Breaking News

Diddigar Kaya 22


 DƘ 


22


Yana kallon tsakiyar idanunta da suka kumbura don kuka yace 

"kika sake cewa tak zan sake ki ki faÉ—i se ki san ba'a sonki an tsaneki da kyau.."


Haushi maganan ya bata kawai ta sake sakar mishi kuka, idanunshi ya runtse kawai ya juya da ita a hannunshi suka nufi kofa.


"Baby taso ki zo"

Ya kira husna, da gudu ta bisu ita ce ta buÉ—e mishi kofa ya sanya Fauziyyan, ta shiga baya ita kuma, ya zagaye ya shiga ya ja tare da ficewa daga gidan, minti minti yake kallonta har suka isa asibiti bata bar kukan da take yi É—in ba.


Nan É—in ma saÉ“arta yayi zuwa office na Jafar husna na binshi a baya, a kan gadon office É—in ya dire ta yana cewa 

"washhh Allah, mutum kaman buhu"


Ɗago rinannun idanunta tayi ta zabga mishi harara ya ware mata nashi gabaɗaya alamar ni kike harara? Se tayi saurin maida kanta ƙasa, idanunshi na kan kumatunta da hannunshi ya kwanta har Jafar ya shigo daga ward.


"Subhanallah kai kam yau gidanka da alama ba sa'a kuka tashi, garin yaya ta taka kwalba haka kuma kuka barshi har kafan ya kumbura ba'a zo asibiti ba Faizan?"


Yana É—auke idanu daga kanta yace 

"bayan mun zo da Fatima ne ta taka so saida kuma na koma na sameta hakan"


Yace

"sannu Amaryarmu"

Kai kawai ta É—aga mishi.

Cikin sanyin muryarta tace 

"Ina yini"


Ya amsa yana isowa da kayan aikinshi wurin gadon, se da ya gama kallon kafan kan yace za'a mata allura kan ya fara taɓa kafar, nan fa idanunta suka raina fata, duk bala'inta in aka zo fagen allura tsoron shi take.


Daga yadda reaction É—in ta ya nuna ya gane tana tsoron Allurar, har aka gama HaÉ—awa ya matso yana cewa ta gyara idanunta na kan allurar yayinda gogan kuma nashi ke kanta, idanunta na da kyau a kowani yanayi...


Girgiza kai tayi muryarta har yana rawa tace a cire haka ba se an yi allura ba, a hankali taji shigar tattausan hannunshi cikin nata, ÆŠayan kuma ya saka ya rungumo ta jikinshi, fuskanta ta binne bisa kirjinshi har yana jin hucin numfashin ta wadda a take gabaÉ—aya tsikar jikinshi suka tashi, har aka yi Allurar dukansu basu farga ba saida Jafar yace 


"Romeo and Juliet an gama Zaku iya É—agowa"

Da sauri ya saketa yana É—an matsawa ya zabgawa Jafar harara, ita kuma ta dukar da kanta.


An sha gumurzu kan aka cire kwalban tayi kuka sossai wadda har saida yaji a ƙasan ranshi be kyauta ba, bayan an gama ya ɗan Harare ta yace

"taɓararriya kawai"

Bakinta ta tura mishi ya kai hannu kaman ze É—alle mata bakin tayi saurin saka duka hannunta biyu ta tare tana zare idanu wadda ya saka shi sakin murmushi yana girgiza kai, shi duk labarinta da ake bashi be ga ko É—aya ba banda sanyin hali da tsoro kaman farar kura.


Fita suka yi da Jafar zuwa masallaci suka yi sallar magrib, bayan sun dawo suka shiga wurin Fatima sun samu ta farka, dukkansu biyu da kyar ta amsa musu gaisuwar su, babu wadda ya sake magana sbd ganin yanayinta se Faizan ne ya bata umarnin tashi su wuce, haka ta mike yace taje mota ta jira shi gashinan zuwa.


Ita kuwa tana zuwa motan ta buÉ—e baya ta shiga a dole tana fushi da shi na goyon bayan Fauza da yayi, yana isa office na Jafar ya samu ma har baccin wahala ya É—auke ta.


Haka ya sa hannu ya É—auke ta, ta gyara kanta kan kafadanshi ta cigaba da baccin ta, husna ta biyo bayansu Jafar da ya rakosu ganin Fatima a baya ya sa hannu ya buÉ—e mai gaba ya sanyata.


Ashar Fatima ta lailayo ta buga, da sauri ta sauko tace 

"Ya Faizan wai me kake nufi dani ne?"


Yana gyara Fauza yace 

"kaman ya kuma Fatima? Duk maganan da zamu yi yanzu ki bari mu je gida pls"


Tace 

"in bari mu je gida? Na rasa cikina sbd wannan karuwar...."


"Shutt uppp Fatima!!"

Ya daka mata tsawar da har saida Fauza ta tsorata tare da watsakewa daga baccin da ya cika mata idanu.


Itama cikin kukan baÆ™in ciki tace 

"ba zan yi shiru ba yaya, ba zan yi shiru kayi ta zaluntata ba... Ta É“arar min da ciki baka ce mata komai ba, asibitin ma ka zo ka ajiyeni kayi tafiyarka wurinta, ni da ya kamata ka É—auko ka kawo mota baka É—auko ni ba ka je ka dauko ta a hannu sbd tayi bacci, ni gani Æ´ar iska marar gata... To Alhamdulillah na gode Allah da baka sameni a watse kaman kofar taxi b......"


Mari yake shirin sauke mata sbd yadda ranshi ya ke tafarfasa Jafar yayi saurin riƙe shi.


Ita dae Fauza bata ko motsa ba banda idanu da take binsu dashi, sbd yadda idanun Fatiman ya rufe bata yi shiru ba tace 

"ka barshi ya mareni Jafar, ya mareni tunda ni ce karamar dangarshi me daaÉ—in hawa, ba se ka mareni zaka nunawa duniya cewa ni É—in ba jininka bace, ba se ka mareni zan san cewa kana fifita wanchan karuwar Æ´ar shaye sha...."


Marin da bata sha É—azun É—in ba shi ta sha yanzu saida ta kusa kaiwa Æ™asa, hannun da ya nuna ta da shi har yana rawa yace 

"Ki kiyaye ni Fatima, ki kiyayi ganin É“acin raina kuma ki rufe min baki ki shiga motar nan mu tafi...!"


Jafar yace 

"Haba Faizan in ita ta rasa hankalinta tana faÉ—ar abubuwan da basu dace ba kai be kamata ka biye mata ba, ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi har ita ta sauko kan ka nuna mata rashin kyautawar abunda tayi É—in, zafin kishi ne kawai ke dawainiya da ita da kuma na rashi da tayi ka san dae se ta fi ka jin zafin hakan"


Kallonshi Faizan yayi yace 

"zafin kishi? In zafin kishin ne se aka ce a rashin hankali yake zuwa?"

Juyawa yayi kanta yace 

"I can tolerate anything but don't u dare cross ur boundaries... Ki wuce ki shiga mota mu tafi I won't repeat myself"


Yana kai nan ya buÉ—e motar ya saka husna da har ta fara kuka, kan ya juya ga Jafar yace 

"zamu yi magana"


Daga haka ya zagaye ya shiga motar, ya tayar idanunshi na zube kan hanya, saida yayi kaman mintuna uku da tayarwa har yana shirin jan motan yayi gaba kan Fatima dake kuka ta shiga, ita dae Fauza sannu bata ce musu ba ya tsaya restaurant ya musu takeaway kan suka nufi gida.


Yanzu ɗin ma zagayawa yayi ya buɗe kofa ya ɗauke ta, ko Fatiman be kalla ba ya nufi ciki, a kan gadonta ya ajiye ta har ya juya ze fice tayi saurin riƙe hannunshi wadda dukkansu saida suka ji har cikin ƙashinsu.


Fuskanshi ya juyo ya kalleta cikin sanyin murya tace 

"I'm sorry...! Ban san hakan ze faru ba da ban biye mata ba, pls kayi hak'uri"

Ta karashe tana duƙar da kanta ƙasa.


Zama yayi yana É—an murza hannunta dake cikin nashi ÆŠayan kuma ya É—aura a kan kumatunta da har yanzu yake kumbure ya É—an shafa dukkansu suka lumshe idanu, wani sanyi ya ji a ranshi wadda be san na menene ba, É—ago idanunta tayi ta kalleshi dasu daidai shima ya buÉ—e nashi dake lumshe.


Chan Æ™asan maÆ™oshi yace 

"it's not ur fault, haka Allah ya tsara cikin ba me zama bane... Amma me ya HaÉ—a ku?"


Tiryan Tiryan ta bashi labarin abunda ya faru bata É“oye komai ba, yadda suke kallon juna a cikin idanu kuma ta bashi labarin ba rawar murya ko wani kame kame ya san cewa babu Æ™arya a cikin labarin nata, murmushi ya saki kawai da nufin tsokanarta yace 


"Eyye ashe Æ´ar gurguwa kunnuwanta na ji da kyau tunda har ta ji sadda loudspeaker ke sanar da cewa ita É—in ta zama matar Faizan"

Da sauri ta zare hannunta tare da kare fuskanta tana murmushi shima yana murmushi yace 


"Haba Æ´ar gurguwa kunya kuma?"

Baki ta turo tana cewa 

"ni Allah ni ba gurguwa bace"


Yana miÆ™ewa tsaye yace 

"Toh Ladi chogal"

Ihu ta sake tana kukan shagwaɓa ya fice abunshi yana dariyar shagwaɓar tata.


Se bayan ya fita ta saki murmushi ashe ya Faizan haka yake?.


Abincin da ya sayo ya koma ya É—auko, a plate ya juye takeaway biyu da ruwa ya sa kan tray ya É—auka ya kaiwa Fauza É—in, yanzu kam be ce mata komai ba ya ajiye mata ya baiwa husna nata kan ya juya ya fita.


Na Fatima ya É—auka ya nufi É—akinta dashi Dukda yadda yake jin É“acin rai na abunda ta mishi É—in amma be fasa zuwa ba.


Tana zaune tana kuka ya shiga É—akin, abincin ya ajiye mata kan ya juya shima yaje ya ci nashi, an riga an yi isha so É—akinshi kawai ya shiga ya watsa ruwa yayi sallah, bayan ya idar ya mike yaje ya duba maganin Fauza ya nufi É—akinta dashi.


Samu yayi tana sallah daga zaune, toilet É—inta ya shiga yana yabawa tsaftarta don bayin ta ba zaka ce ana anfani dashi ba ya samu roba ya tare ruwan zafi ya samu Towel ya fito.


Husna tayi bacci ya É—auke ta ya É—aura ta kan gado ya sauya mata kaya daidai lokacin ita kuma ta idar.


Da taimakon shi ta koma bakin gado, ya janyo stool ya zauna tare da É—aukan kafan ya É—aura kan cinyar shi.


Ruwan da zafi sossai haka yayi ta danna mata tana raki tana yarfa Hannu, da muzurai da komai aka gama dannar ya bata magani ta sha, yace 

"dube ta..!"


Baki ta turo kayan bacci yaje ya É—auko mata ya ajiye mata gefenta kan ya dube ta yace 

"akwai wani abu kuma?"


Kai ta girgiza yace 

"tohm se da safe Allah ya qara sauƙi"


Tace 

"thank you"


Ya juya ya fice ta bishi da kallo har ya maido mata da kofan ya rufe.


Maganin Fatima ya É—auka ya nufi É—akinta.


Har yanzu tana kuka, zama yayi bakin gadon yace 

"Fatima!"

Yadda ya kirata É—in dole ya sa ta É—aga idanu, yace tashi zaune.


Mikewa tayi ta zauna, yace 

"menene matsalarki? Me yasa kike ganin an miki rashin adalci?"


Kallon tambaya ta ma kake ta mishi, kan ta É—auke idanunta bata ce komai ba, shima É—auke nashi yayi yace 

"Ki tashi ki ci abinci ki sha magani"

Yana kai nan ya ajiye mata maganin ya tashi ya fice abunshi don ta ƙi magana.


Ya gaji ainun so yana kwanciya bacci ya sureshi, da asuba yana dawowa daga sallah kenan ya hangi É“acewar mota kaman kuma ta Fatima, me gadinshi ya tambaya ya tabbatar mishi da yanzun nan Fatima ta fice.


Be ce komai ba ya haura yaje yayi kwanciyar shi don yau bai da wani aiki, be tashi ba se karfe goma da rabi.


Wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya ya fito, zaune ya same su suna kallon wani animation, zama shima yayi ta dube shi tace 

"Ina kwana?"


Ya amsa da lafiya yana kallon kafafunta yace 

"ya jikin?"


Ta amsa da 

"Alhamdulillah"


Duk shiru suka yi, ta san Fatima bata nan don itama ta hangi fitanta ta window kuma bata ji alamun dawowarta ba, ta barshi da yunwa kuma be dace ba tunda sun yi girki kuma ya saura.


Miƙewa tayi tana ɗan ɗingisa kafafunta ta nufi ƙasa da kallo ya bita har ta ɓace mai, sanye take da blue Indian gown da ya zauna mata sossai a jiki, be kai ƙasa ba se wandon shi da ake hangar adonshi daga gwiwar kafanta, yana da tsagu me tsayi daga gefe da gefe, ta ɗaura gyalen ɗaurin turban a kanta, ba karamin kyau tayi ba barin ma da ta gyara fuskanta ta saka lip gloss, bata jima ba ta dawo.


A gabanshi ta ajiye tray É—in da ta hauro dashi É—in.


Wani fancy bowl ta zuba kifi da yafi yanayi da soup don yayi kauri ta ɗaura kan plate ɗinshi, a idanu kaɗai abun sha'awa ne gwanin kyau bare a baki, akwai kuma warmer a gefen plates ɗin ta buɗe ta ɗaga miyan ta ajiye gefe doya da ta soya da kwai ne ya ji kwai ta zuba a plate ɗin kan ta matsar mai, ta sake miƙewa ta fice chan se gata da wani karamin tray wadda shayin shi da ta saba dafa mai ne ciki, ta zo ta ajiye mai ganin ya fara cin abincin ta tsiyaya mai da kanta.


Idanunshi na kanta yana kiyasta abubuwa masu yawa a ranshi yace 

"thank you"


Ta miƙe tana ɗan murmushi bata zauna a parlorn ba se ta nufi ɗaki.


"Fauza!"

Ya kirata yadda kowa ke kiranta, da sauri ta juyo yace 

"kin sha magani?"


Kai ta gyaÉ—a mai yace 

"to dawo ki zauna"

Dawowa tayi ba musu ta zauna a parlorn.


Bayan ya gama cin abincin da kanshi ya tattare kwananukan amma kitchen É—in sama ya ajiye, a tare suka yi spending time me yawa Dukda babu me magana cikinsu banda husna da ta ishe Fauza da surutu sede ta amsa da eh ko a'a, azahar da aka kira ya saka su duk mikewa.


Ya fita be dawo gidan ba se yamma lis.

Yanzu ma abincin ta kawo mai tuwon semo ne da miyan busashiyar kubewa sbd shi tayi tuwon don ta san yana so, ita kam indomie ta dafa ta ci, husna ma tuwon ta ci, se bayan magrib ya zauna cin tuwon gefen shi papers ne, bayan ya gama ya wanke hannu ya dube ta kan yace 


"Dukda ban so ki fara karatu nan kusa ba saide Baba prof ya ƙi aminta da kudiri na hakan ya sa dole na shiga nemar miki admission kuma Alhamdulillah yau gashi kin samu, ina so ki san rayuwarki na da da na yanzu ba ɗaya ba, idan da kin yi abubuwa masu yawa ganin u r free yanzu kina da aure, matsayin aure kuma ya wuce duk wani matsayi da kike tunani, duk laifin da zaki aikata yanzu ki sani ba iya ke da zuri'arki ba har mijinki da ƴaƴanki wannan image ɗin baze mantu a idanunsu ba, sannan zunubinki se ya fi na da sbd kin wulakanta sunnah, in Allah ya kaimu gobe zaki je ki ƙarasa sauran abubuwan da ban karasa ba ki fara shiga aji"


KarÉ“an admission da ya miko mata tayi tace 

"na gode Allah ya saka da alkhairi in shaa Allahu zan kiyaye"


Wayanshi ne ya É—auki ringing ganin baba prof yasa ya É—aga tare da sallama bayan sun gaisa baban yace 

"Faizan me ya faru? Meyasa zaka bar matarka tayi yaji kuma ta kamo hanya daga Abuja zuwa yola a mota bayan ka san ba lafiya ne da ita ba?"


Yace 

"Yola ta tafi kenan? Hmm baba maganan nan ba na waya bane ta zauna  a gidan in Allah ya sa Fauziyya ta warke zan zo"


Baba yace 

"Assha Fauziyyan ma ba lafiya?"


Yace 

"Eh amma da sauƙi"


Baban yace ya bata, miƙa mata yayi a ladabce ta gaishe shi ya tambayi jiki take ce mishi ai ta warke ma bayan sun gama ya ba jadda da suke tare itama ta mata sannu tana tambayar me ke damunta, tace kwalba ta taka amma da sauƙi.


Miƙa mishi wayan tayi tana Kallonshi, kallon lafiya kike kallo na yayi mata se tayi saurin kau da kai ta miƙe.

"Gulma"

Ya faɗa yana maida kanshi ga TV🤣


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya ta wannan layin

09039206763.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments