Breaking News

Diddigar Kaya 18


 DƘ


18


Bata san me ya hau kan Fatiman ba ta dena shiga mata sabga girki ma idan ita zatayi bazata ci ba, se ta koma dafa nata ita kaÉ—ai ita Fatiman nayi musu su biyu.


Tsakanin ta da shi kowani asuba ze tasheta sallah, anan take gaishe shi ba zasu sake haÉ—uwa ba se wani asuban sbd bata fita a sadda taji motsin su a parlor, babu ruwanshi da komai nata tunda bata rasa ci da sha ba don be katangeta ta harkar abinci ba kullum kawo abubuwa ake a loda a fridge se abunda taga daman dafawa.


Iyakaci ta ci ta sha ta kwanta, a sati biyu da suka yi tayi wani irin kara girma fatanta ya sake yin fresh sbd zama wuri É—aya, kaÉ—aici duk ya dameta gashi bata da waya bare ta ji mutanen gida.


Yau bata nemi abinci ba sbd wani series da ake yi a Star life da ya É—auke mata hankali bata kula da lokaci ba kawai taga magrib yayi ko da tayi sallah bata tashi ba har tayi isha kan ta mike ta ninke hijab É—in ta ajiye, sanye take da wani half gown wadda iyakanshi kaurinta purple ya zauna mata das a jiki, gyale ne yake dashi se ta mishi É—aurin da ya fitar da jelar gashinta yana reto, É—an kunne fashion purple ne a kunnenta haka ta buÉ—e kofan ta ta fito.


Dasu ta ci karo yana zaune hannunshi da remote Fatima kuma na kwance a kan cinyar shi cikinta gwanda ne a bowl da ta yanka kanana tana ci a hankali, jin motsin ta yasa duk suka ɗaga idanu suka zuba mata kowa da abunda yake saƙawa a ranshi..


Kaman bazata yi magana ba se tace 

"Sannunku"


Be amsa ba ya maida kai TV haka Fatima ma bata amsa ba, a wuya yarinyar ta tsaya mata barin ma yadda take kara murjewa tana kyau kaman ka sure ta, ba don umarnin da aka bata na ta É—auke kai a kanta zuwa É—an wani lokaci ba da bata barta tana morewa zamanta gidan ba.


Kwafa ta ja a ranta tana cewa

'Fauza kema maganin ki'

Daga haka ta nufi ƙasa abunta, kitchen ta je ta fara Haɗa macoroni salad ɗan daidai na cikinta, bayan ta gama tayi smoothie na ayaba da madara ta zuba a cup, kyuiyar haurawa taji dashi don se ta sake fito da kwanukan bata iya bari a ɗakinta don haka dining kawai ta karasa ta zauna ta fara cin abincinta.


Da ma ze yiwu da ta ce a dawo mata da kayan ɗakinta ɗakin ƙasan tana rayuwanta hankali kwance, da kyar ta gama ɗan abincin taje ta dauraye plate da cup ɗin ta mayar ta kara kimtsa kitchen ɗin don tsabtar gidan banda dakunan masu gidan har yau bata dena ba.


Haurawa ta nufi yi yanayin da ta iske su ne yasa tayi saurin É—auke kanta ta nufi É—akinta Dukda sun riga sun HaÉ—a idanu dashi, janyewa yayi wadda hakan ya sa Fatima Juyawa se ta ganta tana kokarin shiga É—akinta, tana ji Fatima na tsaki sede bata juyo ba Dukda kuwa so take tayi waya da su jadda kaman me.


Haka dae ta kwanta tana ta juye juyen kewa kan bacci ya sure ta, washegari da asuba da ya shigo É—akin ya jima tsaye yana kallon yadda ta kwanta É—in a matukar takure irin kaman mutum na kaÉ—aici haka, se ta É—an bashi tausayi bubbuga gefen pillown yayi tayi miÆ™a wadda ya saka shi saurin É—auke idanu daga kanta kan ta miÆ™e zaune bakinta na motsin Adu'a kaman yadda ta saba tana gamawa tace 


"Ina kwana"


Ya amsa 

"lafiya"


ÆŠan tsayawa yayi be fita kaman yadda ya saba ba yana tunawa da Fa'iza ta zo gidan basa barin ta tayi mintuna arba'in É—aki dole zasu zauna da ita su yi hira a ci abinci ayi kallo duka, amma in ba jiya ba ya manta rabon da ya ganta tana tafiya zata kitchen ko wani abu Sam basa haduwa se a É—akinta in ya zo da asuba ba dole ta takure wuri guda ba!


"Kina da wani matsala ne?"

Ya tambaya.


"A'a amma don Allah ina so zan yi waya da su Jaddah yau sati biyu kenan rabon da in ji muryarta"

Ta karashe tana Kallonshi da idanun baccin ta waenda suka kara girma da haske ba kaman na normal wasu mutanen ba da in sun tashi idanunsu yayi ja.


Wayanshi ɗaya ya fitar daga aljihunshi fara sol design ne da bata taɓa gani ba don ba iPhone bane ba kuma dangin su tekno bane.

"Yanzu yayi sassafe da ƙira, anjima se ki ƙira su"


Hannu tasa garin saurin karÉ“a hannayensu suka shafi na juna, duk É—aga kai suka yi suna kallon junansu kan ya É—auke nashi yana furta 

"saura ki kira waenda basu dace ba ki ga ikon Allah"


Yana kai nan ya juya ya fice.


Baki ta karkace tana tuna su waye ne basu dace ba? Kwafa tayi su sakina ne kilan yake nufi, ajiye wayan tayi taje tayi alwala ta zo tayi sallah.


Bayan ta idar ta koma ta kwanta se seven ta tashi ta fara gyaran É—akinta tana gamawa taje tayi wanka ta shirya cikin wani Hot red top da black wando ta É—aura black É—an kwali, bakinta ta sanyawa red lipstick se tayi wani irin kyau, kwalli ta zana a idanunta kan ta É—auko wayan ta zo kan kujera ta zauna.


Sliding tayi se wani hotonshi hadadde ya bayyana, sanye yake da kayan aikinshi cikakke yayi wani irin kyau gashin kanshi na sheki yana dariya ne tsaye a matakalar jirgi aka É—auke shi, kurawa hoton idanu tayi na mintuna masu yawa kan ta sauke ajiyar zuciya tana shiga call logs.


Bata san da me yayi saving number É—in jadda ba se kawai ta shigar da numbobin tunda tana dasu a kai.


"Jaddah na"

Ta faÉ—a bayan an É—aga wayan ko sallama bata yi ba.


Jidda da ita ma muryarta ya bayyana jin daaÉ—in ta da jin muryar Fauzan tace 

"Na'am Fauza ta ya kike? Ya gidanki?"


Shagwabewa tayi tana cewa

"shine ko kewata baki yi ba ko Jaddah"


Jaddah tace 

"na isa ban yi kewar baki abun magana ba? Ai ba karamin kewanki nayi ba babu me sakani magana da shari'a, babu me nemo faÉ—a in tare, babu wacce kullum ke sakani kumbiya kumbiya idan professor ya aiko nemanta"


Dariya Fauxa tayi tana jin tayi missing old life É—inta, rayuwa fa kenan! Waye ze yarda yanzu Fauxa tayi sati biyu bata nemi faÉ—a ba, ai da a da É—inta ne ko Fatima bata nemeta ba wallahi ita se tayi yadda tayi ta nemeta faÉ—a, amma gani take yanzu ta wuce level É—in sede in an nemeta a samu.


"Jaddah to meyasa bakya nemana?"

Ta faÉ—a tana tura baki.


"Kullum sede wannan me katon kan yace min baya gida ko kin yi bacci..."


Hannunta É—aya ta É—an sa baki tare da zaro idanu tace 

"khaihh Jaddah Ya Faizan É—inne me katon kai? Wlh kanshi daidai ne"


Salati Jaddah ta É—auka muryarta cike da farin ciki da dariya tace 

"innalillahi.. Fauziyya yau ke kike karbawa Faizan faÉ—a? Azzalumin?"


Da sauri ta katse wayan kunyar duniya na kamata, me ya kaita? Wlh ta ma rasa ya aka yi tayi wannan subutar bakin, ai se ta shiga bakin duniya in dae Jaddah ce.


Jaddah kuwa a É“angarenta har sujada tayi na jin daaÉ—i, ko basu zama kaman yadda take so ba alamu sun nuna lamuransu akwai haske, da Faizan na cutar da ita ta tabbatar ita ce ma zata fara kawo sukarshi yau wace rana!


Sake kiran layin tayi da kyar Fauziyya ta É—auka..


"Eyyaa Jaddah kewa!"

Ta fara kawo maganan dake ranta.


"Ina jin kaÉ—aici da kewa sossai, babu inda nake zuwa babu wadda ke zuwa guna banda waya bare in dinga jin muryarku, jadda ko Ya fadyaa da kika ce zasu zo basu zo ba har yau"


Jaddah tace 

"haka aure dama ya gada barin ma a wuri me nisa, kiyi hakuri zan mishi magana ko wayan ne se ya saya miki ai ba wani matsala kuma bayan wannan ko?"


Kai ta gyaÉ—a tace 

"babu"


"Ina Fatima kwana biyu itama bamu gaisa ba"


Tace

"Ina ga ta tafi school"


Hira sossai suka yi jadda tayi ta faÉ—a mata abubuwan da suke faruwa a gidan, wadda ya mata ta dara wadda be mata ba ta tofa albarkacin bakinta wani kuma tayi Kwafa, barin ma su ya Farhan kam.


Da kyar suka yi sallama don har katin Jaddah ya kare ta sake kira da wayan Faizan É—in.


Bayan ta sauke wayan fuskanta cike da annashuwa ta shigar da layin Mammi.


"FIRST LOVE"

Sunan da taga yayi saving kenan da emojis ɗin heart, murmushi ta saki tana tuna nata uwar wadda basu taɓa magana ba tunda ta zo.


Bayan mammi ta É—auka suka gaisa take tambayarta kafanta tace 

"Fauziyya kafafun nan se godiyar Allah amma kam da abunda yake nema"


Fauziyya bata gane zancen ba tayi mata Adu'ar samun lafiya, bugan cikinta mammi tayi tayi don taji ko Faizan É—in na mata wani abu sai de ko É—aya bata kawo wani laifinshi ba don be matan ba, shakuwa ne dama chan babu tsakaninsu, zaluntarta da ya kan yi in ta mishi abu kuma ya daina tunda bata mishi koman ba.


Daga karshe da dabarun zama da miji da kuma nasihu mammi tayi ta mata kuma tana É—auka wannan karo kam har tana mamakin kanta.


Bayan sun gama ta kira Ammi..


"Assalamu Alaikum Ammi"

Fauza ta faÉ—a bayan Ammi ta É—auki call É—in.


"Wa'alaikumussalam warahmatullah Fauziyya ke ce?"


Shiru tayi jin muryar Ammin nata babu É—auki sossai kaman yadda muryar jadda da mammi suka bayyana mata kewanta da suka yi tace 

"ni ce Ammi, kuna lafiya? Ya baba?"


Ta amsa da

"lafiya kalau ya gidan naki? Fatan dae baki bari ana hawa kanki kaman yadda kike da?"


Meyasa kowa ke mata nasiha ta zauna lafiya da mijinta amma mahaifiyarta kuma na shirin kawo rabuwar hankalinta? 


"Ammi ai babu abunda suke min, muna zaune lafiya"


"mene? Ashe dama karyar kiyayya kike yiwa Faizan ɗin kenan, na tabbatar shi kuma a wurinshi ba haka take ba don kiyayyar namiji bata taɓa gushewa, kuma bata sauyawa, kiyi tunani dae... Sannan ki sani mijinki ba ke kaɗai ba har ni ba ƙaunata yake ba ke hatta mahaifinki don gani yake mahaifinki kusan rabi da kwatar dukiyarshi na Mahaifinsu ne shiyasa yanzu yake saka idanu akan harkokin business na babanki fiye da yadda yake sakawa Faraj da ya fara kula da na babansu"


Shiru tayi cikin dan nazari kan tace 

"Ammi wannan duk ba wani abu bane, kilan ba yadda kike tunani bane don na san dukkaninmu da Baba Alhj da Baba prof duk iyaye muka ɗaukesu kuma matsayin abu guda babu banbanci, sannan Ammi ai maganan yaya Faizan baya kaunarki tun da nake na san yana zuwa gaishe ki amma baki taɓa buɗe baki kin amsa ba kuma har yau har gobe kenan be tsane ki b....."


"Rufe min baki, ina nuna miki gabas kina yamma... Ke kika sani"

Tana kai nan ta kashe wayan..


Da idanu tabi wayan cikin mamakin Amminta, ta jima sossai tana nazari dayawa daga cikin É—abi'un Ammin nata sede ta rasa a wani mataki ko matsayi zata É—aura shi.


Baba prof ta kira shima yayi farin cikin jin tana cikin ƙoshin lafiya ya kuma yi mata albishir da result ɗinta na neco ya fito kuma yayi kyau don har yayiwa Faizan maganan yi mata registeration na jamb.


Taji daaÉ—i sossai tayi ta godiya da Adu'a ga baban, nasiha ya sake mata ya kuma gargadeta da Adu'a kaman yadda ya bata wani takarda da ke É—auke da Adu'o'i masu yawa ya kuma umurceta da ta lazimcesu kuma tana yi É—in sossai.


Bayan sun gama ta kira babanta shima ya ji daaɗin jinta lafiya ƙalau Dukda kullum a tsorace yake kar ta shukawa Faizan abunda ze zama silar tsinkewar zumuncinsu, idan har ze ga wayan Faizan se gabanshi ya faɗi da Tunanin ze ce mishi Fauza ta yi wani abun sede duk be ji ba, tun yana tsoracen yanzu har ya fara sakewa.


Nasiha shima yayi mata wadda be mata a lokacin barin ta gidan ba kuma ta ji daaÉ—i suka yi sallama tana ji matar nan na Mtn na cewa one minute remaining.


Sosa kai tayi bayan ta sauke tana kallon wayan yau ƙaniyarta Faizan ze ci ta ƙarar mai da katin waya.


Balcony É—inta ta fita tana kallon harabar gidan da Gidajen unguwar da yawanci kusan irin nasu ne benaye, wayan ta sake É—agowa ta shiga camera tare da Juyawa ya bata background É—in unguwar Ta fara pictures style kala kala tana murmushi barin ma da taga yadda tayi kyau.


Seda ta gaji ta dawo ɗakin ta zauna a coffee chair ɗin tana kallon pictures ɗinta, tana cikin scrolling taga nata sun ƙare sun shiga na wayan, bata tsaya ba ta cigaba da scrolling yawanci hotunanshi ne wasu ya sani wasu be sani ba, daga yanayin hotunanshi zaka san yana da zafin kai don kusan duk babu wadda yake cikakken dariya banda na fuskan wayan.


A kan wani ta tsaya wadda aka dauke shi be sani ba shima da uniform É—inne hannayenshi rike da abun tuka jirgin kunnenshi sanye da headphones É—insu ya É—an wai go kaman ze yi magana ne aka É—auka ba karamin kyau yayi ba.


Scrolling tayi ta wuce se taga hotonshi da Fatima, Fatiman ce ta ɗauka kwance a jikinshi kaman a wani wurin shakatawa ne, se wasu a bakin ruwa wadda ba tantama Legos ne don ta san chan ne kaɗai za'a samu beach haka, yana sanye da kananun kaya tana sanye da wasu hoodies orange, baki ta taɓe zata wuce se wayan ya ɗauki ringing.


'My number' ta ga an saka, to wani number kuma? Har wayan ya kusa katsewa kan tayi kundunbala ta É—aga 

"Fauziyya... Ina ta kiran Fatima bana samunta ki fita ki kama mata aiki su Faahim zasu kawo mana yini da yaran nima Ina dawowa nan ba da jimawa ba"


Kusan rikicewa tayi da sauri kuma tace 

"Toh"

Kashe wayan yayi ba tare da ya sake furta komai ba.


Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke...a fili ta maimaita sunan nata

"Fauziyya.."

Sai de bata ji ya mata kaman yadda shi ya kira É—in ba don har faÉ—ar mata da gaba yayi.


Tuna su Ya fadyaa ne zasu zo yasa tayi saurin mikewa ta fito parlorn saman babu motsin Fatima don haka kasa tayi, ba wai tana tsoron Fatima ne yasa bata shiga kitchen É—in saman ba, kawai tana tsayuwa ne limits É—inta gudun fitina da tadawa iyayenta hankali, Allah kaÉ—ai ya san yadda zuciyarta yayi haske da taji yadda suke farin cikin da jinta ba kaman da da a duk sadda za'a kira sunanta se gabansu ya fadi ba.


Abinci ta fara HaÉ—awa me rai da lafiya, Allah ya sa ma komai za'a kawo gidan a gyare ake kawo shi kuma cooker É—in me kai har shidda ne a take ta HaÉ—a pineapple rice kamshinshi duk ya cika kitchen É—in, bayan ta gama ta yi mishi pepper chicken, tayi grilling fish manya guda biyu se ta HaÉ—a zobo, karfe sha É—aya da rabi lokacin kuma har lokacin bata ji motsin Fatima ba.


A dining na sama ta shirya su kan ta shiga É—akinta tayi wanka, ta sanya wani material lace riga da skirt yayi mata kyau sossai ta fita shar da ita, lip gloss kawai ta shafa ta É—aura dankwali harda sarka da abubuwan hannu ta saka.


Daidai lokacin take jin shigowar mota, farin ciki sossai ne ya ratsa ta yau zata kalli mutane, mutane su kalleta ko da basu wani yi shiri da ya fadyaa ba sbd rashin jinta yayarta ce uwa É—aya uba É—aya tana son ta kuma har ranta kaman yadda take jin sauran en uwanta


"oyoyo"

Ta faÉ—a tana rungume ya fadyaa, ya fadyaa ma na murmushi tace 

"oyoyo Fauzan jadda, masha Allah.. Kin ganki kuwa?"


Da gudu yaranta biyu Asma'u(husna) da Sameer suka zo suka rungumeta suna mata oyoyo, cikin jin daaÉ—i ta tarbesu, tana cewa ya Faahim 

"sannu da zuwa yaya Faahim"


Yace 

"uhm karki yi ya Faizan ya jiki ni yanzu ƙani nake, Aunty Fauxan Jaddah yauwa sannunki"


Dariya duk suka yi ta musu iso ciki dukkansu biyu kallonta suke yadda ta sauya, a parlorn sama suka baje suka fara Gaisawa ta kawo musu ruwa da fruits.


"Ina Fatima ne naji gidan shiru"

Fadyaa ta tambaya.


Fauxa na barewa husna lemon É“awo tace

"nima fa tun safe bamu haÉ—u ba kilan tana É—aki kila kuma ta tafi school"


Bayan ta bata ta dubi ya fadyaa tace

"ya fadyaa tun fa wanchan sati Jaddah tace min zaku dawo shine baku zo ba har se yau"


Ya Faahim yace 

"ba gashi mun zo É—in ba dae, Ya Faizan ya ce ya shiga wurin Faisal ko?"


Tace

"eh ya de ce gashinan zuwa"


Kallon juna Faahim da fadyaa suka yi suna gulma, yadda ake zaton jin hayaÆ™i a gidan Faizan ba haka ba, ashe igiyar aure na natsar da mutum? 


"Kinga muna ta shirin tafiya ne zan ga Dr shi kuma ya Faahim ze yi wani course to har yanzu visa É—in husna ne bamu samu ba gashi ma lokaci na ta tafiya"

Cewar Fadyaa


"ai na ce miki mu hakura mu barta wurin su mammi kin ce za'a kara mata dawainiya ga rashin lafiya"

Cewar Ya Faahim 


Fauza tace

"to don Allah ni ku bar min ita kan ku je ku dawo Allah zata debi min kewa dama zaman kaÉ—aici ya isheni"


Zaro idanu fadyaa tayi tace 

"Fauza rufa min asiri da mijinki..."


"Me mijinta yayi ne?"

Faizan ya faÉ—i yana shigowa cikin parlorn, duk É—ago idanu suka yi suna Kallonshi...


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya ta wannan layin

09039206763.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments