Breaking News

Tsutsar nama 45

 *_Typing📲_*










   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_



......Yana kai wayar kunnensa dai-dai nan ma yake jin horn ɗin motar Mansoor ɗin da ƙarar buɗe gate. Wayar ya sauke tare da ajiyar zuciya ya ce, “To Alhamdullah gashi can ma ya dawo ai. Sai ki kwantar da hankalinki

     Ajiyar zuciya Mamy ta sauke kuwa. Ta yunƙura zata miƙe Dad ɗin ya zuba mata ido. “Ina kuma zaki?”. “Zanje na duba shi ne mana. Kofa abincin dare baici ba. Kasanshi kuma da abinci, inba tsaresa akai ba ba wani son ci yake ba”. 

    Kai Dad ɗin ya girgiza. Sai kuma ya ce, “Uhm kinga Safina zauna Please”. Babu musu ta koma ta zauna. Sake cemata yay “Kwanta sai da safe. Tunda dai Mansoor ba jariri bane balle kice baki gama rainonsa ba.” tasan halin mijin nata dan haka bata sake magana ba kuma. Sai dai zuciyarta gaba ɗaya tana akan son sanin a wane hali ɗan nata yake ciki. Amma tunda yace bazata je ba to bata isa fitarba kuwa. Shima dai hankalinsa ya sake maidawa ga aikinsa bai sake bi takanta ba kuma. Ga shi ya haɗe fuska dan bama ya son tace zata roƙesa ko ta takura masa da batun auren Mansoor ɗin kuma.....


          

       💞🌟💞🌟💞🌟💞


    Washe gari kamar yanda doctor ya faɗa aka sallameni. Gwaggo Gudidi taso wucewa da ni can Dawanau gidanta amma Yaya Musaddiq ya roƙeta kan ta barni na koma can gidan ɗin. Tunda har Mansoor yayi magana kan baya son a ɗaga bikin nan a yanda yake koda na kwana ɗaya ne kawai ayi a wuce wajen. Ya kamata kuma muje can gidan Abba a ƙarasa komai daya kamata kada halin Mum ya dameta. Badan Gwaggo taso hakan ba ta yarda. 

        Tarba muka samu babu yabo babu fallasa da ga Mum. Hakama su Baby na zaune a falo amma babu wanda yay min sannu ko nuna farin cikin dawowata garesu. Sai auta ne ya tsillo da gudu ya ruƙunƙumeni. Duk da miskilancin yaron sai da ya furta, “Adda nayi kewarki. Adda Bibaa tace kin mutu bayan sake ganinki ba ashe ƙarya take min”.

    Murmushi kawai na masa tare da shafa fuskarsa. Yayinda Gwaggo ta riƙe haɓa da faɗin, “Ta mutu kuma? To in ALLAH ya yarda ba yanzu ba, mu bazamuga mutuwa ba sai alkairi nan da kwana huɗu. Ke kuma baƙin halin naki sak na uwarki dai ashe, da wani shegen goshinki kamar jirgin tsallake ruwan bagwai”. Ta ƙare maganar tana nuna Bibaa data tura baki gaba zomomo. Na zata Mum zatayi magana. Sai naji shiru ta dai sake tsuke fuska. Ni dai sai ma na yunƙura na nufi bedroom ɗinmu dan so nake na ɗan watsa ruwa ko zanji daɗin jikina. Yanda na tadda ɗakin kaca-kaca sai da ƙirjina ya buga. Abu sai kace turken dabbobi. Wai ni yaushe Bibaa zatayi hankali ni Samraah. Na jima tsaye zuciyata cike da takaici ga ƙyanƙyami dan bazan iya zama a ɗakin ba. Dole na juya na fita cikin ƙarfin hali da son ƙarfafa kaina. Har yanzu duk suna a falon, Gwaggo Gudidi tai saurin faɗin, “Ya kuma kika fito Samraatu lafiya dai ko?”.

        Kaina na jinjina mata a yanayin rashin ƙarfi jiki, cikin yamutse fuska na ce, “Gwaggo zan ɗakko kayan shara ne ɗakin yayi datti ina jin ƙyanƙyami”.

    Dukansu sai da suka ɗago suka kalleni. Yayinda Gwaggo ta riƙe haɓa da faɗin, “To kaji kuma wani sheɗancin kuma, yanzu duk waɗan nan zagada-zagadan ƴan matan uwa wa ƴan matan amarya a gida ashe hotiho suke. Yo ni dama tunda na shigo naga gidan yamun wani harmutsai a ido nasan ana ƙwaɓa hauka dan har bashi-bashi da tsami-tsamin dauɗa nake shaƙowa ma. Yanzu ke Julaila kike ko mima oho miki bayan koyama ƴaƴanki rashin kunya abinda zai taimaki rayuwar tasu ma kin tauyesu basu iya ba. Komai kun tattara akan marainiyar ALLAH. To wlhy ba mugunta kikai mata ba idan ma ke haka kike tunani, su waɗan nan da kike gani ƴan hutu a gabanki su kika kashewa rayuwa, dan su zasu gurji kan ubansu nan gaba kaɗan. Zaku ma ki tabbatar da hakan ke da su ranar da tusa ta ƙarewa bodari, ɗiya mace bata iya komai ba ai bata cika mace ba wlhy, babu kuma namijin da zai juri zama da ita, idan ma ya haƙura ya jure dan yanada kuɗin biyan wasu suyi to bazata taɓa daraja a idonsa ba dan wataran ko shine ƙaruna akan kuɗi zai so matarsa ta masa hidima. Kai ai wlhy baki birgeba kuwa. Ashe ma fuggukar taki da ɗaga hanci kamar ƙofar gora na wofine” ta ƙare faɗa a fusace. Bibaa ta nuna da Baby “Ku dan ubanku Imamu ku tashi ku ɗakko kayan shara, ke kuma zoki zauna anan wazai barki kiyi wani aiki kina fama da kanki. Zakiyya ma na hanya gyaran jiki zata fara miki yau ɗin nan dan duk da gaki nan fes da ke ga kuma ƙarancin lokaci bazai hana nasa a kwaskware min ke ba dan kowa ya sake tabbatar da amarya ƴar gata zan kai”.

      Sosai Bibaa da Baby ke kallonta ransu a ɓace, sai kuma su kalla Mum da taƙi cewa komai. Tsawa ta daka musu, babu shiri suka miƙe a zabure kuwa. Nayi mamakin shirun Mum dan nasan yanda suke ƴar tsama da Gwaggo Gudidi, rashin jituwar tasu ma ce tasa Gwaggon daina zuwa gidan gaba ɗaya. Amma dai dole a wannan shirun nata akwai ayar tambaya.

     Su Baby naji na gani Gwaggo ta turkesu sukai gyaran ɗakin, sau biyu tana maidasu su maimaita wai bai mata ba. Bayan sun kammala sunata zungure-zunguren baki tasa Bibaa ta tattara kayanta ta maida ɗakin Baby. Shima auta aka haɗa masa nasa aka sanda shi ɗakin Mum. Acewar Gwaggo nan sune zasu zauna har sai biki ya tashi. Ni dai dariya ma abin ke ban. Dan Gwaggo Gudidi fitinanniya ce sai dai idan bataso ba zaka ga ta watsar da kai kamar mai shiru-shiru. Halin namu dai na kamanceceniya sosai, ƙila dai ita na gado ma (🤣). Fuu Mum ta tashi batare da tace mana komai ba ta bar falon, mu duka da kallo muka bita, sai dai babu wanda yace komai.


        “Mum na shiga ɗaki waya ta ɗauka, sai faman huci take da jan numfashi, kai daka ganta kasan dama danne komai take da ƙyar kawai. Ko sallama balle gaisuwa batayi ga wanda ta kira ɗin ba ta fara magana a hasale. “Mama magana ta gaskiya bazan iya haƙurin da kikace da wannan tsohuwar ba. Kinga daga dawowarsu yanzu tabi ta addabar min yara. Nidai bazan iya ɗauka ba. Wannan plan ɗin naki na fara jin kamar bazan iya juresa ba. Ina dalili yara tun suna ƙanana sun tare min komai yanzu kuma an saka min ƴaƴa a gaba duk da kwacen saurayi da akaima Baby”.

     Siririyar dariya akayi mai sauti daga can. Sai kuma dattijuwar murya ta fara faɗin, “Jalila wani lokacin idan kina wani shashancin sai nake ganin kamar bani ce na haifeki ba. Ke matsalarki baki iya ɓoye abu aranki. Shiyyasa tun farko ko riƙon yaran nan nace ki yi na siyasa ta yanda koshi mijin naki bazai fahimci baki ƙaunarsu ko son zama daku ba. Amma ina kin kasa. Yanzu kina ganin matsala ta taso kaso biyu bisa uku na mutane har yanzu ke suke zargi da satar yarinyar nan har da ƴaƴanki. Ko ƴan sandan nan idonsu kema na'a kanki. Amma kin kasa fahimta. Ko shi mijin naki badan mun danne masa kai ba tuni kina ganin bake zai zarga ba ne? Shin wai rayuwa babu siyasa ta yiyu haka ne?”.

        “Wai Mama sai kice siyasa, siyasa. Dan kawai ina son na birge wani sai na dinga nunawa wanda bana so so. Nidai a bar wannan maganar, kawai ki faɗa min abinda zanyi na gaba dan na fara ƙosawa da halin tsohuwarnan, zan karta mata rashin mutunci wlhy bazata zo cikin gidana ta hanani rawar gaban hantsi ba”.

       “A'a ban aikeki ba nikam. Ki bari anjima kaɗan zan zo gidan. Dama ga ƴar uwarki nan tazo itama babu jimawa. Kuma ni abinda nasa a raina kofa auren nan akai sai munyi duk yanda zamuyi basu zauna lafiya ba. Dan yanda ta rabashi da takwarata itama bazata taɓa jin daɗin ba. Na fara ji kuma a raina wannan tsohuwar duk itace ke ƙulla komai, maybe ma itace ta amaso asirin da aka juya kan yaron nan. Shiyyasa sam ban sonta tun aurenki da Imam. Amma idan sun san wata su basu san wata ba ai. Daga su har ita zasu ci ubansu ne da ni suke zancen. Yanzu dai ki cigaba da kwantar da hankalinki bana son jin wata fitina. Bari na ƙarasa aiki mu fito”.

       “To Mama dan ALLAH kuyi sauri”.

 Suna ajiye wayar zama tai jagwab a bakin gado, ita kaɗai tasan irin ƙunar da take ji a ranta game da auren nan. Ji take kamar ta sakama yarinyar nan shinkafar ɓera a abinci ta mutu kowa ya huta, dan tafi sauran ƴan uwanta tsaya mata a rai, shegiya ga ƙyawu kamar wadda ta tashi a rayuwar hutu, duk baƙar izayar da take mata kullum zaka ganta fes-fes ga shegen Musaddiq ɗin can kullum cikin saya mata suturu yake. Tanada plans daban-daban da zata iya bi ta wargaza auren nan dama rayuwar yarinyar nan duka, amma Mamanta na hanata. Amma yau kam tana ji in har Mama bata iya tayi komai ba itafa zatabi ɗaya daga cikin plans ɗinta ne. Dan bazata taɓa yarda a ƙwacema ƴarta da tafi so abinda ke nata ba. Sai dai ko duk su rasa, ko kuma ƴarta ta samu ita.......✍️



       _Humm Mom to bari muga yaya wasan zai kaya 🚴_.

    



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments