab take mata.


Dayake yanzu ko parlorn Jaddah baba be yarda ta wuce ba necon tan ma karasa mata ake yi yasa bata fita rana, skin É—inta ya kara wani irin kyau da sheki tayi fresh tayi kiba abunta, nasihohi take sha har ta gaji da jinsu amma tayiwa baba alkawarin bazata sake shan kayan Maye ba har abada.


Yanzu wayanta bashi da anfani don tayi ta neman Zubair bata samu se kawai ta jefa shi kasan akwati.


Ko da Fatima ta zo ma sannu be hada su ba har tayi kwana bakwai ranan ne baba ya kirata yayi mata nasihu masu yawa kan ya faÉ—a mata auren Faizan da Fauziyya da ya hada, ba karamin girgiza tayi da wannan zance ba, tsanar da ta yiwa Fauziyya me yawa ne matuka gashi zata aure mata masoyi ta zama suna shearing komai nashi, abunda ba zata iya amincewa dashi ba kenan.


Ta dawo wurin mamanta hankali tashe cikin matsanancin kuka, Fauza ya sa aka kira mai itama ya faɗa mata, abinka da shiririta irin na fauza dariya kawai tayi ta fito abunta bata taɓa dauka serious bane seda abu ya karato dangi suka fara zuwa nan ne musababbin tashin hankalinta ya fara...

Ko da ta nemi halaka kanta kawai kiran sakina tayi tace ga abunda zata sayo mata ba tare da ita sakinar ta san ita zata sha ba, ta sayo ta bi ribibin en buki ta bata...


DAWOWA LABARI


"FAUZIYYA!!!"

ya fadila ta faÉ—a tana jijjiga ta da karfi, firgigit tayi tare da É—ago kai se taga babu kowa a jirgin se su uku.


"Me haka? Me yayi zafi da zaki É“ata a tunani haka? Kin san tun yaushe muke tsaye akanki?".


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya ta wannan layin

09039206763.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments