Breaking News

Diddigar Kaya 17


 DƘ


17


*Assalamu Alaikum warahmatullah barkanmu da warhaka, fatan duk muna cikin ƙoshin lafiya? Alhamdulillah na gode sossai da adu'o'inku gareni Allah ya saka da alkhairi🥰 jiki yayi sauƙi se a ɗaura daga inda aka tsaya in shaa Allah.*


A hankali ta samu wuri ta zauna akan kujeran parlorn saman chan nesa da inda suke, dukda zuciyarta a tsinke yake don har Ga Allah Faizan na daga cikin waenda take jin shakkarsu don tana tsorace dashi ne tun tana ƴar ƙaramarta, matarshi kawai ya kama suka fita daga ɗakin nata bayan ya ce ta same su a parlor.


Ya É—an yi shiru kan yace 

"Fauziyya kike ko?"


Kai ta É—ago tana Kallonshi wai ita yake tambaya sunanta? Bata amsa ba seda yace 

"wai ba da ke nake magana ba? Kin san Allah ki rufawa kanki asiri ki zauna lafiya da mu tun muna sheda juna, ba zan lamunci rashin kunyarki da fitsaranki ba, ba a kaina kaÉ—ai ba har da matata"


Kallon Fatima yayi yace

"Daga yau ki sallami Baaba ta dinga tsabtace gidan nan tana girka muku abunda Zaku ci da ke da ita, ba zan iya cin jagwagwalonta ba don haka ke zaki kula da nawa abincina da gyaran É—akina"


Fatima na murmushi tace 

"in shaa Allahu habeeby"


Ya sake kallon Fauziyya yace 

"Daga ni har Fatima akwai wadda kika fi shekaru?"


Girgiza kai tayi yace a É—an zafafe 

"baki da baki ne?"


A hankali tace 

"A'a"


Yace 

"madalla! Saboda haka duk safe ke zaki gaisheta, karki kuskura in sake ganin abunda ya faru yau ya faru don bazaki ji da daaɗi ba Fauziyya, matata ta fi karfin wulakantarwanki, Abu na ƙarshe shine babu wani zancen rabon kwana don zaki zauna ne a matsayin ƙanwarmu.."


Kallon Fatima yayi yace 

"ko kina da abun cewa?"


Tace

"ya Faizan na ga baka ja kunnenta akan  shan kayan maye da kuma bin maza ba!"


Wani irin kallo Fauziyyan tayi mata kan ta maida idanunta kanshi jin mai ze ce, se taga ya kauda kai da alama ita yake kallo ganin zata kalleshi ya kawar da nashi idanun, bazata ce ga expression É—inshi ba amma da saisaitacciyar murya ya furta..


"Gate ban amince ki taka ba tare da izini na ba Fauziyya"

Abunda ya faÉ—a kenan ya sallameta, ta mike ta wuce É—akinta ba tare da ta tanka musu ba.


Fatima tace 

"Abunda zaka ce kaÉ—ai kenan?"


Ya ɗan miƙe tsaye kan ya ce

"me zan ce to? Babu wadda ta sani anan garin da ze shigo har gidan nan ya ruÉ—e ta, hakanan tun da ta sanya kafarta cikin gidan nan na yiwa gateman kasheÉ—in bayan ni da ke kar ya bar kowa ya fita daga gidan nan ko ya shigo idan har ba da sanina ba"


Ganin ze wuce room nashi tayi saurin mikewa 

"amma fa kai da kanka ka ce ka ganta a nan garin kenan ai baka san ko akwai wasu bad friends É—inta a nan ba..."


Ya dakata tare da juyowa ya kalleta na seconds kan ya juya kawai ya wuce É—akin shi, zama tayi kan kujeran dabas tana sake sake, ta so ya gayawa Fauziyya maganan da ze hana ta bacci wlh akan shaye shaye da yawace yawace da take yi amma ba komai da ita take zancen.


Itama mikewa tayi ta wuce É—akinta don shiryawa ta dawo turaka.


Samun wuri tayi kan kujera ta zauna tare da ɗaga throw pillow ta ɗaura kan cinyar ta ta zabga tagumi, wai haka zata yi wannan zaman? In aiki ne be dameta ba don horon da ta sha kwanakin nan a gidansu na aiki ba kaɗan bane har ma ta saba, amma bata da waya ba abokin hira, shiru haka ze yiwu kenan? Chan ƙasan ranta kuma maganan Fatima ba ƙaramin kuna yayi mata ba amma ba komai zata yi lokacinta.


TV ta kunna ta rage daren da kalle kalle daaɗi sossai ta ji da ta ga ba wa'azu zuƙa bane, se karfe sha ɗaya ta kwanta don ma ita ba gwanar ci ba ce da dole se ta fita ta nemi abinda zata ci.


Buga kofan ta da aka yi da karfi shi ya tasheta a É—an firgice, dalll haka aka kunna mata bulbs É—in É—akin duka Fararen waenda suke da matukar haske, da sauri ta sanya hannu ta rufe idanunta, duniya ta tsani a kunna mata wuta daga tashi daga bacci.


"Malama tashi ki sama min abunda zan ci karfe bakwai nake da lectures"


Dukda yadda ranta yayi mugun É“aci bata tanka ba, haka kuma bata É—aga idanu ta kalleta ba.


"Da ke fa nake magana malama!"


Har lokacin bata yi magana ba tana calming kanta ne, bayan ta gama Adu'ar tashi daga bacci ta sauka kawai ta shige toilet bata ce komai ba.


Se hakan ya kular da Fatiman, a fili ta furta 

"kammm ni zaki mannawa hauka? Wato ga mahaukaciya tana magana?"

Kwafa tayi ta fito ta je ta zauna a parlorn saman ta É—aura É—aya kan É—aya tana girgizawa, time ta dibar mata in bata fito ba kuma wlh se ta kai karata wurinshi.


Ita kuwa Fauziyya watsa ruwa tayi ta fito ta É—an shafa mai da turare kadan ta saka cotton bubu ta fito, a kan kujera ta wuceta ta nufi hanyar kitchen ba tare da ta ko kalleta bane.


"Ke! Ina zaki je? Ba'a shiga min kitchen kije na ƙasa wannan ɗin abincin mijina kaɗai nake dafawa a ciki gudun barbaɗe"


Juyawa kawai tayi ta nufi ƙasa ba tare da tace komai ba.


Dankali ta fere me yawa ta zuba gishiri tuli guda kan ta soye shi yayi kararau ta juye a warmers ta É—auka ta je ta ajiye kan dining kan ta wuce ta haura.


Har zata wuce É—akinta Fatima ta ce

"Fauziyya..!"


Juyawa tayi ta nufi dining É—in saman, ganinshi a ciki yasa ta ce 

"Ina kwana"


Kaman yadda yayi mata umarni

"lfy"

Shine abunda ya amsa da kan ya cigaba da cin abincinshi.


Kallon kiran me kika min kawai take yiwa Fatiman, ita kuma se tayi shiru na seconds kan tace 

"tunda ni ba zaki gaisheni ba, ina kwana? Fatan kin tashi lafiya?"


Wani irin kallo Fauza ke mata na kina kure haƙurina, ɗaga idanu yayi ya kalleta se tacewa Fatiman

"Ina kwana"


Fatima tace 

"lafiya ƙalau ya kwanan bakunta?"

Bata amsa ba hakan ya sa Fatima cewa

"yauwa kin gama abincin ba?"


KaÉ—an ya saura zuciyar Fauza ya zo wuya tace 

"uhm"


"yana ina to?"


"Kasa"


"ka ji ki, ai anan ne muke karyawa, je ki É—auko mana"

Seda ta lumshe idanu ta buÉ—e kan ta juya ta nufi sauka, shi karan kanshi da kallon mamaki ya bita a sanin halinta bazata bi umarnin Fatima kai tsaye haka shiru ba, ko ta fara sauyawa ne... Kafadan shi yayi shrugging kan ya cigaba da cin abincin shi.


Bata jima ba se gata da food flask ta zo ta ajiye kan dining É—in ta juya zata tafi

"ke bazaki ci bane Fauza?"


Juyawa tayi ta kalleta kawai kan ta juya ta wuce ciki.


Tana shiga ta faÉ—a kan kujera tana ji kaman ta fashe da kuka sbd yadda ranta yayi mugun É“aci gashi bata fitar da abunda ke ciki ba, ita kuma haka take in har bata rama abunda aka mata ba ranta yayi ta zafi kenan da kuna.


Kakari taji me Æ™arfi se kuma taji ana kiran 

"ke! Ke!!"


Ta san ita kaÉ—ai yake kira da ke hakan be sa ta amsa ba, tana kwance kan three seater taji ya turo kofan ya shigo.


"Ke! Bakya ji ina kiranki ne? Ko yadda kwakwalwanki yake a toshe haka kunnuwanki?"


Miƙewa zaune tayi tare da fara kunkuni

"to ai ni sunana ba ke ba...."

Ɗallin bakinta da taji an yi ne ya sakata sakin ƙara tana dafe bakin sbd azabar zafin da ya ratsa ta, hawaye ne ya cika idanunta ta ɗago tana Kallonshi.


Kau da kai yayi yace

"kashe min mata zaki yi? Wani irin jagwalgwalon girki ne kika yin nan? Baki san tana da BP bata cin gishiri bane? Tashi ki wuce mu je"


Mikewa tayi ya sako ta gaba suka fito, Fatima na kwance kan kujera sama sama take numfashi sbd yadda take jin kaman zata mutu, murmushi me kyau ta saki ganinta hakan sarai ta ji yadda ake ta maganan jininta na hawa sossai sbd damuwar da ta sawa kanta na É“arin da take tayi hakan yasa aka hanata cin gishiri, da gangan tayi labtawar da ko loma É—aya tayi se ta ji a jikinta.


Da sauri itama ta karasa gabanta ta duka tana cewa 

"Ya fati sannu! Me ya sameki haka?"


Harara ta zabga mata kan ta cigaba da numfashin ta hannunta dafe da kai.


Rufeta da faÉ—a yayi sossai kaman ze daketa, raurau tayi bayan ya gama idanunta na zub da hawaye tace 

"Yaya Don Allah kayi haƙuri, ni ban iya bane, ban kuma san tana da hawan jini ba... Jiya jiya fa na zo"


Lumshe idanunshi yayi se ya sauke ajiyar zuciya kawai ya wuce É—akin Fatima don É—auko mata hijab su tafi asibiti.


"Na san ba haka kika so ba ko? To mu zuba da ni dake É—an halak ka fasa, in makirci ne ke jiya kika soma amma Fauza kam ta jima a ajin don ina ga har ta gama ma ta fita da sakamako me kyau"


Jin motsin kaman yana dawowa ne yasa tayi saurin karasawa tana É—agota tace 

"I'm so sorry ya fati"


Hijab ɗinta ya miƙawa Fauza ta saka mata, sakawar ma na mugunta ta mata don seda ta karɓa da kanta ta karasa a hankali.


"Karki ci abincin nan, ki nemi wani ki ci bari na kaita asibiti.."


Kanta kasa tana zub da hawaye ta É—an É—aga, har ya kama Fatima a jikinshi sun nufi stairs ya É—an dakata tare da waigowa kaman ya zamar mishi dole  yace 

"kukan nan kuma ya isa haka"


Yana kai nan suka fara sauƙa.


Wani kalar dariya Fauxa tayi tace 

"gobe zaki maimaita abunda kika min munafuka kawai"


Dining taje ta samu abincin shin ma be gama ci ba ya tashi, ta kara akai ta ci tayi Nak ta tattare wurin kan ta zo ta fara kimtsa parlorn da ba wani datti sbd rashin mutane dayawa a gidan.


Bayan ta gama ta koma É—aki tayi kwanciyarta cikin kewan jaddanta kan bacci ya sure ta.


Chan cikin baccin ta taji ana taɓa gefen hannun kujeran da tayi matashi dashi, yadda ta saba yiwa jadda in bacci be ishe ta ba ta tura baki ta mike cikin kunkuni tana kaikaya idanu haka tayi, a hankali ta buɗe idanun nata se suka faɗa cikin nashi, yana tsaye hannunshi ɗaya a aljihu ɗaya na riƙe da Wayanshi, har kaman ze mata faɗan kwanciya bisa kujera se ya fasa.


"Riƙe Jaddah ke son Magana dake"

Ya faɗa yana miƙa mata wayan.


Da sauri ta karÉ“a 

"Jaddah na!"

Tayi maganan tana karya wuya se hawaye..


"Haba Fauza, ke da nake miki kallon jaruma ashe ke É—in raguwa ce kukan ma menene to? Yayyun naki suna miki wani abu ne?"


Yadda ya kakkafeta da idanu yana jiran jin me zata cewa jaddan yasa tace

"babu komai Jaddah kawai nayi kewanku ne"


Tace 

"nima anan hankalina da tunanina duk yana wurinki Fauziyya fatan babu komai ko? In akwai wani abu ki gayamin"


Tace

"ba komai, ina mammi ya kafafunta? Allah sarki yanzu wa ze dinga mata Adu'a oho"

Ta faÉ—a cikin alhini.


Murmushi Jaddah tayi tace 

"tana yiwa kanta amma na san tayi kewanki itama, fadyaa zasu taho ranar Laraba me kike so a kawo miki?"


Zata yi magana ya zare Wayanshi ya sa a kunne tare da Juyawa ya nufi fita yana cewa 

"Zaku ƙarar min da credit, me zata buƙata kuwa yarinyar da ta zo jiya in ba ke ba ma Jaddah"


Zata fara mishi nasihun da suka kashe mai jiki da niyyar da yayi a kan yarinyar yayi saurin kashe wayan, daga Jaddah, Babanshi da mammi duk in sun kira ko ya kira su maganan É—aya ne kar ya sa yarinyar nan kuka kanwarshi ce wacce ko ba aure shi me share mata hawaye ne, hakanan bata da kowa a Abuja in ya cuceta don ba idanunsu Allah na gani kuma ze saka mata.


Yana zama kan kujera se ga call na baba prof suka gaisa kan ya ce 

"na manta ne ban maka maganan karatun yarinyar nan ba, ka san ko bare na aurarwa É—iyata akwai sharadin yin karatu to akan Fauziyya ma ba zai sauya zani ba, idan Neco É—inta ya fito zaka nema mata university of Abuja su cigaba da zuwa da yayarta"


Idanunshi na kan TV ya É—an fesar da iska yana shafa kai yace 

"Baba ba za'a bar maganan makarantar yarinyar nan mu ga kamun ludayin ba tukun? Ba wai ina nufin ba zata yi bane sede ina tsoron komawarta halin da ta shiga a baya ne wadda yanzu se ya fi zunubi da da, tunda yanzu tana da aure"


"in shaa Allahu yanzu bani da shakka akan Fauziyya zata maida hankali tayi abunda ake so, mu cigaba da Adu'a dae kar mu gajiya sannan ka riƙe ta amana kaman yadda ba zaka cutar da farida ba karka cutar da ita Faizan"


Ajiyar zuciya me nauyi ya saki yana sake shafa kanshi Fatima ta fito ta zauna kusa dashi tana cewa 

"ya aka yi ne?"


Ya ce 

"Fauziyya...! Kowa ya tashi amana amana duk sun É—aure ni da jijiyoyin jikina wallahi"


Bakinta ta taÉ“e kan tace 

"amma yaya ka san yarinyar nan da gangan ta so cutar dani É—azu? Ai ko bata san ina da BP ba ta iya girki me yasa bata yi me kyau ba?"


Yace 

"Meyasa ne kike son dawo da abunda ya riga ya wuce Fatima? Yarinyar nan ta baki haƙuri ba shikenan ba? Kina ji dae ina faɗa miki yadda ake bani amanarta kina so ne in yi ta jan matsala tsakaninmu har iyayemu su yi fushi damu?"


Girgiza kai tayi ranta na zafi, wai ina duk tsanar da yake cewa yana yiwa Fauziyyan? Duk a kwana ɗaya baya bata wani wuta wuta kaman ma lallaɓata yake akan wani dalili? Idan ta bar zaman nan ya cigaba a haka akwai matsala dole zata nemi wani hanyar wargaza tsakaninsu.

Da sauri ta miƙe ta ɗauki wayanta dake kan table ta nufi ɗakinta don neman shawarar abin yi...


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya ta wannan layin

09039206763.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments